Showing 63001 words to 66000 words out of 221574 words

Chapter 22 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

127

ta yi shiru bata ce komai ba.

Mummy ta sauke numfashi ta dafata ta ce, "Ikram Rehaan yayan ki ne, dan kin so shi ba laifi bane. Amma soyayyar da ki ke yi masa kamar bata kamace ki ba, kin san Rehaan ba wannan soyayyar yake yi miki ba, yana sonki soyayyar ?an uwantaka ba ta aure ba. Saka irin wannan soyayyar a ranki zai iya cutar dake, kin san bazai kalle ki a wannan matsayin ba.

Hawaye ya sakko mata, ta Wago ta kallo Mamy ta ce, "Na sani Mummy, ina so na koyawa kaina hakan amma na kasa. Yana kallona kamar yadda yake kallon Riyya, yana kallona kamar Janan da Banisha, nasan bazai taSa kallon a wani matsayi in ba wannan ba. Amma ni kuma ina sonsa Mummy, ina ?aunarsa sosai, kuma aurensa nake mafarkin yi.


"Kin san baya kallon ki a matsayin wacce zai aura meyasa ki ka fara yi masa irin wannan soyayyar? Ko dan kin ga yana sakar miki fuska?. Kar ki manta kaf cousins Winsa da ?an gidan nan kaWai yake shiri, kuma ki tuna in ba ke ba babu wacce in ta kira shi kai tsaye zai Wauka. Kin san Rehaan ba ?aramin mutum bane, yana cikin matasan da suke da kuWi a garin nan. Anya ba ki yi gangancin fara sonsa ba?."

Ta goge idonta da suka ji?e da hawaye ta ce, "Mummy ni ba dan kuWinsa nake sonsa ba, ko bashi da komai zan rayu dashi."

"Na sani Ikram, soyayya da ki ka fara yi masa itace illar. Koda Rehaan zai so ki kakarsa baza ta taSa yarda ya aure ki ba, kin san yadda aka sha wahala da ita kafin ta yarda da auren Jafar da Juwariyya. Inda Rehaan zai yarda dake a matsayin matarsa muna daga cikin mutane na farko da zasu so hakan, bani da matsala da Nadira, na san zata yi farin ciki sosai, mahaifinsa ma zai yi murna da hakan. Amma Kakarsa bazata taSa yarda, saboda ba ita ta haifi mahaifin ki ba. Kin san kishi take yi da ?a?an kishiyoyinta kamar me.

"Mummy ni duk ban damu da wannan ba, indai har zai yarda dani shikenan. Sai ya Wauke ni mu koma Uk da zama, ba lallai sai na zauna a nan ba."

"Ki dage da addu'a kawai, amma bana tunanin Rehaan zai amince ya karSe ki matsayin matarsa."

Cikin kuka Ikram ta ce, "Mumny ki daina yi min baki, wallahi ina son Rehaan so mai yawa, in na rasa shi ban san halin da zan shiga ba.

Mummy ta shafa kanta ta ce, "ba baki nake yi miki ba, na san halinsa ne kawai. Kar ki ga Yayan ki zai auri ?anwarsa ki ji a ranki kema zai iya auren ki, kowa yana da ra'ayin sa. Rehaan bashi da ra'ayin auren ?an uwansa, nasan kema kin san da haka. Kafin ke an yi irin ki da yawa amma bai karSa ba.

"Mummy ai da shima Hamma Jafar Win haka yake faWa, amma yanzu Riyya zai aura."

"Na faWa miki shi daban da Rehaan, abinda zai yi Rehaan bazai yi ba. Ki cigaba da addu'a, in Allah ya amince komai zai wuce."

Ikram ta kwantar da ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?kanta a kafadar Mummy tana kuka sosai ta ce, "Amma ina sonsa Mummy, wallahi zan iya cutuwa in ban aure sa ba."

Mummy ta shafa kanta ta ce,"shiyasa na ce ki ta addu'a."

"Mummy ki faWawa Mamy, ko zata saka shi ya so ni, tunda yana son abinda Mamy take so.

"Ikram! Ke bakya fatan ya so ki dan kansa sai an saka shi?."

"Ni ko bazai kula ni ba, indai zan amsa sunan matar shi hakan ya yi min."

Mummy ta yi dariya tana girgiza kai cike da tausayin Ikram ta ce, "Lallai kin yi nisa. Kar ki damu komai zai wuce in sha Allah, ki tashi muje ki ci abinci."

 Mummy ki faWawa Mamyn.

 Zan faWa mata in sha Allah, zamu tattauna akan hakan.

Zata yi magana Mummy ta ce, "kar ki ce komai, ki tashi muje muci abinci kawai." Ta goge hawayenta suka fito tare da Mummy.

? ? ? " " " " " " "

Basu isa Abuja ba sai bayan sallar i'sha, kai tsaye aiport aka wuce dasu basu tsaya hutawa ko wani abun ba.

Bayan sun fito daga mota, kowa a gajiye yake saboda zama, gashi babu batun hutu wani sabon zaman ne a gabansu. Mama ta kalle su ta ce, "to zamu rabu daga nan, yanzu wanda zai tafi daku zai zo. Da zarar kun isa ku kira mu a waya, ban da saSa al?awari."

Labiba ce ta ce, "To Mama. Anty Karima sai mun yi waya" ta faWa ciki Wauki da zumuWi.

Hajiya Karima ta kalli Islaha da tunda suka taso bata ce komai ba, gwara da suka tsaya a gidan Mai ta sauka ta yi sallah, daga nan bata sake cewa komai ba.

Hajiya Karima ta ce, "ba fa haka za ki je kina haWe musu rai ba, tunda mu ka taho ban ji kin ce komai ba, ya kamata dai ki san irin abubuwan da zaki yi in kin je can. Aiki zaki yi musu su biya ki, dole ki saki jikin ki."

Islaha ta Wauke kai bata ce komai ba, ita sallar magrib da i'sha take so ta yi, ba wannan surutan banzan ne a gabanta ba.

Hajiya Karima ta kalli Umma da take duk ta damu kanta kamar wacce aka yiwa dole a tafiyar ta ce, "kar wani abu ya dame ki fa, mutuwar aure ai ba kan ki farau ba, kuma ba kan ki ?arau ba. Kar ki wani damu wallahi, ki je ki haWo kan ?an canjin ki, ki dawo a cigaba da zama. Sai me dan ya sake ki? In ki ka samu kuWin ki ba sai ki yi wani auren ba?."

Umma cikin rauni ta ce, "Aure kuma?."

"To wuce auren ki ka yi? Nawa ki ke?."

Mama ta ce, "mata ne da Worawa kansu fitina walllahi, ni ban ga abin Waga hankali dan ya sake ki ba. Kina da yarinyar da zata kula da ?annenta ba, shikenan an huta ba. In ni ce ita, wallahi a saudian zan Waura aure, dan na nuna masa baya gabana. In ka nunawa namiji ka damu dan ya sake ka ba ?aramin raini bane, komai ace saboda ?a?a, na rasa lokacin da mata zasu waye su daina kallo ?a?a su kama gabansu.

Umma dai ta kasa magana, Wauki da zumuWin da take yi gabaWaya ya kau daga zuciyarta, da tana da iko a lokacin tabbas da ta koma gidan mijinta ta cigaba da zama ita da yaranta, amma lokaci ya ?ure.

"Salamu Alaikum. Hajiya Karima da Hajiya Zulai barkan ku da zuwa."

Ganin wanda ya yi maganar sai suka washe baki, cike da girmamawa Mama ta ce, "Barka dai, mun same ku lafiya?."

Ya yi murmushi ya ce, "Lafiya lau. Ya hanya?."

"Hanya alhadu lillah."

"WaWannan ne?."

Mama da Karima harda saurin haWa baki wajan cewa, "Eh sune."

Ya bisu da kallo yana nuna Islaha da Labiba ya ce, "kai amma waWanan sun yi, zasu yi daidai da gidajen da ake nema. Gaskiya kun yi aiki mai kyau, daga gani baza a sha wahala dasu ba wajan turanci."

Mama cikin son gwaninta ta ce, "ita fa wannan ?ar jarida ce, babu wanda bai santa a Yola ba. Kaima na san zaka iya saninta, tunda yanzu a waya ake sanin mutane."

Hajiya Karima ta cafke ta ce, "ai indai Sangaren turanci ne an bar mata kayanta."

Ya yi dariya yana girgiza kai ya ce, "?warai ina ganin fuskarta a waya. Irinsu ake so, wanda za a iya magana dasu da turanci. Dan gidan da za a kai ta likita ne, yana jin turanci sosai, ba lallai sai ta iya larabci ba......" ya Wan kalli Umma ya ce, "Amma wannan zata iya kuwa?." Ya faWa yana nuna Umma.

Hajiya Karima ta ce, "Me zai hana Oga?."


"Da gani babba ce, babu lallai a samu wani yare akan harshen ta. Kun san yanzu gidajen aikin nan basa Waukar waWanda basa jin larabci ko turanci, kuma daga ganin wannan bata jin ko Waya. Dama dai kamar waWannan Win ne, an fi bu?atarsu."

Mama ta ce, "lah itama ta iya turancin ai, kawai dai yaran sun fita ne. Amma babu abinda baza ta yi ba."

Ya gyaWa kai yana kallon Umma dan shi bata yi masa ba, yafi so a kawo yara kamar su Islaha, baya so aje ta zamar masa kaya, ai ta yawo da ita ba a samu abinda ake so ba.

Ya kalle su yana Waga kai ya ce, "Sun san komai dai ko? Sun san tsari da kason kamfani?."

Mama ta ce, "sun sani, duk mun yi musu bayani yadda ya kamata. Mun faWa musu albashi za a kasa gida uku, mu Wauki biyu su Wauki Waya. Duk na karanta musu."

Ya Waga kai ya ce, "dakyau!. Ban da sata, gulma da komai duk kun faWa musu?."

"Duk sun sani, mun tabbatar baza su yi aikata ba."

"Yanzu jirgin na su ya sauka, mu je a auna kayan kafin a fara boading. Ku yi sallama, dan baza su bar ku shiga ba. Zulai bani takardun nan.

Mama ta mi?a masa, kafin ta ta kalli Labiba ta rungume ta ta ce,"Saduwar alhairi Wiya ta gari, Allah ya kiyaye ya bada nasara. Kin san gargaWina, ban da zubar da mutunci."

Ta yi fari da ido ta ce, "zan yi kewar ki Mama."

Mama ta ce, "nima haka."

Ta kalli Islaha ta ce, "Islaha sai an dawo, Hajiya Maimuna saduwar alkhairi."

Duk suka yi musabaha kafin su fara tafiya ciki a hankali, Labiba ce kaWai take murna amma Islaha da Umma kamar kazar da ?wai ya fashewa a ciki a haka haka suka ciki.

Basu sha wani wahala ba dan ba kaya ne sosai a ciki ba, aka gama auna kayan aka basu tag aka tafi boarding room. A nan Islaha ta ga akwai banWaki, bata yi duhun kai ba ta yi alwala ta yi sallolin da suke kanta.

Ganin tayi ya saka Umma ma ta yi, suka dawo suka yi jugum suna kallon jirgi ta glass Win da yake gabansu.

Basu jima ba aka fara shiga jirgi, wanda yake tare da su ya ce, "mu je."

Ba musu suka mi?e a sanyaye suka fita daga wajan suna takawa kamar basa so. Labiba ce take ta video da selfie, su kuwa a hankali suke takawa cikin wani yanayi.

Lokacin da suka shiga jirgi ganin abun suke yi kamar a mafarki. A econamic class suke, kujeru huWu ne, Islaha ce a ciki har ta tana kallon Window. Sai Umma a kusa da ita, sai Labiba sannan shi.

Duk sun yi shiru babu wnada yake magana, Islaha ta kunna data ta turawa Safeera cewa sun shiga jirgi.

Ba jimawa aka rufe jirgi, aka fara yi musu bayanin da komai da komai na mintina ashirin, daga nan aka kunna jirgi ya fara juyawa a hankali. Islaha ta runtse ido lokacin da jirgin ya fara gudu, ta ri?e hannun kujerar lokacin da ya Waga ya lula zuwa sararin samaniya, tana ji kamar jirgin ya Waga da duk wani burinta na duniya& ..

Safe flight mutanen Saudia=?L? [6/30, 9:54/ AM] KRBBK: RDB2P28
Nana Haleema.

Safeera tunda ta koma gida take kuka, ?an uwan Umma suna tayi mata waya suke yi amma ta ?i Wauka, a ganinta babu amfanin Waukar tunda dai Umma ta riga ta tafi.

Tana tsaka da wannan tunanin ?anenta suka dawo, Rukayya ta shigo a hankali ta ce, "Adda Safeera baki da lafiya ki ke kuka?." Jin muryar ?anwata ya sake karya zuciyar Safeera, ta cigaba da kuka babu ?a??autawa.

Yaran duk suka zageye ta suna kallo, Ru?ayya ta ce, "Adda ki daina kuka, naga Umma bata nan, bara na faWawa Baba baki da lafiya" ta faWa tana mi?ewa ta fita.

Babu jimawa suka dawo da Baba, ya tsaya daga bakin ?ofa yana kallon ta cikin tausayawa sa karayar zuciya ya ce, "Safeera!."

Jin muryar Baba ya saka ta Wago fuskarta ta yi kaca-kaca da hawaye.

Baba ya bita da kallo ya ce, "ki bar wannan kukan, ki yi ha?uri ki tashi ki rarrashin ?an uwanki. Ke ce uwa a gare su a yanzu, shigar ki damuwa zai dame su. Ki daure ji kawar da duk abinda yake damun ki, ki zama jaruma ko dan saboda su."

Rukayya cikim mamaki ta ce, "Baba Umma bata nan ne?."

Ya kalle ta ya Waga kai ya ce, "Umman ku tayi tafiya, kuma zata jima bata dawo ba."

Humaira mai biye mata ta ce, "Katsina ta tafi Baba?."

Ya girgiza kai ya ce, "Umman ku ta Wan yi nisa da ku, zata kwana biyu bata nan. Ku kwantar da hankalin ku, zaku dinga waya da ita in sha Allah."

Rukayya gabanta ya faWi, dan sai take ji kamar Umman mutuwa ta yi ta ce, "Baba ina ta je?."

Ya kalle ta a tausashe ya ce, "kar ki damu, zo ki dafa muku abinci dan ko girki ba a yi ba. In akwai abinda babu ki faWa min sai a siyo."

Rukayya ta fito a hankali ?annenta suka biyo bayanta cikin damuwa mai tsanani.

Baba ya kalli Safeera bayan sun fita ya ce, "ki bar wannan kukan kar ki jawowa kan ki ciwo, kukan ki bazai saka babar ki ta dawo ba tunda ta yi niya sai ta yi. Ki kwantar da hankalin ki, babu abinda zai faru in Allah ya yarda. Tafiyar ta babu abinda zata rage daga cikin farin cikin gidan nan, dan ta tafi ba hakan yana nufin mun daina walwala da farin ciki ba, zamu cigaba da yin komai kamar yadda muka saba in sha Allah. In kina zama a haka ya ?annen ki zazu kasance? Ke kin samu sallama da ita, su kuwa basu san ma zata tafi ba sai yanzu."

"Rukyya zargi take yi kamar babar ta ku mutuwa tayi aka Soye musu. Sai kin saki jiki kina walwala sannan suma zasu sake, in kina a cikin damuwa suma zasu shiga damuwa. Ke ce babba, duk halin da suka ganki a ciki suma a ciki zasu kasance.

Safeera ta goge hawayenta ta ce, "To Baba."

"Mun yi waya da mutanen Katsina, sun ce suna ta yi miki waya bakya Waukar wayar. Ki Wauka ku yi magana, rashin Waukar wayar zai dame su sosai. Ko kin Wauka ko baki Wauka ba Maimuna ta tafi, gwara ki Wauka ku yi magana dasu."

Safeera ta kuma Waga kai ta ce, "zan Wauka Baba."

Baba ya ce, "Yauwa. Ki fito wajan ?am uwanki ku dafa abinci ku ci, ba sai kun ajjiye min nawa ba, bana jin yunwa. In akwai abinda za a siya sai ki faWa min."

Hawaye ya sake sakko mata, ya bita da kallo ya ce, "ki daina kuka, ki Wauka kamar taje Katsina ta dawo ne, kin ji?." Ta Waga kai alamun to Baba ya juya ya fita.

Sai da ta jima a zaune sannan ta fito, ta tarar har sun gama jollop Win taliya sai ?hamshi take yi.

Rukayya ta bita da kallo ta ce, "Adda mun gama, kizo ki ci."

Ta girgiza kai tana zama a kan kujera ta ce, "bana ci Ruky, ku ci kawai."

Rukayya ta yi sak tana kallon ta, cikin sanyin jiki ta ce, "Adda don Allah me ya faru?."

Safeera ta lumshe ido ta buWe ta ce, "Babu komai, ku ci abinci kawai." Rukayya ta zauna suna ci a tray Waya, basu jima da fara ci ba Safeera ta mi?e ta shiga Waki.

Rukayya ma ta tsame hannunta bi bayanta, ta same ta a tsaye a Waki ta ce, "Adda don Allah ki faWa min abinda yake faruwa, ki taimaka min ki sanar dani hankalina ya kasa kwanciya wallahi."

Safeera ta kalle ta ta ce, "Rukayya Umma ta tafi saudia aiki, ta bar gidan nan bamu san ranar dawowar ta ba."

Rukayya ta ce, "Yanzu sai da Umma ta tafi?."

Safeera ta Waga kai ta ce, "Ta tafi Ruky. Ki je ku cigaba da cin abincin saboda su Aysha."

Rahma jikinta a sanyaye kafin ta ce, "To wa ta bari wanda zai dinga kula da Baba?."

Safeera ta ce, "Umma bata yi wannan tunani ba ta tafi. Mu kwantar da hankalin mu, tunda Baba yana nan komai zai zo mana da sau?i."

"To Adda ta ya hankalin mu zai kwanta kina nan kina nan kuka? In baki kwantar da hankalin ki ba mu ma hankalin mu bazai taSa kwanciya ba."

Safeera ta yi ajiyar zuciya ta ce, "kaina ne yake ciwo, magani zan sha zuwa anjima zan dawo mu zauna mu yi hira."

"to Adda, Allah ya ?ara lafiya" ta faWa tana fita a sanyaye.

Ba jimawa ta dawo, ta kalli Safeera ta ce, "Adda Abba na Katsina yana son magana dake."

Safeera ta buWe iso ta yi mata alama da ta ce bacci take yi. Rukkya ta juya ta fita Safira ta kwanta, bata ga amfanin magana da dangin Umma ba tunda dai Umma ta riga ta tafi balle su dakatar da ita, shiyasa babu da wanda zata yi magana, kowa bata bu?atar magana dashi tunda maganar bazata dawo mata da Umman ta ba.

" " " " " " " "

*KING ABDULAZIZ INTERNATIONAL AIRPORT JEEDAH.*

Awansu shida da rabi a sama suna tafiya, Islaha tunda aka tashi bata iya motsi ba, abincin jirgin ma bata iya ci ba, cake kaWai taci sai ruwa. ?arfe shida na safiyar Saudia suka garin Jeddah.

Dukkansu suna bayansa suna tafiya a hankali, sai da suka ?araso wajan da za a buga musu stamp sannan ya kalle su ya ce, "ku je ku hau layi, ga wannan ku mi?a musu."

Basu musa ba suka hau layi suna kallon wajan cikin burgewa. Kaf ma'aikata mata ne, wasu sun rufe fuska da ni?ab wasu kuma fuskar su a buWe. Sai larabci suke yi, ga mutane mabanbanta ana ta kai kawo a wajen, komai nasu very neat babu dauWa ko ?azanta.

Islaha ta ?arasa ta mi?a passport Winta, matar ta karSa Islaha ta bugawa Islaha Stamp Win shiga Sauida bayan ta yi thumb print, Islaha ta koma gefe ta tsaya tana jira a gama dasu. Ba jimwa suka tafi wajan da zadu Wauki kayansu.

A lokacin ya kalle su ya ce, "in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login