Showing 189001 words to 192000 words out of 221574 words

Chapter 64 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

126

plan Win da yarinyar nan take haWawa a kaina, jikina yana bani turo ta aka yi."

Jafar ya girgiza kai cikin tabbatarwa ya ce, "Wallahi babu wanda ya turo ta, infact har yanzu bata san da batun auren ka ba, ita ta neman saurayinta da aka yi garkuwa dashi take, ta ajjiye ka a gefe kamar bata taSa saninka a Jeddah ba."

Ya zuba masa ido ya kasa magana, yana ganin abin kamar rainin hankali. Ta ya za a ce itace matar? In ba shirya wannan abin aka yi ba ta ya hakan sai faru?.

Jafar ya ce, "ni ka daina zuba min ido, ka yi magana kawai."

Rehaan ya ce, "Kawai ina tuna irin abubuwan da suka faru ne, kai tsaye ka san plan ne wannan. Ta ya rayuwarta zata dinga haWuwa da ta wa? Daga hotel sai asibiti, daga asibiti sai guest house, daga guest house sai Jeddah, daga Jeddah sai aure?. Jazy akwai abinda yarinyar nan ta shiryawa."

Jazy ya yi dariya yana girgiza kai ya ce, "na faWa maka babu abinda take shiryawa, ta taimaki kakar ka akan titi, daga nan suka haWu ta kawo ta gida, daga lokacin kuma Daada ta fara wannan maganar."

Rehaan ya ce, "Meyasa take shigowa rayuwata ko yaushe?."

Ya Wage kafaWa ya ce, "oho, kaima kuma ka shiga rayuwarta ai."

Ya girgiza kai ya ce, "Wallahi ban yarda da yarinyar nan ba, akwai abinda take shiryawa a kaina."

Jafar ya yi dariya ya ce, "In za ka saka a bincika sau dubu, amsar itace bata da wani mugun nufi a kanka. Wallahi bata san kai zata aura ba, ta san da maganar auren amma ba ta auren take yi a yanzu ba. Duk wanda zai faWa maka akasin abinda na faWa maka ?arya ce, abinda na faWa maka a kanta shine gaskiya."

Rehaaan ya ce, "Ta ya zata dinga shogowa rayuwata ko yaushe? Da farko otel, hospital, guest house, jeddah sannan yanzu aure. Aure fa
Jazy!" Ya maimaita yana kallon Jafar.

Jazy ya ce, "ka san dai bazan yi maka ?arya ba, ka san dai bazan faWi abinda yake ba gaskiya ba, ka san bazan taSa yin abinda zan cutar da kai ba, ka yarda yarinyar nan bata da nufi ko kaWan a kan maganar nan, bata san da batun auren ka ba har yanzu."

"To ya aka yi ake zancen auren bayan bata sani ba?."

"ban sani ba, amma ita bata sani ba, amma wanda yake ri?onta ya sani."

Ya girgiza kai yana kallon Jazy ya ce, "Bazan aure ta ba Jazy, ban yarda da ita ba, bazan yarda da wannan auren ba."

"Ya kamata ka yarda."

"Bazan yarda ba, wallahi bazan yarda babu plan cikin a haWuwata da yarinyar nan ba, wani ne ya turo ta cikin rayuwata."


"Daman kwai plan Win Allah mana, kuma daman Allah ne ya turo ta rayuwarka ba wani ba."

Ya girgiza kai ya ce, "haka bazai faru ba, akwai wani abun bayan nan. Meyasa sauran mata basu shiga rayuwata ba sai ita kaWai?."

"Ni dai ban ga wani plan ba, kuma na faWa maka na saka an bincika min maganar nan sosai."

Rehaan ya ce, "ta ya hakan zai faru lokaci Waya? In ba plan bane wannan meye?."

Jazy ya taSe baki bai ce komai ba, dan ya gaji da maimaita magana guda Waya.

Rehaan ya bi sa da kallon tuhuma ya ce, "anya babu haWin bakinka a maganar nan? Na lura tun Jeddah kamar akwai abinda ku ke haWawa kai da ita."

Jazy ya Waga hannu sama yana murmushi ya ce, "ban sani ba, Abba ne ya bani labari."

"Amma meyasa ba ka faWa masa karuwa bace!?."

Jafar ya zaro ido waje ya ce, "ni Jafar na faWi abinda ban taSa gani ba? so ka ke Allah ya tsayar damu ya yi mana hisabi na yi bayani da larabci?. Ba da ni ba, na san illar da take cikin yiwa mutum ?azafi akan abinda ba ka da tabbas a kai."

Ya bisa da harara yana kallonsa amma bai ce komai ba, dan ya san yana nufin ?azafi ya yi mata kenan. Ya ja tsaki yana ji an gama raina masa hankali a duniya, mutum kamar sa da iliminsa da komai a ace wai mata za a zaSa masa kamar yaro ?arami.

Ya ja tsaki mai tsaho ya ce, "Bazan amince da auren nan ba, dole a fasa shi!" Ya faWa yana mi?ewa tsaye. Sai kuma ya tsaya cak jin cikinsa ya motsa, ya Wan runtse ido yana dafe cikinsa.

Sai kuma ya fara tafiya, Jazy ya mi?e tsaye ce, "ina za ka je?."

"Zan je na faWawa Mamy, bazan iya auren yarinyar nan ba, bazan iya auren karuwan da ta zubar da ciki ba, sannan Sarauniyar da take yiwa ?an siyasa sata ba."

Jafar ya ce, "Yanzu ka yiwa Abba al?awarin za ka aure ta."

"Ni ban yi al?awari ba!."

"Amma ka amince tunda ka ce to, kuma ka ce ka masa za ka ta ya sa yiwa mahaifiyarsa biyayya."

Ya Wan dafe kai jin jiyoyin kansa suna harbawa, zuciyarsa tana bugawa, tsanar Islaha tana sake tasowa daga ?asan zuciyarsa tana mamaye ko ina na jikinta.

Ya hargitsa gashin kansa ya kalli Jazy, calmly ya ce, "Jazy na tsane ta, wallahi na tsane ta bana so na ganta. Ka ji na ce wallahi ko? I mean my words."

Jafar ya ce, "To ya za ka yi? Biyayya za ka yiwa Abba."

Ya Wago yana kallonsa, Jafar ya bishi da kallo ganin har idonsa ya canja kala zuwa jajeye, ya san ba komai ne yake canja yanayin Rehaan har haka ba, ba komai ne yake taSa shi har ya Sata masa rai ba. Ya yi mamaki da ya ga ransa ya Saci haka, ya yi mamaki da ya ga har mood Winsa ya canja, hakan da ya gani ya tabbatar masa da gaske ya tsani yarinyar.

Jafar a hankali ya ce, "meye na Sata ranka haka? Ni na jima ban ga ranka ya Saci kamar haka ba, ka sassauta wannan Sacin ran please."

Ray ya kalle sa ya lumshe ido ya buWe ya ce, "na tsane ta, bana son ganinta ko kaWan a cikin rayuwata. Ta ya za a ce zata zama matata?."

Jafar ya ce, "ni abinda nake so da kai, ka daina faWar abinda ba ka sani ba, ka daina faWar kalmar da ba ka tabbatar ba a kanta."

"Zan sake maimaitawa ,she is a prostitute& .Kuma zan je na faWawa Mamy, ni bazan aure ta."

"Kar ka faWa mata."

Ya juyo ya kalle sa alamun meyasa ya ce, "hakan bai kamata ba, kuma za ka iya yin danasani nan gaba." Ya wani kalle sa yana harararsa, ya kasa cewa komai yana kallonsa jin wai zai iya yin danasani, ko danasanin me zai yi oho.

Jafar ya ce, "Just obey your father's command, ka aure ta kawai, ba ka san me hakan zai kawo ba. Wata?ila ka ga ya zama alkhairi, ha?urin da za ka yi sai ka ga ya zama riba a nan gaba."


Ganin ya yi shiru bai ce komai ba ya san mamaki yake yi akan ya ce zai yi danasani.

Jafar ya ce, "kana ji, ni ba wai aurenta nake so ka yi ba, ba goyan bayanta nake yi ba, ina faWa maka ka daina yi mata zato akan abinda ba ka da tabbas a kai, sannan ka yarda babu wani plan a lamarin yarinyar nan, sannan ka amince ka yi abinda Abba ya ke so. Bayan nan babu wani abu a raina, babu wani dalilin da zai saka na ce ka amince saboda ra'ayin kaina. Kuma na ba ka shawara ka daina kiranta da karuwa, kuma kar ka faWawa kowa wannan maganar, bai kamata a jita a bakin ka ba. Ba class Win ka bane, in aka ji maganar karuwa a bakin ka za ka zubar da class Win ka."

Ya sauke numfashi ya ce, "a ko yaushe ra'ayinmu Waya da kai, meyasa yanzu ka canja?."

"Ban canja ba Ray, ina faWa maka abinda ya kamata ka yi ne kodan saboda mahaifinka. Ka daina kiran yarinyar nan da karuwa, ko da karuwar ce bai kamata ka dinga faWa ba, tunda ba gani ka yi ba, hasashe ne."

"sai ka ce na daina cewa haka, ka san abinda na gani da idona meyasa ka ke ce min haka? Irin wannan yarinyar ka ke cewa na aura?. Rehaan Yola ne, ko ka manta ne?."

"Ban manta ba mana."

"Abba bai yi bincike a kanta ba, bai ga halayen ta ba?."

"Ya ce shi bai ji wani hali mara kyau a kanta ba, in ka faWa masa a yanzu zai ga kana yi mata sharri ne dan ka gudu daga auren."

Ya dafe kai cikin takaici ya ce, "wai na gudu! Oh my god."

Jafar ya yi masa bai ce komai ba. Rehan ya dinga sauke numfashi kamar wanda ya yi gudu, ya rufe ido yana ji kamar ya kurma ihu saboda takaici da Sacin rai. Da wata daban ce ba Islaha ba sai ya yarda da auren, amma tunda aka ce Islaha ce sai ya ji bazai iya ba.

Jafar ya ce, "yanzu sai mu je gidansu ku tattauna ko? In ka yi mata ta ga zata iya auren ka sai ta taimaka maka ta aure ka, in ba ka yi mata ba a kai kasuwa" ya faWa yana gimtse dariya dan so yake ya sake tsokano sa.

Sai kuma ya kalle sa, saboda takaici ma bai ce komai ba sai numfashi da ya sauke yana cize lips Winsa kamar zai fasa shi da ha?ora.

Jafar ya yi dariya ya ce, "Ango! Ango!!." Yana faWa yana dariya, sai wayarsa ta yi ?ara, yana dubawa ya ga Abba ne yake yi masa waya, ya Wauka ya saka a kunne ya yi magana sannan ya kashe.

Jazy ya kalli Rehaan ya ce, "Abba ya ce ka same shi a Sangaren Daaada, ni dai zan wuce gida, Ba kasafai na cika gaisawa da kakar nan ta ku ba, in ka fito ka same ni sai mu tafi gidansu budurwarta ka, in ba ka same ni ba...."

Kallon da ya Wago yana yi masa ya hana Jafar ?arasawa, ya yi dariya sosai harda tafa hannu ya fita, ya bar Rehaan da kayan takaici..........

Nana Haleema.
[7/27, 11:49/ AM] KRBBK: RDB2P87
Nana Haleema.


Walking slowly ya shiga falon kansa a ?asa, Sacin ran da yake ciki bazai barsa ya Waga kai ya kalli mutanen falon ba, ya nemi waje ya zauna bai kalli kowa ba.

A hankali ya ce, "Ina yini."

Daada ta bisa da kallo ganin ya Wan rame, ta ji labarin ya yi ciwon ciki kuma gashi nan ta gani a kan fuskarsa.

Amma duk da haka sai ta ce, "Gaisuwar tawa ce ko ta iyayenka?."

Ya yi shiru baice komai ba, kuma ya ?i ya Waga kai ya kalli kowa dan duk haushi suke bashi.

Daada ta ce, "na yi maka uzurin raahin lafiya. Ka ji maganar auren ka ai ko?."

Bai motsa ba balle ya amsa mata, bata damu ba ta ce, "Ranar juma'a mai zuwa za a Waura aurenka Muhammad, sai ka fara shirye shirye, in za ka yi shagali ka yi, in baza ka ba dai kai ka sani."

Nan ma bai ce komai ba sai Mama da ta ce, "Shagali kai Daada, bikin Rehaan guda in ba a yi shagali ba a bikin wa za a yi?."

Daada ta kalle ta ta ce, "kin san halin nun?ufurcinsa, bazai bar shi ya yi abinda ya kamata ba. Da ya yi shagali, da kar ya yi duk Waya ne, aure ne wallahi sai an yi."

Ta sake kallonsa ganin ko kallon ta bai yi ba ta ce, "batun gidan da za ka zauna, umarni ne ba wai shawarar wani nake nema a nan ba. Ban ce kowa ya ce min komai ba, ban ce kowa ya kawo min shawararsa akan hukuncina ba...." Ta faWa tana kallon kowa.

Kowa ya yi shiru yana jira ya ji me zata ce, har shi Rehaan Win so yake ya ji abinda zata faWa.

Daada ta ce, "Ban amince Rehaan ya fita daga gidan nan zuwa wani gida daban ba, ban damu da gidajen da yake dasu a garin nan da wajen garin nan ba, ban damu da yana da gidaje masu yawa ba, umarni ne ba shawara ba, a cikin gidan nan nake so ya zauna. ?angarensa ya ishe sa ya zauna da matarsa, dan haka a nan zai zauna ban amince ya fita ba."

A lokacin ya Waga ido yana kallonta, suka haWa ido ta ga yadda fuskarsa da idanunsa suka canja, ya Wan lumshe ido ya buWe a kanta.

Ta ce, "ka ke kallona da wasu idanun ka masu kama da na maguna, ka ji abinda na ce ai ko?."

Ya Wan Waga kai yana kallon ta, muryarsa a sanyaye ya ce, "meyasa bakya sona ne Daada? Duk abinda zan yi farin ciki a duniya sai kin hana shi, duk abinda zai saka min walwala sai kin hana. Abinda zai saka ni ba?in ciki a ko yaushe shine burinki, abinda zai Sata min rai ya hanani walwala shine burin ki. San....."

Abba ya dak???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?atar dashi ya ce, "Rehaan!."

Ya kalli Abba ya ce, "Abba ka bar ni na faWa mata, ta ce aure zata yi min da wata yarinya, duk waWanda suka yi aure a gidan nan kowa an bashi dama ya auri zaSinsa, amma ni da yake ba a sona an ce ban isa ba, sai dai na auri wacce aka zaSa min. Ka ce na yi ha?uri kuma na yi, ka ce na yi ha?uri na karSi auren na ha?ura na karSa, yanzu kuma kana ji tana cewa na zauna a nan..." ya ?arasa faWa cikin Sacin rai, amma maganarsa a hankali take fita, kuma a kakkatse.

Mama ta ce, "Rehaan ba ka da kunya ashe? Daada da mahaifinka ka ke faWawa haka?. Daadan ba ita ta haifi mahaifinka ba, bata isa da kai ba kenan?."

Ya kalli Mama zai yi magana Abba ya ce, "Ya isa haka Rehaan, kar ka ce komai."

Ya Waga kai ya mayar da kansa ?asa, muryarsa a sanyaye ya ce, "a yaushe haka ka ke cewa kar na ce komai, na yi shiru Abba."

Daada ta saki baki tana kallonsa, sai kuma ta gyaWa tana girgiza kai tana kallonsa ta ce, "lallai jinin indiyawa wuyan ka ya isa yanka....."

Ta sake kallonsa ta ce, "Na isa Win ne, shiyasa nake yanke duk abinda na ga dama a kan ka. Kuma wallahi sai anyi auren nan, ko za ka sha fiya-fiya ka kashe kan ka sai an Waura auren nan da gawar ka. Kuma billahillazi in ka ?ure ni ka Sata min rai, a yanzu zan kira iyayen ka a Waura auren kowa ya huta!. In kana musu ka nuna min ban isa nayi hakan ba."

Yana jin yadda Abba yake kallonsa shiyasa bai ce komai ba, ya sunkuyar da kai yana ji kamar ya tashi ya fita amma ba ya son yi saboda Abba, kuma ya san ?arshe zagin a kan Mamy zai ?are duk da bata wajan.

Mama ta girgiza kai ta ce, "ai sai ya nuna miki shi ba jinin fulani ne gabaWayansa ba, sai ya nuna miki akwai baragurbi a cikin jininsa."

Abba ya ce, "Saddi?a ya isa...." Ya faWa yana kallon ta.

Abba ya kalli Daada ya ce, "Daada ki cigaba da yanke hukuncin da ki ka ga dama, dole kowa ya bi."

Daada ta ce, "daman abinda zan faWa kenan, kuma dole ayi wallahi, in kuma ban isa ba zan gani."

Abba ya ce, "kin isa, tunda ki ka faWa hakan za a yi." Kafin a sake yin magana Rehaan ya mi?e ya fita daga falon.

Yana fita ya ji wayar ta yi ?ara ya Wauko ya duba, ganin Abba ya kiransa kuma ta katse duk a lokaci Waya, sai ya fahimci sa?o ne dan ya dakatar dashi daga barin gidan, ya koma da baya ya tafo Sangaren Abban ransa a Sace sosai.

Bai jima da zama ba Abban ya shigo ya ga ya jingin da kujera ya lumshe idonsa.

Abba ya ?arasa ya zauna akan kujera yana kallonsa, cikin sanyin murya ya ce, "Rehaan da mahaifiyata ka ke sa'in sa?."

Ya Wago a hankali ya kalli Abba ya ce, "bata yi min adalci ne Abba, bata sona."

Yadda ya yi maganar sai dai Abba ya ji tausayinsa, ya san Rehaan ya wuce irin wannan auren, ko a ?auye an daina irin wannan aure balle a cikin birni, a cikin birnin ma namiji mai kyau da aji da kuWi kamar Rehaan. Shi da in ya tashi aure zai iya Wauko ko wacce mace a faWin duniya ya aura, saboda abinda Allah ya mallaka masa, amma ace shine zai yi irin wannnan auren da ko matar ma bai sani ba.

Abba ya tausasa harshe ya ce, "tana sonka mana Rehaan, ya za a yi ta ?i ka bayan kaima jikan ta ne?."

A hankali ya ce, "saboda ni jinin Mamy ne, kuma bata son Mamy."

Abba ya Wan dafe kai cikin rashin jin daWi ya ce, "ka daina faWar haka Rehaan, babu wanda Daada bata so a gidan nan." Ya yi shiru bai ce komai ba, dan ya san Abba yana kare mahaifiyarsa ne kawai, amma duk dinga kowa ya san bata son Daada.

Abba ya ce, "Rehaan yadda Mamy ta isa da kai haka na Daada ta isa dani, tana da ikon yiwa kowa a cikin ku hukunci. Na tabbata ko me Mamy zata yiwa Wan da ka haifa baza ka ji komai a ranka ba."

So yake ya faWawa Abba shi Mamy baza ta taSa yiwa Wansa dole akan abinda ba ya so ba, amma sai ya kasa ya sunkuyar da kai kawai.

Abba ya ce, "nima ita ta haife ni, kana ji tana rantsuwa, zan karya mata rantsuwa ne?."

A hankali ya Wago ya ce, "Amma Abba bana so, meyasa sai ni?. Wallahi Abba ban taSa jin tsanar abu kamar auren nan ba."

Abba ya ce, "ina ba ka ha?uri a madadinta, ina ba ka ha?uri matsayina mahaifinka, dan na san bamu kyauta maka ba. Don Allah ka yi ha?uri ka karSa. " Rehaan ya Waga kai a hankali yana ji kamar ya yi kuka.

Abba ya ce, "na faWa maka in ka aure ta kana da damar auren duk wacce ka ke so daga baya." Ya sauke nunfashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login