Showing 141001 words to 144000 words out of 221574 words

Chapter 48 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

140

ba, tunda akwai tsinuwar uwa a cikinsa. A bi komai a hankali, islaha matarsa ce in sha Allah, amma a bari a daidaita komai sai ayi auren."

Baffa ya sauke numfashi ya ce, "Itace zata juya ni kenan?."

Baba ya dafa Baffa ganin ya fusata da yawa, daga ganin yadda ya fusata ya san an kai shi bango, dan Baffa ba mutum ne mai saurin Waukar zafi ba, tunda ya ga ya fusata sosai ya san abin ya taSa ransa.

Ya ce, "ba juya ka ta yi ba, hankali da nutsuwa ka fita. In aka yi auren nan rayuwar Saheer a gaba za ka duba, tsinuwar uwa ai ba abin wasa bane. Kai ka fita hankali, bai kamata ka biyewa zuciya shaiWan ya zuga ka ba. A yi ha?uri, abar maganar Waurin auren nan a yau, in Allah ya kaimu lokaci sai a yi, amma yanzu a dakatar dashi."

Baffa ya ce, "Baza a fasa auren Saheer da Islaha ba, bata isa ta saka na fasa abinda na yi niya ba, akan Zulaiha bazan fasa aurawa Saheer Islaha ba. Akan auren Saheer da Islaha, zan iya sakin Zulaiha!."

Nana Haleema.
[7/17, 11:50/ AM] KRBBK: RDB2P62
Nana Haleema.

Saheer ya kalli Baffa da sauri jin abinda ya ce, Baba ya kalli Saheer sannan ya kalli Baffa ya ce, "Haba Mustapha, wannan wacce irin magana ce mara kan gado?. Zulaihan za ka saki??."

Baffa ya ce, "A kanta aka fara?."

"Ba a kanta aka fara ba, kuma ba a kanta za a gama ba. Shi kansa Saheer Win ya kalle sa ka gani, ai bazai so ace ta silar aurensa auren mahaifiyarsa ya ?are ba. ShaiWan ne yake zuga ka, ka kwantar da hankalinka, Allah zai nuna mana gaba." Baffa ya shiga Waki bai ce komai ba.

Baba ya ri?e hannun Saheer suka fita daga falon, dan ya ga yadda Baffa ya fusata sosai bazai yi magana a gabansa ba.

Baba ya kalle Saheer ya ce, "ka yi ha?uri ka bar maganar, zuwa gaba sai ayi auren ai ba gagawa ake yi ba. Na san baza ka so auren babar ka ya lalace saboda auren ka ba."

Ya Wan Waga kai ya ce, "haka ne Baba, Allah ya kaimu lokacin."

"Amin. Ka cigaba da yi mata biyayya, ka cigaba da tausarta har ta amince da auren. Kar ka yi abinda bata so, kar ka yi abinda zata yi maka baki a kai, dan baza ka ji daWinsa ba. Ka cigaba da addu'a, in alkhairi ce Allah ya zaSa maka, sannan ita ya saka mahaifiyar ka ta amince, in ba alkhairi bace Allah ya canja maka da mafi alkhairi." Ya amsa da amin suka nufi masallaci don yin sallar juma'a.

A gidansu Safeera ?an uwan Baba mata suna nan, dan ranar za a Waura auren Baba kuma ranar zata tare. Suna gidan sun zo karSar amarya, dan ba ?aramar murna suke yi da auren ba. Ita kanta Safeera tana murna da auren, dan tana son kwanciyar hankalin mahaifinta sosai.

Daga cikin falon Umma suke zaune, Gwaggo Yayar Baba ta ce, "ni na ji daWin haWin nan wallahi, ko babu komai Maimuna zata san ta tafka kuskure, inda ta bari saboda abin duniya aminiyarta ta shigo."

?aya daga ciki ta ce, "Maimuna bata da matsala fa Gwaggo, matsalar ta Waya, shine zaSar abin duniya akan yaranta da mijinta da ta yi, itace matsalar da aka samu da ita. Amma bayan wannan tana da kirki kowa ma ya shaida."

?aya ta ce, "Kuma na ji labarin an ce wahala take sha a can ?asar, duk ga rame ta damu ta dawo."

Gwaggo ta cs, "To ko ha??in mai gidan nan zai barta ne? Barin auren ta yi ta tafi wata ?asa aiki, ai ko wu?anata aure da ta yi sai Allah ya hukunta ta. Yanzu ga amarya zata shigo, Kowa yana yabon halin Atika na kirki da dadtaku. Na ji daWi wallahi, Allah ya saSa halaye." Suka amsa da amin suna cigaba da tattauawa.

Safeera tana Waki duk tana jinsu, bata ji rashin jin daWi ba kaWan, dan ta san gaskiya suka faWa ba ?arya ba, da Umman bata aikata ba da hakan bai faru ba. Sai da ta ji dawowar Baba, su gwaggo suna ta yi masa Allah ya sanya alkhairi da addu'a sannan Safeera ta yi murmushi, ta Wauki waya ta kira Islaha.

Islaha tana kwance akan gado, lokacin la'asar ya kusa a Saudi, tana jiran kiran Saheer amma shiru. Jin kiran Safeera sai ta tsorata, ta mi?a hannu a sanyaye ta Wauko wayar daga gefenta ganin Safeera ce sai ta Wauka.

Islaha tana saka wayar a kunne Safeera ta ce, "Islaha an Waura auren."

?irjin Islaha ya buga dummm, ta ji wani irin abu zuuu yana yawo a jininta, ta ji wani shock kamar jan wutar lantarki, wani irin Wumi mai kama da zazzaSi yana lulluSe ta, zuciyarta ta tafi tunanin yanzu kenan ta zama matar Hamma? Ta zama mallakin Hamma halak malak, ta zama matarsa ta sunnah, ko yanzu akace babu shi sai ta yi masa takaba?. Sai ta kasa magana, bakinta ya yi nauyi sosai, ta ri?e waya a kunne tana jin sautin bugun zuciyarta a kunnenta. Bawai auren Hamma ne bata so ba, gaggawar da aka yi a Waura auren ne bata so.

Safeera da zumuWi ta ce, "Yanzu Baba ya dawo, an Waura aure yau."

Islaha ta ja numfashi mai ?arfi bata ce komai ba, Safeera ta ce, "Ya dai?."

Islaha ta ce, "Nima ban sani ba Safeera, haka kawai nake jin bana murna da auren."

Da mamaki Safeera ta ce, "meyasa bakya murna?."

"Wallahi ban sani ba, ni kaina bazan ce ga dalili ba. GabaWaya ji nake kamar a warware auren nan, bazan iya zama da aure a kaina ba."

"auren Baban?."

Islaha ta buWe ido tana mi?ewa zaune ta ce, "Wanne Baba kuma?."

Safeera ta ce, "ke akan auren wa ki ke magana?."

Islaha ta ce, "Shekaran jiya Baffa ya kira ni, ya ce za a Waura aurena da hamma a yau, dan Wazu ma ya kira ni akan hakan, yana ta shirin tafiya masallaci za a Waura. Shine gabaWaya jikina ya yi sanyi, ko ke na kasa faWawa maganar Waurin auren."

Safeera ta ce, "tabWi! Wai da sai dai na ji an Waura auren ki? Na rantse da Allah sai na yi miki abinda ba ki taSa tunani ba."

"Wallahi ni nauyi maganar ta yi min, sai nake ji gabaWaya bana son a yi aurensa yanzu, bana murna da auren gabaWaya."

"Auren Hamman ne bakya so ko son Hamman ki ka daina?."

"Ina da wanda zan so in ba shi bane? Ina son Hamma sosai, kawai dai aurensa a yanzu ne bana so."

Safeera ta ce, "Yanzu an Waura auren?."

"Ban sani ba wallahi, amma tabbas yau za a Waura sai dai in an fasa."

"to meyaasa za a yi auren yanzu?."

"ina zan sani? Baffa ne ya yanke hukunci."

Safeera ta yi dariyar sha?iyanci ta ce, "ki ce amarya ce da kanta, tunda an sakko daga masallaci na san kin zama matar aure."

Islaha ta ce, "hmm Safeera kenan. Baba ya auri Mamansu Kausar ko?."

"Wallahi fa, an Waura auren."

"Ke kamar bakya ta ya Umma kishi."

"Kishin me zan ta ya ta? Ba fa matar Baba bace."

"Amma Maman kausar aminiyar Umma ce, komai tare suke yi. Dan kawai Umma bata nan sai ta aurar mata mijinta maye gurbinta?. Ni fa haushin ki nake ji akan hakan, sai rawar kai ki ke yi."

Safeera ta yi dariya, dan ta san halin Islaha da kishi, in itace a matsayinta baza ta yi ba. Safeera ta ce, "Wallahi ni ko a jikina, murna nake yi Baba ya samu sabuwar matar da in na tafi aiki ?annena suna makaranta zata kula dashi yadda ya kamata. Kuma dan ba ki san irin kyautatawar da ta dinga yi mana bane, mahaifiyarmu ta ajjiye mu ta bar ?asa, ita kuma ta kamo hannunmu ta ri?e. Ai wallahi ta cancanci Baba ya aure ta, ko Umma tana nan ta cancanci su yi zaman kishi, balle bata nan, kuma ba a san ranar da zata dawo ba."

Islaha ta ce, "Allah ya sanya alkhairi."

Ta amsa da amin kafin ta ce, "bara na kira Sadik na ji in an Waura na ki, yadda zan dawo na tsokane ki son raina" ta faWa tana kashe wayar Islaha ta bi wayar da kallo cikin wani irin yanayi.

Tana idar da Sallah Sahir ya kira ta, ta Wauka cikin faWuwar gaba, amma yadda ta ji maganarsa a sanyaye ya saka ta ce, "Hamma ya dai?."

Ya ce, "kin ji shiru ko? Baba ne ya ce a dakata da Waura auren sai kin dawo. GabaWaya raina a Sace yake a akan hakan."

Ta yi Soyayyiyar ajiyar zuciya, yanayinta ta ya canja zuwa na jin daWi ta ce, "meyasa ya ce haka?."

"Wai gaggawar me ake yi, a jira ki dawo."

"To ai shikenan, Allah ya sa zamu gani."

"Amin. Amma ni ba haka naso ba gaskiya."

"Wata?ila yanzu in aka Waura bazai zama alkhairi ba."

"Haka ne."

Islaha ta ce, "Hamma ya batun Zainab?."

"Bana so na faWa miki ki tayar da hankalin ki, shiyasa na yi shiru."

"Bazan tayar ba, ka faWa min don Allah."

"Ba a ga Zainab ba, duk inda nake tunanin zan ganta ban ganta ba. Har gidan ?an uwanku na gidan na je aka ce bata je ba, har Barr na tambaya ya ce shi ya jima bai ga Zainab ba."

Ta yi shiru bata ce komai ba, ya san ta daman zara damu sosai akan hakan, sai ya tausasa murya ya ce, "amma ki yi ha?uri, kafin na koma zan sake dubawa, in sha Allah rayuwar Zainab zata salwanta ba, Allah zai yi ri?o da hannunta, zai kare ta a duk inda take."

"Allah ya shiga tsakanina da wanda ya zama munafuki a tare dani" ta faWa hawaye yana sakko mata.

Ya tausasa murya cikin rarrashi ya ce, "ki yi ha?uri, in sha Allah zan nemo miki ita."

"Hamma in wani abun ya same ta ni ce sila, Allah bazai yafe min ba."

"Ki yi ha?uri, Allah ya gani ya san taimako ki ke yi, ko dan hakan bazai bari ki wula?anta ba."

Kuka take yi masa sosai yana rarrashinta, sai da ya ji ta Wan nutsu sannan ya ?yale ta. Abin ya haWar mata, ga jin daWin an fasa Waura aure ga tunanin Zainab.

Da?yar ta iya mi?ewa, ta wanke fuskar ta ta fito tana kallon kanta, kallo Waya za ka yiwa idanunta ka san ta yi kuka. Ta Wauki facaemask ta saka, ta saka hijjab ta fita zuwa gidan Rehaan.

Tana shiga falon gabanta ya faWi, dan yana zaune shi da wani bature yana nuna masa abu a file shi kuma yana gani. Tana ?arasa shiga falon Baturen ya tashi da file Win ya fita.

Sai ta ji zuciyarta ta yi nauyi sosai, haka kawai take ji kamar tana jin nauyinsa akan abinda ta dinga yi, ta lumshe ido ta buWe ta kalle sa ta ga kamar bai ganta ba ta ce, "Good day."

Ya Wago ido ya kalle ta, ta yi saurin kawar da kai tana mamakin wannan faWuwar gaban da take yawan ji indai zasu haWa ido.

Ya mi?e tsaye ya harWe a hannu a ?irji yana kallon ta, ya Wan ri?e kai ya ce, "ohhh my god, na gaji sosai."

Ta kalle sa ta ?asan ido, ta turo baki gaba tana hararasa ta ce, "rago kawai, shi komai ya gaji."
Bata faWa yadda zai ji ba, ita kaWai take maganarta. Rehaan ya ji ta, ya yi kamar zai yi magana sai kuma ya Wauke kai ya taSe baki ya Wauki wayarsa zai bar wajan.

Da?yar ta iya buWe baki ta ce, "kana bu?atar wani abu ne?."

Sai ya tsaya ba tare da ya juyo ba, sai kuma ya juyo ya dawo da baya, ya saka hannu aljihu ya Wauko kuWi ya ajjiye a gefen kujera kusa da ita, ya Wan fara tafiya da baya sannan ya ce, "no need, you can go" ya faWa yana bar mata wajan ya hau sama.

Ta bi sa da harara ta ce, "?an rainin hankali, kar ka so Win, da na san haka ne ai da ban fito na zo inda ka ke ba. Dan ka kasance Rehaan yola babu ruwana wallahi, baza ka yi min na ?yale ka ba."

Ta kalli kuWin ta ga riyal Wari biyar biyar da yawa, ta harari kuWin ta ce, "ba dan ina son kuWin ba wallahi bazan Wauka ba, kawai dan amfani dasu ya zama min dole, ko dan na biya su Mama kuWin da suka kawo ni na wuce gida" ta faWa tana Waukar kuWin tana kallonsu.

Ko bata lisssfa ba ta san da yawa, dan gani take kamar sun fi waWancan yawa. Ta yi ajiyar zuciya tana kallon kuWin tana tunanin aikin me take yi masa da yake bata waWannan uban kuWin?.

Sai kuma ta taSe baki, a bayyane ta ce, "ba sata na yi ba, ba kyauta ya bani ba, ba ro?onsa na yi ba, aiki na yi masa kuma ya biya ni, ha??ina ne, kuma halak Wina ya bani" ta faWa tana saka kuWin aljihun rigarta ta fita daga gidan tana takawa a hankali.

After two days...

Nana Haleema.
[7/17, 7:20/ PM] KRBBK: RDB2P63
Nana Haleema.

Suna zaune a falon Maleek suna faWa musu zai yi tafiya shi da matarsa. Islaha tana zaune ta yi shiru bata ce komai ba, sai da ya gama sannan ta Waga kai ta ce, "zan iya faWar wani abu?."

Maryam ta ce, "za ki iya."

Islaha ta ce, "ina so na je Madina na yi kwana biyu, amma ban san ta inda zan fara ba."

Maleek ya kalle ta ya ce, "Is okay, duk lokacin da za ki je sai ku je da Sunaira ki yi ticket Win train ki je."

Islaha ya yi murmushin jin daWi ta ce, "na gode."

Ya kalli Sunaira ya ce, "Ku je da ita station ta siyi ticket duk lokacin da zata tafi." Sunaira ya amsa ya bawa Sunaira kuWin ticket Win. Ita dai Islaha godiya take yi dan ba ?aramin daWi ta ji ba. Basu jima ba suka tafi aka bar gidan a hannunsu.

Daman kwana biyu ba zuwa gidan Rehaan take yi ba, rabon ta da zuwa tun washe garin da ya bata kuWi, daga nan Maleek ya ce mata ya yi tafiya baya nan.

A washe garin ranar ta siyi jaka ta baya, irinta ta ?aramar tafiya, ta saka doguwar riga guda Waya a ciki, ta saka kayan amfani in za ka iya kwana dasu, ta goya jakar ta fito zasu je statiom Win kamar yadda ya faWa.

A hanyar su ta tafiya Islaha ta ce, "Sunaira ina na ne unguwar Khadiyya a Madina, ya zan yi?."

Sunaira ta yi mata typing kamar ko yaushe, Islaha ta dub ta ga ta ce, "in kin sauka ki tari mota ki faWa musu, zasu kai ki ko ina ne. In kuma za ki je masallaci, kawai ki cewa masu mota haram zasu kai ki."

Islaha ta gyaWa kai tana murmushi, a haka suka si yi ticket Sunaira, ta bata da sauran kuWin da zata siyi na dawowa. Sai da Islaha ta shiga train sannan Sunaira ta koma.

Islaha kallon jirgin kawai take yi, dan ticket Win first class aka siya mata, gashi nan kamar jigin sama saboda kyau. Babu jimawa jirgin ya fara gudu dasu a ciki.

Tana zaune da facemask a fuskar ta tana ta kalle kalle, wani abun ta yi video wani abun ta ajjiye wayar. Awa Waya da wani abun suka Wauka suna gudu, kafin ta ji sanarwa sun iso station Win Madina.

Suna fita ta ga inda mutane suke bi, da yawa matafiya ne waWanda suka shigo ?asar, ita dai su take bi har aka fito inda motoci suke, ta samu taxi ta faWi sunan da Umma ta ke, ya faWa mata kuWin da zata biya ta shiga suka tafi. Sai da suka zo sannan ta bashi location Win da Umma ta tura mata, ai kuwa har ?ofar gidan da Umma take ya kai ta.

Islaha ta bi gidan da kallo, gidan babba ne babu laifi, ta fita daga motar ta bashi kuWinsa ta ?arasa. Gate Win bashi da tsayi, sannan lock Win yana saman gate Win kana saka hannu zaka cire. A hankali ta cire, ta taka a nutse ta ?arasa wajan ?ofar tana danna door bell. Ba jimawa aka buWe, ana buWewa suka haWa ido da Umma da take tsaye sanye da ?aramin Hijjab.

Umma ta buWe ido cikin tsananin mamaki ta ce, "Islaha ke ce?."

Islaha ta Waga kai tana murmushi ta ce, "Ni ce Umma."

Umma ta ji wani irin daWi yana mamaye mata zuciyarta, ta rungume Islaha tana ji kamar ?arta Safeera ya gani. Daman kuma duk wanda ba ya ?asar sa in ya ga wanda ya sani sai ya ji kamar ya yi me saboda murna, Umma ta gigice tana jin daWi kamar ta mayar da Islaha ciki.

"Me ki ke yi a nan! Baza ki dawo ciki ba!?." Muryar matar gidan ya ratsa su cikin yaren ta, zuwa lokacin Umma tana fahimtar wani abun a arabic sosai.

Ta saki Islaha tana cewa, "Wannan masifaffiyar mata, Islaha mu je Allah ya sa ta bari ki zauma."

Tare suka shiga falon, ta yi kan Umma kamar zata dake ta tana masifa da arabic. Umma ta bata ha?uri da larabci, ita kuma ta nuna Islaha tana tambayar wacece.

Islaha ta bi matar da kallo, ganin ta yar ?arama da ita bata da jiki, kuma a haife ma ta san Umma ta haife ta, amma ji yadda take yi mata wannan masifa har da ?o?arin duka.

A lokacin bababr ?ar gidan ta zo wajan, Umma ta ce, "Islaha ki yi mata bayani da turanci, ki mata ke ?ata ce, kin zo ki ganni ki koma."

Islaha ta kalli yarinyar ta ce, "Mamana ce, na zo na ganta na koma."

Yarinyar ta taSe baki ta ce, "to ai kin ganta ko? Sai ki koma gida."

Islaha ta haWe rai ta ce, "Ba yanzu ba, ina so mu gaisa kafin na koma."

Yarinyar ta faWawa babarta abinda Islaha ta ce, sai kuwa ta fara zazzaga bala'i da larabci.

Umma ta kalli Islaha ta ce, "ki yi ha?uri, haka suke da wannan tashin hankalin wallahi, gabaWaya ruWa ni suke yi, na rasa ya zan yi."

Islaha ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login