Showing 177001 words to 180000 words out of 221574 words

Chapter 60 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

156

shiru ba, kuma makomar ku kenan." Kowa ya yi tsitt gabansa yana faWuwa, aka kaWa su daji aka fara tafiya.

Tun dare suke tafiya har gari ya yi haske, babu waya babu agogo balle su san ?arfe nawa, haka suke tafiya cikin wani irin yanayi.

Duk sun gaji, sun jigata amma tsoron faWuwa suke yi saboda kar a kashe su. A haka suka iso sansanin su, zuwa lokacin gari ya fara haske sosai, aka nuna musu inda zasu zauna kowa ya zauna cike da gajiya. Saheer ya dinga kallon wajen, ganin mutane da yawa a zaune a filin Allah, sai wata bukka guda biyu daga gefe, sai au da suke da yawa a wajen kowa da bindiga.

?aya daga cikin matan da aka kamo ta ce, "fitsari na ke ji."

Wanda suka taho tare ya ce, "ki yi a nan." Ta sunkuyar da kanta ?asa, ta yi ftsarin kamar yadda suka ce.


Saheer salati kaWai yake yi a zuciyar, ambaton Allah ya yi cikin neman mafita yana kallon mutanen. Dukkansu fuskarsu a rufe ta ke, sun rawani irin naWin buzaye sun rufe har fuskarsu.

?aya ya dafa Saheer ya ce, "Kai bafulatani ne?."

Saheer ya Waga kai ya ce, "Eh."

"A wanne gari ka ke?."

"Yola."

Sai ya Wago ya kalli yan uwansa ya ce, "Wannan bafulatani ne, yana jin yaren da muke magana dashi.

Saheer dai kallonsu yake yi, ganinsu da manyan bindigu, ga over over a hannun ko wannensu, ga kayan harbe-harbe koda za a kawo musu hari ta sama.

?arar machine ya cika wajen gabaWaya, duk ya ga sun mi?e sun nutsu cikin girmamawa. Su biyu ne akan machine Win, suka sauka daga machine suka saka musu kujera suka zauna. ?aya dinga binsu Waya bayan Waya da kallo, kafin ya kalle su ya ce, "Ka kawo tsohuwar ajiya."

Ya kalli Magaji ya ce, "Mutum nawa aka samo jiya?."

Magaji cikin girmamawa ya ce, "Su ashirin ne ArWo." (ArWo shugaba).

Ya girgiza kai yana kallon kowa a cikinsu, ya ce, "kar a taSa matan nan, kar yi musu komai, duk wanda na kama da akasin haka zai tauna gyaWa."

Duk sun fahimci me yake nufi da gyaWa, a yaren masu garkuwa da mutane na wani Sangare in suka ce gyaWa suna nufin bullet kenan, yana nufin duk wanda ya lalata mace Waya a cikin matan sai ya harbe su.

A lokacin aka kawo mace da namiji aka gurfanar a gabansa, ya kalle su ya kalli ArWo ya ce, "kwance shi." Ya kwance namijin, ya kalle su yana girgiza kai ya ce, "Ku ?i ku ba da lambar wayar ?an uwan ku ko? Kun so ku mutu ne?."

A hankali namijin ya Wago ya kalle sa, wanda yake zaune a kusa dashi ya ce, "Wannan yaro ne ma sosai."

ArWo ya ce, "Sai taurin kai, kwanan su biyu amma sun ?i ba da lambar waya, wai babar su bata da waya balle su bayar."

"Wannan macen ?ar uwarsa ce."

"?anwarsa ce."

Abokin ArWo da suke kira da Black ya ce, "?an mata ya sunan ki?."

A hankali ta Wago kai ta kalle su, a lokacin Saheer ya kalle ta yana jin tausayinta, ganinta yarinya ?arama dan bata wuce shekara sha shida ba.

Black ya ce, "ArWo wannan ai kyakykyawa ce sosai, a bani ita mana."

ArWo ya yi dariya ya ce, "Babu hakan a shugabancina, kai k fi kowa sanin haka."

"A bani auren ta, zan ri?e ta hannu biyu."

ArWo ya kalli Wanuwanta ya ce, "Kai ka ji, Black yana son auren ?ar uwarka. Ya sunan ka ma?."

Muryarsa tana rawa sosai ya ce, "Sudais."

Black ya ce, "ita fa?."

"Sudaisa."

"Ku ?an biyu ne?."

Sudais ya Waga kai yana hawaye sosai, Black ya ce, "Ina son Sudaisa, za ka bani auren ta?."

Sudais ku ka kawai yake yi, ya girgiza kai ya ce, "Ni bazan ba da auren....." kafin ya gama faWa an buga masa kan bindiga, a take ya faWi a wajen a sume.

Black ya yi kam Magaji da masifa ya ce, "Gashi nan ka sumar dashi, aurena za a Waura yanzu fa."


Magaji ya ce, "Tuba nake Black, na ji yana yi maka taurin kai."

"Ka saka ya farfaWo yanzu a Waura auren nan."

ArWo ya ce, "Ga wani a zaune, tun Wazu yake kallon mu, ya baka auren ta mana" ya faWa yana nuna Saheer da idanunsa yake wajen.

Sudaisa kuka ta yi sosai, Black ya tsuguna a gabanta ya ce, "In na aure ki zan Wauke ki daga nan, zan je na ba ki rayuwa mai kyau, za ki daina wannan wahalar da ki ke ciki."

Ita dai kuka take yi sosai, ta Wago ta kalli Saheer suka haWa ido, sai ya Wan zuba mata ido yana ganin kamar ya santa, amma sai ya Wauke kansa daga kallon ta yana jin tausayinta sosai.

ArWo ya ce, "Black ka bari ya farfaWo za a Waura auren, amma kafin nan sai an bani ha??ina, dan bazan yi asarar mutane har biyu ba."

Ya kalli Sudaisa ya ce, "Kafin Wan uwan ki ya farfaWo, ki zama matar black, za ki ba da lambar wayar ko ba za ki bayar ba?" Ya faWa yana sakawa ana saita kanta da bindiga.

Sudaisa muryar ta tana rawa ta ce, "Ba mu da kowa, Maman mu kuma bata da waya."

ArWo ya haWe rai ya ce, "in na kuma tambayar ki ki ka maimaita abinda ki ka faWa sai na kashe ki."

Ita dai kuka take yi, a lokacin aka farfaWo da Sudais ya ce, "za ku ba da lambar ko......"

Over over jikin ArWo ta fara ?ara alamun ana magana, ya Wauka yana magana, sai kuma ya mi?e da hanzari suka hau machine suka bar dajin.

Saheer kallon yaran yake yi cikin tsananin tausayi, ya ji Sudais yana cewa, "gwara su kashe mu kawai, bamu da wanda zamu ba da lamba balle a kirasa, gwara mu mutu."

Kuka take yi sosai ta ce, "Ni ban son auren Hamma, kar ka bari a yi auren."

Ya juya ya kalli Saheer da yake kusa dasu ya ce, "Sannu."

Saheer ya Waga musu kai, Sudais ya ce, "yau ku ka zo wajen nan, ba ku san me yake faruwa ba, mu kwanann mu uku. Sun takurawa ?anwata, ba dan an hana su yi mata komai ba da yanzu sun yi mata fyaWe. Ka ta ya ni kula da ita don Allah."

Kuka suke yi dukkansu, Saheer tausayinsu ya kama su sosai, ya lumshe ido kawai bai ce komai ba. A lokacin aka Wauke sunaka mayar dasu inda suke, aka bar su Saheer ko ruwa ba a basu ba, yana kallon mutum biyu sun mutu saboda rashin ruwa, an Wauke su an cilla a wani ?aton ramin da suke cilla gawa.

A kansu rana ta buWe ?wal, babu wanda ya yi ?o?arin Wauke su, a lokacin ArWo ya dawo, yana sauka daga machine ya ce, "ana bawa ajiyata abinci kuwa?."

?aya daga ciki ya ce, "ArWo baka ce a bayar ba."

Ya zauna yana kaWa ?afa ya ce, "Na ce yanzu, a saka mata su shiga daji a samo zolage su dafa a ci. A kawo mana waya."

Wasu suka Wauki mata uku a cikin matan da suke wajen, dan su ba a Waure su aka nufi daji dasu dan su nemo zogale. Wani kuma ya bashi waya ya kalli su Saheer ya ce, "Ban Wauko ku dan na ajjiye ku ba, ku jarina ne, dole na killace ku yadda ya kamata. Ko wannen ku zai bani lambar wayar gidansu, bazan Wauki lokaci na bar ku a nan ina baku abinci ba, ?an uwanku su kawo kuWi su Wauke ku."

?aya bayan Waya aka dinga ba da lamba ana kiran wayar yan uwa, Saheer kallonsu yake yi yana mamakin wannan lamari. Wai ?an ta'adda ne suke da wayoyi da makamai haka, kuma wai a ce an kasa kama su.

Ya kalli Saheer ya ce, "Bafulatani bani lambar ?an gidanku."

Saheer ya ba shi lambar Sadik, dan bazai ba da lambar Baba aka kira wayar Sadik.

" " " " " " " " "

Washe gari da safe da wuri Baffa ya fita basu haWu da Islaha ba. Ta fito daga gida kenan ta ga Sadik, suka gaisa ya ce, "kun yi waya da Saheer kuwa?."

Ta girgiza kai alamun a'a ta ce, "ni ban san ya yi tafiyar bama sai da na dawo daga aiki, ba mu yi magana ba gaskiya."

Ya sauke nungashi ya ce, "gabaWaya ba a samunsa a waya wallahi, kuma ba haka ya saba in ya yi tafiya ba."

Ta taSe baki cikin ko in kula, dan haushinsa take ji sosai ta ce, "zai kira ka Win ne, sauri nake zan tafi aiki" ta faWa tana barin wajan ya bita da kallo cike da mamaki, ganin ana maganar ba a samun Saheer a waya tana nuna ko a jikinta.

Bata tashi dawowa daga aiki ba sai da???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?re, tana shiga ta tarar da mutanen gidan an yi cirko cirko, ga Baffa, ga Sadik a tsaye, kana kallonsu za ka ga tashin hankali a kwance a fuskarsu.

Islaha gabanta ya faWi sosai, ta bi su da kallo kafin ta ce, "Hamma Sadik lafiya?."

Baffa ya sauke numfashi cikin wani irin yanayi ya ce, "masu garkuwa da mutane ne suka kama Saheer a hanyarsa ta tafiya Niger!....

_Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.=?O?
Nana Haleema.
[7/24, 9:52/ AM] KRBBK: RDB2P81
Nana Haleema.

_Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.=?O?

Islaha ta ji kamar an soka mata kibiya a ?irjinta, ta tsaya cak ta kasa ?arasawa tana kallonsu cikin tashin hankali.? Sai kuma ta zabura ta shiga ciki ta ce, "Ban gane an yi garkuwa dashi ba, waye ya yi garkuwa dashi Win?."

Adda ta ri?o hannunta ta ce, "Ki nutsu Islaha."


Ta kalli Adda ta ce, "waye ya yi garkuwa dashi?."

Baffa ya ce, "Islaha ki nutsu, za a faWa miki duk abinda ya faru."

Ta ce, "Baffa ka faWa min, don Allah."

Baffa ya ce, "Wazu suka kira Sadik akan Saheer yana hannunsu, zasu sake kira a jira su."

Islaha ta ja numfashi mai tsaho ta ce, "innallillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Ta faWa hawaye ya sakkowa daga idonta.

Sai kuma ta juya ta kalli Sadik ta ce, "kuma an tabbatar masu garkuwan ne? Kar a sake maimaita abinda aka yi lokacin da na Sata."

A sanyaye Sadik ya ce, "da gaske su ne Islaha."

Ta zauna a kan kujera ta dafe kai tana kuka mai taSa zuciya, hannunta yana rawa saboda kuka ta rasa abinda zata ce.

Baffa ya ce, "mu je a sanar da ?an sanda."

Sadik ya ce, "Baffa ka share batun hukuma kawai, a bari aji abinda zasu ce a biya kuWi a karSo shi. Haka aka yi da aka sace ?anwar abokina, ba a iya karSota ba sai da aka biya wannan kuWin. Babu abinda hukuma suke yi a wannan gaSar, in dai sun faWi kuWi sai an bayar."


Baffa ya ce, "Duk da haka Sadik, gwara hukuma ta shiga maganar nan."

Sadik ya ce, "ban ?i ba Baffa, amma abinda suka faWa shi ya kamata mu yi."

Mama da take kukan rashin Saheer ta ce, "kar a faWa musu don Allah, kar su kashe min Saheer."

Sai abin ya sake karyawa Islaha zuciya, ta yi kuka mai tsuma zuciya, tana ji kamar ta tashi ta yi tsuntuswa ta ganta a gaban Hamma, ta karSosa ita ta bada kanta a kamata a Waure.

Baffa ya yi dauriya ya ce,? "ku daina wannan koke koken, ku je a cigaba da addu'a kawai. Allah ya shiga lamarin mu gabaWaya." Sadik ne kaWai ya amsa da amin, su basa cikin nutsuwarsu gabaWaya..

Adda ta ri?e hannun Islaha suka koma falon Mama, dan yadda take jiri ita kaWai zata iya faWuwa.

Ita kaWai ta shiga Waki ta zauna tana ta kuka babu ?a??autawa, abinda yake Waga mata hankali bai wuce in ta tuna yadda suka rabu ba, in ta tuna hakan sai hawaye ya sake sakko mata, cikin wani irin yanayin da bata taSa jin irinsa ba.?

A lokacin Safeera ta shigo a gigice, Islaha ta mi?e tsaye ta rungume ta sake fashewa da kuka tana faWin, "Hamma..an kama Hamma Safeera....Zasu kashe min shi, zasu kashe min Hamma!.." Ta faWa muryar ta tana rawa sosai.


Safeera cikin rauni ta ce, "yanzu Baffa ya yi sallama da Baba yana faWa masa, shine na zo wajen ki."

Islaha kuka kawai take yi a jikin Safeera, tana ganin abin kamar a mafarki, ganin abin take kamar wasa wai an yi garkuwa da Hamma, garkuwa ba irin wacce aka yi da ita ba, garkuwa ta gaske wacce za a iya kashe shi.

Safeera ta ce, "ki yi ha?uri, addu'a yake bu?ata ba kuka ba, don Allah ki kwantar da hankalin ki, Allah zai kuSutar dashi. In ba ki daina kuka nan ba za ki samu attack, kuma kukan ba shine maganin damuwar mu ba." Ita dai bata daina kuka ba, Safeera ta zanar da ita tana rarrashi.

Islaha cikin kuka ta ri?e hannun Safeera ta ce, "In na tuna yadda muka rabu dashi sai na ji wani iri, sai na ji ban kyauta masa ba."


"Ha?uri za ki yi, ki ta yi masa addu'a, ita yake da bu?ata yanzu ba wannan kukan ba. Kar ki je ki samu attack a wannan koke-koken, ki yi ha?uri."

"Masu garkuwa da mutane fa Safeera, ?an bindiga ne suka Wauke Hamma."

"Na sani, ki yi ha?uri."

Safeera ta dinga rarrashinta har ta samu ta Wan ha?ura, bata koma gida ba ta zauna a tare da ita tana kwantar mata da hankali.

Islaha ta kalli Safeera cikin muryarta da ta dashe saboda kuka ta ce, "Ashe haka ku ka ji lokacin da na Sace? Ashe haka ku ka ji lokacin da aka sace ni?. Haka wancan banzan ya dasawa mu ku ciwo, kuma ya saka ku kuka?. Me zai saka na so wannan mutumin, har abada wallahi." Safeera dai bata ce mata komai ba, ta dinga rarrashinta har ta nutsu sannan ta tafi.

Ranar gidan haka ya rayu shiru, kowa ya nutsu ya koma ga Allah ana zaman jiran tsammani, gabaWaya kowa hankalinsa baya jikinsa, ana tunanin ta inda lamari zai sake Sullowa.

Islaha bata iya baccin kirki ba, da ta yi zata farka ta yi kuka ta koma bacci. ?arfe uku ta tashi tana sallah tana ro?on Allah akan ya bayyana mata Hammanta, ta kuSutar dashi faga hannunsu, ya kare shi daga zaluncinsu.

Da safe da ta tashi haka ta tashi da fuska a kumbure saboda kuka, ko shirin zuwa aiki bata yi ba, saboda bata da wannan nutsuwar a lokacin.

Ta shiga wajan Baffa dan su gaisa, ta same shi shida Sadik da Kawu da Baba a zaune ana ta tattaunawa akan batun.

Ta ?arasa ta gaishe su, kafin su amsa ta ce, "har yanzu shiru?."

Baffa ya kalle ta cikin tausayin yanayinta ya ce, "har yanzu shiru Islaha, muna ta addu'a a kai."

Ta sauke numfashi ta ce, "Allah ya bayyana mana shi." Suka amsa da amin.

Baffa ya ce, "akwai maganar da nake so zamu yi dake, shigowar wannan lamari ne ya saka ni na manta jiya, amma in kin dawo daga wajen aiki ki zo ki same ni."

"Ai bazan je aiki ba Baffa, bazan iya ba" tana faWa hawaye yana sakko mata.

Ya Waga kai ya ce, "shikenan, ki je ki zauna zamu yi maganar in anjima. Ki daina kuka, Allah yana sane da komai, shi ya ?addara mana, kuma shi zai ba mu mafita." Ta Waga kai ta mi?e ta fita ta bar suna cigaba da tattaunawa.

A harabar gidan ta zauna a inda suka saba zama ita da Hamma. Sadik yana fitowa ta mi?e tsaye tana kallonsa har ya ?araso sannan ta ce, "Hamma Sadik da gaske sace shi aka yi?."

Ya bita da kallo ganin duk ta firgice, sai ya tausasa murya ya ce, "da gaske ne Islaha."

"Kuma zasu sake shi?."

"Za su sake shi in sun faWi kuWi an biya in sha Allah."

"Yaushe zasu faWa?."

Ya sauke numfashi ya ce, "ko yaushe zasu iya yin waya."

Ta Waga kai ta ce, "an yi magana da ?an sandan?."

Ya Waga mata kai ya ce, "An yi Islaha."

Ta ce, "shikenan Hamma Sadik, amma don Allah kome yake faruwa ka faWa min, ka ji?."

Sadik ya bita da kallo cikin tausayin yanayinta, magana take yi masa amma kuka take yi, gabaWaya ta canja daga jiya zuwa yau, ta firgice lokaci Waya kamar ba ita ba. Tunda ta bar ?asar yake jin haushinta, amma yanzu sai ta bashi tausayi saboda yadda ta koma wani iri, har rama ta yi akan daga daren jiya zuwa safiya, har ta so ta fi Mama shiga damuwa akan lamarin, dan tunda ya zo gidan ko Mama bai gani ba balle a tambayesa ya ake ciki.

Ya ce, "Zan faWa miki in sha Allah, ki je ki ci abinci."

"Bazan iya cin komai ba."

"In Hamma ya ji bazai ji daWi ba."

FaWar hakan da ya yi sai hawayenta ya ?aru ta ce, "ni bazan ci komai ba sai ya dawo."

Ya murmusa bai ce komai ba, dan bazai iya da rigimarta ba, shi yana da saurin hawa yanzu sai ya rufeta da faWa, Saheer Win ne daidai ita.

Ya fita daga gidan ta bishi da kallo, ta koma ta zauna a wajan cikin tunanin da bata san adadin lokacin da ta Wauka a wajan a zaune ba, yana wajan har sai da rana ta fito sannan ta koma ciki.

" " " " " " "

Su Saheer haka suka buWe ido a filin Allah, gwara matan ya ga an tattare su an saka su a wata ?aramar bukka, amma su a wajen suka kwana bayan an Waure musu hannu da ?afa saboda kar su gudu. Suna jere shi da Sudais, dan yaron tausayi yake bashi sosai, bashi da wata magana sai ta ?anwarsa, hirarsa akan ?anwarsa ce, indai zai buWe baki ya yiwa Saheer magana akan ?anwarsa ne.

GabaWaya wari Sudais yake yi, dan babu batun zuwa yin fitsari sai dai ka yi a wajen, kashi ne in sun ga dama za su kwance ka a kara ka da bindiga ka je ka yi ka dawo.

Suna zane a wannan yanayi na rashin sanin me anjima zata haifar musu. A lokacin Magaji ya zo yana kwance musu hannaye saboda zasu ci abinci. Sudaisa ta kawo abinci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login