Showing 198001 words to 201000 words out of 221574 words

Chapter 67 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

133

tunanin a ransa zai amince ta auri Saheer.

Ya shafa kanta ya ce, "Shikenan, ki yi shiru ki bar kuka. Na ji na bar maganar sai Hamman ki ya bayyana. Ki daina kuka." Ta kifa kanta a guiwar Baffa tana kuka sosai.

Ya yi shiru ya ?yaleta tana kukan, sai da ta gaji dan kanta sannan ta Wago ta goge idonta, ta kalle sa ta ce, "Na gode Baffa."

Ya yi murmushi ya ce, "tashi ki je." Ta mi?e a hankali ta fita daga Wakin.

Baffa ya sauke numfashi ya ce, "A haka za a yi auren, bazan zuba ido rayuwarta ta lalace ba. Zuwa nan gaba zata saba, in bata so nan gaba zata so, in bata gane ba nan gaba zata gane Baffa ya faWa yana kallon Inda Islaha ta bi, dan bazai taSa bari ta auri Saheer ba, duk hanyar da ya san zai bi dan kuSutar da Islaha daga auren Saheer zai yi, bazai taSa bari rayuwarta ta lalace ba.

Nana Haleema
[7/28, 12:20/ PM] KRBBK: RDB2P90
Nana Haleema.

"Ki gudu Sudaisa, kina da damar da za ki gudu yanzu, ki tafi bana so wani ya yi nasarar amsa sunan mijin ki."

Sudaisa tana kuka ta ce, "bazan iya ba, bazan iya tafiya na bar ka ba."

"Za ki iya, ki tafi Sudaisa."

"A'a, bazan iya tafiya ba bar ka ba."

Kafin Sudais ya yi magana aka dam?o wuyansa ana jansa a ?asa, Sudaisa ta bi yo bayansu tana kuka ta tarar an ajjiye sa a gaban ArWo da yake zaune.

Aka nuna maaa Sudais ya ce, "Shawara yake bawa amaryar Black akan ta gudu."

ArWo ya kalli Sudaisa ya kalle ta, bai ce komai ba sai ?arar sautin bingida suka ji, Sudais ya faWi a ?asa alamun shi aka harba, ita kuma ta zube a ?asa a sume.

ArWo ya kalli kowa na wajen ya ce, "Na jima ina tausayinsa, amma shi ba ya tausayin kansa. ?arshen mara jin magana kenan, duk wanda ya bawa wani shawarar gudawa ?arshensa kenan."

Ya kalli Sudaisa sa take a sume ya ce, "Ina Wayan nan da nake ganin su a tare? A je a zo dashi."

A lokacin aka je aka Wauko Saheer, ganin gawar Sudais bai san ya fara kuka ba, ga Sudaisa a ?asa a sume. Hankalinsa ya tashi sosai, ya du?a akan guiwarsa yana kuka. ArWo ya ce, "Matar Black ta suma saboda rashin Wan uwanta, na ga kuna shiri da ita, ka rarrashe ta."

Aka zuba mata ruwa ta farfaWo, ta gigice ta mi?e ta yi wajensa tana girgiza shi, ganin da gaske ya mutu sai ta sake suma. Sai da ta suma sau huWu tana farfaWowa, kafin ta koma kamar mahaukaciya, ko magana bata iya yi, saboda alfarmar Sudaisa sirikin black ne aka binne shi da kayana jikinsa ba a cillar dashi ba.

Sudaisa ta zamarwa Saheer kaya, ko yauahe tana kusa dashi bata iya magana, bata cin abinci bata shan ruwa sai kallo kawai. Har lokacin Black bai dawo ba, kuma ArWo ya ?yale ta akan nufinsa. Shi kansa Saheer ya ji mutuwar Sudais, ya yi kuka sosai, yana tuna amanar da ya bar masa.

Har washe gari Sudaisa tana cikin wanann yanayin, ana bawa Saheer damar rarrashinta amma ta ?i ko magana bata yi. Saheer ya yi iya yinsa amma ya kasa taimaka mata, dole ya ha?ura yana yi mata addu'a.

A ranar suka yiwa kowa duka, sannan suka Wauki? video suka turawa ?an uwan kowa dan su ga halin da suke ciki.

" " " " " " "

Sadik da Baffa suna zaune suna tattaunawa akan kuWin fansar Saheer, suna ?o?arin nemo mafita akan abinda yake damunsu. A lokacin Mama da Hanan suka shigo har Islaha.

Kamar jira ake yi su ahigo sai ga kiran waya ya shigo wayar Baffa. Baffa ya kalli wayar gabansa ya faWi, ya kalli Sadik ya ce, "sune fa."

Kowa sai da ?rijinsa ya buga saboda ba a san da abinda suka zo ba, Baffa ya Wauka ya saka a amsa kuwa ya ce, "Assalamu alaikum."

"Wa'alaiki salam. Yauwa na ce ?an uwan Saheer ne ko?."

Baffa ya ce, "su ne."

"Mun turo mu ku video, ku buWe" ya faWa yana kashe wayar.

Sadik ya kunna wayarsa sai ya ga shi nan suka tura video, ya kunna musu suka ga yadda ake dukan Saheer da bulalai ga hannunsa a Waure. Suka dinga kuka, hankalin kowa ya sake tashi.

A lokacin suka sake kiran wayar, Baffa ya Wauka ya ji sun ce, "Mun ga kamar bakwa son Wan ku, in bakwa sonsa sai mu kashe sa."

"Muna sonsa, kuWin ne suka yi yawa."

"Daman mun faWa mu ku yau za mu kira mu faWa mu ku inda za ku kai mana kuWi, an gama haWa kyWin?."

Baffa a sanyaye ya ce, "Ba a haWa ba, kamar yadda muka yi magana da ku bamu da halin waWanan kuWin da ku ka ambata. Mun nemi inda za mu samu kuWin mun rasa, har gidan da mu ka ciki mun saka a kasuwa amma har yanzu ba a tayawa."

"Bakwa son ganin yaron ku kenan?."

"Muna so, amma muna neman alfarmar a rage mana kuWin, baza mu iya biya ba."


"Mun rage miliyan ashirin, za ku ba da miliyan tamanin ranar alhamis. Kun amsa za ku kawo ko mu kashe shi?."

Baffa ya ce, "wallahi su ma ba mu da hanyar su."


"To ai shikenan, za mu kashe shi mu ?ona gawarsa...." Sai ya dakata ya ce, "ku zo min dashi."

Baffa ya ce, "ku yi ha?uri, kar ku kashe shi don Allah."

"naga kun Wauki abin wasa ne ai, bara ku ji daga bakinsa. Kai zo ka yi magana da yan gidan ku, ka faWa musu mutane nawa mu ka kashe a gaban idanuna."

Saheer saboda wahala da tashin hankalin da yake gani, da damuwa rauni da yunwa, ruWewar mutuwar Sudais, tashin hankali da damuwar da ?anwar Sudais ta shiga, cikim gajiya da sanyin jiki ya ce, "Baffa na san ba ku da hanyar wannan kuWin da suka faWa, na san babu inda za a same su. Kar ku tayar da hankalin ku, kawai ku bari su kashe ni Win daman lokacina ne....." dakata ya yi da magana saboda bindigar da suka buga masa a kai. Saheer ya yi ?ara wacce ta ratsa kunnensu gabaWaya.

ArWo ya ce, "Mu za ka yiwa wannan maganar? Sai mu karSi kuWin kuma mu kashe ka, kuma mun kaahe banza da wofi."

ArWo ya ce, "Ba ku ga irin dukan da mu ka yi masa ba ko?."

Baffa murya tana rawa ya ce, "Mun gani."

"Kuma har yanzu ku kasa haWa miliyan tamanin?."

"Ba mu da ina zamu samu."

ArWo ya ce, "Shikenan, mun dawo hamsin, daga nan ba za mu sake rage mu ku komai ba. Za ku kawo kuWin ko mu kashe sa, baza mu ?ara mu ki lokaci ba, in dai ba a kawo kuWin nan ba zamu kashe shi. Ba mu Wauko shi dan mu dinga ciyar dashi a banza ba, da kun ba da kuWi da yanzu ya dawo.

Baffa zai yi magana Islaha ta firgita ta fizge wayar daga hannunsa, jikinta yana rawa, muryarta tana rawa, hannunta yana karkarwa ta ce, "Kar ku kashe sa, za mu kawo mu ku in sha Allah. Kar ku kashe Hamma, ku ?yalesa zan nemo kuWin na kawo."

Ya yi dariya ya ce, "Yauwa Yarinya, ke kaWai ki ke son Wan uwan nan na ki. Za mu sake kiran ku." Ya faWa yana yanke wayar.

Islaha ta cillar da wayar, jikinta yana rawa kamar wacce aka jonawa wutar lantarki, ta rasa inda zata saka kanta, ta rasa me zata yi ta ji daWi, sai kai kawo take tana tunanin mafita.

Muryar ta tana sar?ewa, numfashin ta yana barazanar barin jikinta, yana sar?e mata maganar da take kan harshenta.

Ta kalli Baffa a wannan yanayi ta ce, "Baffa zan nemo kuWin, zan yi komai saboda Hamma, zan je na nemo miliyan hamsin a duk inda take a kai? musu, in dai za su saki Hamma, zan nemo."

Baffa ya ri?e kafaWunta ya ce, "ba ki da hanyar Islaha, ba naira dubu hamsin aka ce ba, ba dubu Wari biyar aka ce ba, ba miliyan biyar aka ce ba, miliyin hamsin suka ce. Miliyan Way Way sau hamsin. Islaha ba ki da hanyar da za ki samu waWanan kuWin, ki karSi ?addara ki cigaba da yi masa addu'a, in yana da sauran kwana a duniya Allah ya kuSutar dashi, in kuma babu Allah ya sa ?arshen wahalarsa kenan."

"Bazan iya ba Baffa, zan nemo kuWi ne a ko ina suke, na yarda zan yi ko meye indai zan samu kuWin. Bazan iya bari rayuwar Hamma ta salwanta ba, bazan iya zuba ido Hamma yana cikin wani hali na ?yalesa ba, bazan iya ganin Hamma yana neman taimako na Wauke kaina ba......"

Ta girgiza kai tana ja da baya tana kallonsu tana hawaye duk a lokaci Waya ta ce, "Zan nemo miliyan hamsin, ko raina ne zan bayar indai shi zai dawo" ta faWa tana fita daga falon da sauri.

Baffa ya kalli Sadik ya ce, "Sadik ka bi bayana don Allah, kar bari ta je ko ina, ka dawo da ita."

Da sauri ya bi bayanta ya samu zata fita daga gidan, ya yi sauri ya cimma ya ce, "ina za ki je?."

Muryarta tana rawa tana kuka mai tsanani ta ce, "zan je na samo kuWin ne."

"A ina za ki samu? Ba ki da hanyar da za ki samu wannan kuWin."

Sai ta sake fashe masa da sabon kuka ta ce, "haka zan bar Hamma kenan a kashe sa a banza? Haka zan bari Hamma yana neman taimako na ?yalesa? Haka zan bari suna dukan Hamma na kasa yin komai?. Meye amfanina a duniya in ban sadaukar da farin cikina akansa ba, meye amfanina a duniya in ban fito da Hamma daga cikin halin da yake ciki ba?. Ni bazan iya ?yale Hamma a wanann yanayin ba, babu amfanin zamana a duniya bayan na kasa taimaka masa, wallahi bazan iya ba" ta faWa tana rufe fuskar ta da hannunta, ta dur?ushe a wajen tana kuka sosai.

Sadik ya ce, "ha?uri za ki yi, babu abinda za ki iya a kan hakan."


Bata ce komai ba sai kuka, sai da ta ga ji sannan ta mi?e zunbur ta kalle shi ta ce, "ina da mafita, ban sani ba ko za ka bani goyan baya akan abinda zan faWa maka."

Ya kalle ta ya ce, "in dai hanyar bata saSawa Allah ba ce zan amince, ina jin ki."

Ta ja numfashi mai tsaho ta sauke shi a hankali, ta rufe ido tana tunanin yadda zai Wauki maganar, ta buWe iso ta ce, "Ahlin gidan AbdulAziz Yola suna da kuWin da za su bani miliyan hamsin?."

Ya Wan kalle ta cikin mamaki abinda ta ce ya ce, "su za ki je su ba ki kuWin?."

Ta girgiza kai ta ce,  ka amsa min Hamma Sadik."

Ya ce, "Suna dashi mana, meye miliyan hamsin a wajansu?."

Ta yi shiru na wani lokacin, ta rufe ido ta buWe tana furzar da iska. Ta kasa magana, ita kanta bata son furta abinda zata ce, amma kuma ya zamar mata dole ta yi, dan ita kaWai ce hanyar da zata bi dan karSo Hamma, akan Hamma zata iya ba da ranta.

Ta sake rufe ido ta buWe, ta kalle shi ta ce, "Ai daman na faWa mu ku batun aurena da suka zo nema, kuma shi wanda za a aura min Win da kansa ya kawo maganar auren contract na wata biyar& ..

Ta dakata tana ji zuciyarta tana bugawa, ta ja numfashi da ?arfi ta ce,  Zan karSi auren contract Win da ya yi min tayi, zai aureni saboda mahaifinsa, ni kuma zan auresa inda zai bani kuWin fansar Hamma!."

Sadik ya bita da kallo ganin kamar bata cikin hankalinta ne ya saka ta ke wannan maganar. Ya tausasa murya ya ce, "ki Wan samu waje ki zauna Islaha, kamar ba nutse ki ke ba."

Ta ce, "a nutse nake, ina faWa ma ka ne kar na je na yi a bayan idonka daga baya kai da Hamma ku dinga ganin laifina har ku dinga zargina da mummunan abu, shiyasa na sanar da kai abinda zan yi. Ba wai shawara nake nema ba, na faWa maka ne dan ka sani, na riga na gama yanke hukunci a zuciyara. Zan amince na yi auren, shi kuma ya bani kuWin da za a karSo Hamma. Bayan wata biyar in muka rabu, sai na dawo na auri Hamma."

Sadik dai kallon ta yake yi dan har lokacin bai yarda a nutse take ba. Ya ce, "wannan maganar bata da ma'ana Islaha, kina musulma ina ke ina auren yarjejeniya?. Kuma shi mahaukacin ina ne da zai Wauki kuWi masu yawan waWanan ya ba ki dan kawai ki aure sa?."

Ta kalle sa ta ce, "kai ka ce min a wajansu miliyan Hamsin ba komai bane."

"Dan na ce haka ai ba hakan yana nufin zai yu bane, kawai dan za ki auresa sai ya ba ki waWannan kuWin?. Islaha ki nutsu don Allah."

"A faWa maka a nutse nake, kuma haka na yanke, kuma hakan zan yi. Bazan bar ran Hamma ya salwatanta a banza ba, tunda dai auren ba mai Worewa bane zan jure saboda Hamma. Na riga na yanke hukunci akan zan yi Win, ina faWa maka ne dan ka zama shaida koda Hamma zai dawo ya ce ban kyauta masa ba. Ka zama shaida, na yi ne saboda shi, kuma zan dawo gare shi ba tare da komai ya same ni ba."

Sadik ya ce, "Islaha wannan ba shawara mai kyau bace, akan me za ki yi irin wannnan auren kamar a Kdrama ko american series?....."

"Akan Hamma zan yi, kana ganin yadda suke dukansa, kana ganin yadda Hamma ya rame kamar ba shi ba, kana ganin yadda Hamma ya koma kamar wanda ya shekara yana ciwo. A kansa zan sadaukar da kaina balle auren wata biyar."

"Islaha ke za ki aurar da kanki? Ko za ki cewa Baffa auren jarjeniya za ki yi saboda Saheer?. Ba Kdrama bane, ki nutsu ki fahimci a Yola ki ke."

Ta kalle sa ta ce, "ka Wauka Kdrama Win ne kawai, ka Wauka film ka ke kallo kuma ni ce jarumar ciki. Baffa ya amince da auren, zan ce masa na amince ba tare da ya san ?udurina ba. In dai har zai bani kuWin fansar Hamma zan yi, Hamma Sadik!."

"To shi waye wanda za ki aura Win? A cikin ?a?an Abdul Aziz Yola wanne za ki aura har da ki ke ganin zai ba ki miliyan hamsin lokaci Waya?."

Islaha taWan ja numfashi sannan ta lumshe ido ta ce,..

Nana Haleema.
[7/28, 12:20/ PM] KRBBK: RDB2P91
Nana Haleema.

Ganin ya zuba mata ido yana jira ya ji sunan da zata faWa sai ta Wan Wauke kai zuciyarta tana faWa mata ba yanzu ba, kar ta faWa masa sunan ko waye sai ta ce, "faWar bata da wani amfani, na faWa maka ?udurina dan ka zama shaida, zan yi abinda nake ganin shine daidai."

Sadik ya ce, "Kar ki dakusa rayuwarki, ki jira mu ga abinda Allah zai yi."

Ta Wan murmusa ta ce, "akan Hamma zan iya yin komai, ba dakusar da rayuwata ba, in rasa rayuwata ne zan iya yi indai a kansa ne. Bazan iya jira ba, zan jarraba wannan Win, in ya yu daman haka nake fata, in bai yu ba sai na gwada wani." Ganin ya shiru ya kasa magana, sai ta koma da baya ta koma cikin gidan da sauri.

Tunda ta koma take kai kawo a Waki, Sangare Waya na zuciyarta yana faWa mata abinda zata yi ba daidai bane, Waya Sangaren ya faWa mata hakan shine daidai, in ba ta aikata ba a ina za a samu kuWin da za a karSo Hamma?.

Ta kawar da tunanin kar ta aikata, ta ?arasa jakar ta ta buWe, ta Wauki biro da takarda ta zauna tana rubutu a kai.

Bayan ta gama rubutawa ta karanta yadda ya kamata, ta ajjiye takardar tana ajiyar zuciya a hankali a hankali. Kamar lokacin da zata tafi Jeddah, haka wannan lokacin ma ko kaWan ta ?i bawa zuciyarta damar da zata ce tunaninta ba daidai bane, ta dage akan ?udurinta, ta dage akan abinda take kai shine daidai, ta ?i amincewa da ba kan daidai take ba.

Haka ta gama zamanta a Wakin, sannan ta kwana a kan gadon ta yi shiru tana tunanin halin da suka ga Hamma a ciki. Sai kuma ta mi?e ta yi alwala ta zo ta tayar da sallah raka'a biyu, bayan ta idar ta karanta addu'ar da annabi ya koyar damu domin neman zaSin Allah, ta nemi zaSin Allah akan abinda ya zama alkhairi sannan ta kwanta.

Washe gari tana tashi wanka ta yi a gaggauce, ta saka hijjab ta Wauki handbag Winta ta fita da sauri ta fita. Da farko gidan tv ta fara zuwa, ta Wan jima a can sannan ta tafi asibiti. A can ma ta Wan jima sannan ta fito ta dawo gidansu Safeera ta kira Saleem a waya.

Saleem Wauka ta ce, "Hamma Saleem don Allah email address Win Jafar za ka bani."

Daga can Sangaren ya ce, "Wanne Jafar?."

"Wanda mu ka gani a diamond hotel, lokacin da mu ke neman Rehaan Yola."

"Okay, bara na duba in na gan shi zan turo miki. Amma yana jimawa jafin ya buWe mail, sai a kwashe sati Waya bai amsa ba."

"Na gode" tana faWa ta kashe wayar.

Safeera ta ce, "kin ce za mu yi magana kuma kin yi shiru, wani abun ne ya sake faruwa?."

Ta kalle Safeera sannan ta ce, "Jiya sun ce in ba a ba da kuWin fansar Hamma za sa kashe sa, har video suka turo suna dukansa."

Safeera cikin damuwa da sanyin jiki ta ce, "WaWnanan mutane Allah ya shiga tsakaninmu dasu......"

"Amin."

"Yanzu ya ake ciki, An samu kuWin?."


"Ba a samu ba. Amma ni zan samo."

Safeera ta ce, "ban gane ba, a ina za ki samu miliyan Wari?."


"Sun rage hamsin, miliyan hamsin ne yanzu."


"Ina za ki samo waWanan kuWin?.

Islaha ta yi shiru bata amsa ba, dan bata san da wacce fuska zata fahimta ba, kuma ta san halin Safeera in ta faWa mata zata dinga kushewa, ta dinga yi mata wa'azi ita kuma bata so.

Safeera ta ce, "ko saudian za ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login