Showing 60001 words to 63000 words out of 221574 words

Chapter 21 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

176

je. Islaha da ta dinga zuga ki akan kar ki je, to yau da ita zamu tafi.

Kan Safeeera ya sara, daman gashi yana yi mata ciwo, ta dafe kai ta ce,  Umma ban gane ba, kina nufin tare da Islaha da Labiba zaku tafi yau?.

Umma ta ce,  ga zahiri kina gani, daga nan sai Madina in Allah ya yarda. Ki kula da ?annenki kafin na dawo, in bu?atar kuWi ta tashi zan dinga tura miki, daman nemansu zan tafi.

Safeera ta ?arasa ta ri?e mahaifiyar ta tana kuka ta ce,  Don Allah Umma ki ce wasa ki ke yi, ki ce wasa ki ke yi min ba tafiya zaki yi ba.

Umma ta ce,  tafiya zan yi Safeera, zan je na nemo kuWin da zan aurar dake da ?anneki. Ki kula da kanki da ?annenki kafin na dawo.

Safeera ta du?ushe ta ri?e ?afarta ta ce, "Don Allah Umma kar ki yi mana haka, mun fi bu?atar ki sama da komai a rayuwar nan. Ni na yarda zanje, na amince zan je ba sai kin je ba."

Umma ta kalle ta tana hararar ta ta ce, "lokacin da nake lallaSa ki ai iskanci ki ke yi min, dan haka ki sakar min ?afa na wuce."

Baba ya Waga labulen ya shigo yana kallon ta da mamaki da Waure kai ya ce, "Maimuna da gaske tafiya za kiyi?."

Ta kalli Baba duk da faWuwar gaban da take ji, amma hakan ta daure ta ce, "yanzu na gama yi maka bayani fa."

"Duk abinda Yayanki ya faWa miki daman baki ji ba?."

"Ni fa ta dole zan tafi, ba dan son raina zan je ba."

"Yanzu dai sai kin je Win?."

"Jirana ma suke yi zamu tafi Abuja, ta can zamu hau jirgin saudia mu tafi Madina.

Baba ya girgiza kai ya ce, "Maimuna kin zaSi ki watsar da ?a?anki mata ki tafi wata ?asar aikin gidan larabawa, kin zaSi ki barsu a nan ki je inda baki da kowa saboda neman duniya?. Ki bar naki yaran, ki je ki yi bautar yaran wasu?."

Umma ta ce, "ga Safeera nan, meye baza ta yi musu ba? Ai ba lallai sai ni ba."

Baba ya bita da kallo dan bai ga alamun zata fasa ba, bai ga alamun tana jin tausayin ?a?an ba balle shi ta ji tausayinsa a matsayin mijinta. Zuciyarta ta bushe, kuWi kawai take kallo.

Baba ya gyaWa kai ya ce, "na faWa miki baza ki bar ?asar nan da aurena akan ki ba, anyi haka ko?."

Sai a sannan ta ji gabanta ya faWi matu?a, ta Wago ta kalle sa taga ita yake kallo sai ta kasa cewa komai.

Baba ya daure ya ce, "tunda kin zaSi tafiya a kan aurenki da ?a?anki da ?an uwanki baki Waya, ki je Maimuna, ki je ki nemo duk abinda ki ke ganin zaki samo a aikin gidan larabawan saudia."

"In kin bar gida nan ki taho da duniya gabaWaya, ?arewar arzu?in da ki ke hangen zaki samu a aikatau. Kin zaSi yin aikatau a wata ?asa akan zama da yaranki& ..

Baba ta dakata yana gyaWa kai, ya Wago ya sake kallon ta ya ce,  Kamar yadda na faWa miki, indai ki ka zaSi barin ?a?anki ki ka tafi neman kuWi Saudia, ni kuma na rantse baza ki bar ?asar da aurena kan ki ba. Ki tafi saudia, amma ki sani, na sake ki Maimuna!."

Wata irin ?ara Safeera ta yi, tana Wora hannu a kanta cikin gigicewa da tashin hankali.


Su Umma za a tafi aiki, sai mu ce Allah ya sa a dace.=??=??
[6/30, 9:54/ AM] KRBBK: RDB2P26
Nana Haleema.

Islaha haka take yin komai a sanyaye, ji take kamar ta cewa Mama ita ta fasa tafiyar, gabaWaya tafiyar ta fita daga ranta, daman ba a ran nata tafiyar take ba lallaSawa kawai take yi. Amma yanzu da tafiyar tazo sai raunin ya yi mata yawa, ta sake zama mai rauni sosai.

Tana ganin Labiba sai hidima take yi tana shiga ta fita, harda su yin sabon kitso. Ita dai kallon ta kawai take yi, zuciyarta tana sa?a mata abubuwa da yawa, tana ji da tana da dama da iko zata fasa tafiyar da ta yi niya, dan Allah ya gani gabaWaya tafiyar ta ta fita daga ranta ko kaWan. Ranar ko asibiti basu je ba, suna gida suna hidimar tafiya.

Islaha tunda ta dawo daga wajan aiki ta kasa yin komai, tana zaune sai dai ta kwanta ta tashi ko kayan ta kasa haWawa. Jikinta ya yi sanyi, ta rasa abinda yake yi mata daWi, komai ya tsaya mata cak, bata jin daWin duniyar gabaWaya.

BuWe ?ofar da aka yi hakan ya saka ta Wago ido ta kalli Labiba da har wanka tayi, ta shirya cikin doguwar riga kuma tayi mata kyau sosai.

Ta bi Islaha da kallo ganin babu alamun shiri a tare da ita ta ce, "ke bama ki shirya ba kenan, jirgi dai ha mota bace balle a jira ki. Gashi nan in ji Mama, ki saka mata a kayan ki" ta faWa tana cilla mata kayan ta fita ta barta.

Islaha ta sauke numfashi ta mi?e a sanyaye, ta buWe kayanta tana kallo ta kasa taSa komai balle ta san abinda zata Wauka. Kamar mara jini haka ta dinga jawo kayan tana zubawa, ita kanta baza ta ce ga abinda take zubawa ba, kawai ta san ta saka dogayen riguna da hijjabai.

Tana gama zubawa ta zauna a kan gado ta yi tagumi, ta rufe idanunta ta rasa abinda yake yi mata daWi a lokacin. Tana zaune Mama ta shigo tana faWin, "Yauwa Islaha kizo kuci abinci, motar tafiya Abuja tana jiran mu, gabaWaya zamu tafi sai kun tashi sai mu dawo."

Mama ganin yanayin Islahan sai ta bita da kallo mamaki ta ce, "ke jirgi ne fa ba adadaita sahu ba ne, akwai tafiya mi?a??iya a gaban mu, daga nan Abuja zamu wuce ba jimeta ba. Ki tashi ki shirya, dan wallahi in ki ka rasa jirgi kamfani bai san asara ba, sai kin biya abinda aka kashe miki." Islaha ta Waga kawai bata ce komai ba Mama ta fita ta barta.

Bata an shigo ba, kawai ji ta yi an faWo kanta ana kuka, a firgice Islaha ta kalli Safeera da ta rungume ta tana kuka mai tsuma zuciya.

Islaha cikin tashin hankali da tsoro ta ce, "lafiya Safeeraa, me ya faru ki ke kuka haka?."

Safeera bata yi magana ba sai kuka da take yi mai sauti, Islaha ta yi shiru ta bar ta tana kuka, dan itama haka kawai take ji tana da bu?atar zubar da hawaye. Taso ace tana da iyayen da zasu hanata abinda take niya, taso ace tana da uwa ko uba da zasu yi rantsuwa su ce baza ta je ba kamar yadda Baba ya hana Safeera zuwa. Amma ita bata da kowa, ita kaWai take yanke hukuncin da ya yi mata a zuciyar ta, ita kaWai take sa?awa kuma take warwarewa.

Safeera sai da ta gaji da kukan sannan ta koma jan numfashi, islaha ta bata ruwan da yake kusa da ita ta ce, "ki sha." Bata ?i ba ta karSa ta sha tana sauke numfashi.

Islaha ta ce, "me ya faru?."

Safeera ta ce, "Islaha Umma da Baba."

"Me ya faru?."

"Ashe da Umma zaku yi tafiyar nan?."

"Na sani Safeera, ban faWa miki bane dan babu amfanin na Sata miki rai. Amma na san da Umma za a yi tafiyar tun ba yau ba."

Safeera ta goge hawaye ta ce, "Islaha ni kaWai na san abinda nake ji a raina. Baba ya hana Umma tafiyar nan, har Yayanta na Katsina ya kira har gida ya zo ya hanata. Amma ga Umma can ta haWa kaya zata taho gidan nan. Islaha...." Sai ta kasa magana tana jan nunfashi cikin ?unar rai da Saci mai yawa.

Islaha cikin rauni ta ce, "Ki yi ha?uri Safeera."

"Islaha Baba ya saki Umma!."

Gaban Islaha ya yanke ya faWi, ta dafe ?irji cikin kiWima da tashin hankali ta ce, "Saki Safeera!."

Ta Waga kai ta ce, "Daman ya ce mata indai zata bar ?asar nan to babu aurensa a kanta, a gaban idanuna Baba ya cewa Umma ya sake ta. Islaha ji nake kamar ana gasa zuciyata wallahi, me Umma ta nema ta rasa a duniyar nan, me zai kai Umma wata ?asar aiki don Allah!?."

Islaha ta shafa bayanta ta ce, "ki yi ha?uri, babu amfanin Sacin ran tunda ta riga ta aikata. Ki kwantar da hankalin ki, kar damuwar ta saka miki ciwo."

Safeera ta ce, "ni kaWai na san me nake ji Islaha. Yanzu in Umma ta tafi ya zanyi?. Bakyan nan itama bata nan, ina zan saka raina naji daWi? Wajen wa zan dinga kai damuwata? Babu ke babu ita, ina zan saka raina....." ta kasa ?arasawa saboda kuka, muryar ta tana rawa ta cigaba da cewa,

"Waye zai dinga yiwa Baba abinci, waye zai dinga kula da Baba in na tafi wajan aiki?."

Hawaye ya sakko daga idanun Islaha, cikin raunin murya ta ce, "shiyasa nake cewa ki yi ha?uri, in ki ka cigaba da damuwa ke zaki samu matsala."

"Sai da ta ga lokaci ya ?ure, babu damar na faWawa danginta, dan tasan kafin su zo ta tafi. Na kira Abban Katsinan na faWa masa, amma na san wallahi Umma bazata saurare sa ba. Mama Atika ?awarta ce take zugata, duk abinda take yi wallahi itace take saka ta. Kuma da ba haks Msma Atika take ba, tana da kirki, ban ssn me ya canjata haka ba.

Islaha dai bata ce komai ba, Safeera ta ri?e hannunta ta ce, "zan zama marainiya ta ?arfi ta yaji, babu Umma, kema babu ke, babu inda zan saka raina na ji daWi....." hawaye ya sakko mata ta ce, "da na san haka zai faru dana amince na rarrashi Baba ya amince nima naje, da Umma tana gida, sai tafi nida ke."

Islaha ta share mata hawaye ta ce, "ki yi ha?uri, nima kin san ba a son raina zan je ba, kin fi kowa sanin dalilina na tafiya."

"Islaha ga Ummata nan, na bar amanar ta a hannunki...."sai ta kasa magana sai kuka.

Islaha ma ta Wora kanta a bayan Safeera tana kuka mai taSa zuciya. Cikin kuka Safeera ta ce, "Don Allah ki kula da ita, in kin ga zata kauce hanya ki dawo da ita madaidaiciya. Ki ba wa Umma kulawa don Allah, ki dinga bata shawara kina nuna mata abinda ya kamata. Kin san dai ya ake faWar aikin nan, don Allah ki kula min da uwata, kar ki bari ta aikata wani abun da zai zamar mana tabo har ?arshen rayuwarmu!."

Islaha gyaWa kai kawai take yi tana kuka ta ce, "zan yi Safeera, zan yi iya abinda zan yi. Ki daina kuka, ki taya mu da addu'a Allah ya sa mu faWa hannu na gari."

Safeera taja numfashi irin na wacce ta yi kuka ta ce, "bani da kowa yanzu, kin tafi, Umma ma ta tafi, zan zama marainiya. Allah ya kiyaye ku, Allag ya nisanta ku da haram, ya kusanta ku da halal."

"Amin Safeera. Zan dawo, zan dawo mu cigaba da rayuwa kamar yadda muka fara. Ki ta yi mana addu'a kawai, zamu cigaba da magana a waya. Sannan zan bar amanar su Zainab a hannunki, na bar miki amanar su, don Allah ki kula da su, musamman Zainab. Tana cikin matsala, tana bu?atar mai bata shawara, tana bu?atar mai rarrashinta. Kema kin san akwai case a kanta, ki bibiyi case Win, duk abinda ya faru ki dinga faWa min. Akwai abinda nake tunani kuma nake hange a kai, ki tabbatar da komai ya tafi yadda ya kamata, kar ki bar tabiyyar Zainab ta lalace kamar yadda Hafsa ta lalace. Don Allah ki kula min da ita, ina son Zainab kamar ?anwata ta jini."

"Zan yi Islaha, in kina ganin zai yu zan iya yiwa Baba mu Wauko ta kawai ta dawo gidanmu da zama, in sha Allah bazan bari ta yi kukan maraicin ki ba. Sannan duk abinda zai faru zan bibiya kamar kina nan, duk abinda na samu zan dinga sanar miki in sha Allah."

Islaha ta goge hawayenta ta ri?e hannunta ta ce, "Na gode. Zan yi magana da Barr Suraj in na je, komai zai tafi kamar ina nan in sha Allah. In kina fa kayan bayarwa, ki haWawa Zainab Win ki bata.

A lokacin Mama ta shigo ta bi su da kallo ta ce, "To a taso zamu tafi, ki Wauko wannan takardar gwajin da nace ki yi. Ke Safeera zaki raka babar ki Abujan ne?."

Safeera dai bata ce komai ba, ta goge ido tana ri?e da hannun Islaha kamar yadda take ri?e da nata cikin kewar juna. A sanyaye Islaha ta mi?e ta wanke fuskarta, ta buWe handbang Winta ta Wauki sabon facemask ta saka, ta yi rolling kanta da mayafin abayar da ta saka. Safeera ta mi?e ta jawo mata jakarta, kanta yana sarawa saboda kukan da ta yi a haka suka fito falon.

Da Umma suka haWa ido, Safeera ta bi Umma da kallo kamar yarda take kallonta. Umman ta zama wani iri, jikinta a sanyaye yake matu?a, ta zubawa Safeera ido tana kallonta cikin wani irin yanayi mai wahala fassarawa.

Safeera ta Wauke kai daga kallon Umma, ta ri?e hannun Islaha, itama Islahan kallon Umma take yi da take a zaune cikin shirin barin ?asa.

Mama da take ta shige da fice ta kalli Safeera ta ce, "dake za a yi rakiya zuwa Abuja Win ne?."

Safeera ta girgiza kai, ta kalli Islaha muryar ta a sha?e ta ce, "Islaha zan tafi."

Tare suka fara takawa zuwa harabar gidan, Islaha ta ri?e hannun Safeera cikin rarrashi ta ce, "baki yi sallama da Umma ba."

Safeera ta goge hawaye ta ce, "babu amfanin sallama da ita Islaha, ta zaSi duniya sama da mu, ta zaSi aiki akan mijinta, ta zaSi ta bar mu taje inda bata sani ba. Ta je kawai, ba sai mun yi sallama ba."

"Amma hakan ba daidai bane, ko meye ya fari kar ki manta uwace ita, ya kamata ki tuna hakan."

Safeera ta sauke numfashi ta ce, "Islaha itama bata da bu?atar magana dani, da zata yi magana dani da...."


"Safeera!."

Umma ta kira ta tana daga bayan su, hakan ya dakatar da Safeera daga maganar da take yi.

Safeera ta runtse ido hawaye ya sake wanke mata fuska, ta juya ta kalli Umma da take tsaye, Umma? ta ?araso ta ce, "zan tafi Safeera, ki kula da kanki da ?annen ki."

Safeera kasa magana tayi bata ce komai ba, Umma ta shafa fuskarta ta ce, "duk abinda zan yi zan yi shi ne saboda ke, zan yi ne saboda rayuwar ku keda ?annenki. Na fi kowa sonku a duk duniya, duk wanda zai so ku a bayana yake. Zan dawo nan ba da jimawa ba, ki kula da kanki" daga haka ta juya a sanyaye ta koma.

Safeera ta yi murmushin takaici bayan Umma ta Sace ta ce, "ki ji wai saboda mu take yi, mu mun sakata, mun ce muna bu?ata ne?."

Islaha bata ce komai ba, dan ta lura in ta tanka zata iya jawowa Safeera ta faWi wata magana wacce bata dace ba akan Umma ba, ita kuma ba haka take da bu?ata ba.

A hankali suka ?arasa bakin gate, Islaha ta rungume Safeera ta ce, "Zan yi kewar ki Bestie."


"Nima zan yi kewar ki Islaha. Allah ya kare ki a duk inda ki ke, ya yi miki abinda ki ke so. Allah ya sa tafiyar nan ta zama alkhairi a gare ki."


"Amin ?awata, na gode."

Safeera ta raba kanta da ita ta ce, "Allah ya sake haWa fuskokin mu cikin alkhairi."

"Amin Safeera. Sai mun yi waya."

"Ki saka kati sosai, an ce ana jan kuWin kiran waya."

"Zan yi."

Ta gyaWa kai ta saki hannun Islaha ta fita daga gidan a sanyaye.

A haka Islaha ta koma ciki a sanyaye, ta tarar duk sun mi?e tsaye ana niyar fitowa, tana shiga Hajiya Karima ta ce, "ki Wauko kayanki da hanzari, daga nan fa Abuja muka y, tafiya cs mi?a??iya a gaban mu."

Islaha ji take kamar ta ce musu ita fasa, amma in ta tuna bashin da yake kanta sai ta daure ta kawar da komai daga ranta.

A sanyaye ta Wauko handbag Winta, ta jawo trolly bag Win ta fito da ita, ta samu duk suna ?ofar gidan gida, ga wata mota mai Wan girma wacce zata kwashe su gabaWaya.

Aka saka jakar Islaha a booth, Islaha ta kalli ?ofar gidansu Safeera ta ganta a tsaye, ta Waga mata hannu itama ta Waga mata, hawaye ya sakkowa Islaha, ta share hawayen ta buWe motar ta shiga aka ja motar suka bar unguwar.

Nana Haleema.
[6/30, 9:54/ AM] KRBBK: RDB2P27
Nana Haleema.

Ikram kwance a bedroom ta zubawa hotonsa ido tana kallo cikin shau?i da soyayya. Hoton ya yi matu?ar kyau, yana sanye cikin manyan kaya, ya saka hula, kwantaccen gashinsa ya sauka a bayan wuyansa. Ya Wora hannunsa Waya akan hannun kujera, ya yi murmushi mai ?ayatarwa.

Duk wanda ya kalle sa sai ya so ya sake kallo, dan iya ganin hotonsa kaWai ma wata dama ce da ba kowa ne yake samu ba.

A bayyane Ikram ta ce, "yana da kyau, ilimi, kirki, wayewa. Ban damu da kuWin da yake dashi ba, amma ni dai ina sonsa. Ina ?aunar Hamma Rehaan, ina mafarkin ya zama mijina, ina so na rayu dashi har ?arshen rayuwata.

"Wa ki ke so?."

A bazata ta ji tambayar, hakan ya saka ta firgita ta juyo da sauri tana kallon Mummy da ta zuba mata ido tana kallon ta cikin tuhuma, Ikram ta sunkuyar da kai tana mi?ewa zaune.

Mummy ta ?araso ta zauna kusa da ita, ta saka hannu ta zare wayar hannunta tana kallon fuskar wayar dan ganin wanda take kallo tana cewa tana so har haka. Ganin hoton wanda take kallo ya saka ta kalle ta, cike da mamaki da Waure kai, a sanyaye ta ce, "Rehaan ki ke so Ikram?."

Ikram ta shagwaSe fuska tama Waga kai ta ce, "eh Mummy."

"Tun yaushe?."

"Nima ban sani ba."

Mummy tayi ajiyar zuciya cikin damuwa ta ce, "to meye na ajjiye maganar a ranki, meyasa baki faWa min ba?." Ikram

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login