Showing 39001 words to 42000 words out of 221574 words

Chapter 14 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

168

take Soye mana bata so mu san dashi."

Sadik bai ce komai ba, a ransa yana ayyana dan ma baka ga ma?udan kuWin da ta dawo dasu bane, na tabbata da kaima zaka Warsa wani abun a ran ka.

Tabbas yana zargin Islaha akan kuWin nan, dan ya san bata da hanyar da zata samu dala Wari balle rafar dala, ya yi shiru da maganar ne saboda ta ro?esa akan kar ya faWa, amma da sai ta faWa masa inda ta samu. Kuma ro?on nasa da ta yi akan kar ya faWa ya sake saka masa zargi, dan gaskiya shi zargi yake ta bada kanta a bata wannan kuWin. Amma kuma sai ya tuna wanne Wan wahala ne zai bata wannan kuWin dan ta bashi kanta? A lokaci Waya dai bazata samu ba, sai an Wan saba.

Islaha tana barin wajen elevator ta hau ta yi nisa da floor Win theater da suke, yana buWewa ta fita ta tsaya ta jingina da bango cikin rashin sanin abinda ya kamata ta yi a lokacin.

KuWin nan da ta Wauko yana damunta sosai, ta yi danasani yafi cikin kwando, sai dai danasanin bata da amfani, tunda ta riga ta aikata. Danasani akan abinda ya riga ya wuce Sata lokaci ne. Tana so ta yi focusing akan abinda zai faru a gaba,? amma ta rasa abinda ya kamata ace ta yi.

Ta sauke numfashi tana cire facemask Winta, ta lumshe ido tana tuna hanyar da ya kamata ta bi wajan ganin ta samo kuWin nan ta biya shi. Dan gaskiya sai ta biya, baza ta zauna da bashi a kanta ba, mutuwa ake yi ko yaushe, in ta mutu da wannan kuWi ta cewa Allah me?. Bashi da yake hana kwanciyar kabari, haka kawai ta jawowa kanta bala'in lahira bayan wanda ta bari a duniya?.

Bata san adadin lokacin da ta kwashe a haka ba, tana zaune ta jingina ta rufe ido ba tare da ta san tunanin me take yi ba.

Maganar da taji a nesa da ita ya saka ta buWe idanunta, ta ga likitoci a zagaye da wani farin mutum ya saka black Win suit ya juya baya yana magana.

Yadda suka mayar da hankali suka ba sa attension Winsu zai baka tabbacin ba ?aramin girmama sa suke yi, yadda suka nutsu kowa yana magana da girmamawa zaka san ba ?aramin mutum bane. Islaha mamaki take yi ganin yadda duk suka nutsu, ta Wan taSe baki amma still kllon wajan take yi.

A hankali ya juyo yana yiwa na gefen ta magana, a lokacin taga gefen fuskarsa sanye da blue Win facemask da farin glasses a fuskarsa, kafin ya waiwayo gabaWaya kuma ya yi gaba sun binsa a baya kamar jela.

Ta taSe baki ta sake rufe idonta, sai kuma ta buWe da sauri tana sha?ar ?hamshin turaren da ya dabaibaye wajan da take. Cike mamaki ta ce, "kai! Wannan ai ?hamshin turaren wancan baturen da ya sace ni ne."

Sai kuma tayi sanyi ta ce, "babu lallai shine kuma ai" ta yi shiru ta gyara zaman ta dan bata san lokacin da zata bar wajen ba.

Wayar ta yi ?ara, ta duba ta ga Hamma ne yake kira a karo na babu adadi, ta yi ajiyar zuciya ta Wauka ta saka a kunneta. Inda take ta faWa masa, ta kashe wayar ta yi shiru, bata so yazo ya tsare ta tambayoyin abinda yake damunta, kuma gashi baza ta iya Soye masa inda take ba shiyasa ta Wauka.

A kan idanunta ya ?araso inda take, ya zauna a gefenta ya ce, "an yi tiyata cikin nasara."

Ta Wan yi murmushi ta ce, "Allah ya basu lafiya."

"Amin."

Ta yi shiru bata ce komai ba shima bai sake magana ba, ta kalle shi suka haWa ido alamun daman shi kallon ta yake yi.

Ya ce, "meye a zuciyar ki ne? Ban yarda da wannan shiru shirun naki ba, duk wanda ya san halin ki in yaga yadda ki ka koma a yanzu ya san kina da damuwa. Meyasa ki ke keSe kan ki cikin yanayi na damuwa har haka?."

Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, ta sunkuyar da kai ta rasa amsar da zata bashi. Sai wasa take yi da hannunta, ta rasa abinda zata faWa da zata kare kanta a wajensa.

Saheer ya ce, "ina jin ki, faWa min abinda yake damun ki. Kin san duk girman matsala, duk girman damuwa, zan taimaka miki mu ya?e ta ni da ke. Dan haka faWa min damuwar ki, kar ki ji komai, ki faWa min ko meye zan fahimce ki. Wani abu suka yi miki da bakya so mu sani?."

Islaha ta yi ajiyar zuciya, tana ji gwara kawai ta faWa masa, gwara ta faWa masa abinda ya faru ta huta da nauyin da zuciyarta take yi mata. In ta faWa masa zata ji sau?i, zata ji sassaucin abun da yake damunta. Amma kuma ya zai Wauki maganar? A wanne Sangare zai ajjiye ta? Zai Wora ta akan ma'aunin fahimta ko zai kalle ta a akasin haka?. Ta Wago suka haWa ido, ta buWe baki a sanyaye zata yi magana......

Nana Haleema.
[6/23, 11:47/ AM] KRBBK: RDB2P17
Nana Haleema.

Islaha ta Wauke kai daga kallon sa, ta Wan sauke kai ?asa a sanyaye ta ce, "Hamma babu komai fa" ta faWa tana Soye masa dan bata san a yaya zai fahimci maganar ba.

Ya yi shiru bai amsa ba yana kallon ta, jin shiru sai ta Wago suka haWa ido, ya Waga mata gira ya ce, "Ba dani ki ke ba ko?."

"Da kai nake mana Hamma."

A'a, da wani Hamman ki ke ba ni ba, dan kin san ni baza ki faWa min wannan tatsuniyar ba ko?."

Ta shagwaSe fuska ta ce, "Allah babu komai, kawai ina tuna abinda ya faru a lokacin da bana nan ne."

Ya zuba mata ido ya ce, "faWa min me ya faru?."


"Ina tuna a inda aka ajjiye ni, da baturen da ya sace ni, da yadda ya dinga..." sai ta yi shiru bata ?arasa ba.

Saheer ya ce, "ya dinga mene? Ina jin ki, ?arasa."

"Yadda ya dinga sakawa a kawo min abinci, shine abin yake Waure min kai. Na rasa dalilinsa na sace ni."

"Iya abinda ya dinga yi miki kenan?."

"Eh shikenan."

Ya zuba mata ido yana kallo, dan shi zuciyarsa faWa masa take yi ko dai sun yi raping Winta ne shiyasa take a sanyaye? Dan yawanci waWanda aka sace da wahala su dawo ba a yi musu wani abu ba, sai waWanda Allah ya kiyaye.

Ya ce, "akwai abinda ki ke Soye min wanda bakya so na sani. Amma babu komai, tunda an fito daga tiyatar ki tashi mu tafi wajan ?an sanda a cigaba da bincike."

Ta kalle sa taga ya haWe rai alamun babu wasa, ta buWe baki zata yi magana, ya dakatar da ita ya ce, "kar ki ce min komai, ki tashi muje kawai, dan ba za a rufe maganar nan ba na faWa miki."

Bata iya musu da Hammanta, ta yi shiru tana turo baki gaba dan ita kam babu abinda zata ce wallahi, sai ranar da ta biyasa kuWin da aro daga nan sai ta san abinda zata yi a akai.

Saheer mi?e tsaye? yana kallon ta ya ce, "tashi muje." Ba yadda ta iya haka ta bi bayansa jikinta a sanyaye.

Yana tsaye ya jingina da bango yana duba file Win hannunsa, ya Waga ido ya kalli tv da take nuna masa masu shige da fice a asibitin na ko ina. Ya Wauke ido yana tuna wacce ya gani a zaune lokacin da suna magana tayi daidai da mara kunyar yarinyar nan da ya Wauke, kamar wanda aka bawa umarni ya saka remote ya buWe inda take zaune, ya zuba mata ido yana ya sake tabbatarwa da ita Win ce.

Ya taSe baki a bayyane ya ce, "shine mahaifinta" ya faWa yana sake kallon file Win hannunsa, yana kuma karanta sunan Baffa a zahiri.

Ya Waga kai ya sake kallon ta, a lokacin da Saheer ya zauna kusa da ita, ya Wauke kai ya ajjiye file Win ya zauna a akan kujera a lokacin kiran Jazy ya shigo wayarsa. Kamar bazai Wauka ba, sai kuma ya Wauka ya saka a speaker ya ajjiye wayar a kusa dashi.

Jazy ya ce, "kai wai me ka mayar dani ne? ?an aikin ka ko a ?ar?ashin ka nake aiki kana biyana albashi?. Dan ma ina taimaka maka ina yi maka abubuwa da baka san sai ka dinga raina min wayo, har ni na kira ka ?i Wauka sai yanzu da ka ga dama zaka amsa kirana?. Yaronka ne ni ko Wan aikinka?."

Rehaan ya lumshe ido ya buWe ya ce, "Jazy kana da matsala."

Sai ya sake harzu?a Jafar ya ce, "ni ne ma kai, in ina da matsala kai meye da kai?. Tun safe nake kiran ka a waya, yanzu na tabbatar azahar ta yi a inda ka ke, amma dan ka raina ni sai yanzu zaka Wauka?."

Rehaan ya yi shiru bai ce komai ba, Jafar ya ce, "na samu labarin ka sallami yarinyar nan, wallahi ina gargaWin ka akan kar ka sake Waukar wata yarinya ka kai gidan ka, in ba haka ba wallahi sai na faWawa kowa na gidanku. Tunda kai naga har yanzu baka yi hankali ba, baka san ya kamata ba."

Ya lumshe ido ya buWe, ya Waga ido ya sake kallon screen Win daidai lokacin da Saheer ya mi?e tsaye yana ri?o hannunta. Ya jingina da kujera yana kallonsu kamar ya samu wani film a hankali ya ce, "kaine ka haife ni da ka ke yi faWa min haka? Kar ka manta, na girme ka."

"Ban haife ka ba, amma na isa da kai. In aure ka ke so daman kakar ka ta ce zata yi maka aure ai, wata?ila ma alamomin iskanci ta gani a tare da kai ya saka ta yanke wannan hukuncin a kanka. In ba Wan iska ba, waye yake ajjiye mace a gidansa? Allah kaWai ya san me ka yi mata. Banza kawai."

Murmushi ya yi ya shafa fuskarsa yana kallon screen Win gabansa har lokacin da suka bar wajan, ya Wan yi ajiyar zuciya ya ce, "Ka saka maids Win Al Hamra su gyara min apartment? Da safe zan shiga Jeddah."

Jazy ya ja tsaki ya ce, "da yake ga Wan aikinka ko? Ni zan saka maids su gyara maka apartment dan zaka je ko?. Kar ka je, don Allah ka zauna indai har sai na yi magana dasu."

Rehaan ya ce, "kashe wayar sai na tura a gyara min, ka cika ni da maganar banza,? gabaWaya baka da amfani."

"Kai ka sani kuma. Sannan ka faWawa budurwar ka, ta daina zuwa inda nake, wallahi zan saka a kamata. Ni ba Wan iska bane, kai ka san ni ba irin ka bane."

"Ni shine Jazy."

"Har sai ka maimaita? Duk wanda ya kai mace gidansa har ta kwana biyu ai Wan iska ne." Rehaan bai ce komai ba ya yanke wayar, yana ganin kiran Alma yana shigowa ta snapchat amma bai duba ba.

Ya rasa meyasa Alma ta fi tasiri a wajansa in yana England, da zarar ya dawo Nigeria shikenan sai ya dinga mantawa da labarinta. In yana can sai yaji a ransa zai iya aurenta ya zauna da ita.

Ya taSe baki kafin ya Wauki waya ya kira wanda zai kira, ya mi?e a hankali ya sauka ya fita daga asibitin gabaWaya.

Islaha kamar yadda Saheer ya ce wajan ?an sandan suka nufa, da ita dashi da Sadik dashi. Tana zaune a bayan mota ta yi shiru, shi kuma shida Sadik suna gaba suna tafiya.

Safeera ce ta kira ta a waya, ta Wauka suka yi magana kafin ta ce, "Hamma Sadik zamu Wauki Safeera a hanya." Ya amsa suka cigaba da tafiya har suka je inda take, ta shiga motar suka nufi police station Win gabanta yana tsannanta bugawa, dan bata san amsar da zata bayar wacce zata gamsar da Hamma ba.

A can suka samu Ummi da danginta, aka zauna ana tattauanwa akan batun case Win sace ta.

Islaha ta ce, "babu hannun Ummi a sace Win da aka yi."

Dpo ya kalli Ummi ya ce, "Wannan case Win dai na yanzu, kin bar cikinsa. Amma kina cikin duk wanda zai iya afkuwa nan gaba, dan ko ciwon kai Islaha ta yi zamu nemo ki."

Saherr ya ce, "ni ban gamsu da wannan maganar ba, ina so a yi mata tsakani da Islaha, ko ciwon kai Islaha tayi wallahi sai na Waure Ummi. Domin ta furta kalmar sai ta ga bayanta a gaban shaida, kuma ta amsa da bakinta ta ce ta san ta aikata."

Dpo ya ce, "ba ina nufin rufe case Win Ummi ba, ina magana akan case Win sace Islaha babu hannunta a ciki. Tunda ga Islaha a zaune ta tabbatar mana da Ummi bata da hannu a ciki."

Ya kalli mahaifin Ummu ya ce, "Alhaji wannan case Win babu ita a ciki, amma kamar yadda Saheer ya faWa ko cuwon kai Islaha tayi da saka hannun Ummu a ciki. Domin kalmar da ta faWa ba ?aramar kalma bace, tun kwanaki na faWa maka wannan kalmar zata iya sakawa a Waure ta a gidan yari, ita ake kira da baki shi ke yanka wuya."

Mahaifinta ya ce, "na sani, na kuma san duk abinda ka faWa gaskiya. Na gode da karamcin ka sosai."

Dpo ya ce, "yanzu hukuma ta shiga tsakanin wannan kalma da Ummi ta faWa, muna tsakiya akan kalaminta, dan haka ko yaushe in wani abu ya samu Islaha za a wayi gari Ummi tana wajan nan mun ri?e ta."

Ummi tace, "wallahi bazan sake aikata komai ba, bazan yi mata komai ba."

"Hajiya Ummi wannan daga baya ne, kin Waure kan ki da kalaman ki. A yanzu dai babu ke a case Win, amma nan gaba zaki iya shigowa. Alhaji zaku iya tafiya.." Godiya ya yi musu sannan suka yi sallama suka fita.

Ya juyo ya kalli Islaha ya ce, "malama Islaha na dawo kanki. Ki bamu bayanai da abubuwan da za ki iya tunawa, wanda zasu bamu makama akan nemo waWannan mugaye mutane."

Ta Wan sauke numfashi tana jin idon Hamma a kanta yana yawo, ta Wago ta kalle sa a sanyaye ta ce, "bazan iya tuna komai ba, abu Waya na sani, shi ba bahaushe bane, kuma lokacin da aka Wauke ni rufe min ido suka yi ban san ta inda muka bi ba."

"Na faWa miki indai za ki iya faWa mana kammaninsa, zamu iya sakawa a zana mana shi."

"Ko yaushe yana saka facemask bazan bambamce ba gaskiya" ta samu kanta da yin ?arya dan ta Soye gaskiya.


"Lambar mota, katin shaida, lambar gida babu abinda za ki iya tunawa?." Ta Waga kai alamun eh.

Ya sauke numfashi ya kalli Saheer ya ce, "baza mu iya yin komai a case Win nan ba, indai bata faWa mana wata makama ko hujja da zamu yi bincike a kai ba. A lokacin da motar ta Wauke ta, cctv asibitin Rehaan Yola ta yanke, sannan mai napep Win da ya ce mana yaga lokacin da aka Wauke ta, shima ya ce bai ga lambar mota ba, itama kuma sun rufe mata fuska bata ga inda aka ajjiye ta ba. Babu hoto ko wani abu da zai taimaka mana mu binciko abiinda muke son bincikowa."

Islaha ta Wan yi shiru kafin ta ce, "mai napep! Kuna nufin yazo nan?."

Dpo ya kalle ta ya ce, "kin gan shi ne?."

Ta Waga kai ta ce, "lokacin da nake a tsorace akan hanyar, yazo zai wuce sai na tare shi, har muka yi ciniki zan shiga ya kai ni gida, sai zuciya ta bata amince dashi ba, domin ya saka facemask da ba?in glasses bana gane yanayinsa. Sai nace yaje na fasa hawa, sai naga ya fito ya biyo ni, nayi sauri na gudu, ya kamo ni yana buWe wata kwalba da take a hannunsa, wacce ya ri?e ta da ba?in abu."

"Ban san meye a cikin kwalbar ba, amma yana ?o?arin watsa min a fuskata. Yana gama buWewa sai naji an jani da ?arfi cikin mota, daga nan ban sake buWe ido ba sai a wannan gida."

Dpo ya zuba mata ido har ta gama ya ce, "shima mai napep Win ya yi nufin cutar dake kenan?."

"?warai kuwa, duk da ban san meye a cikin kwalbar ba, amma tabbas abin cutarwa."

Saheer cikin tashin hankali ya ce, "meye za a yi ?o?arin zuba mata? Meye a cikim kwalbar?."

Dpo ya ce, "probably acid ne, hydrocloric acid!. Babu abinda za a yi ?o?arin zuba mata a fuska in ba shi ba."

?irjinta ya buga da ?arfi, ta dafe ?irji tana buWe cikin firgici ta ce, "Acid!."

Sadik ya ce, "Sai a nemo Muslim ya nemo mana shi, daman tare suka zo." Ya Waga kai kafin ya Wauki waya ya kira, ba jimawa wani ya shigo yana sara masa.

Ya ce, "a je gidan tv toron giwa azo min da Muslim." Ya amsa ya fita.

Dpo ya ce, "Mai keke napep, waWanda suka sace ki, Ummi, waWanda suka yi waya suna neman kuWin fansa. Mutane huWu suna cikin case Win nan, kuma ko wanne a cikin su abin zargi ne. Musamman mai keke napep, zuciyata bata amince dashi ba ko kaWan. Su kuma waWanda suka yi waya amfani suka yi da Sacewar ki dan su samu kuWi. Amma su waye suka Wauke ki? Da zamu san su bincken zai zo mana da sau?i" Ya faWa yana zuba mata ido yana karantar yanayinta.

Islaha ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, bata so ta yi wani motsi da zai saka ya zargi bata da gaskiya.

Saheer ya ce, "Officer ni ina ganin ko sun tsorata ne shiyasa ta ?i magana? Duk da na san Islaha bata da tsoro, amma yanayin abinda bata saba gani ba zai sakawa ta ji tsoron yin magana. Na santa da wayo, kuma tana ri?e abu komai ?an?antarsa, amma a wannan gaSar tace bata ri?e komai ba."

Officer ya Waga kai ya ce, "Islaha ke da ?awar ki kuje ku jira mu daga waje."

Ta mi?e a sanyaye ita da Safeera, har zata fita daga office Win sai ta juyo ta kalle su, a hankali da sanyin murya ta ce, "A nemo mai napep ya faWi waWanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login