Showing 90001 words to 93000 words out of 221574 words

Chapter 31 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

164

ya ce, "meyasa ban san maganar ba?."

"Nima ban sani ba Baffa, sai bayan ta tafi aka faWa min. Cewa aka yi kar a faWa min, kuma ba ita bace kaWai ba ce, harda Labiba da babar Safeera ?awar Islaha Win."

Baffa ya sauke numfashi ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Harda Labiba?." Saheer ya Waga kai bai ce komai ba.

Baffa ya zubawa Mama ido ya kasa cewa komai, ta ?i kallonsa ta Wauke kai bata ce komai ba tana ji yana kallon ta.

Baffa ya ce, "Harda Labiba ki ka kai?."

Ta ce, "To ai na ji na ta ita ka ke yi ba ai, ta ?at ri?o ka ke yi tunda ita ka fara tambaya."

Baffa ya lumshe ido ya buWe ya ce, "Yanzu sai da ki ka kai Labiba ?asar waje aiki? Me ta nema ta rasa a gidan nan, me ki ka nema ki ka rasa a gidan nan da zaki saka ta fita daga ?asarta zuwa wata ?asa aiki?."

Mama ta yi shiru bata ce komai ba, Baffa ya ce, "duk kashedin da na dinga yi miki akan hakan sai da ki ka aikata?."


A sanyaye Adda ta ce, "Ka yi ha?uri Baaffa, ka ga baka da lafiya. A bar maganar don Allah, in ka warware sai a samu mafita in sha Allah."

Baffa ya ce, "wacce mafitar kenan? Ta Wauki ?an mata har biyu ta kai wata ?asar da basu da kowa ki ce a bar maganar? Ban san inda suke ba, ban san a hannunwa suke ba, ban san a inda suke kwana ba. A wajen kirki suke ko a wajen na banza duk bamu sani ba. Kuma ki ce na kwantar da hankalina?."

Saheer ya ce, "kayi ha?uri ka bar maganar Baffa, zamu yi magana daga baya in sha Allah."

"Ta ya zan bar maganar? ?a?ana ?an mata suna wata ?asar da ba tamu ba, ku dinga cewa na kwantar da hankalina? ?a?ana har biyu kuma ?an mata da basu taSa aure ba, an Wauke su an kai su wani waje ba tare da na sani ba. An yi amfani da rashin lafiyata an yi abinda bana so. Yanzu da raina da lafiyata ace yaran nan basa nan? Don Allah ya ake so a dinga kallona a garin nan?."

Saheer a sanyaye ya ce, "duk da haka ka yi ha?uri Baffa, ya riga ya faru sai mu yi ha?uri."


"Dan baka san irin maganar da za a dinga faWa a kaina ba. Mu fa fulani ne, fulani ne gaba da baya. Fitar wannan maganar babban abin kunya ne a gare ni da dangina. Ace ?a?ana mata guda biyu sun bar ?asar nan sun tafi aiki a gidan larabawa, ba fa wajen Yola suka tafi ba, ba wani garin suka tafi ba Saheer, wata ?asar suka tafi ban sani ba. Saheer in ban damu ba me zan yi?."

"Baffa likita ya gargaWe mu akan gujewa abinda zai saka jinin ka ya hau, ka ga iya wannan maganar zata iya jawowa jinin ka ya hau. Don Allah don Allah ka bar maganar, ni zan san abinda zan yi in sha Allah."

Baffa ya kalli Mama da bata ce komai ba ya ce, "yadda ki ka Wauke su ki ka kai su ki saka a dawo min dasu, in ba haka ba kuma zan yi miki abidna baki taSa tunani ba."

Adda ta ce, "babu batun dawowa Baffa, dole sai sun zauna sun biya kuWin da aka kashe aka kai su. Ka san kuma Mama itama aiki kan aiki take yi, ba wai itace shugaba, tana da na sama da ita. ?ar sallamar da ake bata in ta samo matan bata taka karya ta yi ta karya ba. Dole sai sun biya kuWin da aka kai su sannan zasu samu ?ancin da zasu dawo."

Baffa ya yi shiru ya dafe kansa cikim yanayin da bai san meye ba.

Saheer ya ce, "Don Allah Baffa ka yi ha?uri, a bar magnar don Allah."

Baffa bai ce komai ba Mama ta mi?e ta fita, Baffa ya bita da kallo kafin ya kalli Saheer ya ce, "wani abu nake dubawa akan mahaifiyar ku, wani abu kawai nake kallo shiyasa duk abinda take yi min nake ?yalewa. Amma naga ta kasa ganewa, tana neman ta kai ni bango na kasa Wauke kai na yi abinda zuciyata take faWa min nayi."

A tare suka haWa baki suka ce, "Ka yi ha?uri Baffa."

Baffa ya ce, "Kun yi magana da Islaha? Dan na san Labiba bazata neme ku ba."

Adda ta ce, "Wazu ma mun yi magana da ita, ta tabbatar min da bata da wata matsala ta samu gida na kirki. Na dinga yi mata faWa akan meyasa ta tafi, sai ta ce na tambayi Saheer dalilinta na tafiya, wallahi ba a son ranta ta tafi ba. Kuma ta ce na baka ha?uri, tasan ta yi maka laifi mai girma."

Baffa ta kalli Saheer ya ce, "FaWa min dalilin."

Adda ta kalli Saheer ya yi mata alama da ta yi shiru kar ya faWa, Adda ta ce, "ai bamu yi maganar dashi ba, yanzu zan tambaye sa in sha Allah. Ka huta Baffa, bara mu je, Saheer mu je" ta faWa tana mi?ewa, shima ya mi?e suka fita suka bar Baffa cikin tunanin da ya kasa barin zuciyarsa.

Ya sauke numfashi cikin wani irin yanayi, ko kaWan bai ji daWin maganar nan ba, zuciyarsa zafi take yi akan hakan. Amma bai ga laifin Islaha ba, dan ya yarda da ita, ya tabbatar akwai dalilin tafiyar ta.

Nana Haleema.
[7/3, 5:36/ PM] KRBBK: RDB2P38
Nana Haleema.

Adda suna fitowa ta tsayar da Saheer ta ce, "FaWa min wacce matsala ce ta kai Islaha tafiya aiki Jeeda, bayan ni da kai mun san ta tsani aikin nan?."

Ya Wan sauke numfashi cikin takaicin hakan ya ce, "nima ban sanar mata ba, ki tambaye ta."

Adda ta ce, "ka faWa min Saheer, na san ka san komai."

"Raina min hankali kawai take yi, ta aikata wani abu a Soye sannan ta tafi ban sani ba. Lokacin da aka sace ta, ta faWa min komai akan sace Win da aka yi, tun lokacin zuciyata take rawa. Nayi-nayi ta faWa min dalilin ta na so a rufe case Win Wauke ta Win ta?i. Kwatsam sai na ji ta tafi Saudia, bayan ta tafi sai nake jin labarin ashe itace ta biya kuWin aikin Baffa gabaWaya. Ta ya hankalina zai Wauki maganar nan? Ya ki ke so na kalli Islaha a wannan maganar?."

Adda da mamaki ta ce, "kamar ya ita ta biya kuWin aiki?."

"Kamar yadda ki ka ji. A lokacin ?in faWa min ta yi, sai yanzu Safeera take cewa wai Wauko kuWin ta yi a gidan da aka Wauke ta. Just imagine, wacce aka sace ita ita a Wauko kuWi? Sace Win da aka yi? daWi ne da shi kenan, tunda har ta iya gani ta Wauka."

Adda ta ce, "to waye ya sace ta Win?."

Ta Wage kafaWa ya ce, "shima ta?i faWa, sai ta ce wai bature ne baya jin yaren mu. Ya Wauke ta har na tsahon kwanaki, ya ajjiye ta a gidansa yana bata abinci mai kyau tana kwana a ac, ya rabu da ita ba tare da ya ri?e ko hannunta ba. Ita kuma da yake ga shugabar masu shirme, da ta tashi dawowa sai ta Wauko masa kuWi masu yawan da ta biya kuWin aikin Baffa. Magana ake ta miliyan sha ba ?ananun kuWi bane, don Allah da wanne ido zan kalli maganar nan? Da wanne kunne zan ji wannan dramar ta gamsar dani?."

Adda ta Wan yi jim kafin ta kalle sa ta ce, "kana zargin Islaha ta aikata wani abu ne ta samo wannan kuWin?."

Ya girgizs kai ya ce, "ko kaWan ban taSa zarginta ba, itace take neman saka min zargin ta a zuciyata Adda. Ta tafi da sunan an sace ta, ta dawo da kuWi masu yawa, ta?i faWar wanda ya Wauke ta, ta ?i faWar dalilinta, sannan ta ce a rufe maganar. Yanzu ta bar ?asar da niyar wai zata biya bashin da ta Wauko. Don Allah ko Ihsan Win ki aka faWawa wannna maganar zata amince?."

Adda ta ce, "ni abinda nake so na ji, me ta yiwa wanda ya Wauke ta har ya saka aka sato masa ita? Sannan da ya sace ta kawai ajjiye ta ya yi yana bata abinci?."

"Hmmmm! Kema dai kya tambaya, ajjiye ta kawai ya yi yana bata abinci tana bacci, da ta tashi dawowa kuma sai ga kuWi."

"Ka faWa min, me ya haWa su?."

"Ta ce wai faWa suka yi, rashin kunya ta yi masa a hotel, lokacin da ta je neman Mr Rehaan Yola, sai kuma a asibiti. Na rasa wanne irim tunani ma ya kamata ace na yi."

Adda ta sauke numfashi ta ce, "indai da gaske baka zarginta kamar yadda kace to ya kamata ka amince da abinda ta ce, kaine mutum na farko da zaka fara b da shaidar ta, in da Islaha ?ar iska ce zuwa yanzu kowa ya sani, kai kanka ko zuwa yanzu in baka zama Wan iskan ba to ka rabu da ita. Ni a jikina ina ji maganar ta gaskiya ce, duk abinda ta yi ta yi ne saboda mahaifinka. Na san halin islaha da gaggawa, wani lokacin sai bayan ta aikata abu take zuwa ta yi nadamar hakan. In zuciyar ta tana son abu kawai tana aikatawa ne nan take, kar ka yanke mata hukunci cikin rashin sani, islaha bazata yi wani abu mara kyau ba."

Ya kalle ta ya ce, "kawai rashin kunya sai ya saka a sace mutum?."

"Eh mana, ai baka san wanda ta taSo ba. Kuma ka san halin kayar ka, ba kunya ce da ita ba ko kaWan. Tana da tsiwa mai yawa, zata aikata abinda ya fi haka ma. Kuma wani saboda haka zai iya sace ta, ba lallai sai ya yi mata komai in ya Wauke ta ba. Ai ba ko wanne namiji ne yake Waukar mace dan ya yi amfani da ita ba, wata?ila shi ya Wauke ta dan kawai ya yi mata gargaWi."


"Kuma sai ta satowa mutum kuWi?."

Adda ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Saheer zuciyar ka ta daina rawa akan Islaha, ni wallahi na amince da ita. Ka fi kowa sanin yadda bata ?aunar aikin nan, ba tun yau ake yi mata talla tana ?i ba, ?aramin dalili bazai saka ta cilla kanta a cikin wannan yanayin ba. Ka tsaya ka saurare ta."

Saheer ya taSe baki yana ajiyar zuciya ya ce, "ni na yi blocking Winta, bani da lokacin yin magana da ita a yanzu."

Adda ta ce, "kar ka yi haka, ka yi ha?uri ka tausaya mata don Allah."

"To ni an yi min adalci kenan? Ta bar ?asa ban san lokacin da zata dawo ba. Me take yi a can, a hannun wa take, wacce irin rayuwa take yi duk ban sani ba. Auren ta zan yi fa, itace nake mafarkin ta zama mahaifiyar yaran da zan haifa a duniyar nan, meyasa zata yi min haka?."

Adda ta tausasa murya ta ce, "bata kyauta ba, amma ka yi ha?uri."

"In na yi ha?urin yaushe zata dawo? Ina da kuWin da zan je na Wauko ta ne Adda?."

Adda ta kalle sa jin muryarsa ta yi sanyi, sai ya bata tausayi, dan ta san Saheer yana son Islaha sosai. Ta Waga masa kai ta ce, "komai warware in sha Allah, ka yi magana da ita don Allah, na tabbatar tana tare da damuwar rashin kula ta Win da baka yi."

Ya kalli gefensa sannan ya ce, "na ce mata me? Na faWa mata tsarabar da zata siyo min, ko na ce mata a ina take aiki, ko na ce mata aikin me take yi?."

Adda ta ce, "Haba Saheer, ban sanka da mita ba, ka bar maganar nan, ka je ka yi magana da ita ka ji?."

Ya kalle ta ya ce, "kin san mahaifin Safeera ya saki babarsu saboda tafiyar nan?."

Adda ta zaro iso ta ce, "ban gane saki ba, wanne irin saki?."

Ya taSe baki ya ce, "Wallahi ya sake ta, ya faWa mata sai babu igiyar aurensa a kanta sannan zata tafi, kuma ta tafi Win shi kuma ya sake ta."

"Innalillahi! Me Mama ta saka ta aikata ne haka?."

Saheer ya ce, "lamarin Mama sai addu'a kawai, amma abim yana yi min ciwo sosai. Ta raba aure guda saboda wani banzan aikin da ba duniya zaka je ka samo ba."

Adda ta ce, "ban da abin Umma meye na tafiya? Da girmanta da komai don Allah." Bai ce komai ba ya fita daga gidan ita kuma ta shiga cikim gidan.

******

? ?? Safeera a gaggauce ta shiga gida, tana shiga ta tarar da Gwaggonsu ?anwar Baba tana gidan.

Ta yi murmushi ta ce, "Gwaggo ina yini."

Ta yi murmushi ta ce, "lafiya lau ?ar jarida. Ya na ga ki a firgice haka?."

Safeera ta ce, "Baba yana azumin tsakiyar wata, zan dama masa kunu, ya ce min baya jin daWin na Ru?ayya, shiyasa nake saur" ta faWa yana ajjiye mayafinta.

Ru?ayya ta ce, "Adda ai Maman su Kausar ta aikowa da Baba kunu, gashi nan na kai masa Wakinsa."

Safeera ta ji daWi a ranta ta ce, "da gaske?."

"Wallahi da gaske, harda da ?wai ta soya masa. Kuma daman na yi masa fanke mara sugar irin wanda yake so."

Safeera ta zauna tana ajiyar zuciya ta ce, "kai amma na ji daWi sossi, a gagaguce na dawo wallahi saboda aikin Baba."

Gwaggo ta ce, "ai ya faWa min zancen ?awar Babar ku, tana da kirki sosai, bata jima da fita daga nan ba."

Safeera ta yi murmushi ta ce, "tana da kirki sosai Gwaggo, baki ga yadda take yi mana ba wallahi, tana kula damu sosai kamar sun haWa jini da Umma."

"Ta kyauta, haka ake son ?awa ko aboki su kasance na gari. Tunda ita uwar taku ta watsar daku ta tafi gantali ita ta sani." Basu ce komai ba suka yi shiru.

Gwaggo ta ce, "Baban na ku nake jira ya dawo mu gaisa sai na wuce gida."

Suna nan zauna suna ta hira sai ga Mama Atika ta shigo da sallama. Suka gaisa da Gwaggo cikin sakin fuska, ta mi?awa a Gwaggo kwano ta ce, "Tuwon alkama nayi, shine na miki."

Gwaggo ta karSa ta ce, "kai amma na gode sosai Atika, Allah ya bar zumunci."

"Amin Gwaggo."

"Da haka ake samun ?awaye masu kula da yaran ?awayensu da an more wallahi, ke kam kin yi dace abin ki." Ta yi murmushi bata ce komai ba, a lokacin Baba ya shigo.

Har ?asa Atika ta zube tana gaishe sa, ya amsa da sakin fuska ya ce, "Ya hidima Atika?."

"Alhamdu lillah, ai babu komai."

"Allah ya saka da alkhairi." Ta amsa da amin tana murmushi.

Gwaggo ta ce, "ka ga kaSakin arzu?in da aka aiko min dashi, tuwon alkama da miyar kuSewa harda man shanu. Bayan ta aiko maka da kunun buWa baki, har su doya da ?wai."


Baba ya cika da mamaki, wannan dafe-dafen abincin da Mama Atika take yi ya yi yawa, ya ce, "Atika kar na Wora miki nauyi fa, hidimar nan ta yi yawa. Iya saurraren yaran da ki ke yi ma ya isa, dan Allah ki daina hidimar dafe dafen nan."

Ita dai murnushi take yi sannan ta ce, "Babu komai Baban Safeera, duk an zama Waya. Kuma ina dashi ne shiyasa nake yi, da babu da bazan yi ba." Baba

ya ce, "duk da haka dai ki Wan rage, kar hidimar ta yi yawa." Bata ce komai ba sai murmushi da take yi.

Mama Atika kalli Gwaggo ta ce, "Gwaggo zan koma, na bar Kausar ita kaWai."

Gwaggo ta yi murmuahi ta ce, "To Atika, Allah ya saka da alkhairi." Ta amsa da min ta mi?e ta fita daga gidan.

Baba suka gaisa da Gwaggo kafin ya shiga ciki ya yi alwala ya fito ya je masallaci, bayan an idar ya dawo ya shiga Wakinsa yana cin abinci.

Ba jimawa Gwaggo ta shiga ta same sa ya gama cin abincin yana zaune. Gwaggo ta zauna ta ce, "har ka gama buWe bakin?."

Ya Waga kai ya ce, "Na gama Gwaggo, yanzu zaki wuce?."

"eh yanzu zan wuce, jira nake Wan wajan naka ya zo ya Wauke ni. Amma kafin nan ina da wata magana."

Baba ya ce, "ina jin ki Gwaggo."

"Matar ka ta watsar da ?a?anta ta tafi yawon gantali, zaman yaran nan su kaWai in baka nan akwai damuwa tunda ba namiji ne a gidan ba. Kuma ana so duk inda ?arami yake ya kasance akwai babba a tare dashi."

"Gwaggo kullum da tunanin nan nake kwana nake tashi, yanzu haka nan da sati biyu zan yi tafiya, amma ban san ya zan yi ba. Ina ta tunanin ko na tura su Katsina sai na tuna da aikin Safeera da makaratar su Rukayya, sai na yi tunanin gidan ki sai kuma na ga kar hiidmar ta yi miki yawa. Na dai rasa inda zan aika su."

Gwaggo ta ce, "ai yawon dangi ba nasu bane, duk inda zasu je barin nan ne."

"To zan bar su su kaWai a gidan nan ne Gwgago?."


"Aure zaka yi kawai, tunda kana? da gida da halin ri?e mace ai, meye laifi dan ka yi?."

Baba ya Wan mi?e zaune sosai ya ce, "Gwaggo aure fa?."

Gwaggo ta ce, "Auren fa, ko akwai haramci ne?."

"Babu gwaggo. Amma sai na ga auren ya yi wuri, har yaushe Maimuna ta tafi d zan yi aure? Sai mutane su ga kamar daman jira nake ta tafi na yi aure ai."

"To sai me? Duk abinda mutane zasu ce su ce mana, na ga dai kai ka san matsalar da ka ke ciki ko? Kuma maganinta zaka yi, in zaka biyewa maganar mutane ko baka yi ba sai an yi maganar."


"Haka ne. To ni Gwaggo yanzu in na Wauko batun aure wa zan aura?."

Gwaggo ta ce, "Ga matar nan Atika, meye laifinta?. Ka san halinta ta san naka, ga gidanta da take zaune ga gidanka. Meye aibu dan ka aure ta ka haWa da ?ar ta ka ri?e?."

Baba ya zubawa Gwaggo ido har ya gama kafin ya murmusa ya ce, "Gwaggo Atika ?awar Maimuna ce fa, ?awar ta ce wacce zan kira ta da aminiya, ko nace nace ta zama ?ar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login