Showing 54001 words to 57000 words out of 221574 words

Chapter 19 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

155

bayar a dawo da flaks Win. Wannan ki bawa yaran" ya faWa yana mi?a mata kuWi. Ta karSa fuskar ta babu walwala sosai, dan ji take an takura mata an matsawa rayuwar ta an hanata abinda take so. Sama-sama take amsawa, babu walwala ko kaWan a tare da ita. Daga haka dai suka yi sallama Yaya ya tafi ya barta da tunani.

Nana Haleema.
[6/26, 12:30/ PM] KRBBK: RDB2P23
Nana Haleema.

Islaha tunda Saleem ya taho kawo su gida daga asibiti wajan Baffa ta yi shiru bata cewa komai. Saleem da Safeera ne suke magana sama-sama, ita dai bata saka musu baki.

Saleem yana tsayar da motar Islaha ta ce, "Safeera zo mu je gida mu yi magana don Allah."

Safeera ta kalle ta ta ce, "me ya faru?."

Islaha ta ce, "ki zo mu je" tana faWa ta buWe motar ta buWe gidan dan babu kowa duk basa nan ta.

Saleem ya kalli safeera bayan Islaha ta shiga gida ya ce, "?awar ki tana da damuwa, tun daga dawowar ta daga Sacewar da ta yi, na tabbatar tana da wata matsala da take Soyewa."

Safeera ta ce, "nima naga hakan, in na tambaye sai ta ce min ita babu komai. Amma bara na je na ji me zata ce min. Ka gaishe da Mama don Allah."

Ya wani kalle ta ya ce, "ba wani na gaishe ta, ko sau Waya baki taSa zuwa kin gaishe ta ba."

Ta buWe ido waje ta ce, "bafulatana ce ni fa, da kunya aka san mu. Ina ni ina zuwa gidan ku gaida Mama?."

"Ko ba bafulatama ba" ya faWa yana hararar ta cikin wasa da soyayya. Murmushi ta yi ta buWe motar ta fita shi kuma ya wuce gida.

Safeera a zaune ta samu Islaha ta ri?e ciki tana cize bakinta, Safeera ta ce, "ya dai? Period Win ne?."

Ta girgiza kai ta ce, "ovalution ne."


"TabWi! Kina ?o?arin gane lokacin ovalution cycle Win ki, ni wallahi mantawa nake yi" ta faWa tana zama a kusa da ita.

Safeera ta ce, "ina jinki, lafiya?."

Islaha ta Wan sauke numfashi ta kalli Safeera ta ce, "a duniya bani da wani daga ke sai Hamma. Bani da iyaye, inda na taso kuma gida ne na kowa da kowa, ba wani nake dashi da zan je na yi sirri dashi ba. Ke kaWai nake da ita wacce nake faWawa damuwata na ji daWi. Safeera..." sai kuma ta yi shiru bata ce komai ba.

Safeera a sanyaye ta ce, "ina jin ki, zaki jefa zuciyata cikin dogon tunani Islaha."

"Akan kuWin mutumin nan ne, wallahi kullum sai na yi mafarki mara kyau akan hakan. Ban san tautsayin da ya kaini aikatawa ba, gashi gabaWaya na kasa nutsuwa."

"Kin saka abin a ranki ne shiyasa ki ke mafarki akan abun. Wani mafarin yana zuwa ne in ka saka wani abu a zuciyar ka kana tunaninsa, yawan tunanin sai ya jawo ka yi mafarki akan hakan."

"Hanyar da zan biyasa kuWinsa nake nema Safeera. Ta wacce hanya zan samu kuWin?."

Safeera ta ce, "babu gaskiya, duk hanyar da zaki bi ki samu ma?udan kuWi kamar wannan a lokaci Waya ba hanya ce mai Sullewa ba. Sata, iskanci, fashi, damfara da sauransu. Sune zasu kawo miki kuWi masu yawan wannan lokaci guda. In kuwa ta hanyar halak ne dole sai kin jira, a hankali a hankali in kin tara sai ki biya."

Ta ja nunfashi mai ?arfi ta ce, "Yaushe kenan? Yaushe zan tara wannan kuWi masu yawa?. Shekara goma ko ashirin?."

"To gashi nan dai."

"Safeera ni dai na samo mafita, kuma in Allah ya yarda a shekara Waya zan haWa masa kuWinsa. Zan neme sa a duk inda yake na dam?a masa koda zai saka a kama ni."

Safeera ta bita da kallon mamaki ta ce, "wacce mafita ce wannan?."

Islaha ta Wan yi shiru tana kallon ?asa, ta Wago ta kalli Safeera da take kallon ta tana jin nauyin faWar abinda yake bakin ta.

"FaWi mana Islaha, kin saka ni a tunani fa."

"Na shiga cikin waWanda Mama zata kai Saudia aiki a wannan lokacin, tafiyar baza ta wuce nan da kwana biyu ba."

Safeera ta zabura ta mi?e tsaye cikin mamaki da kiWima haWi da tashin hankali. Islaha ta ri?o hannunta ta ce, "ki zauna mana."

Safeera ta ce, "ban gane me ki ke nufi ba, maimaita na ji da kyau" ta faWa tana komawa ta zauna.

Islaha a sanyaye cikin rauni da rashin mafita ta ce, "cewa nayi zan tafi aiki ?asar larabawa, a can nake tunanin zan iya haWa kuWin...."

Safeera ta dakatar da ita ta ce, "kina cikin hankalin ki kuwa Islaha, kin san abinda ki ke faWa min?."

"Na sani mana, ni da kaina nake faWa miki abinda na yanke."

"Gaskiya ban yarda kina cikin hankalin ki ba Islaha, ban yarda kin san abinda ki ke faWa ba wallahi. Anya a inda aka sace ki basu gurSata miki tunani ba? Anya basu masu baki kayan maye kin sha tunanin ki ya gushe ba?."

Islaha ta runtse ido, ta san dole Safeera tana shiga ruWani akan hakan, tunda sune masu ya?i da son kawo ?arshen matsalar. Dole zata firgita in ta ji ita da kanta zata je.


Cikin sanyin murya ta ce, "Safeera! Wallahi ina cikin hankali da nutsuwa, abinda nake faWa miki shine asalin gaskiya ta. Har nayi international passport na bawa Mama, Wazu da safe Mama take sanar dani da har an yi min visa."

"Innallilahi wa'inna ilaihir raji'un, Islaha!" Sai ta kasa faWa ta zubawa Islaha ido bata ce komai ba.

Islaha ta ce, "babu yadda zan yi Safeera, ina da bu?atar sauke nauyin da yake kaina shiyasa na yanke hukunci ban faWa miki ba. Wallahil azim ni kaWai na san nauyin da ?irjina yake yi min, ni na kaWai na san zafin da nake ji akan abinda na aikata. Ke kin san wacece ni, kin kowa sanin halina, ban taSa Waukar zaren wani ba balle naira biyar. Dole hankalina ya tashi, dole na rasa nutsuwata. Mafarkai nake yi marasa kyau, har mafarki nayi na mutu kuWin sun hana ni kwanciya a kabarina."

Safeera ta ce, "Akan wannan zaki dakusar da rayuwar ki, akan wannan zaki kashe kanki ki lalata tarbiyyar ki Islaha?. Meyasa baza ki bi wata hanyar ba, meyasa baza mu neme sa mu ba sa ha?uri akan hakan ba?."

Islaha ta goge hawayen idanunta ta ce, "Yanzun nan kika faWa min hanyoyin da suke kawo kuWi, a cikin wanda ki ka faWa wanne zan Wauka?."

"To meyasa baza ki sauke tsiwa da girman kai mu je a basa ha?uri? Meye a cikin ido ban da ruwa? In ka san ka yi laifi baka Waga kanka sama kace kai baza ka ?as?antar da kai ba. Wacece ke da ki ka Worawa ranki girman kai? Meye a cikin kalmar ha?uri Islaha?."

Islaha ta yi shiru bata ce komai, Safeera ta ce, "rashin ba da ha?urin nan, da wannan maganar, sun saka na ji kamar komai da ya faru ke ki ka tsara."

Ta Wan murmusa ta ce, "Safeera kamar baki sanni ba?."

"Meyasa za ki yanke wannan hukuncin ba tare da na sani ba?."

Islaha ta ce, "Na san zaki hanani ne, shiyasa na je na yi duk abinda ya kamata ban faWa miki ba."

Safeera ta dafata ta ce, "ni da ke muke so mu ya?i yawan fitar da yara da ake yi ?asar waje da sunan aiki, yara nawa muka tattauna dasu waWanda aka fita dasu? Mata nawa ne suka bamu labarin yadda rayuwarsu take juyewa sama ta dawo ?asa saboda hakan?. Kin manta ina zaki je ne? Kin manta irin abubuwan da aka faWa mana suna faruwa a can Islaha?."

Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, Safeera ta ce, "wannan ba tarbiyyar ki ba ce, tafiya ki bar ?asa ba daidai yake da tarbiyyar ki ba. Ni da ke muka zauna a kan case Win Umma, mu ka yi magana dake akan zamu je Katsina wajen iyayenta don a hanata zuwa. Meyasa ki ke son tafiya bayan wannan ?aramar matsala ce?."

"Safeera dole ce ta saka, kuma wannan matsalar ba ?arama bace Safeera."

"?aramar matsala ce mana, in mu ka neme mutumin nan muka bashi ha?uri komai wucewa zai yi. A yadda ki ke ba da labarinsa na tabbatar yafi ?arfin naira miliyan goma sha bakwai, yadda ki ke faWarsa dan ya ce ya bar miki abu ne mai sau?i a wajansa. Meyasa baza mu bi hakan ba, sai ta hanyar tafiya wata ?asa aiki?."

Islaaha ta yi shiru bata ce komai ba, Safeera ta ja tsaki cikin takaicin taurin kan Islaha ta ce, "baza ki iya ba sa ha?uri ba ko?."

Islaha ta ce, "kema kin san bazai yu ba."


"Wallahi Islaha ji nake kamar na tsinke ki da mari, wannan girman kan da ki ka Worawa kan ki babu inda zai kai ki sai danasani. Yanzu kin zaSi ki bar ?asar ki ki tafi wata ?asar aiki a gidajen fararen fata ko?. Kin yarda ki watsar da tarbiyyar ki akan titi akan ki furta kalmar ha?uri a wajan wanda ki ka yiwa laifi?."

"To ina zan gan shi balle na ba sa ha?urin?."

"In ki ka nemo kuWin a ina zaki gan shi ki ba shi?."

"Neman sa zan yi duk inda zan gan shi."


"Wannan ma sai ki neme sa ki basa ha?uri, ai ba aljani bane balle ace ya Sace daga duniyar da muke ciki."


"Safeera ni ya yi laifi fa, kuma bayan ya yi min laifin ya sace ni. Kuma haka ki ke so na basa ha?uri?."

Safeera ta ja tsaki ta mi?e tsaye, Islaha ma ta mi?e ta ri?e ta ta ce, "Safeera kema kin san bazan iya ba, shiyasa na nemo mafita a gare ni da rayuwata. Ki yi ha?uri, na san kece mutum na biyu da baza ki ji daWin hukuncina ba, bazan iya Soye miki ba shiyasa na faWa miki, amma tafiya babu fashi. Na yi miki al?wararin bazan watsar da kaina ba, na yi miki al?warain iya albashina kawai zan karSa bazan karSi kuWi ta wata hanya mara kyau ba. Ko a wata Waya na tara kuWin zaki ganni na dawo, bazan Sata lokaci a can ba. Ba neman kuWi naje yi ba, neman kuWin da zan biya bashi zan je nayi."

Safeera ta kalle ta ganin da gaske take magana, ga rauni ya bayyana a tare da ita.

Safeera hawaye suka sakko daga idanunta ta ce, "Islaha ta ya zaki tara wannan kuWi a wata Waya da iya albashi? Kuma in ki ka tafi baza ki dawo ba sai kin gama biyan su Mama kuWin da suka kashe suka kai ki, sai kin biya kamfani kafin ki fara morar kuWin. Kina ganin duk zaki iya hakan a ?aramin lokaci?."

Islaha ma kuka take yi a hankali ta ce, "in sha Allah zan iya, zan nemi halak ba haram ba. Ki yarda dani, bazan yi komai da zai lalata tarbiyyata ba."

Safeer ta goge idonta ta ce, "na yarda dake bestie, ni na san wacece ke. Amma ina so ki sani daga ranar da ki ka tafi duk mai yi miki kallon mai mutunci zai daina, an riga an yiwa tafiyar nan kuWin goro, ko da iya halak Winki ki ke nema a can, an lalata hakan a idanun mutanenmu na nan. Shaida mai kyau daga bakin kuma mutune rahama ce, bana so a fara yi miki wani zargi mara daWi."

"Duk wanda ya zarge ni shi da Allah, duk wanda ya yi min ?azafi akwai ranar tsayuwa Safeera."

Safeera ta ce, "na ji. Ya zaki yi da Saheer? Na san ko za a sake ya?in duniya bazai taSa amincewa da tafiyar nan ba. Ya zaki yi dashi? Ya zaki yi da su Zainab da abinda ki ke bincike a gidan? Kina so ki ce min ?udurin ki ya danne na gidan marayu? Tafiyar ki ta fi bincike akan zargin lalata yaran da ake yi mahimmaci?....."

See you on monday guys=?
?
[6/29, 11:53/ AM] KRBBK: RDB2P24
Nana Haleema

Islaha ta ja numfashi mai tsaho ta sauke, ta Wan yi shiru kafin ta lumshe ido ta buWe ta kalli Safeera ta ce,  Na san Hamma bazan taSa Waukar maganar nan ba, shiyasa nake fatan Allah yasa tafiyar ta kai jibi, kin ga gobe ya ce min zai koma Niger, in dai ya tafi shikenan.

Safeera ta bita da kallon tausayi ta ce,  nufin ki ko ya dawo bazai sani ba?.

 Dole zai sani, da kaina zan faWa masa amma sai na tabbatar bana nan. Indai har na tafi damuwar ba mai yawa bace, kafin na tafi ne wallahi bazai taSa bari ba. FaWa zai ta yi, ya kuma takura min sai na faWa masa dalilina na tafiyar.

Safeera ta ce,  yanzu ya za a yi kenan?.

 Sadik zan yiwa waya, zance masa ina so mu haWu, sai na faWa masa komai da komai. Na san da wahala ya fahimce ni, amma zan ro?esa sosai, zance don Allah kar ya faWa masa har sai na tafi.


 A shawara ta kar a faWawa Sadik, babu lallai ya iya ri?e maganar bai faWawa Saheer ba. Ki bari in kin je sai su ji labari, duk da na san zasu zo su tutsiye ni akan maganar, ni kuma zan faWa musu abinda yake faruwa kawai.

Islaha ta Wan yi shiru alamum tunani kafin ta ce,  To mu gwada hakan mu gani, amma ina jin tsoron Sacin ran Hamma.

Safeera ta ce,  dole ransa ya Saci, shi da yake so ayi bikinku nan da wasu kwanakin masu zuwa, amma a wayi gari kin bar ?asar, ai dole ransa ya Saci.

Ta ja numfashi mai tsaho ta ce,  babu yadda zan yi ne, ni kaina dole ce ta saka ni zan yi. Har istikhara nayi akan tafiyar, shiyasa na saka a raina in har Allah ya nufa naje to akwai alkhairi a zuwana, in kuma ban je ba babu alkhairi a zuwan, tunda na nemi zaSin Allah kuma na san zai zaSa min.

 Babbar matsalar ki a rayuwa shine gaggawa, duk da in mutum yana cikin yanayi na neman mafita yana aikata duk abinda ya zo ransa ne. Amma ke tun asali haka ki ke, kawai da zuciyar ki ta Warsa miki abu sai ki hau kai ki zauna, ki kasa fahimtar kuskuren abun har sai kin aikata. In ba dan haka ba, meye ya kai ki Wauko kuWi don Allah? Sannan me ya kai ki yanke hukuncin tafiya saudia? Dan kina ganin baki da iyayen da zasu hana ki ko?.

 Ina da Hamma, na san shima in ya ji bazai bari ba. Kamar iyayena yake, duk abinda yace na bari ina bari.

 Dole ki rage gaggawa, duk inda gaggawa take daga shaiWan take.

 Ga sakamakonta ina gani Safeera, da ban yi ba da ina nan hankalina a kwance. Yanzu kuwa mafarkai nake yi marasa kyau, har mafarki nayi na kasa tsallake siraWi. Shiyasa hankalina ya tashi, nake nemawa kaina mafita.

Safeera ta ce,  Zainab da Hafsa fa? Case Win da ki ke ta bibiya fa? Kina nufin zaki tsallake ki tafi ki bar yara a cikin garari?.

Ta yi ajiyar zuciya ta ce,  Zan bar maganar a hannun Barr Suraj, na san zai yi komai kamar ina nan. Kuma kema kin nan, zan dinga saka ki kiyi magana dasu.

 Amma kin san ba kamar ke ba ko? In dai ki ka bar ?asar nan an ajjiye batun case Win Islaha.

 Allah zai kawo min yadda zanyi.

Safeera ta ce,  Allah ya kyauta. Aikin ki fa?.


 Zan yi droping Winsa, in na dawo zan cigaba in sha Allah.

 Kafin shekara Waya za a manta da fuskar ki, kina kan matakin Waukaka a yanzu, in ki ka yi ?aura aka daina ganin zaki dakusar da kan ki.

 To ya zan yi?.

 A ganina ki yi creating content a can, ko da video flowers ne ki dinga Wauka ana yawan ganin fuskar ki a media. Tunda kina da followers, hakan zai saka baza a manta dake da sauri ba.

Islaha ta Waga kai ta ce,  Allah ya bani iko.

Safeera ta amsa da amin a lokacin aka buWe ?ofar aka shigo da sallama.

Suka amsa suna kallon Mama da ta shigo da babbar trolly bag ta ce,  islaha ga jakar zuba kaya nan, in anjima za a siyi ticket Win ku, jirgin jibi da daddare zaku hau. Ki zuba duk abinda ki ke da bu?ata, ki zuba kaya masu kyau kar ki tafi da marasa kyau. Sannan zaki iya yin siyayya in kin je Jedda ki siyar ki ri?e kuWin ki. Ana siyan goro, doya, fara, man shafawa, da sauransu. Goro dai ya fi kawo kuWi, amma wucewa dashi tun daga nan Nigeria yana da wahala, amma da kin wuce in Allah ya taimake ki a Jedda ma ya wuce zaki yi murna.

Islaha cikin ya?e ta ce,  Na gode Mama, ba sai na siyi komai ba.

Mama ta ce,  shikenan, ni zan ba da sautun da za a siyar min ki saka a jakar ki, in aka siyar ki mayar da kuWin naira ki turo min kuWina. Sannan akwai yaji, saboda abincin larabawa babu WanWano, ina dashi na siyarwa in za ki siya.

A sanyaye islaha ta ce,  To Mama. Hamma yana nan?.

Mama ta ce,  ke kar ki damu da Saheer babu abinda ya isa ya yi, ba haifar ki ya yi ba, kuma ba auren ki yake yi ba. Bai isa ya hanaki abinda ki ke so ba.

Ta langwaSar da kai ta ce,  Don Allah Mama bana so ya sani, tunda gobe zai koma Niger don Allah kar ki faWa masa.

Mama ta Waga kai ta ce,  naji& & 

Mama ta juyo ta kalli Safeera ta ce,  Ke Safeera ana ta tafiya ke baza ki je ba? Ga ?awarki nan zata tafi ta bar ki a nan, ko da yake da babar ki za a yi tafiyar ta faWa tana juyawa ta fita.

Safeera ta bi bayanta da harara ta ce,  babu inda Umma zata je in Allah ya yarda. Matar nan makira ce, wato dan zaki je ki samo mata kuWi shine

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login