Showing 192001 words to 195000 words out of 221574 words

Chapter 65 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

119

ba tare da ya yi magana ba.

Abba ya sake tausasa murya ya ce, "ka yi min al?awari za ka bar auren nan ya yu, ka Waukar min al?awarin baza ka lalata auren ba, ka yi min al?awari baza ka sake yin wata magana a kai ba."

Ya kalli Abba ya ga shi yake kallo, Abba ya Waga ka alamun haka yake nufi. Ya yi shiru ya kasa amsawa, bai san ya zai yi da Abba ba.

Abba yace, "alfarma ta farko da na taSa nema a wajanka wannan ce Rehaan, na san ban kyauta maka ba, amma mahaifiyata nake yiwa biyayya. Ka yi min al?awari akan hakan?."

Ji yake kamar ya yi kuka, Abba ya saka shi a tsaka mai wuya, Abba ya Waure sa da jijiyoyin jikinsa. Tsakani da Allah ta ya zai Wauki al?awari akan abinda ba ya so, ta ya zai Wauki al?awarin da ya san bazai iya cikawa ba?.

Abba ya ce, "ina jinka, za ka yi min Rehaan abinda na nema?."

A hankali ya Waga kai alamun zai yi, Abba ya ce, "ka yi al?awarin?." Ya jima a haka bai motsa ba, sai kuma ya Waga kai alamun ya yi.

Abba ya murmusa ya ce, "Na gode sosai, kar ka zama mai saSa al?awari a wanann lokacin, a duk lokacin da ?in auren ya taso maka a zuciyar ka, ina so ka tuna al?warin da ka yi min."

Shi dai bai motsa ba yana zaune yana ji kamar an saka shi a cikin wuta sbaoda zafin da yake ji.

Abba ya ce, "Za ka yi taron biki ne?."

Ya Wago kai ya ce, "Bana so, inda zai yu bana so kowa ya san za a yi auren nan Abba, in dai ba a cikin gidan nan ba, don Allah kar a sani. Ka yi min wannan alfarmar nima!."

Abba ya ce, "ta ya auren ka zai Suya? Kaima ka san bazai yu ba."

"A saka ya yu, a rufe shi ya zama babu wanda ya sani. Ko a falon nan ne ku Waura auren ba sai a masallaci ba."

Abba ya bisa da kallo ganin da gaske yake maganar ya ce, "Meyasa ba ka so a sani."

"Saboda bana so."

"Ba ka yi ha?urin ba?."

"Na yi Abba, yin ha?urin ne ya saka na ce bana so a sani."

Abba ya ce, "shikenan Rehaan, tunda ba ka so a sani zan san abinda zan yi a kai in sha Allah."

Rehaan ya ce, "ka san wacece yarinyar?."

Abba ya Waga kai ya ce, "eh na sani, har na turawa Jafar adireshinta, sai ku je ku gaisa. Tana da kirki sosai, sai da na tabbatar da nagartarta sannan na amince ka aure ta.

Rehaan ya yi wani murmushin takaici jin ana yabon yarinyar da ya san wacece ita, wai tana da nagarta. Ya buWe baki zai yi magana sai ya fasa, ya yi shiru yana jin Abba.


Abba ya ce, "ka kwantar da hankalin ka, nima da ace yarinyar bata dace dakai ba bazan amince ba. KuWi ne kawai bata kai ka ba, amma komai nata da na haWa shi da naka iri Waya."

Ya kawar da kai yana mamakin ya aka yi halinta na banza ya Suya ne?.

Abba ya ce, "tashi ka je, Allah ya yi albarka. Ina so ka tuna da al?awari kaya ne." Ya amsa da amin ya tashi ya fita, Sangarensa ya koma sai kuma ya sakko ya shiga mota aka ja shi ya fita.

" " " " " "

Islaha tana gidansu Safeera a kwance kamar mai zazzaSi, gabaWaya jikinta babu ?arfi sai kwanciya take yi a duk inda ta samu dama.

Safeera ce take ta rarrashinta, ita dai sai dai ta Waga kai amma Allah kaWai yasan yadda ta damuwa Satan masoyinta.

Sai da ta yi sallar magrib sannan ta fito, a hankali suke tafiya babu wanda yake yiwa wani magana dan bata da nutsuwa balle ta ce wani abun.

A lokacin wata ba?ar motar ta wuce su ta yi parking gab da ?ofar gidansu Saheer, basu kula da ita ba suka cigaba da tafiya a nutse har suka zo inda motar take.

Suna zuwa wajan aka buWe motar murfin motar ta tare musu hanta, suka kalli motar a tare suka Wauke kai.

Wani mutum sanye da ba?a?en kaya ya fito ya ce, "Barka Islaha."

Ta Wan tsaya ta kalle sa, ganin bata san shi ba sai ta sake Waure fuska a da?ile ta ce, "barka" ta faWa tana niyar barin wajan.

"In ba za ki damu ba ina so zan yi wata ?aramar magana dake."

Ta Wan juyo ta ce, "gaskiya zan damu, na gode."

Ya yi murmushi jin amsar da ta bashi ya ce, "magana ce akan Satan Saheer."

Cak ta tsaya tare da waiwayowa ta kalle shi ta ce, "me ya faru?."

Ya kalli Safeera ya sake kallon Islaha ya ce, "Ina so ki shiga motar nan, akwai inda nake so mu je, in sha Allah za ki samu mafita akan matsalar ki."

Islaha ta kalli Safeera da take kallon mutumin ta ce, "kamar ya ta shiga mota?."

Ya kalli Safeera ya ce, "yi ha?uri Safeera, ba cutar sa ita zan yi ba."

Safeera ta buWe ido jin ya kira sunanta, sai ya yi murmushi ya ce, "Babu abinda zan yi mata na cutarwa, kawai ina so ta shiga motar ne, ni kuma zan kai ta inda zata samu maganin damuwarta in sha Allah."

Islaha ta kalle sa a kaikaice ta ce, "sai aka ce maka ina bu?atar taimakon ka ne?."

Ya Wan murmusa dan kafin ya zo an karanta masa halayenta ya ce, "ko ba ki ce ba kina da bu?ata, ki shiga kawai."

Ta harare sa, hararar up and down ta ce, "Bazan shiga ba, da kai da maganin damuwar ta ka ku je bana bu?ata."

Ta juya zata bar wajan ya ce, "in ba ki shiga ba za ki yi danasani Islaha, zai fi miki ki zo ki shiga mu je."

"Sai maimaitawa ka ke yi kana cewa baza ka cuce ni ba, yadda ka ke faWa ya tabbatar min da kai Win macuci ne. Bazan shiga ba, in ka ga za ka Wauke ni ka saka a motar sai ka yi. Aikin banza kawai, baka san me yake damun mutum ba ka zo ka ishe sa da surutan banzada wofi!" Ta faWa a fusace tana kallonsa.

Maimakon ya ji haushi sai ya yi murmushi ya ce, "ki yi ha?uri, ban faWa dan na Sata miki rai ba. Amma don Allah ki shiga motar nan mu je." Ta ja wani dogon tsaki ta yi gaba abinta.

Safeera ta kalle shi ta ce, "to kai akan me ka takura sai ta shiga motar ka ne? Ka ?yaleta mana, ko ana dole?."

Ya Wan yi murmushi ya ce, "Ba a dole, amma ana bu?atar ta shiga Win." Safeera itama ta yi tsaki ta bi bayan Islaha da ta shige gida abinta.

Waya ya Wauko yana dannawa kafin ya saka a kunne, cikin ladabi da gimamawa ya ce, "ta ?i shiga motar Sir."

Ya yi shiru alamun ana bashi amsa kafin ya ce, "Okay Sir" ya faWa yana kashe wayar ya shiga mota ya bar unguwar.

Nana Haleema.
[7/27, 11:49/ AM] KRBBK: RDB2P88
Nana Haleema.

Washe gari har aka yi sallar azahar bata fito ba, tana Waki a kwance ko breakfast ta kasa yi. Tana ji ana zancen za a siyar da gidan da ake ciki a karSo Saheer bata iya fitowa ba, sai daga baya ta mi?e ta yi wanka ta shirya ta fito daga gidan. Gidan radio ta yi nufin zuwa dan ta kai koken ta ko Allah zai saka mutane su ji su taimaka mata, bata so ta je gidan radion da take aiki, shiyasa kawai ta hau napep ta tafi ko Safeera bata faWawa ba.

Kallon window napep Win take yana tafiya a hankali, a haka ya Wauki passenger maza guda biyi ita dai tana zaune bata ce komai ba, dan inda sabo an saba haWa mata da maza a napep guda Waya.

Islaga sai ta ga ya canja hana, gabaWaya bai Wauki hanyar da ta ce masa zata je ba.

Kasancewar bata da duhun kai sai ta ce, "A'a, Malam ina za ka je ne? Ni ba nan na yi ba."

Ya yi shiru bai ce mata komai ba sai cigaba da tafiya da ya yi bai motsa ba.

Islaha ta ce, "magana nake yi maka fa, ina za ka kai ni?..."

Nan ma ya yi shiru bai ce komai ba, ta fusata ta ce, "Wallahi zan yi....."


?iff maganar ta tsaya, yi jin wani abu kamar bindinga daga gefenta.

Ta buWe ido ta kalli wajen a hankali, ta ga bindinga ce wanda yake zaune a gefenta ya saka mata alamun ta yi shiru.

Ta kalli fuskarsa ta ganta a buWe bai rufe ba, amma ba ita yake kallo ba titi yake kallo. Ta yi Wif, duk rashin kunya da tsiwar sai ta yi shiru gabanta yana faWuwa.

Islaha ta fara tunane-tunane, tana tunanin ta faWa ta gefe kawai, dan gwara ta faWa ta window tunda bata san inda zasu kai ta ba. Ta dinga kallon gefenta tana so ta faWa amma tana jin tsoro, dan motoci suna ta kai kawo a wajen.

Tana wannan tunanin suka shiga estate Win da babu yawan mutane a cikinsa sai manyan gidaje kamar su yi magana da bakinsu.

Abin mamaki wani bababn gida ta ga an yi horn an buWe sun shiga da napep, har lokacin bindigar tana gefenta bai cire ba kuma bai yi magana ba.

Suna tsayawa duk suka fita, Waya ya kalle ya ce, "fito."

Duk da tsoron da take ji hakan bai hanata ta ce, "bazan fito ba, ina ne nan?."

Ya Wan yi murmushi dan an zana musu halayenta tsaf, duk sun san zata yi taurin kai. Ya ce, "za ki fito ko sai na fasa kan ki?."

Ta runtse ido ganin yana nuna ta da bindiga, fito daga napep Win ba dan komai ba, sai dan bata so ta mutu bata sake ganin fuskar Hamma ba.

Ya nuna mata wata ?ofa ya ce, "ki je ki shiga wannan ?ofar yanzun nan." Bata ce komai ba ta bi wajen da ya nuna mata, dan sai take ji kamar umarni kawai yake bata.

A hankali ta shiga falon da yake da haske ko ina, ta tsaya a falon tana kallo dan bata san me zata yi ba. Gashi dai bai yi kama da sato ta da aka yi a wancan lokacin ba, amma wannan Win ma sata ce tunda ba a son ranta aka Wauko ta ba.

A wannan lokacin Jafar ya fito daga kitchen yana amsa waya, jin maganar mutum sai ta kalli wajan suka haWa ido.

Jafar ya Wan zaro ido waje cikin mamakin ganinta, ya katse wayar ya kalle ta ya ce, "Miss Islaha."

Fuskar ta babu walwala ta ce, "Mr Jafar me na yi maka ka saka aka kawo ni nan?."

Yadda ta yi maganar cikin sanyi ya saka ya ce, "ki zauna miss, amma bani na saka aka kawo ki ba."

Islaha bata zauna ba, ta kalle sa ta ce, "To waye?."

Kafin ya bata amsa aka buWe wata ?ofa, ta kai kallonta wajan ta gan shi ya fito cikin jallabiyya brown mai kyau da Waukar ido.

Kwata-kwata ba inda take tsaye yake kallo ba, ita kuma shi take kallo cikin mamaki da a'aljabi haWi da takaicin sake arba da fuskarsa a duniya. Lokaci Waya ?wa?walwarta take faWa mata kenan dai shine ya sake sato ta a karo na biyu, tunda ga shi ya saka an nuna mata bindiga an kawo ta inda bata yi niya ba.

Jafar tunda ya fito yake kallonsa, sai ya yi murmushi ya kalli Islaha ganin ta zuba masa ido tana binsa da kallon mamaki da wata irin fuska ta marasa mutunci.

Ya gyara tsayuwa dan yana so ya ga yadda za a kwashe tsakanin mai girman kai da mai rashin kunya.

Kafin ya gama tunanin yadda abin zai kasance Islaha ta ce, "Wannan abin ne ya saka a Wauko ni kenan...." sai ta kalli Jafar ta ce, "akan wanne dalili zai Wauko ni? Sata ko kisan kai?."

Jafar ya yi dariya ya ce, "ban sani ba, nima na gan ki ne kawai"

"To ya saka a mayar dani inda aka Wauko ni, ina da abubuwan yi da yawa ba zaman banza nake yi ba. Meye haWina dashi da zai saka a kawo ni nan? Ko an faWa masa yanzu dah da zai sace ni ya kwana lafiya?."

Jafar murmushi yake yi ya ce "ask him."

Ta juya ta kalle shi, ta ga ya zauna akan kujara kamar ma bai san dashi take magana ba. Wani irin takaici ya mamaye mata zuciya, ita ko magana dashi ma bata so balle har ta tambaye shi dalili, tunda ya ce mata ?ar iska karuwa take jin bata taSa jin tsanar kowa kamar yadda take jin tsanarsa ba.

Ta kasa magana, ta yi shiru ba dan ta kasa ba,
sai dan takaicin da yake gangaro daga zuciyarta.

Falon ya yi shiru babu wanda yake magana a cikinsu, kowa ya yi shiru ba kamar Rehaan da ya yi banza da ita.

Islaha ta katse shirun ta ce, "Ina da wani personal agender da kai da za ka saka a kawo ni nan?."

A lokacin ya Wago ya kalle ta suka haWa ido, ta ?i Wauke idonta daga cikin nasa ta ce, "Tun muna shaida juna da kai, ka saka a mayar dani inda ka Wauko ni, ni ba ?ar tsana bace da za ka sace a duk lokacin da ka ga dama."

Ya Wauke kai daga kanta ya yi mata banza, takaicinta da haushi da tsana ya hana shi magana, bai san haka yake ji a kanta ba sai yanzu da take tsaye a gabansa, sai ya ji a baya ba komai yake ji ba kamar abinda yake ji yanzu.

Takaici ya kusa kai Islaha lahira, ga shi bata da wani ?arfi yadda ya kamata balle ta yi masa hauka, raunin zuciyarta ya taSa mata gangar jikinta, ta yi sanyi sosai, ba dan haka ba da sai ta Wauki wani abun ta fasa masa kai.

Jafar dai yana zaune yana so ya ga ta inda Rehaan zai fara, haka kawai ya Wauko ?ar mutane shi ya fi ?arfin ya je gidansu.

Rehaan kamar zai yi magana sai ya fasa, ya Wago ya sake kallon Islaha yana maimaita kalmar future wife Winsa ce a tsaye a gabansa, ya Wauke kai ya gyara zama bai ce mata komai ba.

Islaha ta kalli Jafar ta ce, "don Allah ka saka a mayar dani gida, ina da abinda zan yi da yawa. Bani da lokacin wannan shirmen, bani da lokacin Waga murya a yanzu, ko wanne second na lokacina yana da mahimmaci a gare ni."

Jafar ya yi murmushi yana jan kujerar dining ya zauna ya ce, "Bani na Wauko ki ba Islaha, shine ya saka aka Wauko ki."

"To me zai yi min da zai saka a Wauko ni?."

"Ki tambaye shi."

"Wallahi ba?in ciki da haushinsa zai iya sakawa na sha?e shi har sai ya daina numfashi. Bana Waukar abinda kowa zai iya Wauka, zuciyata daban take da ta sauran mutane, abinda nake ji daban da na sauran mutane, bazan shiga lamarinka ba, kaima kar ka shiga nawa."

Jafar da ya ga dai Rehaan Sata mata lokaci zai yi sai ya ce, "ya Wauko ki ne akan maganar auren ku."

Ta Wan yi jim tana kallonsa kafin ta ce, "auren mu, ban gane ba."

Jafar ya ce, "eh auren ku, kin manta za ki yi aure ranar friday?."


"Ni ban gane ba fa, kamar ya zan yi aure ranar friday?."

Jafar ya ce, "kin gane mana, ai na san kin san da auren da aka ce za a yi miki ko?."

Islaha sai ta tuna da maganar Baffa ta ce, "oh! Wai shine daman wanda ake so a li?a min Win nan?."

Jafar ya girgiza kai yana dariya bai ce komai ba, yadda ta yi maganar ta bashi dariya sosai, wai wanda ake so a li?a mata.

Ta ce, "yanzu na gane, sunan ya zo Waya da sunan mahaifin wanda aka faWa min....."

Ta yi wani murmushin rainin hankali ta ce, "To ba a faWa masa cewa na ce bana yi a kai kasuwa ba? Ko faWa masa aka yi na rasa masu sona ne da har za a yi min tallansa har cikin gida?."

Jafar ya Wage kafaWa ya ce, "ask him Miss."

Ta kalle Rehaan da ba ita yake kallo ba ta ce, "babu wani aure a tsakanina da kai, magana ta baki ma baza ta sake haWa ni da kai ba har abada balle aure. Ni ina da wanda zan aura, tallan aurenka da aka kai min kuna a kai kasuwa, ni a wajena bani da lokacin magana da kai balle auren ka....."

Ta dakata tana harWe hannu a ?irji ta ce, "Malam zan ce maka ko Alhaji? Ka saka a mayar dani kamar yadda ka Wauko ni."

Sai a lokacin ya ce, "So go and tell your father to inform Abba about what you said, so the marriage can be called off."

Ta bisa da harara tana yi masa kallon up and down ta ce, "gani ga ka ai, ba sai an faWawa kowa ba. Na ce maka bana yi, sai a ha?ura ko?."

Rehaan ya lumshe ido yana jin Wan dama dama a ransa, jin ta ce bata so kuma baza a yi auren ba ya yi masa daWi, ko haushin rashin kunyar ma ba ya ji, tunda bata so abin ya zo da sau?i.

Ya ce, "Kina da plan mai girma a kaina, kina shigowa rayuwata ta ko wanne Sangare. Yanzu kuma kin zo ta Sangarren aure...ina so na faWa miki, ni Rehaan na fi ?arfin ki, ki canja tunani."

"Hey Mr man! In na shiga rayuwar ka na ce na shiga rayuwar wa?...." Ta nuna sa da yatsa ta ce, "na ce na shiga rayuwar Rehaan Yola? To na samu ribar me?."

"Mr man ina so ka faWa min da ni da kai waye ya shiga rayuwa wani, sannan ka tuna har gida aka kai min katin gayyatar auren ka, ka ga ni nake da bakin da zance nafi ?arfin ka, tunda kai aka kawo min tallah, ba ni aka kai maka tallah ba....."

Ta yi dariyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login