Showing 123001 words to 126000 words out of 221574 words

Chapter 42 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

171

san halin ki, ba yau ki ka saba jin halinsa a bakin Umma ba, ba yau ki ka san abinda Baba yake yi a bakin Umma. Tunda haka ne ba sai ayi auren a wuce wajan ba?."

Ta Wan yi shiru tana murmushi, ta kalli Kausar da take kallonsu ta ce, "Kausar ba ki ce komai ba."

Kausar wacce bata wuce agemate Win Rukayya ?anwar Safeera ba ta ce, "ki amince Mama, ina goyan bayan hakan."

"Bakwa ganin na ci amanar ?awata? Ta yarda dani, ta bar min amanar gidanta, kuma ta dawo ta ga na auri mijinta?."

Safeera ta yi caraf ta ce, "babu wani cin amana, ko tana nan dan kin auri Baba ai ba laifi bane, balle kuma bata nan."

Ta Wan yi murmushi tana jin daWi a ranta, dan yadda ta san halin Baba yana tsarewa iyalansa komai na rayuwa, zata so ace ta aure sa Win. Bai ragi iyalansa da komai ba, duk ?arfinsa akan ya nemo ya kawo musu yake ?arewa. Za ta so ta rayu a ?ar?ashin wanda zai ri?e ta hannu biyu, ya girmamata kuma ya san darajar ta. Mama Atika ta ce, "shikenan Safeera, na amince."

Safeera ta rungume Mama cikin farin ciki ta ce, "mun gode sosai Mama, Allah ya saka miki da alkhairi, Allah ya ba ki ha?urin zama damu."

Ta shafa bayan Safeera tana murmushin jin daWi, dan gaskiya abin ya zo mata bazata, kuma ta ji daWi, ta karSi auren hannu biyu.

Safeers ta mi?e ta ce, "bara na je na sanar da Baba, sai ya zo ku yi zance ko?."

Mama ta kai mata duka tana dariya, Safeera ta kauce ta fita tana dariyar farin ciki.


A zaune ta samu Baba, ta shiga kamar an cillo ta tana kiran sunansa, ya Waga kai ya kalle ta ya ce, "Safeera lafiya?."

Ta zauna a kusa daahi ta ce, "Baba ina da wani albishir da zan yi maka."

Ya kalle ta ya ce, "ina ji Safeera."

"Mama Atika dai ta amince."

Baba ya girgiza kai cikin mamaki dan ko kaWan tunaninsa bai kai wajen ba ya ce, "ta amince da me?."

Ta Wan Sata fuska ta ce, "auren mana."

Ya ri?e haSa ya ce, "Yanzu Safeera zuwa ki ka yi ki ka same ta? Ni na ce miki ki je ku yi maganar nan ne?."

"Baba ai ka amince, itama amincewar ta na je nema kuma na samu. Yanzu kawai ayi magana a Waura auren ranar juma'a a huta."

Ya kalle ta ya ce, "Ranar juma'a! Har kin yanke lokaci?."

"Eh mana, to me za a jira?."

"an faWa miki haka ake auren ba a bada komai ba?."

"To Baba ai kana da abinda zaka bata Win, kawai ka je ku yi magana."

Ya yi murmushi bai ce komai ba, dan bai san me zai cewa Safeera ba. Safeera ta ce, "Ni sai na raka ka ma." Ya kalle ta, sai ta mi?e da sauri ta fita tana dariya.?

Ya girgiza kai yana murmushi, zai yi ne kawai dan ya ga suna farin ciki da hakan, kuma danginsa gabaWaya sun bada goyan baya a kai, kuma yana so ya aure ta Win ko dan ta kula yaransa in ya bar garin.

Baba ya sauke numfashi, ya cigaba da abinda yake yi yana tuna Umma, zuciyarsa tana faWa masa ko tana ina yanzu, ko ta samu kuWin da take nema bai sani ba. Ya Wan sauke numfashi yana tuna kishin Umma, duk da ba matarsa bace a yanzu, in ta ji labarin Atika zata aure sa sai ta yi jinyar kanta. Ya Wan yi murmushi, ya cigaba da abinda yake yi.

? ? ? ?? " " " " " " "

Suna zaune zaman meeting na ?ungiya, sun yi shiru ana sauraren abu a cikin wayar. Yadda suka nutsu da kyau zai baka tabbacin abin mai mahimmaci suke ji, dan daga yadda suka ba da hankali su a kai ba za ka san ba ?aramin abu bane.

Sai da aka gama jin muryar tass, aka juyo ana kallon juna, kowa da abinda yake tunani. Babban cikin su ya kalli Mama, ta Wan tsorata ta ce, "ya ku ke kallona kuma, laifina ne?."

Wanda yake zaune a gefe ya ce, "in ba laifin ki ba laifin waye? Ace yarinya ?arama har ta samu damar yi miki recording kina yi mata irin wannan maganar? Yanzu ba dan ya zo hannunmu ba ya kenan?."

Mama a kiWime ta ce, "ban yi tunanin tana da wannan wayon ba, kuma wallahi Islaha ce ta saka ta."

"Komai ki ce Islaha, komai Islaha. Ita wacece da baza a Wauki mataki a kanta ba? Haka zamu zuba ido ta Sata mana gari?."

Mama ta kalle sa ta ce, "babu yadda ban yi ba, har sace ta na saka a yi, amma yarinyar nan duk abinda na haWa mata kaucewa take yi."

?aya daga ciki ya ce, "Zainab ce a gabanmu yanzu ba Islaha ba. Me ya kamata a yi? Na tabbatar akwai masu recoding Win nan da yawa, ba a san iya adadin mitanen da aka turawa dan su ajjiye ba. Tunda har bincike Islaha take yi baza a bar recording Win a wajen mutum Waya ba, za su rarraba shi inda ba a yi tunani ba, ko da ya Sace daga wajen Waya, Waya yana dashi."

Mama ta ce, "wa zata turawa in ba Islahan ba, ita ce dai kawai. Yarinyar nan har hotunan Hafsa ta Wauka a hotel, ba dan Allah ya kiyaye ba da yanzu muna prison."

"Kina prison dai, wa za a Waure in ba ke ba? Ke ce uwa a gidan, kuma ke ce ki ke fito mana da yaran nan, ke gwamnati zata kama ba mu ba" ?aya daga ciki shima ya faWa yana kallonta.

Mama ta dafe kai cikin takaici da tashin hankali ta ce, "wai ni Zainab zata yiwa recording, ni zata nemi tonawa asiri?. Na rantse da Allah bazan bar yarinyar nan ba, sai na yi mata abinda nata taSa tunani ba. Ni zata naWa a waya? Ni zata wula?anta?."

Baban cikinsu ya ce, "kawai ku yanke shawara, me ya kamata ace an yi?."

"A Satar da yarinyar kawai, dan zaman ta ba ?aramin bazarana zai zamar mana ba. Ita kanta ma shaida ce, ko babu wannna muryar shiada ce mai girma. Magana ake ta gidan nan na gwamnati ne, ko ya ya gwamnati ta san da maganar nan ba za a tsaya neman wata hujja mai ?arfi ba, ko Zainab Win ce kaWai ta ba da shaida shikenan mun gama yawo. Tunda an kasa mallake ta har ta amince da ?udurin mu, kawai a san yadda za a yi da ita."

Mama sai jikinta ya Wan yi sanyi jin ana zancen za a kashe Zainab, murya a sanyaye ta ce, "a kashe ta kenan?."

Wanda ya yi maganar ya wara hannu ya ce, "meye amfaninta? A kashe ta kawai, itama ta ?asar wajen in ta dawo a yi maganinta, a kashe su duka su biyun ai basu ?arfin kisan ba. Saboda rai biyu zamu ha?ura da aikin mu ne?."

Babban ciki ya ce, "gaskiya ne wannan, abinda ka faWa shi ya kamata ayi. A Satar da yarinyar nan daga garin nan, in hakan bai yu ba a kashe ta!. Itama mai goya mata bayan, a wannan lokacin bana son kuskure, a tabbatar an yi maganinta!."

Mama a sanyaye ta ce, "kisa ya yi tsuri boss, a bani dama na san abinda zan yi."

Cikin faWa ya ce, "sau nawa ana ba ki damar? Dama nawa aka ba ki ki ke wasa da ita?. Nan aka ba ki kwangilar sace yarinyar, nan ashe ba ke ki ka Wauka ta ba. Yanzu kuma kina so a sake ba ki dama dan ki Wauki mataki?...."

Ta yi shiru bata ce komai ba ya ce, "Na gama baki dama, a wannan karon da kaina zan Wauki mataki, ai ba fin ?arfina suka yi ba. Ke kin san muna yin komai saboda idanun mutane, amma yanzu bazan sake saurare ki ba. Kisa shine daidai da Zainab, dole mu tabbatar ta daina numfashi!."


Nana Haleema.
[7/13, 12:11/ PM] KRBBK: RDB2P54
Nana Haleema.

Mama ta kalle sa a sanyaye ta ce, "Tuba nake, amma a wannan karan baza a same ni da kuskure ba."

"Me za ki yi mata?."

"Daji zan aika ta kawai, yadda baza a yi zargin wani abu akan gidan ba."

"Kina nufin ta haukace kenan?."

"?warai."

?aya daga ciki ya ce, "in wata ran ta samu lafiya ta dawo daidai fa?."

Ta kalle shi ta ce, "ban da aikin wajen wanda zan je, in ya yi aiki tamkar rubutu akan dutse ne. Wallahi sai ta haukace."

Duk suka yi shiru Mama ta ce, "a bani wannan damar don Allah, bazan ba ku kunya ba in Allah ya amince. Kisa ya yi tsauri, ba mu san wa ta turawa recording Win ba, in aka kashe ta za a yi zargin mu ne. Amma in ta haukace, ta shiga daji, shikenan mun huta."

Boss ya ce, "me ku ka ce?."

Suka ce, "duk abinda ka ce boss."

Ya kalli Mama ya ce, "An baki dama, amma in aka samu matsala..." kafin ya ?arasaa ta ce, "wallahi babu matsala a harkar nan, ku bar komai a hannuna."

Cikin gamsuwa aka amince da shawarar haukata Zainab, suka cigaba da tattaunawa akan yanayin tsarin aikinsu, kafin kowa ya watse.

Mama tana barin wajan kai tsaye wajan bokan ta wuce. Ta yi bayani yadda ya kamata, sannan ta saka a yi aikin da zai Satar da hankalin Islaha daga kan su, ta manta da duk abinda yake faruwa ta yi harkokin ta, shi ya bata abinda ya kamata ta yi sannan ta koma orphange.

Tana shiga aka kira wayarta, ta Wauka ta ce, "na gama komai, zuwa gobe za ku ji labari mai kyau. Zainab baza ta shura ba, tunda ta fitar da recording Win muryata ai ta shiga uku. Ku bar komai a hannuna, zan Satar da ita wallahi. In kuma nata haukace ba, zamu kashe ta!."

Zainab da ta ji komai, gabanta ya faWi ta bar wajan da sauri. Hannunta yana rawa ta kira wayar islaha amma sai larabci ake yi mata. Jikinta yana karkarwa ta yi mata voice note tana hawaye, tana gamawa ta Wauki kuWi a jakarta ta fita a guje.

? ? ? ? ?? " " " " " " "

Islaha bacci ne ya Wauke tunda dare ya yi, bata farka ba sai sha biyu na dare, tana mi?ewa zaune wayar ta ta jawo tana dubawa. Da voice note Win Zainab ta fara karo, ta buWe tana sauraran abinda take faWa. Bata san ta mi?e tsaye ba, a firgice ta tsaya akan ?afarta jikinta yana rawa sosai.

"Innallahi wa'inna ilaihir raji'un!."

Shine abinda take maimaitawa cikin kiWima da tashin hankali, jikinta har rawa yake yi, kanta yana sarawa saboda tashin hankali.

Zagaye Wakin take yi, duk da akwai sanyin ac amma gumi tsatstsafo mata yake yi cikin tashin hankali da tsananin firgici mai yawa.

Ta kira lambar Zainab amma bata shiga, ta yi mata voice note amma babu alamun datar ta a kunne take. Ta Wora hannu a kanta ta fashe da kukan damuwa da rashin sanin abinda zata yi.

Sai kuma ta zabura ta kira lambar Safeera, daga can Sangaren Safeera ta gama shirin kwanciya kenan tunda suma dare ya yi.

Ganin kiran Islaha sai ta murmusa, daman tana da niyar kiran ta bata labarin auren Baffa da Atika.

Tana Wauka Islaha cikin kuka ta ce, "Safeera na shiga uku, zasu kashe Zainab Safeera. Ki taimaka min ki je ki gano ta, ki taimaka ki je gidan ki ga in tana nan!. In zainab ta rasa ranta ta silata bazan yafewa kaina ba."

Hankalin Safeera ya tashi ta ce, "Ban gane zasu kashe ta ba, su waye zasu kashe ta Win?. Ki nutsu, ki yi min bayani yadda zan gane."

"Safeera ki fara zuwa ki gano min in tana nan, bazan taSa samun nutsuwa ba indai ba lafiyar Zainab na ji ba."

"Goma na dare ta wuce Safeera, Baba bazai barni na fita ba. Kuma ko da na je kin san a rufe gida gate, baza a bar ni na shiga ba. Ki kira ?an uwanki na gidan ki ji in tana ciki mana."

Islaha ta sake fashewa da kuka ta ce, "Bata nan, An ce min ta bar gidan Safeera!. Ina zan saka raina in wani abun ya samu Zainab?."

Saferra jin yadda Islaha take kuka sosai sai hankalinta ya sake tashi sosai, ta ruWe itama, cikin taushin murya ta ce, "ki faWa min me ya faru?."

"Komai ma ya faru, na lalata rayuwar Zainab, tunda ni na bata shawarar ta dinga yi min recording tana turo min, da ban saka ta yi ba da bata yi ba, da ba a yi ?o?arin kashe ta ba. Ina zan saka raina in aka cutar da ita ta silar hakan?." Safeera zata yi magana Islaha ta kashe wayar tana kuka sosai.

Ta nemi number Saheer ta kira sa, bai Wauka ba ta ajjiye wayar ta cigaba da kuka mai tsuma zuciya. Tashin hankalin ta bata ?asar balle ta je ta Wauke Zainab, damuwar ta ta yi nisa da Zainab balle ta kai mata Wauki.

Babu jimawa Saheer ya kira ta, tana Wauka ta sake saka masa kukan da yake jin sautinsa sosai.

Shiru ya yi mata bai ce komai ba, yana jin yadda take sauke numfashi tana fitar da kuka mai sauti. Ya san in ya ce zai yi magana bazata ji sa ba, gwara ya yi shiru ta gama kukan sai su yi magana.

A hankali ya ji tana sauke nunfashi alamun kukan ya tsaya ya ce, "ki nutsu, kar ki jawo numfashin ki ya sar?e. Kin san ba cikakkiyar lafiya ce dake ba."

A hankali take sauke numfashi kafin ta ce, "Hamma!."

Jin yadda ta kira sa ya saka ya ce, "Na'am, ya aka yi?."

Ta lumshe ido ya buWe, a sanyaye ta ce, "Hamma Zainab!."

"Me ya samu Zainab Win?."

"Za su kashe ta Hamma."

"Kisa kuma! Su waye?."

"Su Maman orphage."

"Mafarki ki ka yi akan hakan?."

Hawaye ta sakko mata ta ce, "wayar nan da muke yi mafarki ce?."

Ya ce, "Aa, a gaske ne."

"To da gaske ne abinda na faWa maka, za su kashe Zainab Hamma."

Saheer cikin rashin fahimta ya ce, "da gaske ne me? Ki yi min bayani yadda zan gane. Ki nutsu, sai ki faWa min abinda ya faru."

"Hamma sun samu recording Win da Zainab ta turo min har na tura maka na ce ka ajjiye min, saboda shi zasu kashe Zainab saboda ta naWi muryar Mama ta turo min."

Saheer ya ce, "su waye suka samu recording Win?."

"Maman orphanage."

"ya aka yi ki ka san sun samu har zasu kashe ta?."

Hawaye ya sake sakko mata ta ce, "Zainab Win ce ta faWa min, kuma an tabbatar bata cikin gidan yanzu, na saka a n duba an ce bata nan."

Saheer ya ce, "Islaha anya ba mafarki ki ka yi ba? Ba fa film mu ke kallo ba, zahiri ne." Islaha sai ta yanke wayar, ta tura masa voice note Win Zainab.

Sai da ta tabbatar ya gama ji sannan ta kira sa, ya kiWime ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Yaushe ta tura miki?."

Islaaha ta ce, "tun Wazu, ban gani ba sai yanzu dana farka daga bacci. Hamma in wani abun ya samu Zainab mutuwa zan yi, ni na saka ta ta dinga yi min recording ko yaushe, ni na saka Zainab ta dinga tura min duk abinda ya faru. In suka yi mata wani abun bazan yafewa kaina ba, ko meye ya same ta ni ce sila, Hammaaaaaaaa!" Ta ja sunan cikin heart breaking, muryarta tana cracking cikin tashin hankali.

"Kwantar da hankalin ki, in Allah ya yarda babu abinda zai same ta. Yanzu zan saka Sadik ta je ya sanar da hukuma halin da ake ciki, zan saka a baza neman ta ko za a dace a ganta. Kar ki damu, ki kwanar da hankalin ki, zan yi komai kamar kina ?asar, kin ji?."

Ta girgiza kamar yana gabanta ta ce, "bana so hukuma ta shiga maganar nan tun yanzu, na fi so na gama tattara komai sannan hukuma ta sani."


"Shikenan, zamu bayar da cigiyarta. Amma na tambaye ki."

Kafin ya yi tambayar ta ce, "Ya aka yi aka san ta yi recording Win, har aka san ta turo min ko?."

Saheer ya ce, "haka zan tambaya. Ya aka yi suka san da recordong Win a wajan ki?."

Ta ce, "ban sani ba Hamma, wallahi ban sani ba......" ta faWa tana kuka, sai kuma ta ce, "Ka ga kenan lokacin da aka goge hotunan Hafsa shima? masaniya suka samu a akan hakan, shine aka saka wani a cikin office Win su Safeera ya goge."

Saheer ya Wan yi shiru yana tunani sannan ya ce, "bayan ni, waye ya san da recording Win a wajan ki?."

Islaha ta ce, "kamar dai hotunan Hafsa, daga kai sai Safeera, ta ce min ta faWawa Saleem har ta tura masa saboda gudun Sata, sai Brr Suraj."

Ta yi tunanin zai yi faWa akan Suraj kamar yadda ya saba, amma sai ta ji bai ce komai ba ya yi shiru kafin ya ce, "lokacin hotonan Hafsa ma iya mu haka muka sani ko?."

Kamar tana gabansa ta Waga kai ta ce, "A daren kai da Suraj ku ka sani, washe gari Safeera da Saleem suka sani. Ko mintina ashirin ba a yi da saninsu ba aka rasa hotunan."

Saheer ya ce, "Yanzu kuma gashi recording ya fita, ta silar sa har ana ?o?arin cutar da Zainab."

Ya sauke numfashi yana ya ce, "Islaha!."

"Na'am!."

A sanyaye ta amsa ya ce, "a tsakanin ni, Suraj, Safeera, Saleem akwai munafuki a cikin lamarin ki. Akwai wanda yake da hannu a cikin lamarin nan, zai nuna yana tare dake amma a bayan idonki yana tare dasu. Tabbas akwai suspect a tsakanin mu."

Islsha ta dafe kai cikin tsananin damuwa, ta kasa furta komai, dan tabbas maganar Saheer gaskiya ce.

Saheer ya katse mata tunani ya ce, "ya zama dole ki nemo waye munafukin a cikin mu, kafin nan ki daina faWa mana komai akan abinda ya shafi binciken ki. Ki dinga ajjiyewa a wajan ki, kar ki yarda da kowa, ki yarda da kan ki. Ko ni Win kar ki yarda dani, kar ki yarda da Safeera, balle Suraj. Ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login