Showing 147001 words to 150000 words out of 221574 words

Chapter 50 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

136

Waya side Win.

Yana juyowa suka haWa ido, dan ya cire glasses Win idanunsa. Islaha gabanta ya yanke ya faWi, ta yi saurin Wauke kanta tana mamakin wacce irin ?addara ce take haWasu ko yaushe? Ita ba wata danginsa ba, amma ko yaushe sai su haWu. Bata ce komai ba, tacure a waje Waya, ta kifa kanta a jikinta tana kuka mai sauti.

Rehaan yana jinta, duk da ta rufe rabin fuskarta da face mask amma ya gane ta, haushinta ya sake mamaye masa zuciya. Ya ja tsaki ya Wauke kai yana jin kukanta a kunensa, bai san ?addara da ta saka shi siyan ticket na kusa da ita ba, ji yake kamar ya mi?e ya koma wani wajan saboda takaici.

Kuka take yi sosai, sanyin ya yi mata yawa ga ciwon da yake damunta. Ta yi shiru bata ce komai ba, bata cikin yanayin masifa dan tana kan ciwo, sau?i take nema, amma bata san inda zata same shi ba. Ga sanyi, ga ciwo, gashi bata da mai taimaka mata.

Muryar ta a sar?e ta ce, "Don Allah ka kashe ac, zan mutu."

Banza ya yi mata kamar bai ji ba, bai ma motsa ba balle ta fahimci ya ji har ya kashe Win.

A daidai lokacin mararta ta murWa sosai, bata san ta ri?e hannunsa ta matse ta saka kuka mai ?arfi ba.

Kukan ta duk sai ta jawo hankalin mutanen da suke zaune a train Win, da sauri ma'aikatan suka ?araso wajan ta ana tambayar ta abinda yake damunta.

Shi dai takaici ya gama mamaye masa zuciya, gashi ta ri?e masa hannu ga mutane a kansu sai kallonsa ake yi kamar wani tv.

Ya ja siririn tsaki dan bai san me zai ce musu ba, gabaWaya zaman jirgin ya ishe shi, ba ya son ganin fuskar yarinyar ko kaWan. A lokacin wani ma'aiakcin train Win ya ?araso, ganin hannunta a cikin na Rehaan, sai ya kalli Rehaan sai ya ce, "Me yake damun ta?."

Rehaan ya Wago ya kalle sa, ya harare sa ya yi masa banza bai ce komai ba, dan indai a kanta ne bazai yi magana ba, bai ga dalilin da zata shiga shiga rayuwarsa ko yaushe ba.

Train staff Win ya ce, "she's your wife?."

Nan ma ya share sa yana ?o?arin zame hannunsa a hankali ba da ?arfi ba, amma ta ri?e sosai ga zafin da hannunta ya yi yana ratsa fatar hannunsa.

Ta daina kukan sai hawaye kawai take yi, tana jan numfashi kamar mai na?uda, a hakan ma dauriya take yi, ita kaWai ta san adadin ciwon da yake nu?ur?usar ta.

Ganin sun kafe shi da ido sai ya Wan kalle ta, muryarsa a hankali ya ce, "suna tambayar ki, ki faWa musu me yake damun ki."

Islaha idonta yana rufe, ta buWe ido ta kalle sa suka haWa ido dan ita yake kallo, yadda ya ga fuskar ta ta koma sai jikinsa ya Wan yi sanyi, ba sai ance maka bata da lafiya ba, kana kallon ta kasan babu lafiya.

Ta Wan mi?e zaune sosai sannan ta ce, "paracetamol za a bani kawai."

Da gaggawa aka kawo mata aka bawa Rehaan dan ya bata. Kamar ba ya so haka ya karSa, ya mi?a mata yana kallon ta. Islaha hannunta yana rawa ta raba hannunta da nasa ta karSa ta sha, ta koma ta kwanta ta lumshe ido, sai kuma ta tattare ?afarta, ta haWe da ?irninta ta saka kanta a ciki.

Wayarsa kawai yake dannawa kamar bai san abinda yake faruwa ba, sai daga baya ya kashe ac tana kwance a haka tana jin sau?in ciwon a hankali sai ciwon kai da ya dame ta.

Dan ita bata san irin ta ba, bata son ac a mota balle kuma a jirgi. Yanzu sai ac mota ta saka ta ciwon kai, ko za a saka tafi son a saka kaWan, kar ta yi yawan da zata dame ta. Kafin su je Jeddah ta Wan ji sau?i, train yana tsayawa ya fita bai sake waiwayenta ba, itama ta mi?e tana tafiya a hankali, larabawa suna ta yi mata sannu, sai dai ta Waga kai tana fatan Allah ya sa bata yi staining wajan ba.

A haka ta fito, a lokacin rana ta buWe sosai, ta tsaya daga can gefe tana ji kamar jiri yana Waukarta. Bata san inda zata bi ta hau mota ba, dan ba a nan suka zo da Sunaira ba, nan arrived area ne, gabaWaya bata gane wajen ba, ga ciwon da yake damunta.

Rehaan kuwa kai tsaye inda ya bar motarsa ya je ya ba da pass Win ajiyar aka bashi, yana zaune yana kallon ta. Kallon ta yake yi, ba sai an faWa ba, kai da ka ganta ka san gaske bata jin daWi, yana so ya taimake ta amma kuma ba ya son abinda zai haWasu a waje Waya, shiyasa yake kaucewa, amma Allah ya sani yana so ya taimake ta musamman da take tsaye a kan titi kamar zata faWi.

A hankali ya ?arasa da motar kusa da ita, ya sauke glass a hankali yana kallon ta. Islaha idanunta a rufe suke, amma tunda motar ta zo kusa da ita ta ji ?hamshin turarensa, ta buWe ido suka haWa ido, ta sunkuyar da kai ?asa tana ji kamar ta faWi.

Kamar ba ya son magana ya ce, "mu je."

Bata da yadda zata yi, in a son ranta ne itama baza ta shiga motarsa ba, amma da yake neman taimako take yi sai ta motsa daga inda take, ta yi kamar zata faWi ta yi saurin dafa motar.

Rehaan ya ce, "ki shiga back seat" ya faWa ganin kamar kafin ta ?araso front Win zata iya faWuwa.

Islaha a hankali ta shiga bayan motar, ?hamshin turarensa ya mamaye motar, ta jingina a hankali shi kuma ya ja motar suka tafi.

A hankali yake tafiya, babu sautin komai a motar, sai ?arar wayarsa kuma baya amsawa. Idonta a rufe suke, tafiya kawai take ji ana yi, tafiyar mai laushi babu gargada, sai zaman ya yi mata daWi sosai, dan ba a motsa ta balle ta ji wani abu.

A? har suka je unguwar ya tsayar motarda yana kallonta ta mirror, idanunta a rufe suke har lokacin, yanayinta gabaWaya ya koma na marasa lafiya, yana so ya ji me yake damunta amma sai ya ga kamat bai shafe shi ba. A lokacin ta buWe ido suka haWa ido, ta sauke ido ?asa ta kalli unguwar ta ga har sun zo.

Ta Wauki jakarta ta kalle sa ta ce, "Na gode." Bai ce komai ba ta buWe ?ofar ta fita, shi kuma ya danna remote Win gate Winsa ya buWe ya shiga, bai tsaya ya ga inda ta shiga ba.

Islaha tunda ta shiga ta kwanta a kan gado, Sunaira ta zo tana yi nata sannu da zuwa ganin bata da lafiya sai ta fita ta ?yale ta.

Shi kuwa Rehaan yana ajjiye motar ya shiga cikin gidan, ya hau sama ya shiga wanka bayan ya fito ya yi sallar azahar ya kwanta bacci. Sai la'asar ya farka, ya sake yin wanka ya saka jallabiya ya sakko ya shiga masallaci ya yi sallah sannan ya fito. Yana fitowa ya shiga coffee bar Win da yake kusa da gidan su, ya zauna tana duba menu, kafin ya yi order aka kawo masa black coffee da brownie, sai kuma biryani rice.

"Hii Rehaan." Aka faWa ana zama a kusa dashi.

Ya Wago kai suka haWa ido da Ubaid, sai ya basa hannu suka gaisa kafin ya ce, "Hii."

Ubaid ya ce, "kwana biyu ina ka je? Bana? ganin ka."

"Madina" ya bashi masa a nutse yana cigaba da cin abincinsa.

Ubaid ya ce, "Nima na je, mun je tare da Babyna, na rigata dawowa ne kawai."

Rehaan ya kalle sa yana mamaki, ya rasa meyasa Ubaid ya raina sa, ba ya iya Soye yana neman mata, har faWa yake yi ya je da wacce ba matarsa ba Madina suna aikaita saSon Allah, ko kunya ba ya ji faWa yake yi kamar ba babban abu ya aikata ba. Sai kuma ya tuna shi ?asar ce, ba wani abu bane a wajansa.

Ubaid ya ce, "wallahi ina son ?an matan ?asar ku, Allah ya yi musu wata baiwa ta musamman, wacce sai ka shiga za ka gane. Rehaan black sun haWu sosai, akwai albarka a tare dasu. Irin abinda za ka samu a tare dasu bazai misaltu ba wallahi."

Rehaan ya ji kamar ya sha?e masa wuya, ba ya son wannan maganar ko kaWan, Sata masa rai take yi ta fusata shi lokaci Waya. Ya daure ya share bai ce komai ba, haka kawai ya ji abincin ya fita daga ransa, ya kalle sa ya ce, "na faWa maka ka daina bani labari ko?."

"Ina so kaima ka WanWana ne shiyasa. In kana so zan turo maka ita ta kwana biyu a wajan ka, na yi maka al?awarin za ka so hakan."

"No need"

Rehaan ya faWa yana harararsa Ubaid shi kuma yana dariya, dan wani lokacin da gangan yake tsokanarsa, dan ya san ba ya so. Rehaan ya mi?e ya biya kuWi ya fita yana jin haushi.

Yana shiga gida ya ji wayarsa ta yi ?ara alamun shigowar sa?o, da ya ga Ubaid ne sai ya yi tsaki ya jawo laptop ya fara abinda yake gabansa dan gobe yana da morning duty.

Waya yake yi ta ko ina, maganar harkar kasuwancinsa yake yi, gabaWaya ya takura saboda amsa waya, wannan ya kira sa wannan ya kira sa. Ya jima a haka, sai dai ya tashi ya yi sallah ya dawo, har aka yi sallar i'sha yana a haka.

Maganar Ubaid ce ta faWo masa a rai, sai ya tuna da sa?onsa ya Wauki wayar ya ga ?aramin video ne, kuma viewonce ya tura masa.

Kamar ya share kar ya buWe sai kuma ya buWe, video yana loading shi kuma yana kallon laptop Winsa.

Wani irin yarr ya ji a jikinsa lokacin da ji abinda yake fitowa daga video, ya kalli wayar sai ya yi saurin Wauke kai ya kashe video, ya dafe kansa ya yi shiru cikin takaicin Ubaid wanda bai taSa ji ba.

?aramin video ne, babu fuskarsu amma akwai muryarsu cikin fitar hayyaci wanda ya ke nuni da dukka basa hankalinsu.

Wani irin dum dum dum haka ya ji zuciyarsa tana yi, ya runtse ido ya saki wayar ta faWi a ?asa, jin muryoyin yake yi yi har tsakiyar kansa, ya sauke numfashi yana jin haushi da tsanar Islaha tana mamaye masa ko wanne Sangare na jikinsa.

Bai taSa jin tsana mai muni lokaci Waya kamar tsanar ta ba, danasanin taiamka mata ya mamaye masa rai. Sai yanzu ya ke tunawa ashe ma tare suka je Madina da Ubaid Win, tunda ga shi ya ganta ita kaWai babu shi.

Ya cize bakinsa cikin takaici, ba?in cikin taimaka mata yana yi masa dirar mikiya, ji yake kamar ya dawo da wajen baya, ya jawota ya zabga mata mari sannan ya cilla ta kan titi mota ta take ta. Da ana dawo da abinda ya wuce, da ya dawo dashi ya goge taimaka mata da ya yi a ranar.

A bayyane ya ce, "Allah ka yi maganin matan da suke zuwa ?asar waje suna lalata mana sunan matan ?asar mu, Allah ya shiga tsakanin mu dasu, ka yi mana tsari dasu gaba da baya."

Duk yadda ya so yakice takaicin Islaha daga idanunsa amma sai ya kasa. Shi mutum ne da yi rayuwa a cikin turawa, lokacin da yana makaranta suna sha ganin mace da namiji suna abinda suke so, ya gani sau babu adadi musamman a school, amma bai taSa jin takaici akan hakan ba, bai taSa jin ya tsani wanda ya aikata ba, bai taSa jin haushi ko zafin abin ba.

Amma yanzu kam ya ji takaici da ba?in ciki wanda bai taSa ji ba tunda ya zo duniya. Shi kansa tunani yake yi, meyasa ya damu da ita har haka? Amsar itace; bai sani ba, amma yana tunanin dan ta kasance bafulata kamar sa ne, shiyasa yake jin haka.

? ? Islaha kuwa ta Wan ji sau?i babu laifi, a haka ta yi bacci sanin ba sallah zata yi ba ta sa ki jiki ta yi baccinta, dan Sunaira da ta ga bata da lafiya bata takuta mata ba kuma daman masu gidan basa nan.

Cikin bacci ta ji ana kiran sunanta, ta buWe ido a hankali tana kallon inda ta ji maganar, da hanzari ta mi?e ganin Labiba a dur?ushe a gabanta.

Da mamaki mai yawa Islaha take bin Labiba da kallo ta ce, "Labiba!."

Labiba ta kifa kanta a kan gado, cikin ciwo da tsananin azaba ta ce, "Islaha, ki taimaka min mu je asibiti, taimaka min ki raka ni don Allah. Zan mutu, zan mutu Islaha!."

Hankalin Islaha ya tashi, tsoro da firgici suka shige ta, ta ri?e Labiba ta ce, "meyasa same ki? Me ki ke ji?."

"Marata! Ki taimaka min zan mutu."

Ta diro daga kan gadon, ta shiga baWaki ta wanke baki a gaggauce ta fito ta saka hijjab.

Ta kalli Labiba ta ce, "za ki iya tashi?." Labiba ta Waga mata kai kawai, dan ita kaWai ta san azabar da take ji.

A haka suka fita Islaha ta tsayar taxi ta ce a kai su asibiti ma fi kusa. Labiba tana jikin Islaha tana ta yi mata sannu, sai shafa fuskarta take yi ganin yadda take gumi kamar wacce zata haihu.

Nana Haleema
' [7/19, 10:59/ AM] KRBBK: RDB2P66
Nana Haleema.

Islaha jin abu mai Wumi yana taSa ?afarta ya saka ta kalli ?afarta, ganin jini ya saka gabanta ya faWi, sai take tunanin wanne irin jini ne wannan a jikinta? Ita ba mai haihuwa ba mai zai saka ta ga wannan jinin?."

A lokacin suka iso asibitin, da hanzari aka zo aka shiga da Labiba ganin yadda jini yake zuba a jikinta duk ya Sata Islaha.

Sai bayan an shiga da Labiba, a lokacin Islaha ta bi jikin Labiba da kallo, ta duba jikinta ta ga ba daga jikinta jinin ya zo ba, daga jikin Labiba ne. Ta kalli kayanta duk hijjab Win ya Saci, ta biya mai taxi ta shiga ciki da sauri.

Bata ga inda suka shiga da Labiba ba, ta zauna a reception ta dafe kai tana tunanin abinda yake damun Labiba har haka. Ta sake kallon jinin, ta ga yadda ya Sata, ta yi tsaki ta rasa me zata yi.

Sai ta mi?e ta ?arasa reception ta tambayi inda zata ga Labiba aka faWa mata tana emergency. Aka tambayi details Winta a wajan Islaha ta faWa sannam ta wuce can.

A tsaye ta tsaya tana kai kawo cikin rashin sanin abinda yake faruwa, sai da likita ya fito ta ?arasa wajan sa ta ce, "me yake damunta Dr?."

Zuwa lokacin har an turawa Dr details Win Labiba, dan haka ya kalle ta ya ce, "Labiba?."

Ta Waga kai alamun eh, Dr ya ce, "she had miscarrige!."

Wani irin bugawa ?irjin Islaha ta yi, ta maimaita kalmar miscarriage a ranta, tana tunanin meye ma take nufi, dan kanta ya manta meye ma kalmar misscarrige take nufi.

Dr ya ce,? "ta samu bacci yanzu, za ki iya zuwa wajan ta" ya faWa yana nuna nata Wakin.

Har ya Sace Islaha ta kasa motsin kirki, sai daga baya ta shiga a sanyaye tana ji kamar ta yi kuka saboda yadda take ji zuciyarta tana bugawa.

Ta tsaya tana kallon Labiba tana tuna kalmar Sarin ciki da aka faWa mata, har an canja mata kaya zuwa uniform na asibitin, tana kwance tana bacci an saka mata ruwa.

Islaha ta zauna a gefenta tana kallon ta cikin wani irin yanayi na bugawar zuciya. Sai maimaita kalmar take a ranta, ta rasa wanne irin tunani ya kamata ace ta yi.

Sai bayan azahar Labiba ta farka, suka haWa ido da Islaha da take zaune ta yi tagumi tana kallonta, amma ta cire hijjab Win ta ajjiye a gefe.

Islaha ta ce, "Sannu."

Labiba ta Waga kai ta ce, "me ya same ni?."

Islaha kai tsaye ta ce, "kin samu miscarrige ne."

Labiba ta kasa Wauke ido daga kan Islaha jin abinda ta ce, sai kuma ta sunkuyar da kai tana jin kunya ina ma bata kira Islaha Win ba, ina ma ita kaWai ta zo da Islaha bata san sirrinta ba.

A lokacin nurse ta shigo, aka tafi da Labiba Wakin scanning, Islaha dai tana zaune a Wakin bata je ko ina ba.

Gajiya ta yi da zaman, ta mi?e tana kallon abayar jikinta, sai ta shiga banWaki ta wanke inda jinin ya Sata, tana yi tana mita ta ce, "Aikin banza, ni ba yin ciki ba ni da wanke jinin shege. Allah ka kiyaye mu, ka cigaba ba mu kariya gaba da baya."

A haka ta Wan wanke, sai kuma ta ga rigar ta ji?e da yawa, kawai sai ta Wauki uniform na asibitin ta saka, ta shanya rigar a kan ?ofar banWakin, ta fito ta hau kan gadon da niyar in Labiba ta dawo zata tashi.

Tunani take akan lamarin Labiba, tana mamakin ciki, kuma a ?asar Saudia aka same shi, kuma yadda Labiban ta sunkuyar da kai ya bata tabbacin ta san da cikin, ta girgiza kai tana jin babu daWi a ranta. Bata taSa ganin wacce ta samu ciki ba ta hanyar aure ba ido da ido sai Labiba, shiyasa abin yake Waure mata kai sosai.

A lokacin aka buWe ?ofar Wakin, ta juya ta kalli wanda ya shigo dan a tunaninta su Labiba ne, bata gane waye ba dan scrub ne a jikinsa irin na likitoci, sannan ga hular tiyata ga face mask.

Kafin Islaha ta yi magana an juya an fita daga Wakin an rufe Wakin, sai ta taSe baki ta koma ta yi kwanciyar ta, dan gaskiya bazata tashi ba sai Labiba ta dawo.

Rehaan da ya yi mistake Win Waki ya tsaya bayan ya fita ya yi shiru, ya tafi tunani yana girgiza kai, yana sake tambayar kansa kamar yarinyar can ya gani, yarinyar da ya taimaka mata a train. Sai zuciyasa take faWa masa me ya same ta har haka? Ko ciwon train Win ne har yanzu bai bar ta ba?.

Ya shiga office yana cire hular kansa ya zauna yana tunanin da bai san dalili ba. Ya kalli landline yana tunanin ya tambayi reception amma yana tunanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login