Showing 132001 words to 135000 words out of 221574 words

Chapter 45 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

115

wallahi sai dai duk abinda zai faru ya faru, amma bazan taSa bari Saheer ya auri Islaha ba!" Tana faWa ta shiga Waki dan nemo mafita.

Baffa bayan sun fita ya kalli Saheer ya ce, "ba ka gama haWa lefen ba?."

Saheer ye ce, "an gama Baffa, daman kuWin aikin ka ne ya tsayar da komai. Amma ka yi ha?uri kar ka yanke hukunci cikin fushi, ka kwnatar da hankalinka saboda lafiyar ka."

Baffa ya kalle shi ya ce, "kana son Islaha ko babarka ta saka maka zargi ta?."

Ya girgiza kai ya ce, "Har abada bazan taSa zargin Islaha ba, na san halinta fiye da kowa."

"Kana sonta ko baka so?.

"Baffa kaima ka san amsa ta akan hakan."

"Ka shirya karSar aurenta a yau?."

"Ko yanzu ne a shirye nake?."

"Za ka iya jira har sai ta dawo da auren ka akanta ko baza ka iya ba?."

Ya sauke numfashi ya ce, "akwai yarda a tsakanina da ita, wallahi ko shekara dubu zata yi da aurena a kanta zan jira har ta dawo."

Baffa ya murmusa ya ce, "da zarar ta kira ka ka sanar dani, zamu yi magana da ita, bana so na yanke hukunci ya zama kamar ban kyauta mata ba. Amma da yanzu yadda zan fita masallacin nan, wallahi bazan dawo ba sai igiyoyin auren ka uku sun hau kanta, daga nan sai babarka ta saka bindiga ta kashe kanta."

Saheer ya murmusa, wani irin daWi yana mamamaye masa zuciya, Allah Allah yake ya fita ya sake kiran Islaha.

Baffa ya ce, "Jeka, in ka same ta kazo ka haWa mu."

Ya gyaWa kai ya fita yana sake kiran wayarta amma bata Wauka. Ji yake kamar ya shiga cikin wayar ya jawota ta Wauki wayar, gabaWaya zumuWi da shau?in aura masa ita a ranar ya cika masa zuciya.

(Tofa, ana wata ga wata>?#?)

" " " " " " "

Islaha lokacin da Saheer yake yi mata waya suna kitchen ita da Sunaira, ta bar wayar a Waki bata san yana kira ba. Sallar la'asar ce ta shigar da ita ciki, kuma bata kalli wayar ba ta yi alwala ta yi sallah ta zauna tana azkhar. Har biyar na yamma tana zaune, Sunaira ta shigo ta yi mata tayin fita su je Mall su dawo, Islaha ta amsa ta mi?e ta saka hijjab suka fita.

A ?asa suke tafiya a hankali, ba hira suke yi ba dan ko wanne bai iya yareen wani ba, har gwara Islaha yanza ta Wan iya ?ananun abubuwa a kalmar larabci.

Islaha kallon estate Win take yi sosai, ya tsaru iya tsaruwa, kai ba sai an faWa maka gidan da suke wajan suna da tsada ba. Sai da suka yi nisa suka hau mota suka tafi. Sai da suka shiga mota ta tuna ta bar wayar ta a gidan, ta ji haushi sosai dan ta so ta Wan yi video ta samu na streaks.

Waye mai nasara? Daada ce ko Baffa?.

Nana Haleema
' [7/15, 11:52/ AM] KRBBK: RDB2P58
Nana Haleema.

Islaha basu dawo ba sai magrib, a ?ofar gidan Rehaan motar ta ajjiye su, ta harari gidan cikin jin haushin mai gidan da abokinsa, suka shiga ciki suna ajjiye komai a mazauninsa.

Sai da ta yi sallah sannan ta Wauki wayarta, ta wara ido ganin kiran Hamma babu adadi. Da hanzari ta kira sa, ta yi ringing bai Wauka ba har ta katse. A bayyane ta ce, "Allah ya sa ba laifi na yi masa ya ?i Wauka ba."

Kafin ya kira ta sai ga kiran Umma, Islaha ta Wauka da sallama ta ce, "Umma ina yini."

Umma a sanyaye ta ce, "Lafiya Lau Islaha, ya zaman Jeddah?."

"Lafiya lau Umma."

"Ya ?awar ki? Kuna waya kuwa?."

"Eh muna gaisawa, bata kira ki ba?."

"tunda na zo sau biyu kawai muka yi waya. Islaha zaman ?asar nan gabaWaya ya ishe ni, ina so na samu hanyar da zan koma gida, amma abin ya ci tura."

Islaha ta sauke nunfashi ta ce, "Ina so nazo na gan ki Umma, na yiwa Safeera al?awarin an ba ki kulawa daidai ?arfina. Ina so na zo ban san yaushe ba, kuma ban san a inda ki ke ba."

Umma ta ji daWi ya mamaye ta, ta ji kamar an ce Islahan ta zo, ta ce, "Allah ya kawo ki Islaha, sunan unguwar wai Khadiyya, in ki ka shigo sai ki kira ni, an koya min yadda ake tura location ta whatsapp."

Jin yadda Umman take murna daga cewa zata zo sai zuciyar Islaha ta karye, ta ji ranta dole ma ta je Madina ganin Umma. Ta ce, "zan zo in sha Allah Umma."

Umma ta ce, "na gode Safeer....su Islaha, sai na ganki." Daga nan suka yi sallama ta kashe wayar.

Tana kashewa kiram Saheer ya shigo, tana Wauka ya ce, "ina ki ka shiga ne? Tun Wazu nake yi miki waya bakya Wauka."

"Ban ga kiran ba sai yanzu, dan yanzu na dawo daga mall, sallah kawai na yi."

"Baffa ne yake son magana dake tun Wazu."

"Wallahi ban gani ba, yana ina yanzu? Ka haWa ni dashi."

"lokacin sallar magriba ya taho, kin san da huri yake shiga masallaci."

"amma ban ji daWi ba."

"kin san meyasa yake neman ki?."

Kamar tana gabansa ta girgiza kai alamun a'a ta ce, "ban sani ba."

Ya ce, "bara na kira ki video call."

Bai jira me zata ce ba ya yanke wayar, ya kira ta ajjiye wayar tana kallonsa, ta Wan yi murmushi ta ce, "Hamma kullum ?ara kyau ka ke yi, meye sirrin?."

Ya yi murmushin da yake ?ara masa kyau, ya Wan girgiza kai yana kallon ta da fararen idanunsa ya ce, "ni ba ta wannan tsokanar ta ki bake yi ba, Kin san meyasa Baffa yake neman ki?."

"sai ka faWa Hamma."

Ya yi murmushi yana shafa kansa yana kallon ta cikin shau?i mai yawa, iya faWa mata maganar da zai yi ma shau?i yake ji, ina ga an Waura kuma?. Islaha ta shagwaSe fuska jin ya ?i faWa mata, ta ce, "ka faWa min mana."

Ya ce, "Da ace Wazu kin Wauki wayar, daman tambayar ki zai yi, in za ki amince a Wazun za a Waura aurenmu dake bayan sallar azahar. Shiyasa na dinga jera miki kira amma amma ban same ki ba, wallahi ji na yi kamar na zo na Wauko ki."

Haka kawai ta ji gabanta ya faWi matu?a ta buWe ido waje tana dafe ?irji ta ce, "Aure Hamma!."

Shima ya buWe ido kamar yadda ta yiya ce, "Eh mana."

Islaha ta ce, "da gaske ka ke?."


"Na taSa yi miki wannan wasan?."


"Baka taSa ba, abin ne na ji sa har jinina, wallahi gabana sai faWuwa yake yi."

Ya harare ta ya ce, "Meye na faWuwar gaban? Bakya son auren nawa ne?."

Ta girgiza kai ta ce, "Abin ne yazo min coincidences, ban taSa tunanin hakan ba shiyasa. Kuma da gaske Baffa yake?."


"Wallahi da Wazu da kin Wauki wayar da na yi miki, kin kuma amince, da yanzu kin zama matar Saheer" ya faWa yana zuba mata ido.

Sai kallon ya yi mata nauyi sosai, ta sauke ido ?asa tana wasa da abin hannun da ya bata.

Saheer ya bita da kallon mamaki ya ce, "Hmm! Da ace Baffan ma ya yi magana dake cewa za ki yi ba ki amince ba ko?."

Ta Wago ta kalle sa tana zaro idanu ta ce, "Ni haka na ce?."

"Gashin nan kin zama wani iri daga ba ki labari."

"Kawai jikina ne ya yi sanyi, amma da a guje zan amince."


"Meye na sanyin jikin? Aure fa kawai za a Waura, kina nan Jeddah ina Nigeria. Sai kin dawo sannan za a yi biki."

Ta sauke kai ?asa ta ce, "Hamma duk inda aka ce za a Waura aure, ai dole jiki mace ya yi sanyi."

"yanzu in ya tambaye ki me za ki ce? Kin amince a Waura yanzu ko sai kin dawo?."

Yadda ya zuba mata ido ya saka ta kasa cewa komai, in dai a ra'ayinta ne baza ta yarda a Waura mata aure yanzu ba gaskiya, ta fi so sai ta gama komai da yake gabanta, dan ta san halin Hamma da kishi, in aurensa ya hau kanta wani abun bazai bar ta ta yi ba, musamman Sangaren da Barr zai shigo ciki. Amma baza ta iya ?in amincewa ba, zata amince ko dan saboda Hamman yana so, daga jin yadda yake bata labari cikin zumuWi ta san ya ji daWin maganar sosai.

"Beddo am!."

Ta kalle sa ya ce, "Tunani ki ke yi akan za ki amince ko baza ki amince ba?."

Ta yi murmushin dole ta ce, "A'a, kawai ina tunanin yadda zan fara rayuwa da auren ka a kaina a ?asar nan ne, dan ni na hango har an Waura auren."

Sai kuwa fuskarsa ta washe, annuri da farin ciki suka bayyana akan fuskarsa sosai. Ya gyara zama ya ce, "Ni kaina ina lissafin yadda zan ji kewar matata a kusa dani, har na siyi bankin da zan fara tara kuWin da zan zo Saudia wajan matata."

Ta yi dariya sosai, shima dariyar ya yi ya ce, "Ni dai kar ki kwafsa min, in Baffa ya tambaye ki ki tausaya min ki amince don Allah. HaWuwa ta gaba ina so ya kasance da aurena a kan ki, yadda zan nuna miki adadin kewar ki da na yi ba tare da kin ce, Hamma babu kyau fa" ya ?arasa faWa yana kwaikwayon muryarta.

Dariya ta yi sosai tana rufe fuska da hannunta, ya yi murmushi yana kallon kyawawan hannayenta marasa kauri dogaye.

Cikin sanyin murya ya ce, "?arya na yi, ba haka ki ke faWa ba?."

Ta cire hannunta tana su?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 nkuyar da kai tana murmushi ta ce, "Amma meyasa Baffa ya ke son a Waura aurenmu a yau?."

"Mama ce wallahi, itace ta tunzura shi har ya yanke hukunci.....Islaha ana kiran sallah, in an idar zan kira na haWa ki da Baffan." Ta amsa da to ya kashe wayar.

Ta jingina da gado tana tunanin wannan sabuwar chakwakiyar da ta kawo mata kai, Allah ya sani bata ra'ayin wedding fatiha before ceremony. Kuma ana Waura auren nan takura ta Hamma zai yi, duk da bashi da matsala da aikin ta amma akwai mutanen da zai iya hanata magana dasu, kuma dole ta hanu tunda matarsa ce. Kuma yadda yake nuna shau?inta a kwanakin nan bazai iya barinta har sai an yi biki bai yi mata komai ba, ita kuma bata son hakan Allah ya sani. Tana wannan tunanin aka yi sallar i'sha.

Ta san daman bazai kira ta ba sai bayan sallar i'sha ta nigeria, saboda Baffa ba ya dawowa daga masallaci sai ya yi sallar i'sha.

Ko ya wayarta ta yi ?ara sai gabanta ya faWi, gabaWaya bata so kiran Saheer ya shigo kwata kwata, dan bata son ya haWa ta waya da Baffa. A haka ta mi?e ta je suka ci abinci dan har lokacin matar gidan basu dawo ba.

?arfe sha Waya na Saudia, wanda ya yi daidai da tara na Nigeria. kiran Saherr ya shigo, tana kalla gabanta ya faWi ta ji kamar kar ta Wauka, ta runtse ido ta buWe, ta Wauki wayar a sanyaye ta sama a kunne.

Tana sakawa a kunne Baffa ya ce, "Islaha."

?irjinta ya buga da ?arfi, ta Wan runtse ido sannan ta ce, "Baffa barka da dare."

"Barka dai Islaha, ya aiki?."

"Alhamdu lillah, ya ?arfin jiki?."

"Jiki ya warware Islaha."

"Allah ya ?ara lafiya."

"Amin Islaha, yaushe ne dawowar ta ki?."

Islaha ta ce, "na kusa in sha Allah."

Baffa ya murmusa ya ce, "Allah ya dawo dake lafiya."

Ta amsa da amin sannan ya ce, "Islaha wani hukunci nake so na yanke a kan ki da Hamman ki, shine na kira na ji ra'ayin ki a kai."

Islaha ta ce, "Baffa kana da dama da ikon yanke ko wanne hukunci a kaina, ba sai ka tambaye ni ba, kawai ka yanke min hukunci a matsayin ka na uba a gare ni."

"Na sani Islaha, na san na isa dake gaba da baya. Amma hakan bazai saka na tauye ki ba, dan kina yi min biyayya hakan bazai saka na cutar da rayuwar ki ba. Ki faWa min ra'ayin ki, kina so a Waura auren yanzu ko sai kin dawo?."

"Baffa wallahi na ba ka zaSi, ka zaSa min abinda ka ga ya yi daidai dani."

Baffa ya yi murmushi mai sauti, ya ce, "baza ki zaSa Win ba ko?."

Islaha kamar tana kusa dashi, ta sake sunkuyar kai ta ce, "Baffa ka zaSa min kawai, na san baza ka yi min abinda zai cutar dani ba."

Baffa ya yi murmushi cikin jin daWi da farin ciki ta ce, "Shikenan Islaha. In Allah ya nuna mana jibi juma'a, bayan sallar juma'a za a Waura auren ki da Saheer. Hakan ya yi miki?."

Gabanta ya faWi, ta runtse ido ta ce, "Ya yi Baffa. Allah ya nuna mana, Allah ya ?ara maka lafiya da tsahon rai mai amfani."

"Amin Islaha. Allah ya yi miki albarka, ya cigaba da ba ki kariya a duk inda ki ke." Ta amsa da amin kafin su kashe wayar.

Baffa yana kashe wayar ya kalli Saheer da yake kusa dashi, ya yi murmushin jin daWi ya ce, "Yarinya mai tarbiyya, ina ji a raina ina Islaha ?ata ce, ina ma ni ne na haife ta."

Saheer ya murmusa yana ji kamar ya mi?e ya taka rawa saboda murna, ji yake kamar ya jawo jibi ta zo Islaha ta zama mallakinsa.

Baffa ya ce, "gobe zan aika ka a siyo goro da alewa na Waurin aure, jibi babu abinda zai saka a dakata daga Waura muku aure in sha Allah."

Ya yi murmushin jin daWi da farin ciki ya ce, "Allah ya kaimu Baffa."

Baffa ya ce, "Amin. Ka je ka sanar da waWanda zaka sanar, dan lokacin ya ?ure ba sai an yi gayya gagaruma ba, in bikin ya zo sai a yi taro."

Cikin zumuWi ya mi?e, yana ji kamar ya rungume Baffa dan daWi da farin ciki. Saheer yana fitowa suka haWu da Mama a tsaye da alama ta ji komai. Ya sunkuyar da kai ita kuma ta ce, "biyo ni."

?irjinsa ya buga da ?arfi, ya bita a sanyaye zuwa falon ta. Suna shiga ta juyo ta kalle sa ta ce, "Ban amince da auren Islaha ba, ban amince ka aure ta ba Saheer. Ka je ka samu mahaifinka, ka faWa masa baza ka aure ta ba."

Ya buWe ba ki zai yi magana ta ce, "Wallahi in ka amince da auren nan sai na tsine maka, ka ji na ce wallahi, babu abinda zai saka na dakata dafa tsine maka albarka Saheer, in kana ganin bazan iya ba ka aikata Saheer!."

Saheer ya zare ido yana kallon Mama jin abinda take faWa, ya haWWiye yawu da?yar, yana ji idanunsa suna cikowa da ruwa, ya buWe baki zai yi magana ta ce, "kar ka ce min komai, ikon da nake dashi a kanka nake so na gani. In har kana jin tsoron bakin uwa kar ka amince, in kuma baka jin tsoro tsinuwata ka aure ta ka ji!" Tana gama faWar hakan ta shiga Waki.

Saheer ya bi ta da kallo, yana ji zuciyarsa tana girgiWi kamar zata faWo daga ?irjinsa, ya sauke numfashi mai tsaho, yana ji kamar wuta ce a kusa dashi saboda tiririn sa yake ji, ya ja ?afarsa da?yar ya fita daga falon, yana ji kamar ya yi kuka.....

Ga ?oshi, ga kwanan yunwa=?)?>?-?>?#?
[7/16, 12:11/ PM] KRBBK: RDB2P59
Nana Haleema.

Saheer a sanyaye ya fita ?ofar gida, ya tarar da Sadik a zaune a mota yana jiransa, ya shiga motar yana jan numfashi mai tsaho. Sadik bai kula da yanayin da yake ciki ba ya ce, "An kawo kaya, zamu tura zuwa inda ya kamata. Ka ga list Win mutanen da...." Maganar Sadik ta ma?ale ganin ko kallonsa ma ba ya yi.

Sadik ya ce, "Yane?."

"Akan maganar Waurin auren nan ne."

"Ba ka son auren nata ne kuma ko meye?."

Ya kalle sa ya ce, "a duniya akwai mai son auren Islaha in ba ni ba?."

Sadik ya ce, "to meye na damuwa akan hakan?."

Ya sauke numfashi ya ce, "Islaha ta amince auren....."

Sadik ya tari numfashinsa, bai bari ya ?arasa ba ya ce, "daman ya za a yi ta ?i amincewa? Ai dole ma ta amince da auren, tunda ta gama...."

Cikin tsawa ya ce, "ya ishe ka malam!."

Sadik ya murmusa ya ce, "to na yi shiru, ina ji."

Ya yi masa banza ya ?i magana, Sadik ya yi dariya ya ce, "ina da abin yi, in baza ka faWa ba na kama gabana."

Saheer ya sauke numfashi ya ce, "Baffa ya ce jibi za a Waura aurena da ita, Mama kuma ta ce indai aka Waura auren sai ta tsine min."

Sadik ya zaro ido cikin kiWima da mamaki ya ce, "kai! Abin har ya kai ga haka?."

Saheer bai ce komai ba sai lumshe ido da ya yi ya buWe sannan ya ce, "ban sani ba, ban san me zan yi ba yanzu."

Sadik ya ce, "Ha?ura za a yi zuwa lokacin da zata janye kalamanta, ai ba a yi auren ka Islaha tana wannan fushin ba, ga furucin da ta yi a kan ka, dole sai mun jira ta janye sai a san abinda ya kamata ayi."

Saheer ya Wan Waga kai ya ce, "Sai abinda Baffa ya ce, ni wallahi kam kaina ya kulle."

Sadik ya ce, "Dole kan ka ya kulle, kana son Islaha, ga damar aurenta ka samu, amma Mama ta hana. Sai ha?uri, ka cigaba da addu'a kawai."

Saheer ya yi shiru yana kallon ?asa, ya rufe ido ya buWe zuciyarsa tana bugawa da sauri sauri. Ya kalli Sadik ya ce, "Ina son Islaha Sadik, rasata daidai yake da rasa rayuwata gabaWaya."

Sadik ya ce, "Haka zalika Mama mahaifiyarka ce, tsinuwar ta daidai yake da tarwatsewar rayuwar ka."

"Na sani, ba ina nufin na zaSi Islaha akan Mama ba, kawai dai ina faWa maka yadda nake sonta, in na rasata ban san wanne hali zan shiga ba."

Sadik ya taSe baki, dan shi gabaWaya Islaha ta sire masa, da abokinsa zai yarda ma da ya ce masa ya nemi wata wallahi. Bai yarda da ita ba, akwai abubuwan da take Soyewa, kuma tana da Soyayyiyar Wabi'a wacce bata so a san da ita.

Saheer bai kuma cewa komai ba ya fita, Sadik ya yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login