Showing 93001 words to 96000 words out of 221574 words

Chapter 32 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

132

uwa."

Gwaggo ta ja tsaki ta ce, "ko uwa Waya uba Waya suke ?arewar ?awance, in baban su Waya uwa Waya tunda babu Maimuna zaka iya auren ta, balle wani ?awance, abu indai ba haramun bane shikenan. Yadda take kula da yaranka na tabbata zaka samu kwanciyar hankali a auren ta, mai son naka ai ba abin wasa bane ba."

Baba ya yi murmushi ya ce, "Gwaggo ni gaskiya babu batun aure a gabana balle har na yi tunanin zan iya auren Atika."

Gwaggo ta ce, "ya kamata ka kawo sa kuwa, dan bazan zuba ido kana barin ?an mata su kaWai a gida ba. In aka fahimci baka nan hauro musu fa?. In kuwa da babba idanunsa? ma makami ne babba."

Baba ya girgiza kai dan ya san gaskiya ta faWa, ya ce, "zan san abinda zan yi in sha Allah, komai zai yi daidai Gwaggo."

"Daidaita komai kawai ka auri Atika, ai ba aibu a lamarin."

"Ikon Allah! Gwaggo ita an faWa miki zata iya aure na ne hala?."

"Ka gwada ka gani, zan iya rantse maka akan zata amince. An ce tafi shekara sha biyar tana zawarci, wallahi kana yi mata tayi zata amsa. Ai kai ba irin wanda za a ?i bane, ta san yanayin yadda ka ke tsayawa akan iyalanka ai."

Ya girgiza kai ya ce, "Shikenan gwaggo, zan yi tunani zan kuma yi addu'a."

Gwaggo ta ce, "ko kai fa, haka zaka ce daman. Allah ya sanya mana alkhairi" ta faWa tana mi?ewa shima ya mi?e.

Sai da ya raka ta har waje Wanta ya zo ya Wauke ta a mota ta tafi.

Ya bi motar da kallo yana murmushi, yana tunanin maganar Gwaggo yana ganin kamar ba abu ne da zai yu ba.

*JEEDAH..*

Slowly take tafiya kamar bata so, hannunta ri?e da ledar Nahdi pharmacy ta shiga gidan Maleek ta wuce Wakin da yake nata ta cire hijjab Win jikinta.

Ta buWe ledar ta ciro pad da panadol da pack Win facemask da ta siya. Ta sha panadol Win ta zauna a gefen gado ta dafe kai dan yanayin ta babu daWi as usuall.

Kwana biyu Maleek ya yi tafiya, aikin ya Wan ragu sai gidan Rehaan da take shiga, kuma har lokacin bata taSa ganin mai gidan ba.

Yanzu ma can take niyar zuwa amma bata jin daWin jikinta, a wannan yanayin ba kasafai ta cika son zama cikin jama'a ba, dan yanayinta ko yaushe zai iya canjawa ta fara yiwa mutane faWa. Gashi tana ?asar da ba nigeria ba, kar ta je ta aikata abinda zai zamar mata matsala.

Tana jin kanta cikin kaWaici, sai ta ji tana bu?atar rarrashi ba tare da an yi mata komai ba.

Ta jima a zaune a haka, kafin ta mi?e ta shiga banWaki ta saka pad Win ta fito tana jan numfashi da?yar. Ta ji daWin maganin da ta sha, amma duk da haka tana jin ciwo sosai.

Hijjab Win ta saka aka turo ?ofar aka shigo, Sunaira ta gani suka yi maganar bebayen da suka saba. Islaha ta ce mata zata shiga gidan da take zuwa, daga nan ta jawo ?afa slowly tana takawa a hankali zuwa gidan.

Magriba ta yi lokacin, duhu ya yi amma ko ina haske kamar dare bai yi ba. Tana shiga motar cleaners tana fita, ta bisu da kallo ta ce, "ko meyesa bazai Wauko chef daga wani wajan ba oho, ba dan kuWi nake nema ba da me zai kai ni aiki kamar wata baiwa?."

Sai da ta yi typing lock code Win ?ofar sannan ta tsaya tana jira ?ofar ta yi ?ara sannan ta buWe, ta yi tsaki ta ce, "Aikin banza, gida kamar gidan tuba duk an bi an rufe sa da lambobi."

Sautin lock Win ta ji alamun ta buWe, ta shiga falon yana nan yadda yake kamar kullum babu kowa.

Haka kawai ta ji falon yana bata haushi, ta yi tsaki tana hararar falon ta ce, "aikin banza, kullum baya nan, ni ga ?ar aiki sai dai na yi masa aiki na ajjiye, yana can yana hutawa ina gaban stove zafi yana tafasa ni."

Islaha ta taka a hankali zuwa inda kitchen Win yake. Ta kunna hasken ta ga komai yana inda yake ko cup Win da sha tea babu.

Ta kama ?ugu ta ce, "wai yana cin abinda nake dafawa ma kuwa ko wahalar banza nake yi?." Sai kuma ta sake yin tsaki ta ?arasa ta haWa komai na tea ta Wora akan stove ta kunna.

Ta rasa me zata dafa ranar, duk ranta a Sace yake bata san me ya kamata ta yi ba. Loades fries nw ya zo ranta, hakan ya saka ta Wauko irish potatoes irin na ?asar manya manya, babu wahalar peeling sannan ga auki. Guda uku kacal ta gyara ta yanka yadda ake soya dankalin turawa.

A lokacin ta ji marar ta tana Waurewa, idanunta ya ciko da hawaye, ta fara kuka mai sauti ita kaWai tana yi tana share hawayenta. A haka ta soya ta ajjiye, ta buWe fridge ta Wauko chicken breast ta yanka ?ananu ta saka spices ta zuba a fan ta Wora akan stove Win.

Ta koma gefe tana jan numfashi tana jin yadda take flowing a hankali. A hankali ta ?arasa ta kwashe kazar, ta buWe fridge Win ta Wauko mayonnaise ta zuba a ?aramin bowl, ta zuba ketchup a kai, ta Wauki lemon ta zuba kaWan, ta saka chili powder da maggi ta yi mixing a haWe.

Casrool ta Wauka mara girma sososai, ta zuba dankalin a ?asa sannan ta kawo wannan kaza ta zuba a sama, ta zuba cheese, sannan ta zuba cream Win da ta haWa ta sake zuba cheese. Ta Wauka ta saka a cikin oven, mintina kaWan ta cire ta kalla ta ga loaded fries Win ya yi kyau sosai.

Dafa kitchen island ta yi tana jan numfashi mai ?arfi, bata daina kuka ba har lokacin, dan ita kaWai ta san irin abinda yake ji a jikinta. BuWe murya ta yi tana kuka mai matu?ar sauti dan ta san babu kowa a gidan, tana kiran sunan Hamma da Safeera.

A lokacin Rehaan ya shigo gidan, yana buWe falon ya ji sautin kuka har tsakiyar kansa. Gabansa ya faWi lokaci Waya, ya fara tunanin waye a gidan yake kuka haka?. A hankali ya ajjiye wayarsa akan table ya shiga ciki a hankali ya nufar inda yake jin kukan.

A tsaye ya ganta ta juya baya ta ri?e kitchen island ?am jikinta yana rawa. Kallo Waya ya yi mata ya gane itace housemaid Win, uniform Win jikinta sun tabbatar masa da wacece.

"Are you Okay?."

Rehaan ya furta a tausashe yana kallonta, dan daga ganin yanayinta bata da lafiya.

Islaha ta firgita jin magana a bayanta, kuma ta san babu kowa a gidan sai ita kaWai. Firgtar da ta yi, sai tsantsin tiles da Sawon dankali guda biyu da suke a ?asa, suka ja ta da ?arfi, ta yi gaba zata faWi da fuskar ta, Rehaan ya yi hanzarin ?arasawa ciki, ya taro ta ta faWo ?irjinsa gabaWayanta......

An haWu fad'?
=?%?

Nana Haleema
' [7/6, 9:35/ AM] KRBBK: RDB2P39
Nana haleema.



_Masoyan Ragayar Dutse marubuciyarku ta shiga gasa da littafinta na KIRAN RABO, kuma like da comments Win ku a first five episode shine zai bata nasara. Don Allah ku danna wannan link Win ku je Youtube, ku danna min like sannan ku yi comment akan video. Ku duba episode Win baya, shima ku yi like da comment saboda Allah._ https://youtu.be/POak37bdMTE?si=dU33KLoRcvufRf7S

& &

Kanta yana kwance a kirjinsa, jikinta ya saki gabaWaya, sai ?hamshin turarensa da yake shiga hancinta yana ratsa kanta da zuciyar ta a hankali.

Rehaan sai da ya yi da gaske ya rike ta, yadda ta faWo jikinsa gabaWaya sai da ya kusa faWuwa, dan bai Wauka jikinta zai saki haka ba, sai ya ji ta sakar masa jiki tana kwantar da kanta a ?irjinsa.

Hannunsa Waya yana waist dinta, ya zagaya dashi har cikinta ya rike ta yana kallon gashin kanta da yake ba?i sosai, ga kitson da ta yiwa kanta, irin na fulanin daji guda biyu kacal.

Ya Wago ta yana kallon fuskarta, amma idanunta a rufe yake sai hawaye da yake sauka a hankali, ya Wan zubawa fuskar ta ido na wani lokaci, sai kuma ya Wauke kansa daga kallonta. Daga yanayin uniform Win jikinta ya san itace housemaid Win da Ubaid yace masa ya turo, ya ri?e fuskarta yana Wan jijigawa.

Camly ya ce, "can you hear me? What's wrong with you?."

Islsha tana jinsa amma tana bu?atar kwanciya a halin da take ciki, tana jin muryarsa da ?hamshinsa har cikin zuciyarta, amma kuma ta kasa buWe ido ta ga waye.

Har lokacin yana ri?e da ita sai dai ya raba ta da jikinsa, bai kuma magana yin ba ya ri?o ta a yana sake ri?e hannunta suna takawa a hankali suka fito falon, ya zaunar da ita yana kallon yadda take kuka har lokacin.

Coat Win jikinsa ya cire, ya kwance necktie ya cire, ya rage bottuns Win saman rigar. Ya cire tucked in ya koma kitchen, ya dau?o ruwa mai madaidaicin sanyi ya ?araso ya mi?a mata ya ce, "take it."

A hankali ta fara buWe ido tana kallon abinda ya mi?o mata, bata gani sosai yadda ya kamata, amma tana ganin mutum a tsaye yana mi?a mata ruwa amma baza ta ce waye ba.

Ta karSi ruwan ta sha ta ajjiye, ya bar wajan ya ?arasa ya Wauko panadol ya dawo ya bata guda Waya, dan ya ga alama tana cikin radaWi, yana kula da yadda ta ri?e kanta yasan tana bu?atar pain reliever.

A hankali ta karSa ta sha ta koma ta jingina da kujera, gabaWaya ?hamshin falon ya canja ya koma ?hamshinsa. Gashi ya kunna ac ta fara fita a hankali, sai ?hamshin ya haWe da sanyin ya ba da wani yanayi mai daWi.

A hankali ta fara jin relief ta koma sauke ajiyar zuciya a hankali, ta bu?e ido ta kai kallon ta gare sa, sai ta ga ya dora ?afa kan ?aya yana danna waya hankalinsa kwance.

Sai kuma ta ga ya Wora waya a kunne yana magana cikin turanci, bai jima ba ya sauke wayar.

Islaha gefen fuskarsa take gani, gashinsa ya rufe gefen fuskarsa, ta mi?e zaune sosai gabanta yana faWuwa matu?a. Ta mi?a hannu ta Wauki glass cup Win da ya mi?a mata, ta kai bakinta zata sha kenan Rehaan ya juyo suka haWa ido.


Gabanta ya faWi, glass cup Win hannunta ya faWi ?asa, ruwan da ta sha ya sar?e ta ta fara tari. Islaha kallonsa take yi tana tari kamar yadda yake kallon ta

Sai kuma ya Wauke kansa daga kallon ta ya cigaba da abinda yake yi ita kuma ta sake firgicewa. Da sauri ta mi?e tsaye tunawa da babu Wankwali a kanta balle hijjab Win da ta shigo dashi, da sauri ta koma kitchen ta saka ta fito a hankali tana kallonsa kamar bai san da ita a wajan ba.

Kallonsa take yi ?irjinta yana bugawa, kamar bai san ta fito ba duk da yana jin motsinta kuma ba kallon ta yake yi ba.

Ita dai ta kasa banbance yanayin da take ciki, gizo yake yi mata kamar yadda take yawan ganin fuskarsa a mafarki yana tambayarta bashinsa, ko kuma shi Win ne dai?. Tunda ta zo Jeddah take mafarkin sa, ta san kuma saka abinda ta yi masa a ranta ne ya saka take ganinsa, amma yanzu abin ya fara bata tsoro matu?a, tunda gashi ta fara ganinsa a zahiri.

Gab da zata wuce ya sake juyowa ya kalle ta suka sake haWa ido, yadda ta firgita hijjab Winta ya taWeta ta baya ta zube a ?asa, kuma bata daina kallonsa ba. Sai kuma ta mi?e da sauri ta juya ta fita da sassarafa bata sake waiwayonsa ba.

Shi dai bai motsa daga inda yake ba, shi kansa yana ganin kamar ya san fuskar, kawai bazai tsaya ya tsaurara tunani a kanta ba ne, bashi da wannan lokacin. Sai ya yi tsaki tunawa da maganar Ubaid, ya sake kallon inda ta zauna yana tuna duk abinda Ubaid ya faWa a kanta.

Ya yi ?aramin tsaki ya mi?e yana tuna yanayinta, ya shiga kitchen yana kallon abinda ta haWa komai tsaf sai Sawon dankali guda biyu da yake ?asa.

Ya saka hannu ya Wauke ya saka a dusbin, ya ?araso ya zuba tea yana buWe casrool Win yana kallon abinda yake ciki. Fork ya Wauka ya ci abinda ta yi, sai kuma ya zauna a kan dining Win da yake kitchen Win ya ci sosai, ya sha tea sannan ya mi?e da tea Win a hannunsa ya hau sama.

Islaha a yanayi na ruWani ta koma, ta cire hijjab Winta ta ajjiye tana kallon kanta yana tuna fuskar wanda ta gani. Ta dafe kanta da hannu biyu a bayyane ta ce, "da gaske shine ko kuma...."

Sai kuma ta katse waccen maganar ta ce, "nan fa ba Yola bane, ya aka yi ya zo nan kuma?."

Ta Wan runtse ido jin mararta tana murWawa, ta buWe idon ta ce, "Ya aka yi ya zo nan? Shine wai ko ba shi bane?" Ta faWa da ?arfi jin tunanin yana neman yi mata yawa.

BuWe ?ofar ta ji anyi, ta kalli wanda ya shigo ta ga Maleek ne, ta bisa da kallom mamaki dan ta san baya nan.

Ya ?araso ya ri?e kafaWarta ya ce, "Islaha are you Okay?."

Sai a lokacin ta tuna maganar da ta yi da ?arfi ne ya ji har ya shigo, ita ta manta ma da ?arfi take magana, a ruWe take sosai. Ta Wan matsa baya tana Waukar hular ta saka a kanta, sannan ta Waga kai alamun lafiya lau take.

Ya bita da kallo ya ce, "you look so stress, and why are you shouting?."

Islaha kamar zata kuka ta ce, "i'm not feeling wll."

"Okay, let me take you to the hospital."

"No, i'm feeling better."

"No, let me call my friend, he is a dr."

"No Sir, i'm Okay."

"are you sure?."

Ta Waga kai alamun eh sannan ya ce, "don't stress yourself, ki kwanta ki huta." Ta Waga kai shi kuma ya fita.

A hankali ta zauna tana tunanin wannan lamari, ita ta kasa banbance abinda idonta ya gani dan gani take kamar ba shi Win bane. Ta ya zata ganshi a Jeedah bayan ta san a Yola yake? Shine ko kuma gizo yake yi mata saboda kuWinsa da ta Wauko? Sai ta sauke numfashi, ta jawo wayarta ta shiga lambar Hamma ta ga har lokacin bai yi unblocking Winta ba. Ta rufe ido ta sauke nunfashi a hankali cikin kewar sa mai tsanani, kamar wasa ta ga kiran??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????sayana shigowa.

RuWewa ta yi, ta gigice ?ijrinta yana bugawa ta mi?e tsaye, hannunta yana rawa tana kallon sunan Hamma da yake yawo a kai, murmushi take yi tana zubar da hawaye ganin sunan masoyinta yana kiran ta.

Wayar ta katse bata Wauka ba saboda ruWewa, wani kiran ya sake shigowa, daWi ya mamaye mata zuciya a bayyane ta ce, "Ya sake kirana, ya kuma kira, Hamma yana kira" ta faWa hannunta yana rawa kafin ta Wauka.

Ta saka wayar a speaker ta toshe bakinta da hannunta ta kasa cewa komai, shima daga can Sangaren kasa yi mata magana ya yi shiru yana jin saukar numfashin ta a hankali. Saheer ya murmusa har ta ji sautin murmushin.

Calmly ya ce, "Matar Hamma!."

Sai kawai ta fashe da kuka mai matu?ar sauti, ya sauke numfashi a tausashe ya ce, "na kashe wayata, na sake yin blocking Winki?."

Kai take girgizawa kamar yana ganinta, ta kasa magana sai kukan da ya sar?e ta ya hanata cewa komai.

Saheer ya ce, "Islaha!."

Muryarta tana cracking ta ce, "Hamma!."


"Matar Hamma, ki bar wannan kukan mu yi magana. Kar ya sar?e ki samu attack, ki nutsu mu yi magana."

Ta kasa cewa komai sai ya kashe wayar, sai ta ga video call yana shigowa, ta zauna sosai ta Wauka fuskar hammanta ta bayyana mai cike da annuri.

Kanta a sunkuye yake ta kasa Wagawa ta kalle sa, ya ce, "bakya so ki ganni ko?."

Ta girgiza kai ta ce, "kunyar ka nake ji Hamma, bazan iya haWa ido da kai ba, ina jin nauyin kallon ka."

Ya yi murmuahi ya ce, "Wago ki kalle ni." A

hankali ta Waga kai ta kalle sa suka haWa ido, ya ce, "filter ki ka saka ne?."

Ta girgiza kai alamun bata saka komai ba, kuma bata yi magana ba, ya ce, "fuskar ki ta kumbura kaWan, sannan ta yi ja alamun kin yi kuka sosai. Baki da lafiya?."

Ta Waga kai a hankali ya ce, "me yake damun ki?."

A sanyaye ta ce, "ciwon kai ne."

Ya girgiza kai ya ce, "kin sha magani?." Ta Waga kai tana tuna wanda ya bata magani, tana ganin abin kamar a mafarki ya faru, kamar zata buWe ido ace mafarki ne haka take hango abin a idanunta. A sanyaye ta ce, "na sha, kuma har ya fara dainawa."

"To ki je ki huta kar na dame ki, na san ku dare ya yi ko?."

Ta Waga kai ta ce, "an yi sallar i'sha."

"to ki kwanta, gobe zamu yi magana ?" Ya faWa da sigar tambaya yana kallon ta.

Ta girgiza kai tana shagwaSa ta ce, "Ni dai kar ka kashe."

Saheer murmusa ya ce, "ina so ki huta, gobe in kin samu lokaci ki yi min magana, sai kira ki mu yi hira."

"In ka kashe baza ka kuma kira na ba."

"Zan kira ki mana."

Ta kalli idonsa ta ce, "baza ka sake ?in kula ni ba?."

Duk da ya kula da hasken da ta yi, da ramar da ta yi bai yi mata magana ba ya ce, "bazan sake ba matar Hamma, ki huta kin ji?." Ta Waga kai tana murmushi.

Ya bi jelar kitson ta da kallo ya ce, "da kan ki kika yi kitson?."

Ta kalli jelar kalbar sannan ta ce, "da kaina na yi...." da shagwaSa ta ce, "na sha wahala, hannuna ya dinga ciwo. Na yi awa biyu ina yi."

Ya yi dariya ya ce, "Wannan gashin naki ai yafi ?arfin ki daman, ke daman ba ?wari ba."

Ta yi murmushi ta ce, "To bani da wanda zai yi min."

Ya sake yin dariya kaWan ya ce, "Sai da safe."

Zata amsa kenan aka Wan ?wan?wasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login