Showing 186001 words to 189000 words out of 221574 words

Chapter 63 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

116

"Kwana biyu suka bayar."

Sadik ya ce, "in sun kuma kira mu faWa musu ba mu da halin wannan kuWin su taimaka su rage, in aka yi sa a zasu rage. Tunda daman ciniki ake yi dasu, ba da sun faWa ake Wauka a bayar ba."

Baffa ya sauke numfashi bai ce komai ba, dan bai san wanne irin tunani zai yi akan haka ba. Abinda suke ji a waje ga shi ya zo gidansu, har cikin Wakinsu. Sadik ya dinga rarrashin Baffa ganin ya Waga hankalinsa sosai, shi kansa hankalinsa a tashe yake, amma yana Soyewa ne saboda halin da Baffa yake ciki.

" " " " " " "

Suna kashe wayar suka kalli Saheeer ArWo ya ce, "Baban ka ya ce basu da miliyan Wari, kuWi sun fi ranka kenan."

Saheer ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Basu da wannan kuWin, basu da hanyarsa."

"Ba bafulatani bane? Ya siyar shanunsa mana."

"Ranka ya daWe wanne shanu ne zasu yi miliyan Wari a wannan lokacin?."

ArWo da yake goge bindiga ya kalle sa ya ce, "in ba a kawo ba za a cilla ka cikin ramin marasa amfani."

A lokacin wani matashi ya ?araso wajen da machine, ArWo ya kalle su har suka ?araso. Aka gurfanar da matashin a gaban ArWo. ArWo ya yi murmushi ya ce, "Barka da zuwa."

Mutumin ya Wan dake ya ce, "Barka ranka ya daWe."

"KuWin fansar Bala ka kawo ko?."

"Sune ranka ya daWe."

"Nawa ne?."

"Miliyan biyar aka ce, da waya guda huWu, da wannan machine Win" ya faWa yana nuna machine Win da ya zo a kai.

ArWo ya ja jakar ya buWe ya ga dubu dubu ne a ciki, ya Wauke wayoyin ciki yana kallonsu sabbabi duk a kwalayensu. Ya tura masa kuWin ya ce, "ka lissafa, naira Waya in babu ka yi kuka da kan ka." Mutumin ya fara irga kuWin kamar yadda aka ce, yana yi yana gumi jikinsa yana rawa sosai.

A lokacin Magaji ya ?araso wajen ya ce, "ArWo mai cikin can da take cikin matan can ta haihu, ta samu Wa namiji amma ita ta koma."

ArWo ya ce, "Har yanzu ba a Wauko mana likitoci ba? Har yanzu ba a samu mai amfani a cikin san?ammmun ba?."

Kafin Magaji ya yi magana ya kalli Saheer ya ce, "Kai baka iya aikin asibiti ba?."

Saheer ya ce, "Ban iya ba."

"Mtsw! Ba ka da amfani."

Ya kalli ba?o da yake irga kuWi ya ce, "Ba?o fa, ka iya likitanci?."

Ya Wago ya kalle sa jikinsa yana karkarwa, ArWo ya ce, "Kar ka ji tsoro, babu abinda za mu yi maka, in ka iya likitanci ka taimaka mana ka duba wacce ta haihu."

Murya tana rawa ya ce, "Na iya."

Ya yi dariya ya ce, "Dakyau ba?o...Magaji a Wauke shi a je dashi ya duba ta, ina akwai wanda bashi da lafiya yau mun samu likita. Bar irga kuWin, alfamar likitancin da ka iya ko nawa ka kawo mun karSa." Aka tafi dashi inda matar ta haihu.

Ya je ya same ta a kwance kaca kaca cikin jini, ga matan sun zagaye ta suna kallo, ga jaririn an naWe shi da Wankwali yana ta kuka, ita kuma tana kwance tana jan numfashi da?yar. Ya duba ta ya kalli Magaji ya ce, "Da ranta, ba mutuwa ta yi ba, gajiya ce da yunwa, tana bu?atar a saka mata ruwa."

"Mu je a faWawa ArWo."

Tare suka dawo wajen ArWo aka faWa masa, ya Wan Waga kai ya ce, "Tunda bata mutu ba a ?yaleta kawai, ina da ciwo a hannuna, me za a siyo a wanke min likita?."

Jikinsa ya yi sanyi tunawa da halin da matar take ciki, amma babu damar magana ya faWi abinda za a siyo. Ya Wauki waya ya kira, babu jimawa sai ga duk abinda ya faWa an kawo masa, harda ?arin maganin ciwon kai da ?ananun abubuwa.

Ya wanke masa ciwon kamar yadda ya ce, ArWo ya kalli magaji ya ce, "Kukan jaririn can ya cika min kunne, a kawo waya a kira mijinta, in bazai kawo kuWi ba duk mu kashe su, kar su zamar mana kaya." Shi dai yana du?e yana wanke masa ciwo, ?irjinsa yana bugawa har ya gama.

ArWo ya ce, "A kawo amaryar Black ya wanke mata ciwon ta."

Aka je aka Wauko Sudaisa da kanta yake a fashe, yana wanke mata tana kuka bayan ya gama ya ce, "Za a iya bata magani?."

ArWo ya ce, "ka bata komai, wannan ai ta gida ce." A cikin magungunan da aka kawo ya buWe ya bata na zazzaSi ta ce, "ArWo a duba Hammana, da wannan Hamma" ta faWa tana nuna Saheer.

ArWo ya ce, "Ayi yadda take so...." Ya juyo ya kalle ta yana murmushi ya ce, "Amarya kuma amanar Black." Alfarmar Sudaisa aka bawa Saheer maganin ciwon kai da zazzaSi, aka bawa Sudais aka wanke masa ciwukan jikinsa.

ArWo ya bita da kallo ya ce, "Black ya yi min shigar sauri, kamata ya yi a ce ni na aure ki ba shi ba. Amma matar abokina matata ce, nima mijin ki ne, yau zamu yi daren amarcin mu" ya faWa yana binta da shegen kallon da gabanta ya faWi.

"An samu labarin shigowar sojoji nan da mintina goma, kowa ya shirya!."

Abinda aka faWa ta over over hannun ArWo kenan, ya kalli su Magaji ya ce, "A kwashe min kadarorina a killace su waje Waya, kar a bar wani abu ya samu Waya daga cikinsu, mu zamu ji da sojojin."

Magaji ya ce, "Ya za a yi da jaririn can? Kukan sa zai iya tona mana asiri."

Ya kalli Magaji ya ce, "A bashi ?aramar gyaWa kawai, a aika shi inda zai huta daga wannan wahalar."

Magaji ya amsa ya bar wajen, su dai sun ji ihunn matan wajen, sai tsawar da Magaji yake yi musu, ashe har ya murWe kan jaririn an cilla shi cikin rami. Wannan rashin imanin ya ja zuciyar mai jegon ta buga, itama ta bi Wanta.

Saheer sai da ya yi kuka, shi kuma Likita tuni an sallame shi shida Wan uwansa sun tafi. Haka aka tattare su aka shiga dasu wani waje, Sudaisa da Sudais da Saheer a waje Waya aka bar su, saboda baza a takura masu ba saboda Sudaisa. Duk an kwashe su an Soye a cikin bukka saboda su Win jari ne, ana jiran shigowar sojojin da aka samu masaniyar zuwansu.

" " " " " " "

Mamy tunda aka yi kiran sallar asuba take kallonsa Rehaan, ta kasa tashinsa ya yi sallah saboda ta san bai jima da yin bacci ba.

A hankali ya buWe ido, sai ta kunna hasken Wakin tana kallonsa ta ce, "Good morning Rehaan, lokacin Sallah ya yi."

Ya Wan mi?e zaune da?yar yana saule numfashi a hankali, sai ya Wan nutsu sannan ya kalle ta ya ce, "Morning Mamy."

Mamy ta ce, "Ya ciwon cikin?."

Ya girgiza kai ya ce, "da sau?i."


"to tashi ka yi alwala kar a tayar da sallah, an yi kira."

Ya mi?e a hankali ya sauka daga kan gadon, Mamy ta zuba masa ido tana kallo har ya mi?e tsaye sosai yana runtse idonsa. Bai kalle ta ba ya shjga bathroom Win ita kuma ta fita daga Wakin.


A falo ya same ta bayan ya fito ya ?arasa inda take ita kuma tana kallonsa ta ce, "za ka iya zuwa masallaci?."

Ya girgiza kai alamun bazai iya zuwa ba, shinfiWa masa sallaya ta ce, "To ka bi jam'i daga nan." Bai musa ba ya hau kai ya tsaya ya tayar da ra'akatal fijir. Yana idarwa aka tayar da sallah suka yi sallah tare da masallaci.

Bayan ya idar ya jingina da kujera idanunsa a lumshe, ya jima a haka kafin ya buWe ido ya kalle ta ya ce, "Good Morning Mamy."

Ta Wora hsnnunta a gashinsa ta shafa ta ce, "Ya jikin ka?."

Ya yi murmushi ya ce, "na ji sau?i."

Ta yi murmuahi ta ce, "za ka sha tea ko?."

Ya Wan rausayar da kai ya ce, "Kar ki wahalar da kan ki."

Bata ce komai b ta mi?e ta sauka ta shiga kitchen ta kawo masa black tea mai zafi, dan ta san ba ya shan madara.

A kan kujera ta same shi, iyama zauna ta ce, "ka yi azkhar?."

Ya Waga kai alamun ya yi, ya mi?a masa tea Win ta ce, "ka sha sai ka koma bacci."

A lokacin Abba ya shigo falon da sallama, duk suka Waga kai suna kallonsa har ya ?araso. Ya zauna gefensa, ya zama sun saka shi a tsakiya sannan ya ce, "ni ai ban san ya dawo ba, sai yanzu Riyya take faWa min......" Ya kalli Rehaan Win ya ce, "Sannu Rehaan, ya ciwon cikin?."

A sanyaye ya ce, "Na ji sau?i Abba. Lokacin da na dawo je zan gaishe aka ce baka nan, shine na shigo nan."

Ya kalle shi cikin tsananin tausayi ya ce, "wannan ciwon ciki yana wahalar da kai, kalli yadda ka rame lokaci Waya. Na rasa wanne irin ciwo ne wannan, an yi duban duniya ba a ga komai ba."

Rehaan ya Wan sauke numfashi bai ce komai ba yana sipping tea a hankali. Sai kuma ya ce, "Ina kwana Abba."

"Lafiya lau. Yanzu ya daina yi maka ciwon?."

"Ba ya yi sosai, sai kaWan."

"Allah ya ?ara lafiya."

"Amin Abba."

"Ka kwanta in ka gama shan tea Win, in ka sake yin bacci za ka ji daWi sosai."

Abba ya kalli Mamy da take gefensa a zaune ya ce, "Nadira mu bar shi ya huta, mu je ko?" Ya faWa yana mi?ewa, babu yadda Mamy zata iya haka ta mi?e ta fita ba dan ta so ba, in a son ranta ne yadda suka kwana tare a haka zasu yini.

Suna fita ya ajjiye tea Win hannunsa ya kwanta kan kujerar ya lumshe idonsa.

Bacci ya yi sosai har bayan sallar azahar yana bacci, sai ?arfe biyu na rana sannan ya farka, kuma sai ya ji daWin baccin dan babu sauran ciwon kamar Wazu. A haka ya tashi ya yi wanka ya shirya cikin ?ananun kaya ya zauna a falon.

A lokacin Mamy ta shigo ita da Riyya da Banishs da kuma Jafar. Ya Waga kai yana kallonsu kamar yadda suke kallonsa.

Mamy ta yi murmushi ta ce, "Lallai jiki ya yi kyau."

Ya yi murmushi ya ce, "na ji sau?i Mamy. Ina yini."

"Lafiya lau, ka tabbatar ka ji sau?i?." Ya Waga kai yana kallon Banisha da take kallonsa.

Ya mi?a mata hannunsa ya ri?ota ta zauna a kusa dashi, ta kallesa ta ce, "ya daina yi maka ciwon?." Ya Waga mata kai yana murmishi.

Ya kalli Riyya da take ri?e da tray a tsaye, ganin yana kallonta sai ta ajjiye ta ri?e hannunsa ta ce, "Ya jiki?."

"Na ji sau?i Riyya."

Ta ce, "Ga lunch na kawo maka."

Ya Waga kai ya ce, "Na gode."

Ta ta yi serving Winsa white rice da vegetable sauce wacce aka yi ta da chicken breast. Maimakon ya karSa ya ci sai Mamy ta karSa, ita ta dinga bashi abincin har sai da ya ci da Wan yawa sannan ya ce ya isa.

Jafar dai yana tsaye yana kallonsu cikin burgewa, gabaWaya ahlin Mamy abin sha'awa ne, suna son junansu sosai, suna ?aunar farin cikin juna, suna son kowa ya rayu lafiya ba tare da wata lalura ba. Babu kamar Rehaan, kamar duk sun fi son Rehaan akan kansu, in Rehaan babu lafiya su kan iya kasa bacci, su saka shi a gaba suna kuka har gari ya waye.

Jafar ya ce, "Mamy ki ?yale sa ya ci da kansa, sai wahalar mana dake yake yi."

Ta yi murmushi ta ce, "kaima zo ka zauna na ba ka da kaina."

Ya yi dariya dan shi wallahi Mamy burge shi take yi matu?a, bata wani siriki dashi kamar Rehaan take kallonsa. Tsaf in ya zauna zata bashi abinci a baki kamar yadda ta bawa Rehaan, sai dai shi ya ji kunya ba dai ita ba. Yana ganin banbanci sosai tsakanin iyayensu da suka kasance jinin fulani, da kuma Mamy da take yar wata ?asar, yana ganin yadda ake jan yaro a jiki ana nuna masa soyayya a zahiri, ba kamar fulani da suke yin fulako ba. Mamy bata jure rashin lafiyar Rehaan ko kaWan, ko a gaban waye tana nuna Rehaan Wanta ne, sai dai ka ce duk abinda zaka ce.

Ya zauna yana murmushi sannan ya ce, "na ?oshi Mamy."

Rehaan ya karSi tea Win hannun Mamy ya ce, "zan sha da kaina Mamy." Ya cigaba da shan tea Win suka yi shiru suna kallonsa.

Jin an yi sallama ya saka duk suka juya suna kallon Abba da ya shigo. Abba ya ?araso ya ce, "lallai Rehaan jiki ya warware, na yi tunanin bacci ka ke yi, na le?o Wazu na ga kana ta bacci."

Rehaan yana murmushi ya ce, "na ji sau?i Abba."

"Na ga alama kam, gashi nan ka yi kyau abin ka." Rehaan ya yi murmushi yana kallon tea Win hannunsa kamar mai ganin wani abun a ciki.

Mamy ta ce, "zamu fita ni da Riyya, zamu je mu taro ba?i."

Abba ya yi murmushi ya ce, "mutanen India sun fara sauka kenan."

Ta Wan gyaWa kai tana murmushi ta ce, "Eh sun fara, zan kai su guest house su zauna."

Da mamaki Abba ya ce, "baza su zo nan ba?."

Ta Wan girgiza kai ta ce, "gwara su zauna a guest house Win." Bai ce komai ba ta mi?e ita suka fita dasu Banisha da Riyya.

Abba ya kalli Rehaan ya ce, "ka dawo bikin Jafar ko bikin Riyya?." Shi dai murmushi yake yi amma bai ce komai ba.

Abba ya sauke numfashi ya ce, "Rehaan maganar auren ka ta tabbata, da gaske dakai za a haWa aurenku ranar juma'a in sha Allah. In Allah ya kaimu jibi saura sati Waya."

Nana Haleema.
[7/27, 11:49/ AM] KRBBK: RDB2P86
Nana Haleema.

Rehaan ya Wago ya kalli Abba sai kuma ya sauke kai ?asa bai ce komai ba. Abba ya tausasa murya ya ce, "Ka yi ha?uri Rehaan, na san za ka ji ba a kyauta maka ba, amma ka yi ha?uri baka san me Allah ya Soye ba."

Calmly ya ce, "Abba amma ban san yarinyar ba, kawai sai na aure ta? A jira ni na kawo matar da kaina mana, duk daren daWewa ai zan yi auren."

Abba ya ce, "haka ne Rehaan, amma ka yi ha?uri kamar yadda na ce, ka karSa da zuciya Waya, kar ka kalle sa da wani abun daban. Na san za ka ce meyasa sai kai kaWai, kaf ?an uwanka babu wanda aka yiwa haka sai kai. Ina so na tuna maka tabbacin kai Win na daban ne kenan, Waukakar da Allah ya yi maka ce ta kawo haka. Babu yadda zan yi, mahaifiyata nake yiwa biyayya, kaima ka yi min biyayya ka amince."

Ya Wan sauke nunfashi bai ce komai ba dan bai san me zai ce ba, wanne irin aure ne wannan kamar na wasan yara.

Abba ya kalli jafar ya ce, "ga Jafar nan, ya yi bincike mai yawa akan yarinyar, kuma ya tabbatar tana da ilimin addini dana zamani. ?ar jarida ce cikakkiya, kuma tana da tarbiyya da kamewa, in Allah ya amince baza ka yi danasani ba."

Rehaan ya Waga kai ya ce, "To."

Abba ya ce, "yauwa Rehaan, Allah ya yi albarka, yadda ka ta ya ni yiwa mahaifiyata biyayya Allah ya sa ka ga amfanin yi min biyayya."

Jafar ne kaWai ya amsa da amin Abba ya ce, "Sannan in sha Allah duk macen da ka gani ka ce kana so ka aura zan shige maka gaba har sai ka mallake ta. Baturiya ko ?an india jinin babar ka, kai ko wanne yare, ko wanne ?abila, indai ka kawo bazan ba da goyan bayan a juya maka baya ba. Kai ko ba musulma bace, indai ta yi maka za ka aure ta, tunda addini bai hana ba zan ba ka goyan baya koda kowa zai ?i goya ma ka baya a kai. Sai na tabbatar ka samu abinda ka ke so."

Rehaan ya ce, "To Abba" ya sake faWa a ta?aice dan bai san me zai ce ba.

Abba ya ce, "Jafar zai raka ka kaje ka ga yarinyar, daga nan sai ka dawo a Wan yi shirye shirye a kai mata da lefe da komai na al'ada, In kuma kuWi za ka bata a matsayin kayan lefen sai a bayar a yi."

To kawai ya sake cewa kawai bai ce komai ba.

Abba ya ce, "ka tuna kwana tara auren ya rage, aje ayi abinda za a yi kafin lokaci ya ?ure."

Rehaan ya ce, "To Abba."

Abba ya shafa kansa ya ce, "ka cigaba da ha?uri, Waukakar kenan, hausawa sun ce Waukaka abar gudu ce kuma abar nema."

Ya kalli Jafar ya ce, "sai ka Wora daga inda na tsaya." Jafar ya amsa sannan Abba ya mi?e ya fita.

Jafar ya kalle sa cikin tsokana ya ce, "Ango." Bai kula ba sai shan tea Winsa da yake yi kamar baya so.

Jafar ya ce, "Wan gata Abba da Daada, aure kawai za a yi maka cikin kwana tara, gaskiya kana lokacin ka." Nan ma ya yi masa banza bai ce komai.

Jafar ya ce, "ka dai yiwa Abba biyayya kawai malam."

Sai a lokacin ya kalle sa ya ce, "wai aure, sai ka ce wani toy, ni Rehaan za a yiwa haka."

"Babu mita Rehaan, kawai ka amince."

"Kamar a film, ko sanin yarinyar ban yi ba. Kamar sadakata aka bata fa."

"Na faWa maka wacece?."

"Kai ka santa ne?."

"kaima ka santa."

Ya Wan zuba masa ido kafin ya Wauke kai bai ce komai ba.

Jafar ya ce, "Yarinyar nan da sace, yarinyar nan da ku ka haWu a Jedda, itace dai matar ka."

Rehaan ya juyo yana kallonsa alamun ban gane ba, Jafar ya yi dariya yana Wora ?afa kan Waya ya ce, "da gaske nake maka, wallahi itace, ka san dai bazan ce wallahi akan ?arya ba. Abba yana faWa min sunanta na gane ta, na saka a yi bincike a kanta a kan hakan."

Ya ajjiyd mug Win hannunsa ya ce, "Jaazy ka daina yi min wasa."

Jazy ya ce, "ba wasa nake maka ba, wallahi da gaske nake. Itace wacce Daada take so ta haWa auren ku."

Ya Wan yi shiru yana kallon waje Jazy, har Jazy ya ce, "ka zuba min ido kana kallona."

"Jazy akwai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login