Showing 84001 words to 87000 words out of 221574 words

Chapter 29 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

167

?asa a guiwa ba ta shirya ta nufi gidan. Da sallama ta shiga suka amsa suna kallon ta cikin sakin fuska.

Safeera ta ce, "sannu da zuwa Mama Atika." Atika ta murmusa ta zauna ta ce, "Yauwa Safeera, ya gida ya ?annen naki?."

Saferra ta ce, "Lafiya lau. Ina Kausar?."

"Tana gida, ta ce na gaishe ki."

"Ina amsawa."

Atika ta ce, "Mun yi waya da da Umman ku, ta ce ta kira ki baki Wauka ba, shiyasa ta ce nazo na ga lafiya."

Rukayya da ?annenta suka haWa baki suka ce, "Mama Atika don Allah ki kira mana ita."

Atika ta murmusa ta ce, "to bara na gwada, kun san yanayim ?asar da take sai a hankali" ta faWa tana Waukar wayar ta kira wayar Umma amma ba a Wauka ba.

Ta kalle su ta ce, "ba a Wauka ba, amma gobe zan kira muku ita da kaina."

Jikinsu duk ya yi sanyi alamun ba haka aka so ba. Atika ta kalli Safeera ta ce, "Ya aikin naki?." Safeera ta ce, "Alhamdu lillah."

"Amma za ki cigaba da zuwa ko?."

Safeera zata yi magana Baba ya yi sallama ya shigo. Mama Atika ta sauka har ?asa ta gaishe sa, ya amsa ya ce, "yau ke ce a gidan?."

Cikin fara'a ta ce, "Ni ce. Mun yi magana da Maimuna ne ta ce don Allah nazo naga ya yaran suke, shiyasa na fito."

Baba ya gyaWa kai ya ce, "kin kyauta" ya faWa yana shiga Waki.

Atika ta ce, "Safeera kar ki ce zaki ajiiye aikin ki akan wannan abun, ki yi ha?uri ki cigaba da zuwa."

Safeera ta ce, "Mama Atika in na tafi waye zai dinga kula da gidan? Sannan in Baba ya dawo abincinsa fa?. In suka dawo daga makaranta ban dawo ba Baba bai dawo ba ina zasu je?."

Mama Atika ta ce, "ki ji wata magana, ni ba uwa ce a wajen ku ba kenan ko Safeera?." Safeera ta Waga kai ta kalle ta Mama Atika.

Mama Atika ta ce, "kalle ni da kyau, ni ba uwa bace da baza su iya zama a wajena su ci abinci kafin ki dawo ba? Kina tunanin akwai abinda bazan iya yi muku ke da ?annen ki ba?."

"A'a Mama, kar a Wora miki nauyi ne shiyasa."

"Babu batun nauyi, yadda Kausar take ?a a wajena haka kuma ku ke gabaWayan ku. Babu yadda ban yi da babar ku ba amma ta ?i ji tace sai ta tafi, ni daman ku nake ji ba wani abun ba. Mahaifin ku yana yin tafiya wani lokacin, in ya tafi da wa zai bar ku?. Wanna dalilin ya saka na ce tunda ita bata yi wannan tunanin ba ni nayi, duk abinda ya samu kizo ki faWa min, in tafiyar ta kama Baban ku, sai ku taho wajena mu zauna. Danginta ba a garin nan suke ba balle ace ku je can, kinga ni kaWai ku ke da ita."

DaWi ya mamaye zuciyar Safeera, amma bata nuna ba ta ce, "Mama bama so mu takura ki ne, kuma..."

Mama Atika ta daktar da ita ta ce, "Kar ki sake faWar maganar nan, ni mai tsayawa akan lamarin ku ce a ko yaushe. Yanzu akwai abinda ku ke so?."

Safeera ta murmusa cikin jin daWi ta ce, "Babu komai."

"Gobe ki shirya ki tafi aiki, in zaki tafi ki kawo min makullin gidan. Ke Rukayya in kin dawo daga makaranta ki zo ki karSa a wajena." Ta Waga kai alamun to.

Baba da yake jin komai, ya fito da fara'a ya ce, "Atika ba a Wora miki nauyi ba?."

Ta yi dariya ta ce, "babu komai. Auren Saeera za a yi nan da wani lokaci, suna bu?atar uwa a tare dasu, kuma in sha Allah zanyi iya abinda zan iya dan basu kulawar da ta kamata.? Na yiwa Maimuna al?awari, kuma zan cika in sha Allah."

Baba ya Waga kai cikin jin daWi ya ce, "madallah, Allah ya ?ara zumunci." Ta amsa da amin. Baba ya fita cikin jin daWin kalamanta.

Safeera ma ta ji daWi sosai, lokaci Waya ta sake dan sun saba da Atika ?awar Umma ce.

Safeera ta ji daWin karamcinta, hakan ya rage mata nauyin da take ji a ranta. Daman dangin Umman sun ce ko zasu koma Katsina, itace daman bata so kuma ga mafita an samu hakan ya yi mata daWi sosai.

" " " " " " " "

Islaha suna tsaye a gaban dining table yana zuba abincin dinner, sai da ya gama ya fara ci a nutse sannan yankalle su ya ce, "you made this?."

Islaha ta Waga kai alamun itace, ya girgiza kai ya ce, "perfect." Ta yi murmushi tana sunkuyar da kanta shi kuma yana cigaba da cin abincinsa.

Sai da ya kama kaf suka kwashe kayan suka wanke, Islaha ta Wan ci abincin dan kayan ?hamshinsu ba wani daWi suke yi mata sosai ba. Bayan sun kammala ta shiga Waki ta yi wanka ta canja kaya zuwa mofty ta zauna tana tunanin Saheer.

Waya ta Wauko ta buWe sa?on Mama, ta buWe voice note Win ta ji ta ce, "an samu waje ko waya baki yi min ba, ke haka za a yi dake? Haka za a yi dake tun ba a yi cikin ba harza a haihu?."

Kafin ta ba ta amsa kiran ta ya shigo kamar jira suke su ganta online.

Tana Wauka Mama ta fara masifa tana faWin,? "dan wula?anci baza ki iya kirana ki faWa min a inda ku sauka ba, haka za a yi dake kenan ko? Kin je kin fara shan laban kina cin kaji kin manta yadda tsarin yake ko?."

"Mama ina yini."

"Da ban yini ba ai da ban kira ki ba."

"Ki yi ha?uri, aikin ne da yawa shiyasa sai an yi a hankali."

"Wannan ke ta shafa bani ba, kuWi ne in ki ka samu sai an raba an bani nawa, duk abinda zai biyo baya keki ka jiyo."


"Ki yi ha?uri." Mama ta ja tsaki ta kashe wayar.

Islaha bata damu ba ta kira Saherr, ta kasa jurewa sai an kwana biyu kamar yadda tace sannan zata kira sa, hakan ya saka ta kira ko zata Wauka.

Har ta gama ringing bai Wauka ba, ta buWe sa?onsa tana karantawa ?irjinta yana bugawa cikin tsananin kewarsa. A hankalinta danna vn ta ce, "Hammana ka yini lafiya, ya aiki?. Ka yi ha?uri Hamma, na san na yi kuskure, ka bani dama na wanke laifina."

Tana turawa ta ga ya yi blue alamun har ya buWe, ta tsaya tana jiran amsa amma shiru bai ce komai ba kuma ta tabbatar ya ji.

Ta sake yi masa wani ya sake buWewa, daga ?arshe sai ta ga dp ya koma fari saSanin hoton addu'a da yake kai, in ta tura sa?on sai ya yi tick Waya alamun an yi blocking number.

Hankalin Islaha ya tashi, ta gigice ta rasa yadda zata yi. Daga ?arshe ta zauna ta ci kuka son ranta, ta share hawaye ta kwanta tana jan numfashi cikin rashin mafita.

? ? Ball suke bugawa a babban wajen ball Win da aka tanada a gidan Rehaan, Rehaan yana tsaye sanye da complete set Win kayan barcelona, ya tufke gashinsa a tsakiyar kansa.

Yadda suke ball Win da jikinsu da ?arfinsu sai ka Wauka turanwan gaske ne, ko kuma biyansu ake yi.

Lokacin da suka gama Rehaan yana ri?e da ruwa yana sha, suka taho suna hira har suka ?araso tsakiyar compound Win gidan Rehaan.

Duk suka yi masa sallama, ya rage daga shi sai Ubaid da ya cika sa da uban surutu.

Rehaan ya ce, "ina ta so na tambaye ka sai na manta, har fita nayi zan shiga wajen Maleek na dawo. Kana da extra maid? I want it for my chef."

Ubaid ya shafa gemu ya ce, "yes i have it. She's from Nigeria, Yarinyar ta haWu sosai, zaka ji daWin ta."

Rehaan ya kalle sa sai ya ja tsaki bai ce komai baz Ubaid ya ce, "Riyar dubu Waya ta raba ka da ita, zaka mori lokacin ka yadda ka ke so. Kuma ta iya soyayya sosai Rehaan, zata shagwaSa ka. Zan iya ara maka ita na lokaci Waya ta zo ku kwana tare. Wallahi ta yi, ga skin Winta very soft and smooth."

Rehaan ya ja tsaki ya ce, "ka bar su bana so."

Ubaid ya yi dariya ce, "i'm telling you, ?an Nigeria sun fi arab zama too hot, komai so sweet."

Reehan bai kuma ce masa komai ba ya koma ciki zuciyarsa cike da takaici. Allah ya sani baya son wannan Wabi'a, yana kishin ?an ?asar sa sosai, yana so a martaba ?an ?asarsa, amma duk sun gantalar da ?imar ta bi rariya. Cikin takaici ya shiga Waki, ya yi wanka ya shirya ya tafi asibiti.


Islaha ta Wan sake, ta saba da wasu abubuwan sosai. Ta fahimci Maleek yana da kirki sosai, bai taSa ?o?arin yi mata wani abu ba, sai dai a gaisa daga nan ba ya cewa komai zai fita. Damuwar ta bai wuce Hamma ba, ya ?i ya yi unblocing Winta, gabaWaya ta damu, har sim card na ?asar suka je ta yi register amma da kira shi sai ya ?i Wauka, ?arshe ma sai ya kashe wayar.

Ta yi ajiyar zuciya ta fito falon, a nan suka haWu da Maleek zai fita, suka gaisa ya kalle ta ya ce, "Are you able to work as a chef in another house as well, or would that be too much for you?."

Islaha ta Wan yi jim bata amsa ba, sai kuma ya Waga kai alamun zata iya.

Ya girgiza kai ya ce, "The house in the middle close to us, gidan abokina ne. He's looking for someone to cook and make tea for him. If you're willing, you can also work there, he pays well and he's very kind.

Islaha ta ce, "yeah i can."

"Okay. Let's go, I'll show you the house."

Islaha ta koma ciki ta Wauko hijjab ta fito ya fita itama ta bi bayansa. Tunda kuWi take nema, dole ta haWa da gidan tunda ya ce yana biya dakyau.

A wannan lokacin ta ga Labiba ta fito saka shara a babban trash Win da yake wajan, suka haWa ido Labiba ta Wauke kai ta koma ciki itama ta Wauke kanta.

Tunda suka nufi gate Win gidan gabanta ya yanke ya faWi, ta dinga addu'a ranta, bata san dalilin da ya saka take jin faWuwar gaba ba, gashi bata san mai gidan ba balle tace tsoron aikin take yi, haka kawai tana cike da fargaba.

Bayan sun shiga compound Win gidan ya juyo ya kalle ta ya ce, "Shima Wan nigeria ne kamar ki, amma yana kiwon damisa."

Islaha ta Wan buWe ido cikin mamaki, Maleek ya murmusa ya ce, "yeah." Bata tanka ba suka cigaba da tafiya.

Gidan shiru babu sautin komai sai na tsuntsaye kaWan kaWan, sai kallon gidan take yi tana girmama girmansa, duk yadda take ganin kyaun na Maleek sai taga wannan yafi sa komai, ya tsaru sosai, ya sha adon flowers a ko ina.

Suna zuwa wajen babban ?ofar ta ga Maleek ya saka card ya buWe ?ofar falon, ya kalle ta ya ce, "ki shiga, akwai kitchen ki yi abinda ya kamata. Ki yi komai kamar yadda ki ke yi min, na yarda dake shiyasa na zaSe ki. Note, ba ya son milk tea or milk coffee, baya shan madara" ya faWa yana mi?a mata katin, ta karSa ya juya ya barta a wajan.

Gaban Islaha ya faWi, ta taka ta ?arasa cikin falon a hankali ?hamshi yana dukan hancinta.

Falon da duhu sosai, hakan ya saka ta nemi switch ta kunna take haske ya gauraye ko ina. Ta bi falon da kallo ganin yadda ya tsaru, komai a tsaftacce, komai yana mahallinsa.

Laptop ce a ajjiye akan table Win, bayan ita babu komai a wajen. Ta kalli sama ta ga upstairs Win wanda yake sama zai iya gano na ?asa, irin mai balcony Win nan ne saman, na saman in yana tsaye tsaf zaku yi hira.

Islaha ta Waga kai ta fara tafiya dan neman kitchen ta yi abinda zata yi ba kallon falo ba.

?ofar farko da ta buWe ta ga kitchen Win ne, mai mahaukacin girma da tsari, ta kunna haskensa tana sake kallon ko ina cikin mamakin girmansa.

Gashi babu wasu tarkace, gas stove, sai oven da microwive, sai mixer da blander kawai ajjiye a wajan.

Ita dai a tsorace ta ke kallon ko ina, kafin ta ?arasa ta buWe drawer a nan ta ga glass tea pot mai madaidaicin girma, ta Wauka ta ?arasa gaban sink ta Wauraye sannan ta dawo ta Wora akan gas Win.

Hijjab Win ta cire, ta sake Wauka ta zuba ruwa madaidaici ta dawo ta Wora ba tare da ta kunna ba. BuWe buWe take yi amma bata ga komai na kayan tea ba, ta Wan yi tsaki kamar ance ta kalli gefe, a nan ta ga wani carbinet na glass, ta ?arasa ta buWe ta ga da kayan tea kamar hauka. Tea leaves ma sun fi kala talatin. Black, green, red duk akwai.

Ta Wauko normal black, ta Wauko cimmanon stick guda Waya, cardamon Waya, clove guda biyar sai citta.

Ta ?arasa ta zuba a ciki ta sake dawowa, ta Wauki mint powder ta dawo ta zuba a cikin tea Win ta kunna wuta. Tana tsaye ya tafasa, ?amshi ya mamaye ko ina.

Ta Wauko flaks Win da ta gani, ta juye a ciki. Sai bayan ta juye take kallon flaks Win ganin kamar gold aka yi sa saboda kyau da Waukar hankali, gashi Wan ?arami daidai mutum Waya ko biyu.

Sai da ta gama ta tafi tunanin me kuma ya kamata ta dafa. A bayyane ta ce, "ko me zan dafa oho. Ni bana son sabgar mutanen nan, sun cika iyayin tsiya. Allah ya taimake ni can gidan da Sunaira, shiyasa nake jin daWin yin abubuwa tana taimaka min."

Sai ta tuna ance Wan nigeria ne, ta duba ko ina taga akwai komai na amfani, nan take ta Wora mandi rice.

Cikin lokaci kaWan ta gama, ta yi grill kaza ta yi ganishin komai a warmer. Ta wanke kayan ta mayar da komai mazauninsa kitchen ya zama kamar ba ayi komai ba.

A kan dining Win da yake kitchen Win ta ajjiye, ta Wauko plate da komai ta yi serving a wajan, sai da ta tabbatar ta yi komai yadda ya kamata sannan ta saka hijjab Winta ta fito daga gidan.

Tana shiga gidan Maleek Rehaan yana dawowa, ya shiga gidan a gajiye ya kunna haske, coat Win jikinsa ya cire, ya ware gashinsa ya sauka, ya cire takalminsa ya saka room slippers, ya shiga kitchen dan ya Wauki ruwa.

Turus ya yi ganin abinci a ajjiye, ya ta fi tunanin ko Jazy ne yazo, sai kuma ya tuna ai basu yi maganar zuwan sa ba.

Text Win Ubaid ya gani, sai ya buWe yana karantawa, ya ja numfashi yana kallon yadda aka tsara komai cikin tsafta daidai da ra'ayinsa.

?an tsaki ya yi yana Waukar flaks Win ya zuba tea a glass mug Win da ta ajjiye masa. A yadda yake so ya fi so komai a yi masa, da akwai dama a bashi tea Win a baki hakan ya fi masa, ba ya son wahala shi kam ko kaWan.

A hankali ya kai tea Win bakinsa ya sha, sai ya Wan yatsine fuska jin cloves Win ya fito sosai, amma sugar Win ya yi masa yadda yake so, ya haWWiye a hankali yana kallon tea Win kamar mai karantar wani abun a ciki.

Da mug Win a hannunsa ya juya ya fita daga kitchen Win ya hau sama a hankali.

Yana shiga Waki kalaman Ubaid suka faWo masa a rai, sai ya ta ya yana kallon tea Win a bayyane ya ce, "itace ta yi min kenan?." Ya Wan yi tsaki kaWan ya ajjiye cup Win akan mirror yana cire rigar jikinsa.

Sai da ya yi wanka ya shirya, ya kalli tea Win da ya rage a ciki, ya Wan yi tsaki dan sauka da mug Win ma a wajansa babban aiki ne.

Ya Wauke ido ya sauka ya shiga kitchen ya buWe abincin yana kalko jin ?khamshin spices Win sun daki hancinsa. Abincin ko a ido ya yi kyau sosai, a yi garnishing Winsa da parsley da green peper, ko ba a ce ba abincin zai yi daWi. Rehaan ya Wauki spoon Win da aka naWe a tissue, ya warware ya Wan Wibi kaWan ya kai bakinsa yana ci.

Irin abincin ?asar ne dai, ?hamshin da taste Win da komai iri Waya.

Ya taSe baki ya ce, "ta yi order a wani resturant."

A lokacin ya Wauki plate ya yi serving kansa ya zauna yana ci a hankali. Bai ci da yawa ba ya tashi ya fita daga gidan dan akwai inda zai je.

Labiba tana zaune tana waya ita da Mama, Mama ta ce, "Labibatuna a cikin kwanakin da basu wuce takwas ba har kin samo waWannan kuWin? Naira miliyan Waya nake gani fa, Labiba ban taSa ri?e miliyan tawa ta kaina ba sai yanzu, Labibatuna Allah ya ui albrka."

DaWi ya mamaye zuciyar Labiba, ta yi fari da ido kamar tana gabanta, ko yanzu ta tabbatar ta fi ?arfin Hannan ta ce, "Babu yawa fa Mama, zuwa nan da wani satin zan sake turo miki wasu."

Hajiya Kariman ta ce, "Allah ya saka miki albarka Labiba, wannan ke ce farar haihuwa mai son taimakawa iyayen ta. A ina ki ka samu kuWin haka?."

"Kyauta ce kawai, kin san in ka iya aiki kuma kana jin turanci suna yi maka kyauta mai aji. Wannan kawai kyauta na samu, shiyasa na saka aka raka ni aka mayar da kuWin naira na turo muku."

Mama ta ce, "kin kyauta Wiyata, Allah ya cigaba da dafa miki kin ji. Ki cigaba da kyautata musu, ki Wora daga inda ki ka tsaya, kuWi su cigaba da shigo mana babu ?a??autawa."

Ta yi dariya, a lokacin Aisha ta shigo ta zauna a kusa da ita tana kallon ta, Labiba bata daina waya ba ta ce, "Amin Mama. Yanzu kin tabbatar da na fi Hanan amfani?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login