Showing 105001 words to 108000 words out of 221574 words

Chapter 36 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

144

mai yawa da tsaho ai tufke shi zai yi miki wahala."

"In san in ina yanayin nan kaina in ba a haka yake ba damuna yake yi wallahi, hasken ma da ki ka ga na yi shine" ta faWa dan bata so su dinga cewa ta yi haske, kar a ga kamar hutawa take yi, ita kuma ta san wahala take sha.

Nana Haleema.
[7/7, 6:26/ PM] KRBBK: RDB2P44
Nana Haleema.

_Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments Win ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link Win ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode Win baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/y7KtU9yRxrs?si=Q-KB7p8hKxcVfv1L

Safeera ta yi dariya tana kallon Islaha ta ce, "ashe period ki ke yi, to a kan wa ki ka sauke kwandon masifar da ki ka saba?."

Ta Wan yi dariya ta ce, "ni kaWai na dinga ihu a kitchen, har sai dai mai gidan ya zo yana tambayar lafiya."

Safeera ta yi dariya ta ce, "duk abinda period yake sakawa ban yarda da gaske bane sai a kan ki, in aka faWa gani nake ?arya ne, amma a kan ki na yarda. Ya yi spoiling mood Win ki, ya canja ki, ki sake komawa masifaffiya daman kuma itace, ya saka ki haske, ya saka ki ciwo, ki zama lazy, ki zama mai rigima......Kai Hamma zai yi fama, Wannan watan waye ya dinga rarrashin ki to?."

"Dallah can ban sani ba. Kin san me?."

"Sai kin faWa."

"yanzu na gama waya da Hamma, ya yafe min mun koma kamar da. Yana ta jaddda min kar na yi abinda zan bashi kunya, na cigaba da ri?e kaina kamar yadda na saba. Ya ce da zarar ya samu kuWi zai biya su Mama kuWin da suma kashe a kaina, zai siya min ticket na dawo. In ya so sai mu je a bawa wanda na Waukowa kuWin ha?uri."

Safeera ta ce, "Ke hankalin Baffa ya tashi, ga ciwo ga damuwa, Baffa harda hawaye akan ya ji kin bar ?asar."

"Allah sarki Baffa, yanzu zan kira Hamma na ce ya bani shi mu gaisa."

"Yana sonki wallahi, yana jin ki kamar ?ar cikinsa. Kuma ya san duk gwagwarmayar kin yi ta ne saboda shi."

Islaha ta ce, "ya cancanta ne, ri?e ni ya yi kamar ?ar da ya haifa, ya bani tarbiyya da ilimi."

"Haka ne kam. Allah ya sa ki dawo nan da lokaci kaWan. Kin san hankalin ?an da toron guiwa ya tashi, ?an commentse section sun buWe wuta su in ba ke ba zasu daina bibiyar mu."

Islaha ta yi siririyar dariya ta ce, "Yanzu Hamma ya bani labari. Ni ban ma duba ba."

"Hankalin Chairman ya tashi, ya ce daga tafiyar ki zuwa yanzu an rasa followers masu yawa, ina ga in aka kwana biyu?. Don Allah shi dai na yi convencing Win ki ki dawo."

Islaha ta sake yin dariya tana saka hularta ta ce, "na yi kewa sosai."

Safeers ta ce, "ni sai nake ganin me zai hana baza ki ?ir?iri wani program ba, ki samu topic ki dinga magana a kansa don wayar da hankali. In ya so sai ki yi amfani da sunan tv da kuma logon mu, ki yi video ki watsa. Hakan zai saka a cigaba da ganin fusksr ki, kuma baza a yi saurin mantawa dake ba."

Islaha ta ce, "ina naga cikakken lokacin da zan yi?."

"Za ki samu, kamar yanzu da ki ke zaune za ki iya saka camera a gaba ki Wan wayar da hankali koda na minti biyar ne, yadda Allah ya saka miki kalaman hikima akan harshen ki yanzu za ki ga kin faWi abu mai mahimmaci. Don Allah ki yi Islaha, rashin ganin ki zai iya taSa carrier ki, in ana ganin ki akai akai baza a manta dake ba."

Ta sauke nunfashi tana shafa fuskar ta ce, "zan yi shawara da Hamma, in ya bani dama zan yi Safeera."

"To matar Hamma.."

Islaha ta zuba mata ido ta ce, "Safeera meyasa har yanzu ba ki yi magana da Umma ba?."

Ta kalli Islsha ta ga yadda ta mayar da fuska irin babu wasan nan. Safeera ta yi dariya ta ce, "to tsoron ki zan ji? Wannan haWe fuskar na meye?."

"Ki amsa min kawai."

"Islaha Umma zubar damu tayi ta tafi wata ?asar neman kuWi, mahaifinmu ya sake ta saboda hakan, bata saduda ba ta girgije mu ta yi tafiyarta. Neman ta Win me zan yi?."

Islaha ta ce, "Mahaifiyar ki ce fa, ko me ta yi miki bata cancanci ki watsar da ita haka ba. Ta damu da rashin magana dake, da mu ka yi waya sai jaddda min take yi don girman Allah na taimaka na saka ku yi magana. Safeera ki ajjiye wannan ciwon da ki ke ji a ranki, ki yi magana da ita, tana son jin muryar ki, don Allah ki yi magana da ita."

"Islaha zafi nake ji a raina, in na tuna ta zaSi duniya akan mu da mahaifin mu."

"Ke kina da mahaifiyar da zata so ta ji maganar ki, ni kuwa bani da ita. Ban san kowa nawa ba, suna nan ko basa nan ban sani ba. Na tashi cikin marayu, na tashi cikin maraici, ban san kowa na sai Maman da ta raine mu a gidan. Wani lokacin ina ji kamar ina tuna mahaifiyata, amma sai naga kamar a mafarki ne ba gaskiya ba...."

"Nima da da tana nan da ban zo inda nake yanzu ba, da tana tare da ban fuskanci ko wacce matsala ba balle har a Wauke ni......Safeera! Dan ba ki san abinda nake ji bane a duk lokacin da nake jin kewar iyaye, ke ga ki kina tare dasu suna so ki yi magana amma kin ?i."

Ta share hawayen da ya zubo mata ta ce, "Safeera ki manta da Umma ta bar ku, ki yi magana da ita matsayin ki na ?ar cikinta."

Safeera jikinta ya yi sanyi, tausayin Islaha ya mamaye nata zuciya. Ko sati uku bata yi babu mahaifiya ba, amma ita kaWai ta san kewar ta da take ji a ranta. To ina ga Islaha da ta rabu da ta ta tun tana yarinya? Ta rayu tsahon shekaru babu ita, kuma bata san inda take ba, bata da tabbacin akwai wanzuwar mahaifiyar ta ta a duniya, wani lokacin tana jin abin a kamar a mafarki. Tabbas Islaha itace ta san meye kewar iyaye.

Safeera ta ce, "zan yi, zan je wajan Maman Kausar ta bani lambar Umman ta saudia sai na kira ta."

"Ko ke fa, Allah ya cigaba da bamu ikon jure jarabawar rayuwa."

"Amin Bestie. Ina Labiba kuwa?."

"Tunda na zo au Waya na ganta, na fita na ganta ita da wata mata sun hau taxi."

"Lallai an samu duniya. Hanan tana nan itama tana cin karen ta babu babbaka, Mama kullum cikin saka mata albarka take yi."


"ke baki san gasa suke yi akan kawo kuWi ba? In wannan ta kawo dubu goma yau, gobe sai wata ta san hanyar da ta bi ta samo ashirin. Gasa suke yi akan nemo kuWi ba ta hanyar halak ba."

"Uwarsu ce ta Wora su akan hakan ai, kuma ita wai gani take haka kawai mazan suke Waukar kuWi su basu."

Islaha ta taSe baki ta ce, "Su suka sani dai, matsalar su ba tamu ba. Zainab fa? Tunda na tafi kun yi magana da ita kuwa? In na kira ta sai na ji wayar bata zuwa."


"Wallahi ba mu yi magana ba har yanzu, Brr Suraj dai mun haWu mun gaisa."

"Don Allah ko za ki je ki duba min ita?."


"Shikenan, zan je in Allah ya yarda. Ya batun binciken ki akan gidan?."

"Shine na ce ki je ki ganar min ita ai, itace makamina."


"To shikenan, zamu yi magana in Allah ya yarda." Daga haka suka yi sallama suka kashe wayar.

? ? Lokacin da Baba ya dawo suka nuna masa duk abinda Maman Kausar ta yi.

Baba ya girgiza kai ya ce, "Safeera ?awar babar nan ta ku hidimar da take yi ta yi yawa sosai, kar na hana ta ga kama bana yabawa da kulawarta gare ku, amma ta Wora kanta nauyin ku wanda Allah bai Wora mata ba."

"Wallahi nima haka na ce Baba, in na yi magana sai ta ce ai duk an zama Waya."

Baba ya sauke nunfashi ya ce, "Allah ya saka mata da alkhairi."

"Amin Baba."

"Zan yi tafiya kwananan Safeera, ina ta tunanin inda zan bar ku. Gaskiya bazan bari ku zauna wajan Atika ba, hidimar zata yi mata yawa sosai."

Safeera ta ce, "Ka je ka dawo Baba, zamu zauna a wajan nata, in ya so kafin tafiya ta gaba sai a Wauki mataki."

Ya kalli Safeera ya ce, "wanne mataki kenan?."

Safeera ta sunkuyar da kai ta ce, "Baba kamar yadda Gwaggo ta ce, me zai hana baza ka auri Mamansu Kausar Win ba kawai?."

Baba ya girgiza kai tana kallon ta ya ce, "?awar babar ki ce fa Safeera, kina ganin hakan ya dace?."


"Baba ko Unma tana nan dan ka aure ta ai ba damuwa bane, kuma ko da auren tsakanin ka da Umma ba laifi bane balle babu auren. Kawai in dai akwai hali ka aure ta Win Baba, ka ga baka da fargaba in zaka yi tafiya, sannan itama zata dawo ?ar?ashinka, babu batun hidimar ta ta yi yawa."

Baba ya sauke numfashi ya ce, "Shikenan Safeera, zan yi shawara akan hakan."

Ta gyaWa kai ta ce, "To Baba, sai anjima" ta faWa tana tashi ta fita ya bita da kallo yana tunanin mafita akan hakan.


? ?? Hajiya Karima suna kan waya ita da Mama suna tattaunwa akan Islaha, Hajiya Karima ta ce, "Labiba ta ce min yarinya ta waye, har gidajen larabawa take shiga. Gidaje manya manya. Ke kin san yarinyar zata yi farin jini, ga kyau ga gashi."

Mama ta ce, "ai na san za a rina, na san karuwanci kawai zata je tana tafkawa a gidajen larabawa wallahi."

"To ki kwaSi Saheer, babu shi babu ita koda zata dawo. Aure tsakaninsu a dakatar dashi babu batun yinsa. Baza mu zuba ido ya Wauko mana ita a matsayin sirika ba, shine kaWai namiji da ki ka mallaka, in ya kawo ta mun shiga uku."


"Har sai kin faWa ma, ai yadda ta tafi Win nan ta bar zuri'a ta har abada, daman ba so nake yi ba, zan amince ne saboda wani burina. To yanzu bazan amince ya auri ragowar larabawa ba wallahi."

"Hakan shine ya kamata. Kar ki bashi fuskar da zai ce zai aure ta wallahi, ki rufe ido ki ce in ya aure ta sai kin tsine masa. Ke da ina da yarinya mace ma ai da Saheer ya yi mata, matsalar da aka samu bani da ita. Yanzu ba abin na yi hanyar yaran ?awaeye ba, yarinya ta zo ta ?oshi ta zama ?ar iska."

Mama ta ce, "Bar ni dashi kawai Karima. Daman Iskaha ta ga babu Idon Saheer ba sai abinda Allah ya yi ba? Ni fa shiyasa na ji daWi da ba a haWa su gida Waya da Labiba ba, dan Sata min yarinya zata yi wallahi."

"Tsaf zata lalata ta wallahi, kin ga yanzu kowa ya san inda dare ya yi masa. Ke Alhaji Musa ya faWa min wai Maimuna ta ce ita so take ta dawo, na she?e da da dariya na ce waye ya faWa mata borno a gabas take."

Mama ta ce, "Bata san ita da dawowa sai ta biya kuWin nan cif ba, in ba haka ba ta wuce gidan yari."

"Bar ?ar wahala, ta Wauka zuwan ai sau?i ne dashi. Ina zuwa" ta faWa tana kashe wayar.

A lokacin Saheer ya shigo, Mama ta bi sa da kallo ta ce, "yauwa zauna, ina neman ka daman."

Ya zauna ta ce, "kana da labarin abinda budurwar ka take aikatawa a Jeddah?."

Gabansa ya yanke ya faWi, ya kalli Mama ya ce, "na me kenan?."

"Na iskanci mana, Labiba ta faWa min gida gida take bi na larabawa dan ta tara kuWi. Ka ga sai ka cire ta daga ranka, dan wallahi bazan bari ka auri ragowar wasu ba."

Saheer ya yi shiru ?irjinsa yana bugawa sosai ya kasa cewa komai, dan bai san abinda zai cewa Mama ba, ya san duk abinda zai faWa baza ta yarda ba, gwara ya yi shiru zai fi alkhairi.

Mama ta ce, "ka saka a ranka babu kai babu Islaha, wallahi baza ka aure ta ba ka ji na ce wallahi!."

Ya Wago ya kalle ta jin ta rantse, suka haWa ido ra ce, "Gwara tun wuri ka nemi wata, da in na faWa maka na ce ?ar iska ce ai baka yarda, yanzu in ta dawo maka da cikin balarabe ai ka amince. Ka ji da kunnen ka, babu kai babu ita indai ina da rai da numfashi, zan ga da ni da ita waye ya fi mahimmaci a rayuwar ka!." Mama ta mi?e ta shiga Waki ta barsa da bugawar zuciya.........


Nana Haleema.
[7/8, 11:05/ AM] KRBBK: RDB2P45
Nana Haleema.

_Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments Win ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link Win ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode Win baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/y7KtU9yRxrs?si=Q-KB7p8hKxcVfv1L

" " " " " " " "

Islaha tana kashe wayar Saheer ya kira ta, ta yi murmushi sannan ta Wauka ta ce, "yanzu nake shirin sake kiran ka Hamma."

Ya yi murmushi ya ce, "gashi nima na kira ki."

"Muna ta waya da Safeera ne. Ka san me ta ce?."

Saheer ya ce, "sai kin faWa."

"Wai na yi creating content na dinga yi daga nan, saboda kar a manta da fuska ana ta, yan social media suna ta tambayar inda nake. Shine na ce mata Hamma ya faWa min."

Saheer ya ce, "Hakan shawara ce mai kyau, zai saka kowa ya san kina nan kuma zaki dawo in sha Allah."

Islaha ta yi murnushin jin daWi da farin ciki, Hamma yana bata goyan baya a duk wani abu na cigaba rayuwar ta, yana ?ara mata ?arfin guiwa yi ko da bata so. Koda ta sare yana ?arfafa mata guiwa har ta ji zata iya, ko da zata yi sanyi yana sakawa ta ji zata iya.

A sanyaye ya ce, "Shine na ce mata sai na tambaye ka, in ka bar ni sai na yi."

Ya yi ?ar dariya ya ce, "Ki yi Islaha. Ki samu topics masu kyau ki dinga tattaunawa a kai, hakan zai taimakawa aikin ki harda gidan tv ku."

"To Hamma, zan yi tunani in sha Allah."

"Allah ya taimaka."

"Amin Hamma. Na gode da bayan goyan bayan ka, ko yaushe kana ri?o da hannuna ka kaini inda nake son zuwa."

Ya murmusa yana sauke ajiyar zuciya sai ta ce, "ka san me? Na fara tara kuWin nan fa."

"Har nawa ki ka samu?."

"riyal dubu bakwai, in ka yi converting kuWin zuwa naira sun kai miliyan biyu da Wari shida a yanzu."

Saheer ya ce, "a ina ki ka same su? Ko albashin na ki ne?."

"A'a ba albashi bane. Kasan akwai gidan da nake zuwa ina Wan dafa musu tea na dawo, can ba zama nake yi ba, ina dai zuwa na Wan yi na dawp asalin inda nake. Shine....shine matar gidan ta bani kuWin" Ta samu kanta da Soye masa asalin wanda ya bata kuWin.

Ya Wan yi shiru yana nazari, maganar Mama tana sake yi masa yawo a kansa, yana tuna yadda Mama tace tana yawo a gidanjen larabawa, amma bai bari tayi tasiri ba ya ce, "har gida nawa ki ke zuwa?."

Ta ce, "nan ne fa kawai, shima kawai tea nake dafawa na fito. Matar gidan tana da kirki sosai, shiyasa ta yi min kyauta."

Saheer ya Wan kausasa murya ya ce, "Islaha!."

Jin yadda ya kira ta sai ganbanta ya faWi sosai ta ce, "Na'am Hamma."

"Kin san ba son aikin nan nake yi ba ko?."

"Na sani Hamma."

"Na yarda kina zaune ne dan babu yadda zan yi, kuma tun farko ban san da maganar ba, da baza ki je ba."

"na sani Hamma."

Saheer ya ce, "meyasa ki ke zuwa wani gidan aiki bayan inda ki ke? Ke ba kalar yin aiki a gidan mutane bace, ke kalar hutu da kwanciyar hankali ce, sai dai azo a yi miki girki ba dai ke ki yi ba.
Burina na aure ki na killace ki a gidana, fita ma sai naga dama za ki yi saboda kar wani ya ganar min ke. Yanzu magama ake ta bakya ?asar gabaWaya, kin yi nisa dani balle na zama inuwa a gare ki. Me ya kai ki aiki har gida biyu?."

Calmly ta ce, "mai gidan da nake ne ya yi min magana akai, ni kuma da naga ina son tara kuWin immediately shiyasa na amince. Kuma can ba aiki nake yi sosai, akwai cleaners da suke gyara gidan, kawai tea zan dafa da Wan wani abun."

Ya yi shiru bai ce komai ba, jin haka sai jikinta ya yi sanyi sosai a sanyaye ta ce, "ka yi ha?uri."

Ya sauke numfashi ya ce, "dole na yi ha?uri, babu yadda zan yi. Ki cigaba da zama a Islahan da na sani, kar ki canja kin ji?."

Kamar zata yi kuka ta ce, "Hamma ka fara zargina ne?" Ta faWa hawaye yana sakko mata.

Jin ta fara yi masa kuka sai ya tausasa murya ya ce, "Har abada bazan taSa zargin ki ba Islaha, na yarda dake Wari bisa Wari, in ana yarda da mutum dubu bisa dubu ma na yi miki. Ina tsoron zaman ki a wajan da babu kowa na ki, kar wasu su canja miki tunani ki yi wani abun dan ki samu kuWi da gaggawa."

Muryar ta tana rawa ta ce, "ni bani da kowa ma, wacce nake tare da ita ko turanci bata iya ba sai larabci. Wallahi Hamma bazan taSa aikata wani abu mara kyau ba, na san abinda nake yi, kuma na san haramcin hakan."

Ya sanyaya murya ya ce, "Oh matar Hamma, meye na kukan, uhum!."

"Kaine ka ke magana kamar kana zargin zan samo kuWi ta wata hanya daban."

"Don't deflecte my issue, kin san har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login