Showing 201001 words to 204000 words out of 221574 words

Chapter 68 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

141

sake komawa ki haWo kuWin?."

Ta girgiza kai alamun a'a, sannan ta goge idanunta ta ce, "contract marriage zan karSa, zai aure ni saboda iyayensa, ni kuma zan auresa dan ya bani kuWin fansar Hamma."

Safeera ta buWe baki saboda mamakita ce, "Ban gane ba, yi min bayani yadda zan kwashe."

Islaha ta rufe ido ta ce, "Shi wanda Baffa ya ce zan aura, dashi zan yi auren yarjejeniya."

"Islaha kina da abin mamaki, ko na ce kina da abin dariya wallahi. Kwana biyu kalaman ki kamar na waWanda suke acting, yadda ki ke yin komai kamar?rubuta miki aka yi ki ka karanta ki ke acting a kai."

"Shiyasa bana son faWa miki, dan na san baza ki bani goyan baya ba."

"Akan me zan ba ki goyan baya akan abinda bai kamata ba? Auren yarjejeniya ki ke cewa za ki yi fa."

Islaha yi magana sa?on Saleem ya shigo wyar ta, Wauki wayar bata cewa Safeera komai ba, ta buWe sa?on ta yi copy Win email address Win Jafar, ta je mail Winta ta paste ta fara rubuta masa message.

Sai da ta gama ta tura sannan ta kalli Safeera ta ce, "Abinda na faWa miki shi zan yi, zan je wajensa mu yi magana, in dai ya amince zai bani wannan kuWin ni kuma zan aure sa na Wan lokaci kaWan, daga baya sai mu rabu na dawo na auri Hamma."

Safeera da take kallon Islaha ta ce, "ban gane ba Islaha, wai aurensa za ki yi dan ya ba ki kuWi, sannan daga baya ya sake ki ki dawo ki auri Saheer?." Ta Waga kai alamun eh tana kallon ta.


Safeera ta zaro ido waje ta ce, "na shiga uku, Islaha me ki ke faWa ne haka? Wannan wacce irin magana ki ke yi kamar ta masu taSin hankali?. Contract marrige a addinin mu, kuma a al'adar mu ta fulani? Sunnar Annabin za ku gina akan bayan wasu kwanaki za ku rabu?."

"Dallah malama ki daina Waga min murya, na san duk abinda nake yi, kuma auren gaske za a yi tunda Baffa ya sani. Ba wa'azi na ce ki yi ba, na riga na yanke hukunci, ko me za ki ce ba sauraren ki zan yi ba."

"Dan Baffa ya sani ai ba akan hanyar kirki ku ka gina auren ba. Kuma ke yanzu akan Saheer sai ki yi wannan kwamachalar? In ya fito ya ji kin yi aure nufin ki zai ji daWi ne?."


"Akansa zan yi, in ma abinda ya fi kwamachala ne indai akan Hamma ne zan aikata. Kuma ko da ya fito Win ma ba wani abun damuwa bane, dan ba jimawa aure zai yi ba ya watse, ni kuma na dawo na auri Hamma."

Safeera ta bita da kallon bata da hankali, amma sai bata yi magana a kai ba ta ce, "Shi kuma kawai sai ya Wauki waWannan kuWi ya ba ki dan ki aure sa? Mahaukaci ne shi ko yana shaye-shaye?.

Islaha ta ce, "ban sani ba, amma na san yana da kuWin da zai bani. In ya bani fine, in bai bani ba za a yi soke yarjejeniya."

"Okay, mu yi tunani akan bai baki Win ba, a ina za ki samu kuWin fansar?."

Islaha ta Waga kai ta kalle Safeera sai ta girgiza kai ta ce, "bani da hanyar da zan samu, balle ma a jikina nake jin zai bani."

Safeera ta ce, "saboda kawai zai aure ki sai ya Wauki waWnanan kuWin ya ba ki? Ke ga ?ar gold ko ?ar diamond da azurfa ko?. Miliyan hamsin fa ba dubu hamsin ba."


"Ba ?ar diamond ba ce, amma zan gwada na gani. A rashin ta yi ake barin arha, abinda ka ke ganin bazai faru ba in ka gwada sai ka ga ya faru."


"Shi wanda ki ke magana akan zai ba ki kuWin, waye shi?."

Ta Waga ido ta kalle Safeera, kamar zata faWa mata sai kuma ta ce, "?aryata ni za ki yi in na faWa miki."

Safeera ta ce, "faWi ina jin ki."

Islaha ta ce, "ki jira komai ya tafi yadda nake so, zan Wauke ki muje tare dan ki gani da idon ki. Amma yanzu....." bata ?arasa maganar ba wayarta ta fara ?ara, ta duba ta ga sabuwar lamba ce sai ta Wauka ta saka a kunne.

Jafar ya ce, "Miss Islaha."

Jin hakan sai ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Mr Jafar, Ina yini."

"Lafiya. Na ga mail Win ki, kuma sai na ga kin yi dropping digit Win ki sai na kira."


"Thank god! Gaskiya ni mai sa a ce, an faWa min kana jimawa jafin ka buWe mail. Amma ni within ten minutes ka buWe har ka kira ni."

Bai ce komai ba ta ji dai ya yi murmushi ta ce, "Allah yasa ban takura ka ba, dan Ina son magana da kai ne."

"Kar ki damu, Am all ears."

Ta Wan sauke numfashi ta ce, "ina so na haWu da Wan uwanka akan wannan maganar."

Jafar ya ce, "Gaskiya a yanzu ban san inda yake ba, amma na san yana cikin garin nan."

Islaha ta ce, "Ina so na haWu dashi akan auren yarjejeniyar sa ya ce."

Ya Wan yi murmushi ya ce, "kina ina yanzu?."

"Ina gida."

"Okay, zan turo a Wauke ki sai a kai ki inda za ki same sa."

"Thank you. Amma don Allah ina so ka kasance a wajen, ina so na ganka a tare dashi

"Miss gaskiya am not availabe, beside an fara events Win bikina, bani da wani time yadda ya kamata."

Islaha ta ce, "Don Allah."

Ya Wan yi shiru sannan ya ce, "Okay." Ta yi godiya ya kashe wayar.

Ta kalli Safeera da take kallon ta ta ce, "Ki shirya mu je tare, za ki ganawar idanunki waye shi ba sai na faWa miki ba."

Safeera ta kasa cewa komai, dan tunda ta yi waya da Jafar sai tunanin ta ya tafi Rehaan ne, tunda ta san sunan mahaifinsa ta faWa masu lokacin da ta ce an zo neman aurenta.

Safeera doguwar rigar da Islaha ta bata ta
ta saka, jim kaWan aka kira ta a waya aka ce an zo Waukar ta suka fita.

Farar mota suka gani a ajjiye a ?ofar gidan tana jiransu, suka ?arasa wajan driver ya ce, "Islaha ko?."

Ta Waga kai ya ce, "Mr Jafar."

Bata ce komai ba suka shiga motar suka tafi ?irjinta yana bugawa da gaggawa.

Gidan da ya saka aka kai ta nan ta ga an sake shiga, Safeera dai kallon Islaha kawai take yi har motar ta tsaya. Driver ya ce, "bismillah."

Suka fito a hankali ya nuna musu hanyar da zasu bi suka wuce suna tafiya kamar basa so.

Gab da zasu shjga falon Safeera ta ri?e Islaha ta ce, "Islaha kar ki yake hukunci cikin gaggawa, kar mu zo mu yi danasani nan gaba. Ke kan ki kin san kina da gaggawa akan komai, ki tsaya mu nutsu kar mu yi abinda zai cutar damu."

Islaha ta cire hannun Safeera daga ri?on da ta yi mata ta ce, "Tunda mu ka zo nan magana ta ?are, tunda na yi niya sai na yi, indai akan Hamma ne zan yi ko wacce gaggawa ce. Akan wani daban ma na yi gaggawa na tafi Jeddah balle Hamma? Ki zo mu je kawai."

Safeera ta Waga mata kai suka shiga falon da sallama. Falon babu kowa, amma akwai haske sosai. Suka tsaye suna kalle-kalle ba su san inda zasu bi ba, Driver da ya kawo su ya le?o ya ce, "ku shiga waccan ?ofar, Mr Jafar yana ciki." Suka shiga ciki da sallama, Jafar da yake kallon ?ofar ya amsa yana kallonsu.

Islaha ta Wan yi murmushi ta ce, "Thank you mr Jafar." Ya nuna mata wajen zama sannan ya ce, "Your welcome, Miss Islaha da ?awar ta Miss Safeera." Safeera cikin mamaki ta kalle sa, sai ta kalli Islaha ta ga bata ji wani mamaki dan ya faWi sunanta ba.


Duk ba su lura da Rehaan a kwance akan kujera ba, dan ya kifa littafi akan fuskarsa, ya yi shiru yana jinsu kawai bazai mi?e bane shiyasa ya yi kamar bai ji ba, bai motsa bama balle su gane idanunsa biyu.

Islaha idanunta ya kai kansa, ta Wan yi tsaki ta ce, "Mr Jafar na zo nan dan na saka hannu a takardar yarjejeniyar auren wata biyar."


Jazy ya nuna mata Ray da yake kwance ya ce, "gashi nan ai, dashi ku ka fara kuma dashi za ku gama. Ray ka tashi, your wife is here." Ya yi masa banza kamar bai ji ba, nan kuwa yana jin duk abinda suke faWa.

Jazy ya ce, "na san kana jina fa, dallah malam ka tashi." Kamar bazai tashi ba, sai kuma ya mi?e ba tare da ya cire book Win fuskarsa ba. Ya sauke ?afafunsa a ?asa, ya cire littafin a hankali ya kalli Jafar.

Jazy ya ce, "ita za ka kalla ba ni ba." Ray ya Wan juya ya kalle su sai ya Wauke kai kamar bai gane su ba.

Nana Haleema.
[7/28, 5:31/ PM] KRBBK: RDB2P92
Nana Haleema.

Lokacin da ya kalle su Safeera sai ta ji kamar an jona shocking a jikinta, ta buWe ido sosai tana sake tabbatar da ba fa gizo yake yi mata ba, shi Win ne dai a zaune a gabanta.

Tsabar mamaki da ruWewa bata san ta buWe baki ta ce, "Mr Rehaan!." Ta gefen ido ya kalle ta ya share bai ce komai ba shima Jazy bai ce komai ba.

Islaha ta Wan taSa Safeera ganin zata zubar mata da class ta ce, "Ka yi magana akan auren yarjejeniya ko? To gani na zo zan saka hannu a kai."

Bai ce komai ba sai kallon falon da yake yi kamar mai neman wani abu, can ya hango takardun a? kan tav stand.

Ya kalli Safeera suka haWa ido, ya nuna mata takardar ya yi mata alama da ta Wauko masa.

Safeera kwarjini ya yi mata, bata san lokacin da ta yi nufin mi?ewa ta Wauko ba, Islaha ta zaunar da ita ta ce, "ai ba aikin da ki ka zo yi ba kenan, ba ke za ki Wauko ba, in shi bazai tashi ya Wauko ba ni zan Wauko. Abinda ya shafe shi ne ba ke ba, baza ki yi masa aiki a banza ba." Ta faWa tana mi?ewa ta Wauko ta dangwarar a gabansa.

Ya shafa kansa yana mamakin wannan yarinya mai taSin hankali, ya jingina da kujera yana rufe ido yana ji a ransa in aka bar shi da yarinyar nan wata ran tsaf zai iya sha?e ta ta daina numfashi, ya lura tana da rawar kai, amma zai gyara mata zama a wata biyar kacal.?


Jafar dai ya yi shiru yana danna waya kamar bai san dasu ba, hankalinsa baya kansu yana kan abokansa da suka zo daga wata ?asar yana ba da inda za a kaisu.

Ya buWe ido ya Wauki takardar ya mi?a mata ba tare da ya kalle ta ba. Islaha ta karSa bata kalle sa ba, ta kalli takardar tana karanta abinda yake ciki. Five months contract marriage, shine abinda ta gani da manyan ba?i a rubuce a sama. Sai rules Winsa da ya rubuta mata wanda dole sai ta bi su indai ta yarda da auren.

Rule na farko akan ba ya so kowa ya san shine mijinta, auren sirri ne. Na biyu kar ta faWi sunansa a ko ina a matsayin matarsa, ko me zai faru kar ta ce faWi sunansa. Na uku kar ta saka masa baki akan komai nasa, duk abinda ya ga dama zai yi mana babu ruwanta. Na huWu dole ta yi duk abinda ya ce mata babu saSawa, dole ta bi umarninsa a duk lokacin da ya ga hakan ya kamata, dole ta yi pretending Win matarsa a wajan waWanda suka dace. Babu ruwanta da maganar gidansu, komai zai faru kar ta saka baki.

Ta gama karantawa ta kalle sa tana hararesa, ta sake kallon takardar ta ga ?aramin rubutu inda ya ce zai aure ta saboda mahaifinsa ya ce, saboda ya yi al?awari akan hakan. Sai wajan da zata saka hannu da inda zai saka hannu.

Islaha ta kalle sa ta ce, "na karanta sharaWan ka."

Bai kalle ta ba ya ce, "ki saka hannu."

Ta yi dariya ta ce, "ji mana, ni ma ba ka ji nawa rules Win ba ai ko?" Ta faWa tana buWe handbag ta Wauko takarda ta mi?a masa.?

Ya bita da kallo yana mamaki, tunanin har wasu conditions ne da ita akan aurensa?. Ya yi kamar bazai karSa ba, sai kuma ya karSa yana dubawa.

_Na amince zan yi auren yarjejeniya da Rehaan Yola, amma in ya amince zai bani kuWin fansar wanda zan aura naira miliyan hamsin._

Rehaan yana gama karanta wajen ya Wago ya kalle ta ya ce, "Are you a thief? Fifty million for your marriage?"

A lokacin Jafar ya kalle su jin zancen miliyan hamsin, ya kalli Islaha da take kallon Rehaan, ya kalli Rehaan da yake kallon ta, ya girgiza kai yana tunanin wannan lamari nasu kamar a wasan kwaikwayo, ko a film bai saba ganin mutane kamar Rehaan da Islaha ba. Kuma shi daWi ya ke ji da ya kasance Islaha tana da wayo da magana, in ba dan haka ba da Rehaan ya gama da ita. Amma yanzu da yake faWa tana mayarwa, tana nuna masa itama tana da rules Win da zata ba shi, Rehaan Win zai san ba dan wani abu na sa zata aure shi ba.

Islaha ta kalle sa cikin ko in kula ta ce, "za ka aure ni saboda mahaifinka, wannan shine reason Winka. Ni kuma zan aure ka saboda fifty millions, kuWin fansar wanda zan aura in contract ya ?are. In za ka bani kuWin da zan karSo sa daga wajan kidnappers fine, if not daman ban saka hannu ba."

Ya zuba mata ido kawai yana kallon ta, sai kuma ya kalli Jafar, Jafar dai murmushi yake yi bai ce komai ba, sai kuma Jazy ya Wauke kansa dan babu ruwansa, ya cigaba da danna wayarsa yana dariyar wannan lamari.

Rehaan ya ce, "Ke ?ar fashi ce?."

Islaha ta Waga hannu tana Wage kafaWa ta ce, "babu dole a maganar nan, in baza ka iya ba a fasa daman ba a yi ba. Saboda shi kaWai zan saka rayuwata a cikin rayuwarka, shima rashin mafita da son ceto rayuwarsa ne ya saka zan zauna inuwa Waya da kai, bayan wannan da babu wani abu da zai sake haWa ni da kai har abada.

Ya Wan buWe ido ya ce, "fifty millions for you? Oh God!" Ya faWa yana Wan kulle ido.

Inda wata ce ba ita ba kuWin ba komai bane, amma gani yake in ya bata kuWin ta yi nasara kuma ta samu riba akansa, ga aurenta ga kuma kuWin da zai bata. Kamar ma shine ya nemo ta ya ce zai aura, tunda daga aljihunsa zai fitar da kuWin ya bayar, kamar shi ya ke son auren.

Bai ce komai ba ya cigaba da kallon takardar yana karanta rules Winta bit by bit. Dan ya san sharaWin irin wanna auren, indai ka saka hannu dole ka bi duk abinda mutum ya ce.

Abu na farko da ta rubuta zan cigaba da aikina, ko ?asar waje aikinna zai ta babu ruwanka. Ina da wanda nake so kuma zan aura, zan cigaba da magana dashi kuma na haWu dashi a duk lokacin da na ga dama, babu wanda zai yi min iyaka da ganinsa. Zan yi duk abinda nake so, baza a takura min ace sai na bi umarni ba, dan ba auren gaske na yi ba balle na yi biyayya. Ni ba ?ar aiki bace, bazan yi share-share da girki ba. Baza a hana ni fita duk inda na ga dama ba, in kwana ya kama na yi a waje zan yi babu ruwan mutum da ni.

Rehaan ya gama karantawa dan kaf cikin rules Win bai ga wani rule na kirki a ciki banan ba.

Rule na ?arshe ya kalla, ya ga shi da capital letter ma aka rubuta shi saboda girmansa, an rubuta NO INTIMACY RELETIONSHIP!.

Rehaan ya Wan Wago ido ya kalle ta, shi wallahi ya manta da wani intimacy saboda ba ya gabansa a aurenta, ko kaWan bai kawo hakana a ransa ba balle ya yi tunanin saka shi a cikin rules Winsa. Amma ita da yake abin yana zuciyarta gashi har ta rubuta, ko intimacy Win me zai yi da ita oho mata.

Ya Wan yi ?aramin tsaki ya ce, "it's that all your rules?." Ta Waga kai alamun eh.

Ya Wan yi shiru yana tuna al?awarin da ya yiwa Abba sannan ya kalli Jafar ya ce, "Jazy pen."

Jazy ya ya mi?e masa shi kuma ya yi signing takardar da ta ba shi, sannan ya yi signing akan wata a kusa dashi. Ya sake yin signing akan guda huWu ya cillar da biro akan table Win.

Itama ta Wauki biron ta saka hannu zuciyar ta ko War babu kamar yadda ya yi.?

Ta Wauki Waya wacce ya rubuta rules Winsa, dan ko wacce copy biyu ce, da wacce zata ri?e da wacce zai ri?e, ta saka a handbag.

DaWi ya cika mata rai dan iya saka hannun sa ya yi ya bata tabbacin zai ba da kuWin, sai ta ke gani kamar Hamma ya fito ya gama, ta zama silar fitar Hamma daga cikin u?uba.

Jazy ya Wan yi tafi yana kallonsu ya ce, "Finally, mr and mrs Rehaan."

Islaha ta ce, "ku zama shaida a gaban idanunku aka yi komai, Mr Jafar ka karanta don Allah" ta faWa tana nuna masa takardar.

Ya girgiza kai ya ce, "No need Miss, kar ki damu. Rehaan bazai yi breaking ko wanne rule Win ki ba, ya san duk abinda yake yi."

"A'a Mr Jafar, bana so a samu matsala nan gaba, dan gaskiya bazan jure ba."

"Baza a samu ba Islaha, tunda kuna ganin auren contract shine daidai da ku shikenan."

Rehaan dai kallon ta kawai yake yi yana mamakin ?arfin hali irin nata, wai mutum kamar shi take faWawa irin wannan maganar dan bata da hankali, har tana cewa wai bata so a samu matsala saboda baza ta jure ba.

In ba dan al?awarin da ya yiwa Abba ba ita ta isa ya zauna yana faWa tana ja? Ta isa ta sake ganinsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login