Showing 168001 words to 171000 words out of 221574 words

Chapter 57 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

161

masu gadi."

Mama ta kalli Wan nata tana ji kamar ta juya sama ta dawo ?asa, da tana da iko da yanzu ta ?wace Waukaka Rehaan ta bawa Wanta, shine babba amma ya zama kamar shine ?arami saboda bashi da kuWin da Rehaan yake dashi. Ba wai kuWi ne bashi dashi ba, yana da kuWi kamar sauran ?an gidan, kawai Rehaan ya fita zakka a cikinsu. Ita kuma kallon talakawa take yi musu saboda Rehaan, shiyasa take ba?in ciki da hakan sosai.

Ta girgiza kai cike da takaici ta ce, "Kaima dai ban da abin ka, meye abin damuwa dan za a yi bikin ka Riyya baka sani ba?."

"Ba damuwa na yi ba, sai meye san an yi ban sani ba. Kawai babu daWi ne Mama."

"Kar ka ji daWi. Duk ba kai ka jawo ba? Ga hanyar yin kuWi da shahara nan da yawa amma ka kasa bi ka zama kamar Rehaan. Hannunka kamar rariya, da an ba ka kuWi da sun ?are. Haba, ?annenka wanne irin abun duniya ne basu dashi?."

Hamma Zayyad ya Wan taSe baki ya ce, "To Mama zan canja Allah ya yi ni ne?."

Ta ja dogon tsaki, ta cize leSe tana buga ?wafa. Auren nan na Rehan shine target Winta, shiyasa ta Suya ta yi shiru tana jira ayi sannan ta cigaba da aiwatar da abubuwan da suke gabanta, dan wallahi bazata bar Rehaan lafiya ba, sai ta la'anta rayuwarsa ta WaiWaice

" " " " " "

Islaha bata bar Sangaren Baffa ba sai goma na dare, Baffa ya ri?e hannuta da kansa ya kai ta har Waki ya sannan fito. Mama bata ce komai ba dan ta daina Waga jiyoyin wuya, ta ?ar?ashin ?asa zata yi maganin Islaha.

Ita dai Islaha kwanciya ta yi tana tunanin rayuwarta, haka zata yi zaman aure da mijin da babarsa bata ?aunarta? Anya zata samu farin cikin da take fatan samu a aurensa? Anya zata samu kwanciyar hankali da nutsuwar da take fatan samu?.

Hamma yana sonta, zai bata kulawa irin wacce bata yi hasashe ba. Amma babarsa bata so, duk da ba da Babarsa zata zauna ba amma ita ta haife sa. Tun tana faWa masa aibunta baya yarda, wata ran zai yarda, wata ran za a samu akasin da zata yi abinda zai ce daman Mama ta ce.

Ta girgiza kai Zainab ta faWo mata a rai, ta mi?e ta kira Suraj a waya amma bai Wauka ba, ta koma ta kwanta tana tunanin mafita a rayuwarta.

Washe gari da safe bata ji motsin Mama ba, daman bata cika yi mata karanbani ta shiga Wakinta ba sai dole.

Gidan babu kowa alamun Hanan ma bata nan, ta shiga kitchen ta sha tea, dan ya yi safiya baza ta iya cin komai ba sai rana ta fito sosai. Tea Win kawai ta sha, ta shirya ta fito da niyar tafiya aiki.

Tana fitowa suka haWu da Saheer, suna haWa ido ta Wan yi ajiyar zuciya sannan ta ce, "Ina kwana." Bai amsa ba sai kallon ta da yake yi sannan ya ce, "kin ci abinci?."

Ta girgiza kai ta ce, "Ya yi safiya da yawa, zan ci in anjima."

"Ina za ki je da safe haka?."

"wajan aiki zan je."

"Yanzu?." Ta Waga masa kai alamun eh.

Ya ce, "Ya yi wuri yanzu, na san ba ki da aiki a wannan lokacin. Mu je ki raka ni wani waje, daga nan sai na kai ki." Bata ce komai ba suka fito, bai rufe gidan ba dan Baffa yana ciki.


Tunda suka shiga motar ta lura da yanayinsa ya canja, ya haWe rai sosai kuma ko kallonta ba ya yi. Ta ce, "Hamma motar wajen Sadik Win ce?."

Kai kawai ya Waga mata bai ce komai ba, ta yi shiru bata sake kula shi ba. Sun fi mintina goma a haka, shi bai kunna motar ba kuma bai fita ba.

Ya juyo ya kalle ta ya ce, "Sai na ganki kwatsam, har shekara Wayan ta yi?."

Islaha ta Wan murmusa, daman ta san dalilin Sata ran nasa kenan, babu inda zata raka shi kawai maganar yake so su yi shiyasa ya saka ta shiga mota.

Islaha ta ce, "bata yi ba."

"Bani labari, ya aka yi na ganki a nan bayan na san zaman ki a can bai isa kin tara waWanan kuWin ba."

Ta sunkuyar da kai ?asa ta ce, "Hamma...."

Ya yi saurin dakatar da ita ya ce, "kar ki Soye min komai, in na same ki da Soye min wani abu kamar yadda ki ka dinga yi a baya zamu yi faWa mai muni."

Ta girgiza kai ta ce, "bazan Soye maka komai ba, in sha Allah."

Ya Waga kai ya ce, "ina jin ki."

Ta yi shiru kamar baza ta yi magana ba, dan bata san da wacce fuska zai Wauki maganar ta ba, ita kanta jin maganar take kamar wasan yara balle kuma shi. Ta sanyaya murya ta ce, "kamar yadda na faWa maka ina samun kyautar kuWi a gidan aiki, to a haka na tara kuWin."

Ya sake kallon ta ya ce, "cikin wata biyun ki ka tara miliyoyin nan?."

Ta girgiza kai ta ce, "ba wannan ba, wanda na siyo ticket na dawo gida nake nufi."

"Okay, waWancan fa?."

Ta sake kallon sa ta ga ita yake kallo, sai ta daure saboda kar ya zarge ta ta ce, "Mun haWu da Jafar ne, wanda muka taSa haWuwa dashi a Diamond hotel, lokacin da na je neman Rehaan Yola zamu yi interview. Shine ya ce min na dawo gida aikin bai dace dani ba, shi zai biya Rehaan kuWinsa."

Saheer ya tsaya yana kallon ta jin wata magana mara kan gado, ta sako wasu mutane da bai san da su a cikin labarin ba. Ya ce, "Me ya kawo Jafar cikin maganar nan kuma? Ya aka yi ya san da batun kuWin?. Sannan me ya kawo Rehaan Yola a ciki?."

Islaha ta Wan shiru sannan ta ce, "Shi wanda ya sace ni Win, ashe shine Rehaan Yola ban sani ba, kuma..."

Saheer ya dakatar da ita ya ce, "ban gane ba, kamar ya shine Rehaan Yola, Rehaan Yola dai wanda na sani ki ke nufi?."

"Shi Win dai Hamma. Shine ya Wauke saboda mun haWu sau biyu na yi masa rashin kunya, sannan gidansa ne gidan da nake zuwa yin aiki a Jeddah. A nan muka haWu da Jafar, ya yi bincike a kaina ya san wacece ni, shine ya ce aikin bai dace dani ba, ni kuma na faWa masa dalilin zuwana Jeddah, shine ya ce na dawo gida zai biyasa kuWinsa. Shine kawai na dawo."

Saheer ya ce, "lokacin da kina Jeddah, kin ce min matar gidan ce ta ke yi miki kyautar kuWi saboda tana da kirki, yanzu kuma kin ce Rehaan ne. Meye gaskiyar maganar?."

"?arya na yi maka a wancan lokacin, bana so ka yi min faWa kace ina zuwa wani gidan ne shiyasa na ce maka haka. Amma shi ko aure bashi dashi."

Ya zuba mata ido kawai yana kallon ta, ita kuma ta ?i kallonsa ta kawar da kai gefe tana jira ta ji amsar da zai bata.

Sun kwashe minitina ashirin a haka kafin ya ce, "Wanne series ne, waye ya ya yi directing film Win?. Na san dai labari da tsarwa na ki ne, to waye ya ba da umarni?."

Ta juyo suka haWa ido jin abinda ya ce, ya Waga mata kai ya ce, "a wacce channle ake haskawa nima na gani, ko a youtube ne?."

Islaha ta sauke numfashi jin bai yarda ba, ta lumshe ido ta ce, "Hamma da gaske nake fa."

"Nima da gasken nake ai, ki faWa min sunan series Win na je na kalla. Ko sunansa rainin hankalin Islaha?."

"Hamma...!"

Ya dakatar da ita ya ce, "Ni za ki mayar ?aramin yaro Islaha, ni za ki zauna kina rainawa hankali dan kin ga ina Waukar ko wacce damuwa daga wajen ki?."

Islaha ta ce, "Da gaske nake Hamma."

"Da farko kin ce min ba ki san wanda ya sace ki ba, kin ce ba Wan ?asar nan bane ba, aka yi ta fama dake akan ki ba da wata hujja da za a iya gano waye ki ka ?i faWa. Yanzu sai Rehaan Yola ya shigo cikin wasan kwaikwayon ki, sai ga Jafar ma ya shigo cikin wasan dan a yi acting Win dashi. Da yake kin mayar da Rehaan abokin wasan ki ko, An faWa miki ?aramin mutum ne shi?. Ko kina faWa sunansa ne dan na ji a raina ai kina tare da mai kuWi bara in bar magana? Ko kina faWa min Rehaan ne dan na ji a raina baza ki yi min ?arya dashi ba?."

Islaha zata sake magana ya hanata ya ce, "indai wannan shashancin za ki cigaba da faWin min bana son ji, ki ri?e kalamanki kawai. Gwara ki fito fili ki faWa ki ce Hamma bazan faWa maka ba, ya fi min daidai akan ki dinga raina min hankali kamar wani sa'anki."

Islaha ta ce, "Wallahi da gaske nake, bazan yi maka ?arya ba."

Ya kalle ta ya Wauke kai sannan ya ce, "Da dai bakya yin rantsuwa akan ?arya, amma yanzu kin fara. Ke da bakin ki kin ce ?arya ki ka yi min dan kar na yi miki faWa, wannan ma dan lin yi min ?arya ba yau aka fara ba."

Islaha sai ta yi shiru dan bata san me zata ce masa ba kuma, tunda har ya yi tunanin ta rantse a kan ?arya gwara kawai ta yi shiru da bakinta zai fi alkhairi.

Ta yi shiru shima ya yi shiru, ya zubawa ?aramin titin masu ido ita kuma tana wasa da jakarta bata sake ce masa komai. Baza ta sake cewa komai ba tunda ya yace tana rantsuwa a kan ?arya a je a hakan, gwara ta yi shiru kar ta yi masa rashin kunya tazo tana danasani daga baya.

Shi kuwa tunanin wannan rainin hankalin nata kawai yake yi, ji yake ba a taSa raina masa hankali a duniya kamar yadda Islaha ta yi masa ba, ji yake ba a taSa yi raina masa wayo da wula?anci kamar abinda ta yi a lokacin ba.

Zuciyarsa ta fara Warsa masa abubuwa kala kala a kanta, ya fara zargin kalaman Sadik dana Mama gaskiya ne, tunda gashi ta saka shi a gaba tana raina masa hankali kamar wani yaro Wan shekara Waya.

Ya yi ajiyar xuciya bai ce komai ba, sun jima a haka kowa ya yi shiru babu wanda ya sake magana a cikinsu. Sai daga baya ya ja motar suka tafi wajan aikin bai sake yi mata magana ba.

A bakin gate Win ma'aikatar ya tsaya baice mata komai ba, ta Wauki handbag Winta sannan ta kalle shi, kamar kar ta yi magana sai kuma ta ce, "in na yi ?arya da sunan Ray wacce riba zan samu Hamma? Wanne irin amfani hakan zai yi min da zan rasa da wanda zan yi maka ?arya sai shi?. Amma tunda kana jin abinda na faWa maka a matsayin ?arya shikenan, har kana cewa ina rantsuwa akan ?arya. Duk tunanin da zuciyarka ta baka a kaina ka yarda hakan ne, kar ka tilasta zuciyarka ta amince da gaskiya na faWa, ka yi amfani da yardar ka ya fi" ta faWa tana fita daga motar har lokacin bai ce mata komai ba.


_Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.=?O?
Nana Haleema.
[7/22, 10:14/ AM] KRBBK: RDB2P76
Nana Haleeema.

Sai da ya ga ta shiga wajan aikin sanann ya ja tsaki, a bayyane ya ce, "Islaha ?ar rainin hankali ce, ni zata saka a gaba tana bugawa kamar ball dan ta raina ni? Da farko an sace ta, ta biya kuWin aikin baffa, ta saka aka kulle case, ta tafi Jeddah, ta yi min ?aryar wata mace ce take bata kuWi, yanzu ta dawo tana kallon idona tana faWa min wai Mr Rehaan ne. Mtsww!"ya faWa yana jan motar ya bar wajan.

Yana barin wajan da Sadik suka haWu, Sadik ya shiga motar ya zauna ya ce, "Ya dai na ganka da Sacin rai a safiyar nan, bayan jiya kace min akwai labari?."

Saheer ya kalle shi ya ce, "kalli fuskata Sadik, na yi kama da shashasha?."

Da mamaki ya ce, "ban gane ba, me ya faru?."

Saheer ya ce, "yarinyar nan Islaha ce take neman mayar dani mahaukaci."

Sadik ya yi yar dariya ya ce, "sai yanzu ka sani kenan....Hmmm me ya faru?."


"Na tambaye ta akan ya aka yi ta dawo gida bayan bata gama abinda ta je yi ba, a ina ta samu kuWi, ka san me ta ce?."

"Sai ka faWa."

"Wai Rehaan Yola shine ya sace ta, kuma dashi ta haWu a can, Jafar ya biya mata kuWin kuma ya ce ta dawo gida."

Sadik ya ce, "ban gane ba, wanne Reheen Yola Win?."

"Wanda ka sani, wanda ta je hotel yin interview dashi kwanaki. Wai da shi ta haWu dashi a can, daga nan suka haWu asibiti, ya sace ta, ta sace masa kuWi, ta je Jedda suka haWu......." Sai ya ja dogon tsaki yana dukan motar, ya dafe kai ya ce, "Islaha ta mayar dani mahaukaci gabaWaya."

Sadik ya ce, "bayan mahaukaci ta mayar da kai sakarai wanda bai san abinda yake yi ba. Ta rasa da wanda zata yi ?arya sai da Ray? Kuma duk wannan shirmen da ta lissafa ta ce duk da shi ya fau? Ta rasa wanda zata ?ullawa sharri sai shi?."

"Hmm!" Ya faWa yana jan numfashi kawai bai ce komai ba dan bai san abinda zai ce ba.

Sadik ya ce, "wannan maganar bata da kan gado balle makama, da sunan wani zauna gari banza ta faWa ma sai a yarda, amma sunan wanda ta kira ba abin wasa bane. A ina zata ga Rehaan ma, mutumin da ko yaushe yana Uk? Ko da ma shi Win ne, ace bata taSa ganin hotonsa ba balle ace har ya sace ta bata san shi bane?. Islaha fa ?ar jarida ce, kuma ?ar social media ce, duk wanda yake hawa kafafen yaWa labarai ?arya yake yi ya ce bai san Rehaan Yola ba. To akan me ma zai zubar da class Winsa ya Wauke Islaha fisabinillahi?."


Saheer dai bai ce komai ba, dan gani yake Islaha ta gama katantanwa da hankalinsa gabaWaya.

Sadik ya kuma cewa, "Allah ya kyauta kawai, amma akwai wani abun a ?asa. Ina jin ka, meye labari mai daWin?."

Saheer muryarsa a sha?e ya ce, "share kawai, zuwa anjima zan wuce in sha Allah, komai normal ko?."

Sadik ya ce, "komai ya yi normal, sai mun haWu" ya faWa yana fita daga motar shi kuma ya ja motar ya tafi.

Islaha tunda ta shiga ake ta murnar ganinta, Chairman har office Winta ya shiga yana ta murnar ganinta, ya zauna ya ce, "Malama Islaha, saukar yaushe?."

Ta yi dariya ta ce, "Shekaran jiya."

DaWi ya mamaye ransa ya ce, "ni da ake ta cewa ga Islaha na Wauka wata muka samu daban ba ke ba, sai na yi tunanin kaf gidan nan ke kaWai ce mai irin wannan sunan, ashe ke Win ce dai."

"Ni ce Chairman."

"Barka da sauka Islaha."

"Yauwa Chairman."

"Amma dai an dawo kenan ko? Baza ki sake guduwa ki bar mu ba? Allah in za ki sake sai dai ki nannaWe toron giuwa ki tafi da ita, dan baza mu zuba ido ki saka mu watse ba."

Ta yi dariya ta ce, "na dawo in sha Allah, babu inda zan sake zuwa, muna nan tare."

Ya sauke numfashi ya ce, "har na ji daWi wallahi, da na san kina nan ai da ke za ki yi labaran ?arfe shida. Amma akwai na sha biyun rana ai, Allah ya nuna mna."

Ta yi murmushi ta ce, "Amin Chairman."

"Ki gode Allah Islaha, kina da sa a sosai a rayuwar ki. Kina daga inda ki ke ma Waukakar bata bar ki ba, wannan Wan content Win da ki ke yi ya sake farfaWo damu daga doguwar suman da muka afka da bakya nan."

Ta yi dariya bata ce komai ba, Chairman ya ce, "yau yau Win nan za a fara ganin ki, akwai labarin wasanni da za a gabatar kai tsaye, tashi ki hau camera."

Ta Wan buWe ido ta ce, "Aikin Jamila da Muslim ne fa."

"Yau kema za ki Wana, ni na san za ki iya. Taso maza maza."

"Chairman faWar sunan ?an ball Win nan wani lokacin yana bani wahala, kar na kwafsa fa."

Ya kalle ta ya ce, "Sai dai in wata Islahan, ba dai ke ba, mu je." Ta dole y saka ta gabatar da shirin ba dan tana so ba.

Da yake shirin live ne a radio da tv da kafafen sada zumunta, an sha ruwan comment ana murnar sake ganin fuskar Islaha.

Shigowar Ummi kenan ta samu ba?in labari, ta nufi office Win Islaha dan ta ganarwa idonta. Tana shiga suka haWu, Ummi bata ce komai ba ta juya ta bar wajan da hanzari.

Islaha ta taSe baki, bata bi ta kanta ta wuce record office wajan Safeera, a hanya suka haWu da Safeeran ta taho nemanta, sai suka koma office Win su Islahan dan su tattauna."

Safeera ta ce, "Ya dai? Na ga duk kin canja."

Islaha ta ce, "Hamma ne bai yarda da labarin da na bashi ba, wai har yana cemin ya sunan film Win."

Safeera ta ce, "ba kowa ne zai yarda ba fa Islaha, ni kaina sai da na kai zuciya nesa sannan ya amince da maganar nan. Kowa zai yi tunanin me ya kawo Ray cikin zancen ki, da ace ?arsmin mutum ne babu wanda zai damu, amma sunan babban mutum kamar sa ki ka ambata, iya faWa kawai mutum zai ga kamar kin raina masa hankali ne kawai."

"amma meyasa ke ki ka yarda shi bai yarda ba? Wai har yana cewa ina rantsuwa akan ?arya, wallahi Safeera baza ki bini bashin rantsuwa ba, bazan yi abinda zai cutar dani dan na kare kaina ba. Safeera duk abinda na faWa miki an yi, wani abun ma ban faWa miki ba. Meyasa Hamma bazai yarda dani ba? Shima ya fara zargina kamar Mamansa kenan?."

"ba zargi bane, kawai zai ji kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login