Showing 174001 words to 177000 words out of 221574 words

Chapter 59 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

150

yanke hukunci ba sai ya yi magana da ita, sanann sai ta ga Rehaan Win ta tabbatar zata aure sa. Dan ba a faWa musu sunansa ba, na saka an Soye ne dan mu gwada yanayin su, kuma gashi ya bamu mamaki ya amince."

Ta washe baki ta ce, "Ai daga ganin laraba ka san da juma'arta, ni na san yarinyar nan ta samu tarbiyya mai inganci wallahi. Yau kwana zan yi akan sallaya ina faWawa Allah, sai Ishlaya ta shigo ahlina sannan hankalina zai kwanta."

Abba bau ce komai ba, amma yana jin daWi in ya ga Daada tana farin ciki. Daada ta ce, "a je a cigaba da shiri kamar yadda ya kamata." Ya amsa yana tashi ya fita.

Yana fitowa suka haWu da Jafar zai shuga wajan Daada. Jaazy ya du?a har ?asa ya gaishe da Abba, Abba yana murmushi ya ce, "Ango ka dawo ashe?."

Jazy cikin da kunya da girmamawa ya ce, "Na dawo Abba."

Abba ya ce, "Jeka ku gaisa da Daadan ka zo ina neman ka."

Jazy ya amsa da to, Abba ya fita shi kuma ya shiga wajan Daada. Bai wani jima a wajenta ba, dan ba fuska yake samu a wajanta ba, kawai ya shiga ne dan Mamy tana cewa ya shiga, amma da bazai je ba.

Yana fitowa ya shiga Sangaren Abba ya same shi a zaune a kan kujera. Shi kuma ya zauna a akan carpet yana jiran Abba ya yi magana.

Abba ya ce, "Jafar ina Wan uwan naka? Yaushe zai dawo?."

Jazy ya Wan murmusa ya ce, "ya ce min nan da jibi in sha Allah zai shigo, da?yar na saka zai zo ma, ya ce shi ba sai ya zo ba."

Abba ya murmusa yana gyaWa kai ya ce, "Baturen bafulatani kenan, jini uku ne yake yawo a jikinsa. Ga jinin fulani, ga na indiyawa, ga jinin turawa tunda a burtaniya can ya girma, dole a samu iyayi kala kala a tare dashi."

Jazy ya yi dariya sosai amma bai ce komai ba. Abba ya ce, "Ai kuwa zuwa ya zamar masa dole, dan tare za a haWa aurenku da kai dashi, kamar yadda Daada ta ce."

Da mamaki Jafar ya kalli Abba ya ce, "Tare kuma Abba?."

Abba ya ce, "Tare kuwa Jafar, dan har an yi magana da dangin yarinyar da Daada ta nace a kai, amma sun ce sai sun yi magana da ?arsu in ta amince. Hmmm a ganinka akwai wacce zata ?i wannan tayin ne?."

Jafar ya ce, "gaskiya babu Abba."

"Ka ga shima aurensa ya zo kenan."

Jafar ya ce, "Amma Abba wacece yarinyar? An yi bincike mai kyau a kanta?. Kar a biyewa Daada a yi abinda za a yi danasani, wacce zata zama natar Rehaan dole a tsaurara bincike a kanta, musamman irin wannan auren."

"An yi sosai Jafar, yanayin yadda Rehaan yake dole ayi bincike kafin ayi auren. Na yi bincike da kaina kuma na saka anyi, babu wanda ya buWe baki ya faWi aibun yarinyar. Duk wanda zai buWe baki yabonta yake yi, kowa in zai yabe ta zai ce tana da kirki da hankali. Kuma marainiya ce gaba da baya, a gidan marayu ma ta tashi har ta girma. Daga baya ne ta dawo gidan su wanda ya yi adopting Winta, da shi zai aure ta amma ance mahaifiyarsa bata so an ha?ura. Duk da ance gidan da take babu wata tarbiyyar kirki, matar da take ri?onta tana harkar kai yara ?asar waje aikin gidajen larabawa, amma duk da haka ana yabon halinta fiye da na yaran da ya haifa. Wajen aikinsu, mutanen unguwa, gidan marayun da ta tashi duk na bincika, kuma alhamdu lillah!."

Jafar ya gyaWa kai sannan ya ce, "ma sha Allah! Wacece Abba?."

Abba ya ce, "Sunanta Islaha Maddibo, ?aramar ?ar jarida ce a wata ?aramar gidan tv, ban ri?e gidan tv ba gaskiya, amma yarinyar ta Waukaka a idanun mutane, musamman matasa.

Jafar ya zaro ido ?irjinsa yana bugawa ya ce, "Islaha Abba!."

Abba ya kalle sa ya ce, "haka aka ce sunanta. Ka santa ne?."

Jafar ya ce, "Na santa Abba, na taSa ganinta a wani waje, har muka yi magana tana so na kawo mata Rehaan su yi interview."

Abba ya Wan girgiza kai yana murmushi ya ce, "to itace."

Jafar ya girgiza kai yana mamakin ikon Allah, yana mamakin wannan kwaWo da chakwakiya, yana hango yadda abin zai kasance, yana hango rigimar da Rehaan zai yi akan wannan abun. Lallai Allah Allah ne, in ba Allah waye zai haWa Islaha da Rehaan a matsayin mata da miji?."

Jazy ya ce, "itace wacce Daada take ta magana daman a kanta?."

Abba ya ce, "Wallahi itace, yarinya kamar ta yiwa uwata asiri, gabaWaya hankalinta ya tashi a kanta. Kuma babban abin mamakin har yanzu yarinyar bata san da maganar auren ba, bata san za a yi aura mata wani daga gidan nan ba, balle kuma ta san Rehaan zata aura."

Jafar ya ce, "Ikon Allah!."

Abba ya ce, "me ka sani a game da ita?."

"Babu laifi Abba, ana yabonta sosai. Amma zan saka a yi bincike na musamman, in na ga wani abu mara kyau ko lokacin auren ya yi za a san yadda za a yi a fasa. Dan gaskiya bazai yu a yi auren mutum kamar Rehaan da wacce ba a san halinta sosai ba, zan tsaurara bincike mai kyau, in aka samu akasin alkhairi za a fasa."

Abba ya cr, "hakan yana da kyau, ka saka a bincika yadda ya kamata, bana so ayi abinda za a zo ana danasani."

Jafar ya ce, "Gaskiya ne kuwa."

Abba ya ce, "amma kar ka faWa masa sai ya dawo, na san halinsa, ana faWa masa ya fasa zuwa."

Jafar ya yi dariya yana hango dramar da za a kwasa dashi, musamman da ya kasance Islaha ce. Ya ce, "Bazan faWa masa ba in sha Allah." Suka yi sallama Jafar ya shiga wajan Mamy.

Da Banisha suka haWu a falon Mamy, ya yi murmushi hancinta kamar yadda Rehaan yake yi mata ya ce, "Kiddo ina Mamy?."

Ta ce, "Uncle Jazy Mamy tana apartment Win Hamma Rehaan."

Ya ri?e hannunta ya ce, "zo ki raka ni."

Tare suka je har part Winsa, ya hau sama ya tarar da Mamy a zaune a falon Rehaan na sama, Mamy ta dafe kai ga Riyya tana rarrashinta.

Ya shiga da sallama ta Wago ta kalle sa ta ce, "Jafar ?araso, ?araso ka ga abubuwan da na samu a ?asan gadon Wan uwanka."

Gaban Jafar ya faWi, ya ?arasa yana kallon layoyin da suke ajjiye akan center table. Ya kalli Riyya da take kuka, ya kalli Mamy dan itama kukan take yi.

Ya sanyaya murya ya ce, "A Wakinsa aka samu wannan Mamy?."

Riyya ce ta ce, "Eh! Mun zo yi masa gyara, shine Mamy ta samo wannan."

Ya kalli layoyin ya sake kallon Riyya ya ce, "Samo ashana da reza yanzun nan, ki taho da plate." Ta Waga kai ta Wauko ta kawo masa.

Ya Wauki layoyin bayan ya kira sunan Allah, ya farke ya zaro takardar ciki, bai tsaya karantawa ba ya saka musu wuta akan plate Win suka ?one, yana ?onawa yana karanta Auzubika bi kalmatillahil tammaat min sharri ma kala?.

A kan idonsa suka ?one ?urmus ya Wauki tokar, ya shiga banWaki ya zuba a masai ya yi flushing. Ya fito yana kallon Mamy, cikin son kwantar mata da hankali ya ce, "Koma meye Mamy ya koma kansu in sha Allah, don Allah ki daina kuka."

Kamar jira take ta sake fashewa da kuka ta ce, "Jafar kashe Rehaan suke so su yi ne?."

Ya sauke numfashi ya ce, "waye yake shigowa nan?."

Riyya ta ce, "Babu kowa, ni ce kaWai nake zuwa, wani lokacin sai Janan ko Ikram."

Ya gyaWa kai ya ce, "Kar ku damu, za a yi maganin koma waye. Mamy ki daina kuka."

Ta share hawayenta tana sauke numfashi ta ce, "Na daina Jafar. Ka samu labarin aurensa ko?."

"Yanzu Abba yake faWa min, zan ?ara bincike a kan yarinyar in Allah ya yarda."

"Wai Rehaan za a yiwa irin wannan aure, Rehaan Win da nake tanadin aurensa, shi za a yiwa wannan wula?antaccen auren da ko matar bai sani ba."

"Sai ha?uri Mamy."

Ta girgiza kai bata ce komai ba, sai kuma ta tashi ta sauka daga saman ta barsu a saman.

Ya kalli Riyya da take ta hawaye ya ce, "Meye na kukan kuma?."

Ta ce, "ni kaWai fa nake shigowa, an zuba masa pioson a drink Win da na bashi, sannan yanzu ga kayan asiri a Wakin da ni kaWai nake zuwa. Ba dole na yi kuka ba."

Ya Wago fuskar ta ya ce, "Kina tunanin za a ce ke ki ka saka masa ne?."

Ta buWe baki zata yi magana ya Wora yatsansa a kan lips Winta ya ce, "kar ki ce komai, wannan ba tunani ne mai kyau ba."

Ta cire hannunsa sannan ta ce, "to meyasa suke so su kashe mana shi, kowa a gidan nan ba sauraren mu yake yi ba, laifin mu ne dan mun zo a jinin Mamy?. Shi kaWai ne Yayanmu, sauran Yayyem ?annensu ne, meyasa zasu kashe mana shi?."

A ya zauna a kusa da ita ya rungume ta yana pitting bayanta a hankali ya ce, "ki daina kuka, koma meye ai ya wuce, tunda na ?ona da sunan Allah."

Ta kwantar da kanta a ?irjinsa tana kuka sosai yana rarrashinta. Sai da ya ji ta daina sannan ya Wago ta, ya yi pecking goshinta ya ce, "ki bar kuka, babu abinda zai samu Rehaan in sha Allah, babu wanda ya isa ya yi masa abinda Allah bai yi ba. Ki cigaba da ta ya shi da addu'a, ba wai yana kyautata miki kawai ki ji daWi ba, ki dinga dagewa da yi masa addu'a kin ji?."

Ta Waga kai alamun to, ya share mata hawaye ya ce, "Ko ke fa. Yanzu kin gama gyara masa Wakin?."

"Na gama."

"Me za ki yi yanzu?."

"Zan je na wajan wata vendor ne, zan ga wasu samples Winta."

"Meyasa baza ta kawo miki ba sai kin je?."

"Ai akwai inda zan je."

Ya Waga kai ya ce, "Mu je na raka ki." Bata ?i ba suka sakko daga saman, ta shiga wajan Mamy shima bai bi ta kan matan gidan ba suka fita.


_Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.=?O?
Nana Haleema.
[7/23, 12:11/ PM] KRBBK: RDB2P79
Nana Haleema.

_Don girman Allah ku shiga Youtube ki yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.=?O?
" " " " " " " " " "

Mama tana zaune a gaban Daada tana jira ta idar da sallah dan ta idar mata da abinda yake zuciyarta.

Daada tana idarwa ta kalle ta ta ce, "Saddi?a lafiya?."

Ta yi murmushi ta ce, "Ga dambun nama."

Daada ta karSa ta ajjiye a gefe ta ce, "Na gode da hidima."

Ta yi murmushi ta ce, "sai wata magana da nake tafe da ita, ban san ta ya za ki karSe ta ba."

Daada ta ce, "ina sauraren ki, ko ya take faWa min kawai."

Mama ta sauke numfashi ta ce, "Akan auren nan na Rehaan ne. Daman tambaya zan yi, in ana Waura auren a ina zai tare da matarsa?."

Daada ta yi dariya ta ce, "Gidajen da Rehaan yake dasu har sai ance a ina zai zauna? Ko mata goma zai aura yana da gidan da ai ajjiye su."

Ba?in ciki ya mamaye zuciyar Mama, amma bata nuna ba ta ce, "gaskiya ne. Amma ni a shawara ta mai zai hana bazai yi zamanasa a gida nan ba, Sangarensa har mata huWu zai ajjiye. Kaf gidan nan daga Sangaren Abbansa sai Sangarensa ne masu sama, kin ga akwai wajan ajjiye mata a nan."

"Meye amfanin hakan? Yana da gidaje mai zai yi a nan?."

"Amfanin hakan kin ga ba son auren nan yake yi ba, in ya tare a wani gidan Allah kaWai yasan wula?ancin da zai yiwa yarinyar nan. Ba a san yadda zasu dinga zama ba, kuma zai iya tsallake ta ya bar ?asar babu wanda ya sani. Hakan kuma zai taSa ?imar ki da ?imar gidan nan sosai, dan wula?anta mutum ba halinmu bane. Kuma ga ma?iyan da ya tara, in ya bar yarinyar nan ita kaWai a waWannan tan?ama tan?aman gidan za a iya cutar da ita. In kuma tana gidan kin ga akwai idonmu, wani wula?ancin na sa ma zai ragu, kuma ko da ya tafi ya barta muna nan tare da ita, balle ma wani abun in ya aikata za ki tsawatar masa."

Daada ta yi murmushin jin daWi ta ce, "wato a kaf gidan nan babu mai hankali kamar ki Saddi?a, babu mai hangen nesa da sanin ya kamata sai ke Win kawai. Ai ko ni kin fini zurfin tunani."

Ta yi dariya ta ce, "Wane ni Daada?."

Daada ta yi dariyar jin daWi ta ce, "na ji daWin wannan shawarar ta ki, kuma da ita za a yi amafani. In na bari ya tafi da ita wani waje ai sai ya dinga cin zalinta, nan kuwa ko baya nan muna nan babu abinda zai same ta."

"Abinda na gani kenan, kuma hankali kwance babu tunani mara kyau. Shiyasa na ce bara na zo na same ki, zuwa nan gaba in komai ya warware sai ya tare a inda yake so."

Daada ta ce, "wannan shawara ta yi Wari bisa Wari. Haka za a yi ma babu makawa."

Mama ta yi murmushi ta ce, "Bara na je Daada, sai anjima."


"Babu damuwa, in da wata shawarar ina nan ina jiran ki." Ta amsa tana murmushi ta tafi.

****

Islaha haka ta je ta samu Safeera ta dinga yi mata mita skan abinda Saheer ya yi mata Safeera ta yi dariya ta ce, "to ni da ki ke ta yi min mita ni ce Saheer Win?."

Islaha cike da jin haushi ta ce, "Wallahi Hamma bai taSa bani haushi kamar yau ba, wai bazai karSi abinda bai san da kuWin da aka siya ba. Ni yake faWawa wannan maganar kai tsaye, yana nufin yana zargin a hanyar banza na samu kuWin."

"Na faWa miki dole ya shiga ruWani saboda abubuwan da suka faru."

Ta ja tsaki ta ce, "Shi ya sani. Bazan sake saurarensa ba wallahi, in ya ga dama ya zarge ni Win sai me."

Safeera bata ce mata komai ba ta yi dariya kawai, dan ta san zasu shirya ne. Kuma ita bata ga laifinsa ba, dole ya zargi wani abun a ransa, saboda abinda ta faWa ita kanta sai da ta kai zucoya nesa sannan ta amince.

" " " " " " " "

Motar su tana cikin tafiya a cikin daji da duhuwa, masu bacci suna bacci, masu chating suna yi, masu jin wa?a suna yi. ?arar babura da ihuun mutane ya saka kowa ya firgita ya mi?e, kafin wani lokaci babura sun kewaye motar.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Masu garkuwa da mutane ne!."

Jin kalaman driver sai kowa ya Wauki salati, wasu suka fashe da kuka saboda tsananin tashin hankali. Saheer yana zaune gabansa yana faWuwa, ya kalli mutanen ya ga a ?alla baburan zasu kai goma, kuma ko wanne mutum biyu ne a kai. Ya dinga salati a zuciyarsa, hankalinsa ya tashi sosai.

Duk suka sauka daga kan baburan, dukkansu da ?atuwar bindiga a hannunsu, sun yi carko carko a gaban motar suna kallonsu.

?aya daga cikinsu ne ya buWe ?ofar driver, cikin muryar fulani amma da yaren hausa ya ce, "Malam Driver sakko."

Driver jikinsa yana karkarwa ya sakko daga motar, suka buWe bayan motar suka ce kowa ya sakko daga ciki.

Duk sauka sakko suka kwanta, suka dinga binsu Waya bayan Waya suna kallo. ?aya daga cikin su ya ce, "Yellow a karSi waya da kuWi."

Wanda aka kira da Yellow Win ya ci sunan nasa yellow, dan yana da haske sosai, gashi Wan siriri mai jikin fulani, ya fara binsu ya ce, "Kawo waya da kuWi." Hannun su yana rawa suke basu, har aka zo kan Saheer ya bayar.

Yellow ya ce, "Magaji wannan matar ciki gare ta" ya faWa tana nuna masa wata mata da bindiga, tana zaune tana kuka saSaninsu da suke kwance.

Magaji ya ?araso yana kallon yadda take kuka, ga cikinta nan ya fito sosai alamun ta kusa haihuwa. Ya kalle ta ya ce, "Ya sunan ki?."

Muryarta tana rawa ta ce, "Magajiya."

Duk sai suka saka dariya suna sowa. ya kalle ta ya ce, "ki ce sunan mu iri Waya ne. Kin ci albarkacin sunan ki, baza mu tafi dake ba, kuma baza mu kashe ki ba, zamu bar ki tafi. Tashi ki tafi."

Jikinta rawa yake yi ta kasa mi?ewa, ya ce, "ki tashi babu abinda za a yi miki." Ta mi?e tsaye, ya nuna mata hanya ya cr, "ki bi nan, ki ta gudu kar ki tsaya." Bata iya magana ba ta tafi da gudu Win kamar yadda ya ce, tana kuka sosai.

A take aka Waure hannayensu Hamma ta baya, aka mi?ar da kowa a cikinsu suna binsu da kallo. Yellow ya kalli wata babbar mace, a shekaru ta girma kuma tana da jiki sosai. Ya ce, "Magaji wannan fa kaya ce."

Magaji ya kalle ta ya ga tabbas kaya ce, in aka ce za a yi tafiya mai nisa da ita wahala za a sha. Ya kalli Yellow ya ce, "Ka san yadda zaka yi da ita kawai."

Yellow ya saita bindiga a kanta, ta Waga hannu sama ta zube guiwa a ?asa ta ce, "Don Allah kar ka kashe ni, ina da ?a?an da suke tsananin bu?aata ta." Kafin ta sake magana bullet ya fasa kanta, a take ta zube a wajen matacciya.

Matan da suke cikin su Hamma suka ?walla ihuu, cikin kiWima da tashin hankali mai tsanani.


_Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.=?O?
Nana Haleema.
[7/23, 12:11/ PM] KRBBK: RDB2P80
Nana Haleema.

_Don girman Allah ku shiga Youtube kunyi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.=?O?
" " " " " " " " " "

Tsawa suka yi musu duk suka shiga hankalinsu suna kallonsu cikin tashin hankali.

Yellow ya ce, "In ba ku yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login