Showing 72001 words to 75000 words out of 221574 words

Chapter 25 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

166

yayansu a zauma lafiya. ?auna ?a?ansu suke yi kamar su Wiga musu sabon rai, akan ?a?ansu zasu iya yi miki komai wallahi. Na yi miki bayanin nan, amma daga fita ta har kin canja. Akan cutar musu da yara zasu iya kama ki, kuma a ?asar Saudia ki ke ba Nigeria ba, kulle ki zasu yi a gidan yari, babu ruwan su dake ba ?ar ?asa bace."

A sanyaye Umma ta ce, "ban san ruwan sanyi na kunna mata ba, wallahi ban san ya yi mata sanyi ba."

"Waye ya ce ki bari ta shiga ciki? Ai sai kin fara haWa mata ruwan sannan zaki bari ta shiga ciki. Yanzu da na zafi ki ka kunna mata fa?."

"Wallahi ban sani ba, da na san me sanyi ne bazan kunna ba. Tunda kin ga ban san kan gidan ba, ko awa Waya ban yi da zuwa ba, sai a hankali zan saba."

"Wallahi da ruwan zafi ki ka zuba mata da yanzu sun kira ?an sanda sun tafi dake. Basa jurar ?aramar matsala, son jikinsu ne dasu."

Umma ta yi shiru bata ce komai ba, Shafa ta ce, "akan yaran nan sai zaman ki zai ?are a gidan nan, kin ga dai yau ki ka zo ko? To zaki iya komawa yau. Kinga ke ce da asara, kafin a sake samun wani gidan kin galabaita, gashi baki san gari ba, kuma baki da ko sisi."

Umma ta ce, "to ya zanyi?."

Shafa ta ce, "mu je."

Umma ta biyo ta a sanyaye tana ji kamar ta kifa saboda gajiya mai nauyi, ga kanta yana ciwo, ga yunwar da take ji mai ?ona ciki.

Shafa tabi Wakin yaran da kallo ta ce, "ki gyara Wakin nan, sannan ki je ki dafa musu abinci, lokacin cin abincin su ya kusa."

Umma a galabaice da rauni ta ce, "Hajiya Shafa na gaji, wallahi bazan iya aikata komai a yanzu ba, ina bu?atar hutu. GaSoSina ciwo suke yi min, ga kaina yana ciwo, ga yunwa, ga gajiya. Tafiyar Jeddah zuwa madina ba kusa bace kin sani, tafiya muka dinga yi kamar zamu bar duniya. Gashi mota ta lalace, haka muka zauna a daji ana gyarawa. Don Allah ki ce musu a bari na huta zuwa anjima sai nayi."

Hajiya Shafa ta gyaWa kai tana bin Umma da kallo tana buWe ido tace, "Hajiya meye ma sunan ki?."

"Maimuna nake."

"Maimuna buWe kunnen ki dakyau ki ji abinda zan faWa miki, dan na ga alama baki san inda ki ka kawo kan ki ba...."

"Ina so ki san a inda ki ke, nan ba Nigeria bace, a ?asar Saudia kike, a cikin garin Madina. A cikin Madinan ma ba ziyara ki ka zo ba, ba hutu kika zo ba, a gidan larabawa kike kuma aiki zaki yi su biya ki."

Ta yi ?wafa irin baki san dawar garin ba ta ce, "Maimina ina sake faWa miki basu san Waga ?afa ba, basu san kara ko wani abu hutu ba. Mai aiki akwai sunan ki a wajensu, a haka suke kallon ki ba wacce tazo ta huta ba. Kamar baiwa haka zaki koma a gidan nan, tunda kuWi zasu baki ba kyauta zaki yi musu ba. Dole ki yi abinda suke so a yanzu, babu ruwansu da yanzu ki ka zo ko kin gaji. Indai kina son samun kuWin dole ki buWe ido ki san a inda ki ke."

Umma a gajiye ta ce, "ina son samun kuWi, kuma na san aiki zan yi, amma tsakani da Allah a bari na huta zuwa gobe ko zuwa dare mana. Tun da muka Wauko hanyar garin nan a zaune nake, wallahi na gaji, gajiya mai yawa. Babu abinda zan iya yi yanzu, ko sallah da akwai dama yi min za a yi, ?afafuna jinsu nake kamar ba nawa ba."

Shafa ta ce, "zancen ki ke so, wannan maganar hutun ki ha?ura sai dare. Mu je na nuna miki kitchen ki dafa musu abinci, lokaci yana gudu."

Umma ta bi bayanta a sanyaye tana ji kamar zata kifa saboda gajiya da tashin hankali. Suka shiga kitchen Win, Umma taga babban kitchen ne mai kyau da tsari irin na larabawa.

Ta nunawa Umma komai ta ce, "ki Wauki kajin nan ki gyara su sannan ki gasa a nan" ta faWa tana nunawa Umma oven.

Shafa ta ce, "sai ki dafa shinkafar nan, basa son yaji, basa son WanWano ya yi yawa. In ki ka saka musu yaji mai yawa wallahi babu ruwana. Ga kayan ?hamshin, sai ki yi amfani dashi yadda ya kamata."

Umma dai tana ji ne kawai ba wani fahimta take yi sosai ba, kanta juyawa yake yi tana ji kamar ta faWi a wajen. Da taimakon Shafa suka fara dafa abincin, dan bata san me

Tana cikin dafawa sai ga budurwar yarinya ta ?araso, ta yiwa Shafa magana da larabci ta amsa bayan ta bar wajan ta ce, "wai tana da wanki a Waki, ki je ki wanke musu."

Umma ta tsame hannunta daga wanke shinkafar, ta bi inda aka nuna mata. ?akin wanki ne wanda yake Wauke da injinan wanki guda biyu, sai wajan goga da kayan gugar.

Umma ta sauke numfashi ganin kayan tuli masu yawa sosai, gashi sun yi kaca-kaca kamar kayan ?ananun yara masu rarrafe.

Umma ba iya amfani da komai sosai ba, amma bata fita ta tambayi Shafa ba ta dinga bi a hankali har ta kunna ya fara wankin. Ganin ta fara wankin sai ta samu waje ta zauna tana lumshe iso bacci yana figarta sosai.

A haka tana zaune a wajen har aka yi kiran sallar azahar, ta ji kiran ya karaWe ko ina. Umma ta mi?e da?yar ta fito ta koma wajan Shafa ta tarar har ta gama abinci ta gama gyara waje komai tsaf.

Shafa ta kalli Umma ta ce, "wai har kin gama wankin?."

Umma a sanyaye ta ce, "sallah na ji ana yi, shine na fito nayi zallah sai na koma."

Ta kalli Umma tana girgiza kaita ce, "hmm, Allah yasa su yi miki wannan uzurin, sufa sun fi so da ance kawai a yi, basa son Sata lokaci."

Umma ta wara ido waje cikin mamaki ta ce, "har sallar ma?......"

Nana Haleema
' [7/1, 1:08/ PM] KRBBK: RDB2P31
Nana Haleema

Hajiya Shafa ta yi dariya ta ce, "baki san a ina ki ke bane. Jeki ki yi alawar."

Umma ta juya ta shiga Wakin da aka nuna mata, da?yar ta iya alawala ta fito ta yi sallah, Tana idarwa bata san bacci ya Wauke ta a inda ta idar da sallar ba, ko hijjab bata cire ba saboda yadda baccin ya ci ?arfinta.

? ?? A firgice ta farka jin ana shafa hannunta, ta buWe ido tare da mi?ewa zaune tana raba ido jin ba?on abu wanda bata saba ji ba.

Suna haWa ido taga mai gidan ne da kansa a tsugune a gabanta yana yi mata murmushi.

Gaban Umma ya faWi, ta ja baya da sauri tana so ta yi magana amma bata san me zata ce ba, ta san ba yaren ta yake ji, sannan itama ba nasa take ji ba balle ta tambaye sa dalilin zuwan sa waje. Umma ta ruWe sosai, tashin hankali ya bayyana ?arara a tare da ita. Shi dai ya bita da kallo kafin ya mi?e ya fita.

Umma ta bisa da kallo sai kuma ta tuna da wanki, ta firgita ta mi?e ta koma Wakin wankin ta tarar an sake tulo mata wasu.

A haka Umma ta gama wankin, ko gama bushewa basu yi ba ta fito jin kanta yana sarawa kuma ta san yunwa ce. Tana fitowa suka haWu da matar gidan, ta yi mata alama da ta biyo bayanta, Umma ta bita har kitchen.

Ganin kayan wanke-wanken da suke jibge sai da gabanta ya faWi, ta ji hawaye har taruwa suka yi a idanunta saboda tashin hankali da damuwa.

Matar gidan ta nunawa Umma kayan alamun ta wanke, sannan ta nuna nata wani kwano alamun ga abincinta nan. Umma ta bi kayan wanke-wanken da kallo dan kayan suna da bala'in yawa sosai.

Umma ta ?arasa ta buWe abincin ganin shinkafar da aka dafa ce sai rabin kaza. Hannu yana rawa Umma ta fara ci a hankali dan yunwa take ji sosai.

Kafin ta ci rabin abincin ta ji ana jan hannunta, taga yarinyar nan da zata yiwa wanka Wazu, Umma ta bi bayanta suka fita sai taga yadda suka lalata falon, kuma taga alama ake yi mata da ta gyara wajan.

Umma ta yi ajiyar zuciya cikin wani irin yanayi, ta bi dining Win da kallo ganin sa kaca-kaca kamar yara ?ananu ne suka ci, bayan cin abincin suka haWa da dambe a kai.

Ta lumshe ido tana ?arasa wajan ta Wauki abinda aka nuna mata na aiki, ta fara share wajan sannan ta goge dining Win ta gyara kujuren, ragowar tarkacen kayan da suka bari ta Wauke ta koma kitchen ta fara wankeawanken dan ta manta ma abinci take ci.

Kamar an tuna mata da wayar ta, gabanta ya faWi ta ji tana so ta yi magana da ?a?anta.

Ta juya zata fita ta Wauko ta ga mai gidan a tsaye a falo shi kaWai yana binta da shegen kallo da ya saka ta tsaya cak, gabanta ya faWi matu?a, ta juya ta cigaba da aikin jikinta yana rawa cikin tashin hankali. Tunani take a zuciyarta ina ta kawo kanta haka?.

" " " " " "

"Sadik ina Islaha ne, ban ganta ba kwata-kwata. Ko ta tafi aiki ne?."

Sadik ya kalli Baffa ya ce, "Wallahi Baffa nima bamu haWu da ita ba, amma na san tana wajan aiki, zata biyo in ta tashi.

Baffa ya ce, "Islaha sarkin ?or?ari, Allah ya yiwa rayuwa Albarka."

Sadik ya amsa yana fitowa daga Wakin suka haWu da Hanan zata shiga ya ce, "Hanan don Allah ina Islaha?."

Ta Wan taSe baki ta ce, "Ban sani ba" ta faWa tana shiga Wakin ta bar sa a tsaye yana binta da kallon mamaki.

Sadik ya Wauke kai ya Wauko wayarsa ya kira Islaha amma wayar bata tafiya gabaWaya.

Mama ce tazo zata shiga Wakin, Sadik ya tsayar da ita ya ce, "Mama Islaha tana gida ne?."

Mama ta ce, "Islaha ai bata nan, zaka jima baka ganta ba." Kafin ya sake magana ta shiga Waki ta barsa a tsaye cikin mamaki.

Sadik ya bi Mama da kallo cikin rashin fahimta, ya fita daga asibitin ya hau mota ya nufi gidansu Safeera.

Yana tsayawa a ?ofar gidan kiran Saheer yana shigowa wayarsa, bai Wauka ba dan ya san tatsuniyar gizo bata wuce ta ?o?i, ya san bazai wuce yace masa lambar Islaha bata shiga ba, in ya Wauka bashi da amsar da zai bashi.

Sai bayan wayar ta yanke ya kira Safeera tana Wauka ya ce, "Safeera kina gida ko wajan aiki?." Ya yi shiru alamun ana basa amsa, sai kuma ya fita daga motar ya hango ta ta fito daga gidansu.

Ya ?arasa wajan sai ya ga motar Saleem ta tsaya, shima ya ?araso suka gaisa. Saleem ya kalle Safeera ta ce, "ya jikin ki?."

A sanyaye Safeera ta ce, "Da sau?i."

Saleem ya ce, "Ana ganin ki an san baki da lafiya."

Sadik ya ce, "Sannu Safeera, ban san baki da lafiya ba da ban kira ki ba."

Safeera ta Wan murmusa ta ce, "ciwon kai ne kawai."

Sadik ya kalle ta ya ce, "?awar ki fa? Na kira ta sau babu adadi bata Wauka, ga sarkin rashin ha?uri ya fara damuna da waya akan baya samunta."

Saleem ya ce, "A'a, Islaha ba tayi tafiya ba?."

Sadik da mamaki ya ce, "Islahan ce tayi tafiya, to zuwa ina?."

Saleem ya ce, "nima ban sani ba, amma kowa na gidan tv ya san Islaha bata nan, har Safeera."

Sadik ya kalli Safeera ya ce, "Safeera Ina Islaha take?."

Safeera ta sauke numfashi ta ce, "Eh Islaha tayi tafiya Hamma Sadik."

Sadik mamaki ya mamaye masa zuciya ya ce, "ina ta je? Ina ta tafi bamu sani ba?."

Safeera ta Wan yi ajiyar zuciya ya ce, "itace tace bata so ka sani kai da Saheer, shiyasa baku sani ba."

Da mamaki Sadik ya ce, "tafiya zuwa wani gari to? Me ya kaita garin, kuma yaushe zata dawo?."

Safeera ta kalle sa ta ce, "?asar ta bari gabaWaya ai, ba wani garin ta tafi ba, Islaha bata Nigeria."

A tare suka haWa baki suka ce, "Kamar ya ta bar ?asar!?." Safeera ta yi shiru bata ce komai ba, dan bata san me zata ce musu su yarda ba.

Sadik a ?agauce ya ce, "ki yi mana magana mana Safeera, kalli wayata, Saheer ne yake yi min magana ban san me zance masa ba. Wacce ?asar Islaha ta tafi? Wacce ?asar islaha ta tafi bamu sani ba?." Safeera ta sake yin shiru bata ce komai ba, ita kanta gabanta faWuwa yake yi dan bata san me zata ce ba.

Sadik ya dafe kai ya ce, "Safeera ki buWe baki ki yi magana, kar ki saka jinina ya hau don Allah."

Safeera ta ce, "ta tafi ?asar saudia, yanzu haka ma tana can. Dan tun safe na ga voice note Winta, ta ce min har ta sauka a masauki."

Saleem cikin firgici da tashin hankali ya ce, "Saudia Safeera! Umra ta tafi babu labari?."

Sadik yabi Safeera da kallo dan ya kasa magana, ya girgiza kai cikin mamaki ya ce, "wai me islaha ta Wauke mu ne? Me take Soyewa wanda bata so mu san dashi?. Tunda aka sace ta na lura da akwai abinda ake Soyewa wanda bata so mu sani. Yanzu waye ya kai Islaha saudia Safeera? Kin tabbatar ta bar ?asar nan?."

Safeera ta ce, "Wallahi Islaha bata nigeria, kuma ta tafi Saudia ta ?ar?ashin kamfanin su Mamansu Saheer. Ba ita kaWai ba, harda Labiba da...." Sai maganar ta ma?ale saboda nauyi, ta sunkuyar da kai ta ce, "Da Ummana" ta faWa hawaye yana sakko mata ta yi sauri ta goge.

Sadik ya dafe kai da hannu biyu ya ce, "aikatau Win ta tafi kenan?."

Ta Waga masa kai ta ce, "ta ce bata so ka san ta tafi, bata so ka san dalilinta sai ta bar ?asar."

A fusace Sadik ya ce, "wanne dalili ne da ita da zai saka ta yanke wannan hukuncin?. Ni fa ban yarda da ita ba, zuciyata faWa min take yi yawon banza Islaha ta fara yi, shiyasa ta bar gida ta je ta kwana biyu da sunan an sace ta. Taje ta gama zaman ta a inda ta ga dama, sannan ta dawo da kuWi masu uban yawa ta ?i faWar a inda ta samu, yanzu kuma ta bar ?asar duk bamu sani ba."

Safeera ta ce, "wallahi Islaha bata fara yawom banza ba, ka daina jifanta da wannan kalaman. Tafiyar ta aikin ma rashim mafita ne ya saka ta tayi ta, ba a son ranta ta tafi ba."

Sadik ya zuba mata ido dan ya kasa magana, hakan ya saka Saleem ya ce, "Wacce mafita ce wannan da zata saka ta tsallake mu ta tafi wata ?asar aiki a gidan larabawa?."

Safeera ta ce, "Kamar yadda ta faWa mana yadda aka sace ta, da gaske ta hakan aka sace ta. Ranar da zata dawo ta ga kuWin a falon mutumin, shine kawai sai ta Wauko tana tunanin yanayin da ta bar Baffa a ciki, kar ta dawo ba a samu kuWin aikin ba."

"Bayan aikin Baffa ya kammala kuma sai hankalinta ya tashi sosai, ta dinga mafarkai akan kuWin. Shine ta same ni tana neman hanyar da zata samu kuWin ta biya sa. Na faWa mata samun kuWi kamar wannan a ?aramim lokaci bazai yu ba, nima ban sani ba, ashe har ta gama shirya komai an yi mata visa, sai tafiyar kawai ta faWa min."

Sadik ya bita da harara ya ce, "Safeera kar ki mayar damu ?ananun yara mana, kar ki mayar damu shashashai waWanda basu san abinda suke yi ba, ki faWa maganar da kanmu zai Wauka, ki daina yi mana magana ta rainin hankali. Mu ba mahaukata bane da zamu yarda da wannan shirmen."

Saleem ya jinjina kai ya ce, "ya sace ta, ya ajjiye ta a gidansa bai yi mata komai ba, kuma ya saka aka dawo da ita. Ita kuma saboda ?arfin hali, tana hannun wanda ya sace ta bata kuSuta ba, shine harda Wauko masa kuWi?. Bayan ta dawo kuma ta Soye mana, ta dinga Soye-Soye a kan case Win. Yanzu kuma ta shirya tafiya ta bar ?asar, duk babu wanda sani ba."

Ya Wan girgiza kai ya ce, "Safeera hankali bazai Wauki maganar nan taki mai kama da wasan yara ba, nima ban yarda ba balle Sadik, balle kuma aje kan uwa uba Saheer. Kuna Soye mana wani abun ke da ?awar ki."

Kamar Sadik jira yake yi ya fara bala'i ya ce, "mu zata mayar shashashai ?an iska? Mu za a tsaya ana tsarawa ?arairayi kamar wasu marasa hankali?."

Safeera ta ce, "wallahil azim ban Soye muku komai ba, wallahi Allah abinda ya faru kenan. Islaha ta tafi dan ta nemi kuWin da zata biya wancan bashin sa da taci, ko nace ta je neman kuWin da zata mayar masa a inda ta Wauke. Wallahi duk wani tunani mara kyau da kuke yi ba haka ba, Islaha bata canja ba, tana nan yadda take. Don Allah ku daina zarginta da mummunan abu, Islaha mace ce ta gari"

Sadik ya ce, "Naji mace ce ta gari. Yanzu in taje ta samo kuWin ta dawo, a ina zata samu mutumin ta ba sa kuWi? Ko daman ta san shi daman tun farko?


"Wallahi bata san shi ba, ta ce min zata neme sa."


"?arya ne, wannan ?arya ne wallahi!. Ta tafi yin wani abinda daban a ?asar waje kawai, amma ba wannan tatsuniyar ba."


"Wallahi ba tatsuniya bace, gaskiya ce maganar nan ba ?arya ba. Wannan dalilin da na faWa muku shine ya saka ta tafiya."

Saleem ya ce, "Shikenan munji haka ne, ta ya zata biya shi in bata san shi ba?."

Safeera ta ce, "wallahi bata san shi ba."

Sadik ya Waga mata hannu ya ce, "Ki daina yin rantsuwa Safeera, rantsuwa akan ?arya bata kamace ki ba. Abu ne guda biyu, ko ke da ?awar ki kuna raina mana hankali, ko kuma ?awar ki ta haWa har ke ta rainawa hankali.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login