Showing 69001 words to 72000 words out of 221574 words

Chapter 24 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

157

ake yafawa ta rufe gashinta, ta saka room slippera kalar kayan tana tunanin ta yadda zata fita.

Kallon kanta take yi, kayan sam basu kamata jikin ba amma sun yi mata kyau sosai, ta fito sak a ?ar aiki.

Ta lock key Win da ta sakawa ?ofar, ta fito a hankali tana takawa a hankali kamar bata.

Falon da suka bari ta ?araso, sai ta ga babu kowa sai a.c da take aikinta. Islaha sai ta tuna da yanayinta, tana bu?atar saka facemask gudun samun matsala. Ta juya zata Wauko facemask suka yi karo da mutum.

Islaha ta tsorata sosai, ya bita da kallo ganin ta shirya cikin kayan kamar yadda ya ce, kafin ya yi murmusui ya ce, "where are you going?."

Muryarta tana rawa, "I'm going to get my face mask."

Ya girgiza kai ya ce, "You don't have to wear it, you're very beautiful" ya faWa yana shafa kumatunta.

Da hanzari taja baya gabanta yana faWuwa sosai, ta ce, "I have asthma, so I need it because of the cold" ta faWa muryarta tana cracking ganin yana ta kallon ta. Ya Wan bata hanya alamun ta wuce, a guje ta koma Waki ta rufe ?ifar tana sauke nunfashi.

Sai kuma ta Wora hannu a kanta ta ce, "na shiga uku!."

Knocking ?ofar taji ana yi, da hanzari ta Wauki face mask Win ta saka, tana buWe ?ofar suka haWa ido da balarabiya fara kyakykawa sanye da uniform irin nata.

Islaha bata san ta yiajiyar zuciyar ba, dan a tunaninta Maleek Win ne ya dawo yana ?wan?wasa ?ofar.

Cikin larabci ta mi?awa Islaha hannu ta ce, "barka da zuwa Jeddah. Sunana Sunaira."

Islaha kwata-kwata bata ji me tace ba, ta dai ji ta ce Sunaira. Sunaira ganin Islaha bata gane ba sai ta kuma mi?o mata hannu.

Islaha ta bata hannu suka gaisa ta ce, "Islaha."

Ta yi murmushi ta ce, "ki zo zan nuna miki kitchen."

Islaha bata ji me tace ba ya saka ta ce, "i'm sorry, no arabic."

Itama ta Wan yi murmushi cikin ?aramin ingilishinta ta ce, "No english." Islaha ta Wan murmusa suka fito tare.


A falon farko a nan kitchen Win yake, suka shiga ita dai Islaha kallon kitchen Win take yi saboda girmansa. Daga nan ta nuna mata Wakin wanki wanda aka tanadi komai na wanki a cikinsa.

Suka dawo kitchen Win Sunaira ta Wauki wayarta ta shiga google ta yi rubutun arabic to english ta haskawa Islaha wayar. Islaha ta karanta ta Waga kai suka fara haWa coffee.

Islaha ce ta Wauki tray Win zuwa falon da tayi mata kwantancen nan zata kai.

Da sallama ta tura glass door Win ta shiga, daga ciki taji ya amsa sallamar, ta ?arasa tana kallon ?asa har ta ajjiye masa a kan table bata kalle sa ba.

Maleek ya ajjiye wayar hannunsa ya kalle ta ya ce, "what is your name?."

Islaha tana daga tsaye ta ce, "Islaha."

Maleek ya bita da kallo jin sunan mai daWi, kafin ya maimaita ya ce, "Islaha!."

Ta Waga kai alamum eh, ya murmusa ya ce, "from which state in Nigeria?."

Islaha ta ce, "Adamawa state."

Ya Wan bita da kallo kafin ya ce, "Fulani?." Da mamaki ta kalle sa suka haWa ido, sai ta Waga kai alamun eh.

"Wow! I have a friend from Adamawa state, but his skin color is not the same as yours. Why do you look like this?."

Ta yi shiru bata ce komai ba, ya kalle ta ya ce, "You look so beautiful. Why do you look even better than him?."

Islaha nan ma ta yi shiru bata ce komai ba, dan bata ce komai ba, wannan iyayin nasa ya fara isar ta wallahi. Maleek ya Wan Waga kai ya ce, "well, you looks so beautiful. I like your skin type."

Islaha a gajiye take hakan ya saka ta ce, "thank you."

Ya nuna mata hanya ya ce, "you can go."

Kamar an saka ta a aljanna haka taji, ta yi saurin barin wajan ta koma Wakin da aka ajjiye ta. Uniform Win ta fincike ta canja kaya ta kwanta tana ji kamar ana sassara jikinta saboda gajiya.

Labiba suna shiga Wakin da aka ajjiye ta taga tangamemen Waki mai kyau da tsari kamar ba na mai aiki ba, ta buWe ido tana juyi a Wakin ta ce, "sabuwar duniya."

Matar da take bayanta ta yi darita ta ce, "ki ka shigo cikinta."

Da hanzari ta juyo tana kallonta jin tana hausa, Labiba da mamaki ta ce, "Daman kina jin hausa har haka?."

Tayi dariya ta ce, "Sunan Aisha, kefa?."

"Labiba sunana. Amma na yi mamaki da na ji kina hausa a ?asar nan."


"Ni ?ar Niger ce, kuma na yi zaman nigeria."


"Kai amma na ji daWin haWuwa dake a gidan nan sosai. Naji daWi dana samu wacce take jin hausa."

Aisha ta yi murmushi ta ce, "nima na samu ?awa. Ki shiga kiyi wanka ki fito ki shirya, kin san gidaje irin wannan ba a zama haka. Sai kin jure, zaki sha wahalar aiki, dan wallahi ba a hutawa."

Labiba ta ce, "daman shi ya kawo ni ai, kuWi nazo nema, dan haka ko meye bazai dame ni ba."

Aisha ta yi dariya ta ce, "da alama kan ki a waye yake Labiba, da wuri zaki tara kuWi a gidan nan. Ki shig??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a kiyi wankan zan jira ki."

Aisha ta fasawa Labiba kai jin ta ce a waye take, cikin iyayi ta ?arasa banWaki ana yanga ita lallai wayayayyi.

Aisha ta bita da kallo tana murmushi, ta girgiza kai ta ce, "Sannu da zuwa gidan Ubaid, gidan kuWi kuma gidan jin daWi, gidan nasara kuma gidan rashinta, gidan fantamawa gidan morewa." Ta yi yar ?aramar dariya ta juya ta fita ta bar mata Wakin.

Labiba bata jima ba ta fito, taga an ajjiye nata uniform irin na jikin Aisha, ta Wauka ta saka tana kallon kanta dan ita kanta ta san ta yi kyau.

A lokacin Aisha ta dawo ta bita da kallo tana murmusji ta ce, "kim yi kyau sosai. Kin karanta tsarin gidan nan dai ko?."

Labiba ta ce, "ni saka hannu kawai na yi, ban wani duba soaai ba."


"Lallai kam sannun ki. To babu sata, babu gulma, babu yawo waje barkatai. In ki ka saSa kaWan daga cikin rules Win gidan nan za a iya kama ki. In mun fita zan baki takardar ki sake dubawa dan ki kiyaye dakyau. Mu je na nuna miki inda ya kamata, sannan sai kizo ki Wan huta na Wan lokaci."

Tare suka fito daga Wakin tana nuna mata duk inda ya kamata ta sani, zuciyar Labina fari ?al ganin gida irin wanda take mafarki, gida kamar ba a duniya ba, ga abokiyar aiki ?ar nigeria.

Ta kusa da Ubaid da yake zaune yana danna laptop suka zo wucewa, ya Waga ido ya kalli Labiba ya ganta ta yi kyau a cikin shigar da ta yi, ta yi kyau cikin kayan kamar ka sace ta ka gudu.

Da hannu ya yi musu alamun da suzo, suka nutsu suka ?arasiSo wajen suka tsaya cikin girmamawa..

Suna zuwa ya bi Labiba da shegen kallon up and down ya ce, "ya sunan ki?."

Labiba ta ce, "Labiba."

Ya Wan yi jim ya ce, "Habiba?."

Ta girgiza kai ta ce, "Labiba."

Ya Wan Waga kai ya ce, "from nigeri, right?." Ta Waga masa kai alamun eh tana kallonsa.

Da hannu ya yi mata alamun ta tafi, ta mi?e tana tafiya ya bita da kallo yana shafa kansa, ya girgiza kai don tayi daidai da tsarinsa sosai.


" " " " " "

Tunda ya dawo daga wajan aiki yana tsaye ransa a Sace, ya tsani ya dawo daga wajan aiki kuma ya tsaya neman wani abun da zai sha da kansa, yafi son da ya dawo a kawo masa komai baya son Sata lokaci.

Ya sauke numfashi, dan cikin kwana biyu cleaners ya ke Waukowa su zo su gyara masa gidan, dan shi baya so a haWa shara da girki, ya fi son chef daban cleaners daban.

Ya ja tsaki ya Wauki waya ya kira Jazy, yana Wauka ya ce, "Jazy meyasa wai ka sallami housemaids Win gidan nan? Kana neman haukata ni, ina zan saka raina ne?."

Jin Rehaam yana faWa abinda ba sabon sa ba sai ya bawa Jazy mamaki ya ce, "me ya faru?."

"Na dawo daga aiki, ina bu?atar sha tea amma babu kowa a gidan nan. Waye zai bani?."

"Ka yi order ko ka fita kasha"

"baka da hankali Jafar, ki fi kowa sanin ina son abu bana son Sata lokaci ko?."

Jafar ya ce, "yanzu ya zan yi maka? Ni ka ke so na zama maid nazo ina yi maka aiki, ko kuma daga nan zan turo maka mai aikin gida?. Ina cleaners Win da suke zuwa yi maka aikin gidan?."

"Cleaner chef ne?."

Jazy ya Wan yi shiru kafin ya ce, "Okay ka yiwa Maleek ko Ubaid magana mana, na san akwai housemaids a gidansu sosai, sai a baka Waya."

Ya Wan girgiza kai ya ce, "mun yi magana da Maleek, but bai ce min komai ba har yanzu. Kuma ni permanent nake so, bana son sharing chef, bana so na dawo ina son wani abun ace sai na jira."

"Mr Rehaan samu housemaids ko chef a Jeddah bazai yi maka wahala ba, ka bincika zaka samu. Gidan Maleek ko Ubaid mata ne, kai kuma ka fi son maza."

"Ina son matan, indai za a samu."

"Lallai ka ji uwar bari, sai ka san yadda zaka yi."

Ray ya ja tsaki ya kashe wayar cike da takaicin Jazy.

Ya dafe kai, shi babu abinda ya iya dafawa balle ya ce zai je dafa, tea kwai ya iya shima a dafa ruwa zafi a saka lipton da sugar shine abinda ya iya. Komai yi masa ake yi, ta ya zai juri ko yaushe in ya dawo shi zai dafa abinda zai ci ko sai ya tsaya a hanya, ko sai ya jira rider ya kawo masa?."

A Englaand suna da housemaid Win da yake musu girki ko yaushe, cleaner kuma kullum ana zuwa sau uku ko huWu ana gyara inda suka Sata shiyasa bai iya yin komai ba.

Daman Jazy ne mai ?o?arin girki, da yana nan da bashi da matsalar abinci ko matsalar abin sha ko wani abun.

Ya Wan yi tsaki yana neman number Maleek, dan ba kasafai ya cika sakewa da Ubaid ba, rawar kan Ubaid ya yi yawa, ya fi son shiri da Maleek dan yana da nutsuwa akan Ubaid.

Ya kira number Maleek yana fatan Allah ya sa a samu housemaid Win da za a tura masa a take su zo su fara yi masa aiki, bai damu da mace ko namiji ba, ko ma waye yana maraba dasu. Tunda nema yake bashi da zaSi, amma da a gida ne baya haWa hanya da housemaid mata, ya fi son maza su yi masa komai.


Kuna Maleek zai ba da Islaha kuwa?
Ina labarin Hajiya Umma?
Labiba fa?

Mu je zuwa>?-?=؃? [7/1, 1:08/ PM] KRBBK: RD2P30
Nana Haleema.

*MADINA*
*AL KHALIDIYYAH AREA.*

Umma tunda aka gama gabatar da ita ga mutanen gidan take a gantale a falon gidan, tana kallon falon sanyin a.c yana ratsa ?asusuwanta. Dan sanyin ba Wan kaWan bane, sanyi ne mai yawa wanda ya fi ?arfinta.

Falon yana da girma da manyan kujeru masu girma, ga wani ?aton dining table mai guda ashirin, alamun iyalai gidan suna da yawa ba na yara ba.

Ga wasu ?ofofi a falon wanda bata san na meye ba, ga ?atuwar tv, komai na falon ya yi yadda ya kamata.

Umma dai tana zaune ga yunwa ga gajiya, sanyin duk ya dame ta kuma ba a bata wajan zama ba balle ta shiga ta zauna.

Wata balarabiyar budurwa ce ta fito daga Waki, ta bi Umma da kallo kafin ta ?walawa Mamanta kira cikin harshensu ta ce, "Mama Wannan ba?uwar a ina zata zauna?."

Daga ciki ta ji muryar babar cikin harshen su uwar ta ce, "ki raka ta Wakin ba?i ta ajjiye kayanta."

Ta kalli Mama ta ce, "Mu je."

Umma bata fahimta ba, ita dai taga tana kallon ta kuma tana yi mata magana, amma bata san me take faWa ba. Yarinyar ta yiwa Umma nuni, hakan ya saka ta mi?e ta ta bi bayanta tana sake kallon ko ina na falon.

?aki ne madaidaici da komai a cikin sa, Umma ta shiga tana ajjiye kayanta gana kallon Wakin cikin wani irin yanayi mara daWi.

Umma ta zauna a gefen gado tana kallon Wakin, sai kuma ta mi?e tana kallon ?ofar tana tunanin banWaki ne, ta buWe tana kallon banWakin kafin ta shiga ta yi wanka.

Tana fitowa taga yarinyar nan a tsaye a Wakin tana kallon Wakin. Umma tana fitowa ta bita da kallo kafin ta yi mata alama da tazo da hannunta.

Umma ta canja kaya a gajiye, ta yi tunanin za a barta ta huta amma sai ta ga akasin haka. Ta fito tana takawa a hankali dan ta gaji sosai ma kuwa.

Tana fitowa ta ga mutane harr a falon manya da yara, kowa ya zuba mata ido yana ?are mata kallo kamar sun ga wata mujiya.

Iyayen gidan tana kallonsu ta san sune iyaye, uwa da uban suna zaune a waje Waya, sai sauran yaran duk mata ne da namiji Waya, suna zaune sun yi kaca-kaca da wajan suna ciye ciye kamar ba manya ba.

Umma tana fitowa matar ta kalle ta tayi mata nuni da ta kwashe kayan wajan. Umma a sanyaye ta du?a ta fara kwashe kayan, aka nuna mata kitchen ta kai ta ajjiye.

Tana fitowa yarinyar cikinsu ta zubar da lemo a kan tiles har kan carpet. Aka Wauko abinda gyara waje aka bawa Umma ta goge tiles Win, aka bata ?ramin towel alamun ta goge wajan ta du?a tana gogewa.

Tana gamawa aka nuna mata wata yarinya, ita dai ta kalli yarinyar amma bata san me ake faWa ba.Cikin tsawa matar take yiwa Umma Magana, duk ta ruWata dan ta kasa gane me take nufi balle ta yi.

A lokacin aka buWe ?ofar aka shigo, matar gidan ta kalli wacce ta shigo ta hauta da bala'i ita dai Umma ta yi shiru bata san me suke faWa ba.

Hajiya Shafa da aka dam?a Umma a hannunta ta kalli Umma da ta yi tsuru-tsuru ta ce, "ki ri?e yarinyar ki yi mata wanka, wannan matar bala'i ne da ita sai kin yi da gaske, in ba haka ba tsaf zata dake ki wallahi."

Da mamaki Umma ta ce, "Duka kuma?."

"Kina mamaki kenan? Lallai baki san larabawa ba. Ki ri?e yarinyar nan ki je ki wanke ta."

Umma ta ri?e hannun yarinyar ta ce, "ina ne wajen wankan?."

Hajiya Shafa ta ce, "mu je na nuna miki." Tare suka tafi yarinyar tana turjewa tana ?walla ihu, duk ta cika musu kunne da magana.

Hajiya Shafa ta kalli Umma ta ce, "ki Wauke ta, basa jurar Wansu yana kuka fa, a kan haka zaku Sata dasu wallahi."

Umma ta kalli yarinyar ta ga a ta?aice zata yi shekara goma, sannan gata lukuta ce, ta kalli Hajiya Shafa ta ce, "ta ya zan iya Waukar yarinyar nan, kalle ta fa?."

"Haka zaki gwada, in wacce ta fita aka ce ki Wauka haka zaki Wauka. Kamar baiwa ki ke a gidansu, ko taka ki suka yi suka wuce haka zaki yi ha?uri." Umma ta duka ta Wauki yarinyar da?yar tana hakki.

?akin yaran ta raka ta, suna shiga ta gansa kaca-kaca, an ci abubuwa an watsar ga toys an zubar kamar Wakin mahaukata.

Hajiya Shafa ta ce, "gashi nan, kije kiyi mata wanka sai ki saka mata kaya. Sannan ki gyara waWannan kayan da suka watsar. Maimuna kwana da sanin baza ki yi bacci ba, domin kuwa zasu je makaranta."

Umma ta kalle ta cikin firgici ta ce, "Baiwar Allah zuwa na kenan fa, ko hutawa ban yi ba, ko Wan abinci ban ci ba balle bacci. Wallahi ?afafuna a gajiye suke, zaman motar nan gabaWaya ya sagar min da ?afafu. Tun safe muka taso, aka samu matsalar mota muka kwana a hanya, yanzu gashi har gari ya yi haske. Kuma ace bazan kwanta ba? In ban kwanta ba ai sai na faWi."

Hajiya Shafa ta bi Umma da kallo ta ce, "aiki kika zo yi ai ba hutu ba, kar ma ki saka a ranki wai zaki huta a gidan nan, wallahi aiki zaki zage ki yi kamar jaka, dan kaf aikin gidan nan a kan ki yake, ga kula da yaransu. Su basu san uzuri ba, kuma basu san Sata lokaci ba, in suna so sai an yi kawai babu na gaji."

Umma ta sauke numfashi tana jinjina kai ta ce, "to bara na yi mata wankan."

Hajiya Shafa ta ce, "ya fi miki dai. Sunana Shafa, ni ce waccce suka faWawa suna neman mai aiki a kawo musu, ni kuma na faWawa Oga Musa, shi kuma ya saka aka nemo ki. Duk abinda zaki aikata a gidan nan ni zasu nema su faWawa, dan haka ko rufa min asiri ki zauna dasu lafiya, bana so a Waga min hankali."

Umma ta shiga banWakin tana kallon banWakin, yarinyar ta ?arasa cikin bathtub ta kunna ruwa alamun a ciki ake yi mata wankan.

Umma bata tsaya ?arewa banWakin kallo ba, dan a gajiye take matu?a tana so ta huta. Ta kunna ruwa ya fara zuwa sai yarinya ta ?walla ?ara mai ?arfi.

Umma ta firgita ta taSa ruwan dan ta Wauka ?onata ta yi, saita ji ruwan sanyi ne kuma bai yi sanyin da zata yi wannan ?arar ba.

Kafin ta tsayar da ?arar har an shigo banWakin, da uwar da uban da yayyenta duk sun hallara an nufe ta ana tambayar abinda ya faru.

Tana gani yarinyar tana faWa musu ita dai tana tsaye bata san me ake cewa ba. Matar gidan ta juyo tana yiwa Umma bala'in da bata san me take faWa ba, ta dai zuba masa ido tana kallo bata fahimci ko kalma Waya ba.

A lokacin Shafa ta shigo, suka koma kan Shafa suna faWa mata itama tana mayarwa. Suka fito da ?ar tasu daga ciki suka fita da ita.

Shafa ta bi Umma da kallo ta ce, "Na faWa miki wallahi Allah ba a taSa musu yaransu, ba a taSa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login