Showing 9001 words to 12000 words out of 221574 words

Chapter 4 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

107

aiki ban san inda take ba?. Gwara na rasa komai na dawo mu nemo ta tare."

"Dawowar ka ba ita zata bayyana Islaha ba, ka zauna ka cigaba da neman kuWin aikin Baffa, ka dinga ta ya mu da addu'a, itace abinda take so faga gare ka." Saheer bai ce komai ba ya kashe wayar cikin ?unar rai.

Saleem ya girgiza kai yana jinjina ?arfin son da Saheer yake yiwa Islaha ya ce, "gaskiya Saheer yana son Islaha, ban taSa jin rauni a muryarsa haka ba."

Sadik ya murmusa ya ce, "A dai wannan zamanin, ni dai na jima ban ga masoyi kamar Saheer ba, itama kuma na jima ban ga mace mai ri?o da halicci da soyayya kamar ta ba."

Saleem ya ce, "Allah ya bayyana mana ita."

"Amin ya rabbi."

Kiran Saherr ne ya sake shigowa, Sadik ya Wauka Saheer ya ce, "kuna tare da Safeera ne?."

"Eh yanzu ta bar nan, muna tare har Saleem."

"yauwa, akwai wata ma'aikaciyarsu Ummi, kwanakin baya ta yiwa Islaha barazanar sai ta ga bayanta. Ka tambayi Safeera a gabanta aka yi, aje a kamata ta fito da Islaha. A jikina nake jin itace ta Wauke ta."

Sadik ya ce, "anya zata aikata haka?."

Cikin masifa ya ce, "in ba ita bace to waye? Ka je a kamata ta fito min da matata, in ba haka ba wallahi sai na saka an yi mata abinda bazata taSa mantawa dashi ba. Ka tambayi Saleem da Safeera, su sun san case Win. Ranar da aka bata katin gayyatar Ray ranar abin ya faru."

Saleem ya ce, "Saheer tabbas an yi haka, ta shigo wajan Safeera tana faWa mata, nima kuma ina wajan."

"Yauwa, kaima shaida ne. Don Allah aje a san abinda za a yi a kamata, ta faWa mana inda ta kai Islaha, in ba haka ba mu tafi kotu."

Saleem ya ce, "in sha Allah za a yi hakan yanzu kuwa."

Saheer ya ce, "na gode" ya faWa yana kashe wayar.

Sadik ya ce, "Haba Saleem, ya za ka biye masa?."

Saleem ya ce, "in abinka ya taSa har a bakin allura nemansa za ka yi. Dole Ummi ta shigo ciki case Win nan saboda furucinta, dan haka ka tashi mu je kawai. Wannan babban case ne, kuma Ummi zata iya aikata komai dan ganin bayan Islaha."

Sadik ya ce,? "a kan me?."

"Saboda ta fita Waukaka a wajan aiki mana. Tashi mu je."

Sadik ya mi?e ya ce, "Amma baza a karSi shaidar Safeera ba, saboda ?awar Islaha ce."

"Ba za a rasa cctv ta Wauka ba, mu je dai kawai."

Aka kira Safeera dan a tafi police station a kai report akan Ummi.

*******

Maman Orpanage tana zaune tana kallon abinda yake faruwa, tana ganin yadda duniya ta hargitse akan neman Islaha, ana ta reposting hotonta. Hotunanta sai yawo suke yi a duniya ana cigiyar inda take.

Ta yi murmushi tana kaWa kai ta ce, "aiki ya yi kyau" ta faWa tana Wagowa ta kalli wanda yake kallon ta.

Ya yi murmushi ya ce, "duk abinda ki ka ce shi nake yi ranki ya daWe."

Ta yi dariya ta ce, "Aiki ya yi kyau sosai. Ka yi komai ta yadda babu wanda zai fahimta. Ka yi komai akan lokaci, a daidai lokacin da ake bu?atarsa. Zan ?ara maka naira dubu Wari akan abinda mu ka yi za a baka."

Ya yi dariyar nasara da jin daWi ya ce, "Godiya nake uwar Wakina, Allah ya ja da rai."

Ta kalle sa a nutse ta ce, "bana so a samu matsala, yadda aka yi wannan babu matsala ina so aikin gaba ma ya zama mara matsala. A Wauke wayar ta, a tabbatar an goge komai na kan wayar ta, ko da hotonta ne a goge ta yadda babu abinda zai dawo kai."

"Sannan kar a barta ta dawo nan kusa, ayi nisa da zamaninta kamar shekara Waya zuwa biyu nan gaba. Ta cigaba da rayuwarta a nan, kar ku bari ta ga fuskar ku, ko ta ji wani abu daga gare ku. Tana da wayo, tana da kaifin basira, ?ar jarida ce, tsaf zata iya yin abin da baku yi tunani ba. Ku Wauke wayarta gabaWaya, kar ku barta da waya, in ba haka ba da gidan da ku kan ku zata iya yiwa video."

Ya Waga kai ya ce, "an gama ranki ya daWe."

"Ba zancen an gama ba, Islaha ta wuce tunanaka, tana da wayo, tana da fikira tsaf zata yi abinda ba ku yi tunani ba."

"Ai ranki ya daWe tunda ta shiga hannu zancen ya ?are wallahi."

Ta girgiza kai ta ce, "haka nake so naji, haka nake so naji, dan na tabbatar da komai zai tafi yadda nake so. Zata iya tafiya, zaka ji alert."

"an gama ranki ya daWe, amma in aka samu akasi ko ta yi taurin kai za ki ji wani labarin da ba wannan ba."

"Duk yadda ku ka yi, ku tabbatar kawai bata ganku ko ta ji sunana ba."

"An gama" ya faWa yana buWe ?ofa ya fita.

Ta sauke numfashi ta ce, "matsala ta ?are!."

*****

?ar sanda mace, da maza biyu ne suka nufi ma'aikatar su Islaha, ana zuwa aka nemi ganin Ummi aka nuna musu offfice Winsu.

Aka yi knocking suka shiga akace ai tana office Win Chairman. Suka wuce can, ya basu izinin shiga, suka shiga suka gaisa.

Officer ya ce, "Muna neman Ummi Mubarak ne."

Ummi ta bi su da kallon mamaki ta ce, "gani."

Ya kalle ta ya ce, "muna nemanki a office, za ki amsa wasu tambayoyi."

Ummi gabanta ya faWi, ta zaro ido waje ta ce, "me na yi kuma?."

Macen ta ce, "an shigar da ?arar ki, akan ana zargin da saka hannunki a Satan Islaha Muhammad Maddibo."

Ummi ta buWe ido waje ta ce, "wallahi ban san komai ba, ban san waye ya Wauke ta ba."

?an sandan ya ce, "yanzu zamu je mu dawo, ba jimawa za ki yi ba, in har mun tabbatar da baki da laifi."

Chairman ya mi?e ya ce, "Officer Ummi bata da laifi a kan hakan."

Ya kalle sa ya ce, "duk wata magana zamu yi ta a can, a nan babu abinda zamu yarda dashi."

Ummi ta ce, "na rantse da girman Allah bani da hannu a ciki, ku yarda dani."

"gaskiyarki zata fitar dake, mu je."

Ummi ta firgita matu?a, ta Wora hannu a akanta ta ce, "Wallahi Allah bani bace. Ban taSa shiga police station ba, don Allah ku yi ha?uri."

"Malama Ummi, ki amince mu tafi cikin salama da mutaunta juna, kar ki kawo mana hargitsi cikin lamarin nan."

Muslim da yazo wajen ya ce, "shikenan Officer, ku bani dama na taho da ita a motata, ku yi min wannan alfarmar."

Basu ?i hakan ba suka wuce suka tafi, Ummi tana hawaye ?irjinta yana bugawa da ?arfi, zuciyarta tana barazanar tarwatsewa saboda tashin hankali da tsoro mai yawa

Wai Islaha a hannunwa take ne? Abin ya Waure min kai fa>??>?#?>?#?

1k on telegram
09030398006
Nana Haleema.
[6/16, 9:59/ AM] KRBBK: RDB02P04
Arewapen@nanahaleema11

Rehaan asibiti ya fara zuwa, tunda aka san ya shigo kowa ya shiga hankalinsa, aka mayar da hankali akan aiki sosai, dan kowa ya san halinsa, ba ya karSar kuskure."

Tare suke da mutane a bayansa, yana tafiya ana binsa a baya, aka buWe masa office ya shiga yana kallon wajan secretary Winsa ya ga bata nan, ya juyo ya kalli Dr Abdul ya ce, "where is she?."

Dr Abdul da girmamawa ya ce, "Sir kwana biyu bata zuwa gaskiya."

Da ido ya yi masa alamun meye dalili, Dr Abdul ya ce, "ta yi aure, tana hutu." Bai ce komai ba, aka buWe masa glass door Win office Winsa ya shiga yana bin ko ina da kallo.

Babban Office ne mai kyau da Waukar hankali, komai na cikinsa ba?i da gold ne. Ga hotonsa babba a kafe a office Win, ga awards a ajjiye akan cabinet da aka yi ta dan su.

Ga gadon duba marasa lafiya, ga kujeru masu kyau da aka tanada dan ganin mara lafiya. Komai na office Win perfect and luxury, babu tarkace komai decent irin na ?an gayu.

Rehaan ya nemi waje ya zauna yana kallon mutanen Waya bayan Waya.

Sai kuma ya janye ido yana kallon wani waje daban ba tare da ya ce musu komai ba. ?aramin kuskure yake dubawa, so yake ya ga ?aramin abu da zai yi magana a kai amma bai ga komai ba. Ya kalle su ya yi musu alamun su tafi, suka yi godiya suka tafi.

Sallamar Dr Isma'il ya saka ya Wago kai ya kalle shi yana amsawa. Dr ya ce, "Good Day Sir."?

Rehaan kallonsa yake yi bai ce komai ba, Dr Isma'il ya ce, "Sir, we have a kidney transplant surgery, and a donor is available."

Rehaan ya buWe baki ya ce, "what next?."

"We are waiting for your signature on this document, sir."


Ya kalle sa ya ce, "haka nace maka nazo nan ne dan na yi aiki?."

Dr ya ce, "sorry sir. But it's necessary."

Ya Wan taSe baki ya Wora ?afa kan Waya yana haWe hannu waje Waya ya ce, "So, am I the only surgeon here who is going to perform this operation?."

"No Sir! But it's only you."

Ya Wan sauke numfashi ya mi?a masa hannu ya bashi file Win.

Jikinsw yana rawa ya bashi, Rehaan ya fara buWe na donar Win ya ga kaf gwaje gwajen da aka yi masa is parfect, ya dinga bi bit by bit yana karantawa cike da ?warewa da son gano kuskure.

Shi dai Dr addu'a yake Allah yasa bai yi wani kuskure a kan aikin, so yake kawai ya ga ya gama karantawa bai yi magana ba, ba ya so kuskure ya haWa shi da Rehaan ko kaWan.

Rehaan ya rufe file Win donar ya buWe na mara lafiya, ya dinga bi yana karantawa ya ga komai ya yi yadda ya kamata, babu kuskure har maganin da aka bashi ya yi daidai da ciwonsa.

Ya girgiza kai yana mi?a masa file Win ya ce, "Good job."

Ajiyar zuciya Dr ya yi tare da murmushi ya ce, "thank you Sir."

Rehaan ya jingina ya ce, "Remind me on Sunday night, before monday, in ban samu dama ba sai ka yiwa Dr...."

Bai ?arasa ba sai Dr ya ce, "Dr Peter."

Ya gyaWa kai bai ce komai ba, ya yi masa alama da ya fita, ya yi godiya sannan ya fita.

Message ne ya shigo wayarsa ya duba sai ya ja tsaki ya Wauke kai ba tare da ya duba ba, ya dafe kai da hannayen sa duka biyun yana sauke numfashi a hankali.

Remote ya Wauka ya kunna tv, ya jingina da kujera yana Wan juyawa a hankaki yana jira ta gama kamawa.

Tana gama kamawa ta fara fitar da sauti, hakan ya ja hankalinsa ya ji ana cewa, "Ana cigiyar matashin ?ar jarida mai suna Islaha Muhammad madibbo, ta bar wajan aiki da yamma ta tafi asibitin Nadira hospital, ta fita daga asibitin Nadira hospital da yake babban titi. Ta Sace a tsakanin karfe takwas na dare zuwa tara. Don Allah duk wanda ya ganta ga lambobin waya a tuntuSi makusantnta."

Rehaan ya kalli hoton Islaha da aka hasko, tana sanye cikin jalbab hijjab kalar fari tas, ta yi murmushi, tana zaune a office ta Wora ?afa kan Waya.

?auke kai ya yi daga kallon ta, ya sake kallon tv a lokacin an Wauke ta an shiga wani labaran daban.

Ya Wan taSe baki ya ce, "mara kunya" abinda ya furta kenan, ya mi?e ya Wauki wayarsa ya fita daga office Win ba tare da ya kashe tv ba.

Islaha ta fara daina gani saboda ciwon kai da yunwa, taurin kai ya saka ta yi watsi da abincin ta?i ci, ga yunwa tana ji amma ta yiwa kanta mugunta, ta ?i ci sai juyi take yi akan carpet.

A haka aka yi sallar azahar, da?yar ta iya mi?ewa ta yi alwala ta yi sallah a zaune, tana yi tana layi kamar ?ar maye saboda ciwon kai da gajiya.

Bayan ta idar ta kalli abincin da ta zubar tun asuba, ba shiri ta rarrafa kamar yarinya, ta fara cin wanda ta zubar tana ci tana kuka.

Hannunta har rawa yake yi saboda yunwa, ta Waga flaks Win tea ta zuba a kofin da bai fashe ba, ta zuba a bakinta. Ba shiri ta dawo dashi saboda zafi sai, ta kuma sha cikin gaggawa dan yunwa tana neman hallaka ta.

Tana ci tana kuka tana tuna yanayin da Baffa yake ciki, zuciyarta sai bugawa take yi, jikinta yana rawa, tashin hankali ya yi mata yawa. Sai da ta Wan ci ta koma tana jan numfashi, tana ji nutsuwarta tana dawowa a hankali, cikinta yana ?ullewa.

A hankali ta ji ciwon kan yana raguwa sai kaWan, shima dan kuka take yi shiyasa bai bar ta ba. Ta haWa kai da guiwa ta cure waje Waya tana jan numfashi da?yar, tana goge hawayen da suka ?i tsayawa. ?irjinta ya yi nauyi, ga zafin da take ji in ta ja numfashi.

A hankali ta ji an buWe ?ofar falon an shigo, ta Wago da sauri ta kalli ?ofar, ta ga wani mutum ?ato da ba?a?en kaya hannunsa Wauke da tray Win abinci.

Islaha ta mi?e tana kallonsa, shi kuma ya haWe rai ya ?i kallonta, ya ajjiye mata yana kallon waWanda ta fasa a wajan. Ganin ?ofa a buWe sai Islaha ta tattare rigarta zata gudu, taku Waya ta yi ya cafko hannunta ya dawo da ita baya.

Ta fara kokawa dashi tana neman guduwa cikin fitar hayyaci, tana kuka tana so ta fita daga falon amma ya hanata.

Cikin dakakkiyar murya ya ce, "ke!."

Bata san ta tsaya cak ba saboda tsawar har tsakiyar kanta, bata ?aunar tsawa ko kaWan, bata so a yi mata maganar da zata ji ta har tsakiyar kanta.

Ya Wora yatsansa akan bakinsa ya ce, "shiiii!."

Maimakon ta yi shirun sai ta girgiza kai ta ce, "Su waye ku, me na yi muku ku ka kawo ni nan?."

Bai ce mata komai ba ya juya zai fita, sai kuwa ta taka a hankali ta Wauki flaks Win Wazu ta bi bayansa ta buga masa a kansa, irin yadda take ganin ana yiwa mugaye a film.

Maimakon ta ga ya zube a wajan irin yadda take zato, irin yadda take gani a film, sai ta ga ya dafe wajan ya juyo yana kallon ta irin kallon nan na boss.

Ganin irin kallon da yake mata sai ta ji tsoro, duk da haka bata fasa jefa masa flaks Win ba, ya cafe ya ajjiye a gefe, ya saka hannunsa a bayansa ya Wauko bindinga ya nuna mata.

Islaha gabanta ya faWi, tsoron ganin bingida muraran ba a film ba ya tsirga mata, amma sai ta du?ushe a wajan, ta zube guiwa biyu a ?asa.

Cikin muryarta da ta fara dashewa ta ce, "to kashe ni kawai, ka kashe ni na san bana duniyar, ya fi min wannan tashin hankalin da nake ciki. Don Allah ka kashe ni na rataya a wuyan ka, ka kashe ni ha??ina ya rayata a wuyan ka. In baka kashe ni baka ?aunar Allah, ka Wauki raina ka binne ni a Wakin nan ?arewa kashewa."

Shi wallahi sai ta ba shi dariya, bai taSa ganin yarinya ?ar fitina kamar wannan ba, tana cikin wannan hali amma tana yi masa rashin kunya? Amma bai yi dariya ba, ya sake tamke fuska yana nunata da bindiga ya ce, "in ki ka sake yi min magana, sai na fasa miki kai."

"To daman ai so nake ka fasa min kan, akan me zan yi shiru? Mutuwa nake so na yi, kawai ka kashe ni. In ka kashe ni ka ha?a rami ka binne ni a wajen nan ?arewar sacewa."

"Mutuwa ki ke so ko?."


"Eh, ita nake so" ta faWa tana kallon sa amma hawaye take yi.

Ya girgiza kai yana jan bindigar ya ce, "sai ki faWi kalmar ki ta ?arshe kafin bullet ya fasa miki kai" ya faWa yana nuna mata bindigar a goshinta.

Sai ta fashe da kuka mai sauti, tana tuna yadda Hamma zai ji in ta mutu, tana tuna yadda Safeera zata ji in ta mutu, tana tuna su Zainab dasu Hafsa.

Ta ja numfashi da ?arfi ta ce, "La'ilaha illahu Muhammadu rasullah, SAW."

"Kuma Allah ya isa ban yafe mu ku ba, zan tafi inda zak zo, kafin ku taho ayi mana hisabi" ta faWa hawaye yana sakko, mata tana rufe idonta cikin wani irin yanayi.

Ya yi dariya ya jinjina girman taurin kan yarinyar, kawai sai ya juya ya fita yana kulle ta.

Duhu ta gani alamun an rufe ?ofa, ta ?arasa buWe ido, ta ga baya nan ta koma ta zauna tana kuka harda ihuuuu.

? ? ? ?? *******

"Ranka ya daWe na rantse da Allah bani da hannu a Satan Islaha, wallahi ni ban Wauke ta ba" Ummi ta faWa cikin tashin hankali.

Dpo ya kalli Safeera ya ce, "ki maimaita abinda ki ka faWa."

Safeera ta ce, "ni shaida ce, a kan idona Ummi ta cewa Islaha wallahi sai ta ga bayanta, har tana cewa ta rubuta ta ajjiye. A lokacin har ni da Saleem mu ke cewa Islaha wannan ba kalmar wasa bace, ya kamata hukuma ta shiga cikin maganar, dan baka san me za a aikata maka ba. Sai ta yi dariya ta ce babu abinda zata iya yi mata, barazana ce kawai. Akwai cctv, ta Wauki komai."

Saleem ya ce, "gaskiya ne anyi haka ranka ya daWe, ni da kaina na yiwa Islaha faWa akan ta saka hukuma a maganar nan."

Ummi ta zaro ido t ce, "na rantse da Allah barazana ce kawai, wallahi Allah ni ban faWa dan zan yi mata komai ba."

Dpo ya kalle ta ya ce, "kin yarda kin faWa kenan ko?."

"Eh na faWa, amma wallahi ba da wata manufa na faWa ba. Tsabar kishi ne ya saka na faWa."

"Kin faWa dan za ki aikata, ko kin faWa dan barazana wannan duk bai tashi ba. Kin furta sai kin ga bayan Islaha, yau ba a yi sati biyu ba an nemi Islaha ta rasa. Ko kece ko bake bace ba kece, in kin ga kin bar case Win nan tabbaas anga Islaha, in ba a ganta ba, kotu zata yanke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login