Showing 51001 words to 54000 words out of 221574 words

Chapter 18 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

148

yau gata wai itace da kanta ta kashe kuWi ta yi fasko har ta kawo a tafi da ita. Kai lamarin nan ya yi min daWi sosai."

Hajiya Karima ta ce, "nima ya buge ni, na yi mamaki sosai da ta sakko cikin sau?i haka. Kin ga wannan gidan, da kuWin aikin sai yadda muka yi dashi."

"Ga mai gidan daman babu lafiya, har islaha ta tafi ba sani zai yi ba balle ya Waga min hankali. Ssheer ma barin gari zai yi, su je can su ?arata ni na tura ta inda zan samu."

"Amma fa lamarin nan ya Waure min kai, meye sakko da ita haka?."

Cikin rashin damuwa Mama ta ce, "koma meye wannan ita ta ga zata iya, ni dai taje ta samo min kuWi kawai shine burina."

Karima ta ce, "Kai amma za a yi rububin yarinyar nan, dan Oga Musa ya faWa min akwai fararen fatar da suke son mata irin Islaha, dan gidan da yake magana a kai yace mai gidan irin fatar Islaha yake so, da ta je zai Wauka. Yarinya ga shegen kyau da gashi, ga kalar fatar ta abin kallo ko baka yi niya ba...."

Hajiya Karima ta yi dariya ta ce, "Inda zata bi ?ananun hanyoyin da ake da wuri zata zama Hajiya wallahi."

Mams ta ce, "nifa daman burina kar gidan nan na Jedda ya wuce mu, kuma tunda an samu mun gode Allah, sai a cigaba da shagali kawai."

Karima ta ce, "Ki ji fa, wai ita aikin shekara Waya take so ta dawo. Shashasha, bata san in ta shiga sai Allah ya fito da ita ba."

Mama cikin dariya ta ce, "Ai basu san roman baka ba." Suka tafa suna dariya, suka cigaba da tattauna yadda lamarin zai kasance.

Islaha haka ta shiga Waki jiki a sanyaye, zuciyarta a cushe take akan abinda ta aikata, wani abu take ji ya tokare mata zuciyarta.? Ta san ba daidai ta aikata ba amma hakan shine kawai mafitar ta, bata da mafita da inda zata samu kuWi ta sauke nauyin da yake kanta sai hakan.

Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Allah ka kawo min sau?i cikin lamarin nan, Allah ka bani abinda zan iya, Allah ka bani abinda zan iya Wauka, dan darajar ka. Ya Allah ka bani ?addara mai sanyi, ka kaini hannu na gari, ka bani ikon kiyaye mutuncina a duk inda nake. Allah ka yaye min gagagwa da aikata abu a cikinta, ka bani ikon yin tunani mai zurfi kafin na aikata, amin."

Ta zauna a gefen gadon, sai kuma ta mi?e tsaye dan tana bu?atar magana da Safeera, tana so ta faWa mata abinda yake faruwa amma bata son tayar mata da hankali, bata so ta ji labarin har an yiwa Umma visa fita ?asar waje.

Ta tabbatar Safeera bata sani ba, dan da ace ta sani da tuni ta bata labari abubuwan da suka faru akan hakan. Ta yi ajiyar zuciya, duk da haka tana da bu?atar yin magana da Safeera da kuma Sadik, dole ta yi magana dasu ko dan abinda zai faru bayan tafiyarta, bata so Saheer ya san zata bar ?asar sai bayan ta bari. In ta je can kome zai faru zata iya jurewa, kuma zata rarrashe shi har ya ha?ura ya fahimce ta.

Ta sauke numfashi tana lumshe ido, tunda bata da iyayen da zasu saka ta ko hana ta, gwara ta yi abinda take ganin shine ya dace da halin da take ciki.

Islaha a Jeddah
Rehaan a Jeddah>?-?d'?
=?%?
[6/26, 12:30/ PM] KRBBK: RDB2P22
Nana Haleema

Da sallama Umma ta shiga wajan Baba da yake zaune, ya amsa yana kallon ta har ta ?araso ta zauna. Umma ta Wan kalli Baba ta ce, "ina son nayi magana da kai."

Baba ya Wan kalle ta sannan ya ce, "ina jin ki."

Umma ta ce, "akan batun tafiyata ?asar waje ne, daman...." Kafin ta ?arasa ya Wago ya kalle ta sai ta kasa ?arasawa ta yi shiru.

Baba bai ce komai ba ya cigaba da abinda yake yi, ganin bai yi magana ba sai Umma ta ce, "tafiyar tana matsowa, shine na ce..." nan ma bata ?arasa ba ya Waga kai ya kalle ta.

Baba ya ajjiye abinda yake hannunsa ya ce, "shine me?."

Umma ta yi shiru bata ce komai ba, duk da ?arfin guiwar da take ji kafin tazo, yanzu da take gabansa sai ta ji tayi sanyi ta kasa magana. Sai take jin nauyin faWa masa har an buga mata visa an yi ticket, bakinta sai ya sar?e ta kasa faWar abinda zata ce.

Baba ya ce, "na faWa miki hukunci na akan maganar nan, indai ki ka amince da tafiya ?asar waje to ki tabbatar babu aurena a kan ki."

Umma da mamaki take kallonsa ta ce, "wai da gaske zaka iya sakina? ?a?a huWu ne a tsakanina da kai, kuma dukkansu mata ne. Yanzu sai ka sake ni saboda wannan ?aramar matsalar?."

Baba ya mi?e tsaye ya ce, "indai zaki iya tsallake su ki tafi wata ?asa saboda neman duniya, ina so na faWa miki nima zan iya rabuwa dake. Kuma ina kan bakata wallahi, indai ki ka zaSi barin yaran ki nima zan zaSi barin ki. Baza ki bar nigeria da aurena a kan ki ba, gwara ki tafi babu nauyin kowa kema zaki fi jin daWi" yana gama faWar haka ya mike ya fita daga falon.

Umma ta mi?e tsaye ta ce, "tabWijam! Wallahi bazai yu ba, dole na je ?asar nan na samo kuWin da mata suke samowa. Da gaskiyar woman leader, indai zaka biyewa namiji zaka ?are a wahala da takaicin rayuwa. Yanzu dubi baban Safeera, me yake tsinana min da har zai hana ni tafiya neman na kaina?. Ai wallahi tunda na yi niya sai na je, bazan zauna a nan talauci ya kashe ni ba."

Sai kuma ta sauke numfashi tana kama ?ugu ta ce, "amma bana son auren nan ya rabu, auren shekara ashirin da tara zai rabu saboda haka? Kuma sai da yara duk suka girma sannan hakan zai faru?."

Ta dafe kai cikin damuwa ta furzar da iska waje ta Wauki waya ta kira ?anwarta. Tana Wauka ta ce, "Atika ina cikin matsala wallahi, Babansu Safeera ya sake tabbatar min da indai na tafi sai ya sake ni."

Daga can Sangaren Atika ta ce, "to meye abin damuwa? In ya sake ki ai ba wani abun ne zai faru ba, ?a?a dai ?a?anki ne, kuma zaki je ki samo kuWin aurar dasu ne tunda dukkansu mata ne. ?an mata uku ne a gabanki, a cire batun autar ki ita bata kai su girma ba, amma Safeera da ?annenta duk sun isa aure. In ki ka zauna da me zaki aurar dasu?."

Umma ta ce, "shine tunanina Atika, amma bana son rabuwar auren nan wallahi. Ace aure shekara da shekaru zai rabu saboda tafiya ?asar waje aiki? Kuma sai da yara suka girma, duk sun san meye aure da rabuwarsa sannan zai faru? Abin akwai nauyi Atika."


"meye dan ya sake ki, in ya sake ki ba sai ki sake wani auren ba?."

"Haba Atika, da tsufana, ina shirin aurar da ?a kuma ki ce nayi wani auren?."

"To a kan ki aka fara? Kin ga Maimuna, Kar wannan ya dakusar dake, nima harkar nake so dan bazan samu dama bane shiyasa zan yi ha?uri, amma ke tunda kin samu kar ki yi wasa da ita."

"In ya kira Yayana na Katsina ya faWa masa fa?."

"To ina ruwansa? Zai hanaki abinda ki ka yi niya ne?."

Umma ta ce, "shikenan dai, ina zuwa" ta faWa tana kashe wayar cikin tunani.

Baba ko da ya fita a ?ofar gida ya tsaya cike da tunani, ya san halin matarsa tsaf zata iya tsalleke auren ta tafi. In hakan ya faru bazai ji daWi ba, bazai taSa jin daWi ta tafi ta bar yaranss a gantale ba tare da uwa ba. Shi mutum ne mai Wan tafiye-tafiye neman na abinci, in ta saka ?afa ta tafi in zai yi tafiya da wa zai bar ?a?ansa mata?.

Ya yi ajiyar zuciya, ya saka hannu aljihu ya Wauko waya ya kira Yayanta na Katsina dan ya sanar dashi halin da ake ciki, da farko ya Wauka ta bar maganar shiyasa bai saka magabatanta a ciki ba, amma ya ga alama yanzu dole ya saka makusantata a maganar.

Basu jima suna wayar ba ya sauke wayar ya cigaba da tsayuwa a wajan har mota ta tsaya a kusa dashi.

Aka fito daga motar, mutumin ya ?araso kusa da Baba da fara'a Baba ya ce, "Ashe kana cikin garin na mu."

Alhaji Yakub ya ce, "na shigo garin jiya, kuma na yi niyar na shigo mu gaisa sai ga wayar ka, shine na ce ai ko ban yi niya ba ya kamata ace nazo."

Baba ya ce, "barka da zuwa."

"Barka dai. Ka yi ha?uri, ban san abinda yake fatuwa ba kenan, ai da na yiwa tufkar hanci."


"Mu ?arasa ciki." Bai musa ba suka shiga cikin gidan da sallama.

Umma da fitowar ta tsakar gida kenan ta ji sallar tasu su ta amsa tana kallon su, gabanta ya yanke ya faWi ganin Yayanta da kuma mijinta.

Cikin ya?e da faWuwar gaba ta ce, "Yaya Sannu da zuwa."

Ya yi murmushi ya ce, "Yauwa sannun ki." Ta nuna masa falo ta ce, "Yaya mu shiga ciki." Suka shiga shida Baba ita kuma ta dafe ?irji tana ajiyar zuciya.

Da?yar ta Wauko faranti ta Wora masa pure water guda biyu, ta koma kitchen ta Wauko ?aramin flakass wanda ta zuba kunu tun na safe da kofi ta shiga da sallama.

Suka amsa ta ajjiyewa Yaya ta ce, "Yaya ban san zaka zo ba, da na yi maka tanadi na musamman" ta faWa tana zama da murmushi.

Yaya ya ce, "jiya nazo, daman kuma nayi niyar na shigo mu gaisa, sai yanzu Allah ya yi na ?araso."

Ta dur?usa har ?asa ta ce, "Ina yini."

"Lafiya lau, ya gida ya yara?."

"Alhamdu lilah. Ya mutanen Katsina?."

"Kowa lafiya lau. Da nace musu in na zo Yola zanzo mu gaisa sun ce duk a gaishe ku."

"Muna amsawa."

"ina Safeera da ?annenta?."

Umma ta ce, "duk suna islamiyya. Safeera kuma tana wajan aiki."

Yaya ya ce, "ma sha Allah! Allah ya taimaka."

"Amin Yaya."

"Yaushe ne bikin Safeera ne?."

"Ba a saka lokaci ba har yanzu, Yaron yana aiki ne."

"Gwara haka, gwara ya yi komai a nutse. Allah ya kaimu lokacin."

"Amin Yaya. Ga kunu na kawo maka ka sha, bara na kawo abinci" ta faWa tana mi?ewa.

Yaya ya ce, "yi zaman ki, kunun dai zan sha, abinci kam na ?oshi."

"Ka dai ci har abincin."

Baba ma ya ce, "ya kamata dai ka ci wani abun."

Yaya ya ce, "wallahi a ?oshe nake, zan dai sha kunun tunda daman ina sonsa." Umma ta yi murmushi bata ce komai ba, ?irjinta yana dukan goma goma.

Yaya sai da ya sha ruwa sannan ya kalle ta ya ce, "Maimuna!."

Gaban Umma ya yanke ya faWi, ta Waga kai ta kalle sa ta ce, "Naam Yaya."

Ya gyara zama ya ce, "Meye matsalar ki? Me ki ka nema ki ka rasa a cikin gidan nan?."

Umma ta sauke numfashi kanta yana ?asa ta ce, "babu komai."

Yaya ya ce, "A'a akwai, ki faWa min abinda yake damun ki, ina ji." Umma ta yi shiru bata amsa ba, dan bata san me zata ce masa ba.

Alhaji Yakub ya haWe mata rai ya ce, "magama nake yi miki, me yake damun ki?."

Umma ta ce,"babu komai."

Ya girgiza kai ya ce, "da girman ki, da shekarun ki, da ?a?an mata duk sun kai munzalin aure, ke da kanki kike so ki tsallake su ki bar ?asa saboda abin duniya Maimuna?."

_Shikenan, ta faru ta ?are._

Umma ta faWa a zuciyarta, cike da jin haushi da takaici, dan ta san tunda mutanen Katsina suka ji maganar ta shiga uku.

Alhaji Yakub ya ce, "Wallahi ko a mafarki ban yi tunanin zaki aikata wannan Wanyen aikin har haka ba, ban yi tunanin shirmen ki da rashin girman naki ya kai haka ba sai yanzu. Ke yanzu za ki iya Waukar ?afa ki bar ?asa, ki bar mijin ki da ?a?an ki saboda duniya don Allah?."

Umma ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, dan ta san bazai taSa bata damar magana ba, ko ta faWa bazai fahimce ta ba ko kaWan.

Cikin faWa ya ce, "dan tsabar shirme da neman duniya? Ki rufe ido ki Wauki ?afa ki tafi wata ?asa ki bar yaran ?an mata a Nigeria, in ba shirme da rashin hankali me meye amfanin wannan?."

Nan ma bata tanka ba ya ce, "kin rasa ci da sha a gidan nan?."

Ta girgiza kai alamun a'a ya ce, "faWa min dalilin ki na tafiya, faWa min dalili mai ?arfi da ya saka ki ke son barin ?asar nan ki tafi aiki wata ?asa."

Umma ta kasa cewa komai, dan duk da Baba bashi da kuWi amma yana ?o?arin ganin ya tsare musu komai na rayuwa. Ilimi, abinci, suttura da sauransu duk basu rasa a gidan ba, in ta faWi wani abu makamanincin haka ta yi masa ?arya.

Ya ce, "ina jin ki."

Umma ta ce, "babu komai."

"Haka kawai ki ke neman Sata rayuwar ki, da girman ki da shekarun ki kike son mayar da kan ki baya?. Abinda baki yi da kina ?arama ba, shi zaki yi yanzu da ki ka isa ajjiye jika? Kar ki manta, an saka kawo kuWin auren ?arki Safeera, ko kunyar hakan bakya ji za ki saka wannan shirmen da ya zama ruwan dare a zuciyar ki?."

Umma ta ce, "Yaya da farko ban yi niyar zuwa ba, sai da na faWa masa ya ?yale Safeera ta je amma sai ya ce indai shi ya haife ta wallahi bazata je."


"To faWa miki aka yi shi mahaukaci ne irin ki? Ko an faWa miki bai san abinda yake yi ba kamar yadda baki sani ba?. Haka kawai ki Wauki yariya budurwa ki sahale mata ta tafi wata ?asa aiki? Ba tare da kin san da wa ki ka haWata ba, baki san a ina zata sauka ba, baki san a hannun wa zata zauna ba? Kedai kawai ta je ta samo miki kuWin da baki san ta hanyar da za a samu ba ko?."

Umma ta kalle sa ta ce, "Aiki ne fa kawai Yaya, aikin gida ne irin na gidan larabawa ko gidan turawa, ba wani abu ake aikatawa a can ba."

Ya yi shiru kawai yana kallon ta bai ce komai ba dan bai san me zai ce ba, dan shima ya ga lamarin nata da gaske take ba da wasa ba.

Jin ya yi shiru sai ta Wago ta kalle sa taga ita yake kallo, ta sunkuyar da kai sai kuma ya ce, "Mahaifi. Safeera ya hanata zuwa ne saboda ya isa da ita, tunda shine ya haife ta babu mai iko da ita kamar sa."

"Ni kuma Yayanki ne, na girme miki da shekaru masu yawa, iyayenmu basu da rai, dan haka ni ne uba a gare ni. Dan haka nima na hana ki zuwa saboda na isa dake, zan gani in na isa dake in ban isa dake ba."

"Banda lalacewa da shirme, da girmanki da shekarun ki zaki Wauki ?afa ki ta fi wata ?asa aikin gida? Anya kina da hankali kuwa?."

Baba dai yana zaune ya yi shiru bai ce komai ba, Yaya ya kalle sa ya ce, "Anya tana da hankali?."

Baba ya Wan murmusa ya ce, "tana da hankali, kawai wani abun ne ya rufe mata ido."


"A'a, mai hankali bazai aikata abinda take aikatawa ba. In da ace tana da hankali baza ta yi kwatankwacin wannan shirmen ba. Tafiya aiki fa take tunanin yi wani waje, ba cikin yola ko cikin nigeria ba, jirgi zata hau ta bar ?asa. Kuma wai ita irin huce haushin nan zata yi, wato an hana Safeera tafiya ita bara ta je da kanta, tunda kaine ka haifi Safeera kuma ka hanata zuwa, to ita ai baka haife ta ba. Abinda take nufi kenan, shiyasa take wannan maganar."

Baba dai ya yi murmushi kawai bai ce komai ba, dan kuwa haka Umman ta faWa masa, Safeera ya haifa ba ita ba.

Yaya ya ce, "in ban da lalacewa ma, ?asa kamar Nigeria amma ace wai matan cikinta ne suke fita su tafi wata ?asashen larabawa yin aikii kamar wasu gantallalun mutane?. Tsakani da Allah wanne farar fatar ne ya taSa zuwa nigeria yake aikin wanke-wanke da shara a gidan ba?a?e fata ?an Nigeria?."

Baba ya ce, "babu."

"Amma mu mun mayar da kan mu baya, babu abinda ?asashensu suka fi mu dashi, dan dai kawai lalacewa irin ta ?asar ta mu, an Wauki hakan a matsayin ba komai bane."

Ya juyo ya kalle ta ya ce, "Ahir Maimuna! Kar na ji kar na gani, kar na sake jin wannan maganar mai kama da wasan yara. Ki adana wannan shirmen a gefe, ki cire shi daga ranki ki kalli gaban ki. Wallahi in n kuma jin wata magana makamanciyar wannan sai na Sata miki rai. Kin ji ko?."

Umma ta Waga kai ta ce, "na ji."

"Yauwa, maganar ta tsaya iya haka, maganar ta ?are a iya falon nan, maganar ta tsaya a nan wajan. In kina niyar tafiya ma ki tabbatar kin daina, wallahi in wani abun ya sake faruwa sai na saSa miki, kin ji na rantse."

Umma ta ce, "in Allah ya yarda babu abinda zai kuma faruwa."

Ya ce, "ya fi miki. Kome ki ke hange da zai saka ki kai rayuwar ki can, in so ki san komai lalacewar nan Win shine dai jin daWi ki, baza ki je ki Wauko farin ciki da walwala ba, in kika sake ki ka bar gidan nan, wallahi kin yi bankwana dasu har abada. Abinda suke faWa miki zaki samu a can roman baka ne, suna kwaWaita miki abinda zai saka ki ji ranki yana so, amma in kin je akasin hakan zaki tarar. Kin girma, wannan shirmen duk ba naki bane, kin taso a gidan tarbiyya ,kin samu ilimi daidai gwargwado, wannan shirme da Sata lokacin duk bai kamace ki ba."

Umma tayi shiru bata ce komai ba. Ya ce, "kin ji me nace ko?."

"Na ji Yaya, in sha Allah ta wuce."

"Haka ake so."

Ya kalli kunun ya ce, "zan tafi da kunun nan, in anjima zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login