Showing 3001 words to 6000 words out of 221574 words

Chapter 2 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

105

sai yawo?." Ya yi murmushi suka gaisa har Daady. Daddy ya ce, "Ya jikin?."

"Na ji sau?i sosai."

"Allah ya ?ara lafiya, ya kiyaye gaba."

"Amin Daddy."

A lokacin ?annen Jafar suka shigo suka gaisa suka zauna Daddy kuma ya fita.

Mummy ta ce, "gashi ka zo Jafar yana Uk."

"Wajen Mummy nazo ba wajensa ba."

Ta yi dariya ta ce, "Na gode sosai Rehaan. Ikram kawo masa abinci ya ci."

Bai musa akan kar a kawo ba, daman bai ci komai a wajen Mamy ba, Mummy kuma kamar Mamy take a wajensa.

Ikram ta mi?e ta ciko masa tray da kayan abinci ta kawo masa. Da kanta ta yi serving Winsa ta mi?a masa ya karSa ya ce, "Thank you."

Mummy ta ce, "Jafar ya ce min zaka tafi Jeddah."

Ya Waga kai ya ce, "ina da contract, zan je in gama sai na dawo."

"Allah ya taimaka Rehaan, Allah ya cigaba da kare ka."

"Amin Mummy."

"Riyya ta saka mana kuWi ta ce na shopping ne, mun gode Rehaan, Allah ya albarkaci rayuwarka."

"Amin" ya amsa softly yana shan ruwa.

Sama sama suke hira da Mummy da Ikram, har ya gama ci, ya Wan zauna kaWan sai ya mi?e ya ce, "Mummy zan tafi."

Mummy ta ce, "To Rehaan, a gaishe da Mamy." Ya amsa suka fita shi da Ikram suna hira.

Har mota ta raka shi, tana ri?e da hannunsa ta ?i saki kamar zai gudu. Ya Wan kalle ta ya ce, "Ikram, ya school?."

Ta yi murmushi ta ce, "Alhamdu lillah."

"Allah ya taimaka. Ki koma gida, zan tafi."

Cikin shagwaSa ta ce, "Ni bana so ka tafi, zan zo mu tafi Jedda."

Ya Wan murmusa ya ce, "sai kin zo Ikram" ya faWa yana sakin hannunta. Har zai shiga mota Ikram ta ce, "Hamma Ray."

Ya juyo yana kallon ta kamar yadda take kallonsa, sai ?ifta idanu take yi tana kallonsa ta ce, "I love you."

Ya yi murmushi yana Waga kai bai ce komai ba. Duk da ya saba da faWar i love you ga ?annensa da iyayen sa, but Ikram ya ga alamun ba irin love Win su Riyya take so ba, tana daban yake daga yanayin yadda take faWa zaka san nata is different, shi kuma baya son causing wani abun shiyasa bai ce komai ba.

Cikin shagwaSa ta ce, "you can't say you love me too?."

"i love you, shikenan?."

DaWi ya mamaye mata zuciya, ta Waga masa kai tana jin daWi, sai ta ji babu wanda ya iya furta Ikram da kuma kalmar i love you. Rehaan ya shiga mota tana Waga masa hannu suka fita daga gidan. Ta yi ajiyar zuciya tana jin ?hamshin turarensa yana mamaye ta kayan jikinta. Zama in ya yi a waje sai ka san ya zauna, balle ita da ta yi hugging Winsa.

Ta yi murmushi tana sha?ar ?hamshisa, tana jin ?aunarsa tana sake shiga zuciyarta, ?auna ba irin ta Yaya da ?anwa ba, ?auna ta masoya wanda suke burin aure...

Da alama an samo zaSin Mamy>?-?>?#?

Nana Haleema
09030398006.
[6/15, 12:45/ PM] KRBBK: RDB02P02
Arewapen@nanahaleema11

Tunda suka fizgeta suke tsula gudu akan titi, Islaha kawai jinta ta yi a cikin motar, bata san ta ya aka yi hakan ta kasance ba. Ta kalle su ganinsu su biyu ne kawai a ciki, sai mai tu?a motar na uku, kana kallonsu ka san mutane ne ?arfafa wanda suka yi kama da bouncers.

Islaha ta buWe baki zata yi magana Waya daga cikinsu ya Wora hannunsa akan lips Winsa, ya buWe idanu ya ce, "shii! Kar ki ce komai."

Islaha bata ji kashedin da suka yi mata ba, duk da tana cikin tsoro haka ta daure ta ce, "kamar ya kar na ce komai? Ina za ku kaini, su waye ku?."

?aya ya kalle sa ya yi masa alama da kansa, kafin ta yi zato an saka mata ba?ar hula, an kulle mata fuska.

Islaha ta kurma ihuu tana fizge-fizge, duk da sun Waure mata iya hannu, amma sai fizge-fizge take yi ta ce, "su waye ku? Ina zaku kaini, me na yi muku ku ka Wauko ni?."

Suka yi shiru babu wanda yace mata komai a motar, dan van Win a kulle take, babu wanda zai ji abinda take faWa. Ga glass Win ba?i, babu wanda zai hango ta duk haukan da zata yi. Islaaha ta fara dukan glass Win motar da hannunta tana faWin, "A taimake ni, an sace ni! Wayyo Allah, ku taimaka min!"

Ta faWa tana ihuu sosai tana cigaba da dukan glass Win.

?aya daga cikinsu ya fusata, cikin tsawa ya ce, "ke! In ba ki yi mana shiru ba sai na dalla miki mari!."

Islaha bata yi shiru ba sai ihu take yi kamar ba warning aka yi mata ba.

?ayan ma ya kalle ta ya ce, "baza ki yi shiru ba?."

Bata daina ba sai ma sake ?ara ?arfin ihun da take yi. Wanda ya fara magana a farko?
ya ce, "zan cilla ta window yarinyar nan wallahi."

"A'a, kar ka yi haka. Yi ha?uri mu ?arasa."

Ya yi ?aramin tsaki suka cigaba da tafiya tana fizge-fizge tana kuka.

Ita dai ta ji an tsaya, sai sautin buWe mota da ta ji, kafin ta ji an yi mata Waukar kaza. Wannan ya ri?e kafaWarta Waya, Waya ma ya ri?e kafaWarta Waya, ana tafiya da ita bata san inda zasu je ba, dan an rufe mata fuska.

Ajjiye ta ta ji an yi, sannan suka kunce mata hannunta, kafin su cire mata abin suka rufe mata fuskar ta cire da kanta, a lokacin har sun fita sun kulle ?ofar. Islaha sai da ta Wan jira, idanunta ya dawo daidai saboda duhu, ta bi inda suka ajjiye ta da kallo ?irjinta yana bugawa da ?arfi.

Babban katafaren luxury parlor ne mai kyau da haske, duk inda ake neman haWaWWen falo da kyau da girma yake ya kai. Ya haWu sosai, ga sanyi da ?hamshi da yake yi kamar gidan amarya.

Islaha ganin wannan falo sai ta kuma firgita, ta nufi ?ofar a guje tana jijjiga ?ofar amma kamar babu kowa, ta ?arasa wajan window ta janye lalube, ta buWe glass Win window tana faWin, "ku su waye? Ina ne nan ku ka kawo ni? Don Allah ku zo ku barni na tafi. Babana bashi da lafiya, yana asibiti, don Allah ku buWe ni!."

Tistt kamar babu kowa, dan ko mota Waya babu a ajjiye a wajan, kamar ba yanzu aka ajjiye ba. Ta sake buWe murya ta ce, "Kuna ina!." Nan ma shiru babu motsin komai.

Islaha ta dafe kai cikin rashin sanin abinda zata yi, ta sake kallon falon tana tunanin ina ne nan kuma? Ina aka kawo ta, waye ya ?wamuso ta aka ajjiye ta a nan?.

Kamar an tuna mata, sai ta fara duba aljihun jikinta, a nan ta jiyo wayarta tana nan. Hannu yana rawa ta Wauko ta shiga kiran wayar Sadik amma network error. Ta saka wayar a flightmode ta cire, amma abinda service Win yake nuna mata no service.

Islaha ta dafe kai ta zube a wajan ta rasa abinda zata yi, kuka take yi dan bata san abinda zata yi ba in ba kukan ba. Sai ta kuma zabura ta mi?e, ta sake komawa window tana ihuuu tana hawaye, amma babu wanda ta gani balle aji maganarta.

Ta koma ta zauna ta rasa tunanim me zata yi, hankalinta ya tashi ta rasa abinda yake yi mata daWi. Falon shiru babu motsin komai, sai sautin ac kaWan, sai ?hamshi da yake yi a hankali.

Ta kalli agogo ta ga ?arfe tara na dare, ta sake duba waya ta ga no service, ta cillar da wayar ta sake fashewa da kuka mai sauti.

Kuka ta yi mai isar ta lokaci Waya kanta ya rike, ya yi mata nauyi, tana ji kamar zai cire saboda nauyin da take ji ya yi mata.

Ta sake mi?ewa ta koma wajan window, murya a dashe ta ce, "babu kowa ne! Don Allah ku buWe min, Babana bashi da lafiya, ina so in je in gan shi, ku taimaka min!."

Nan ma shiru babu alamun kowa, sai haske a compound Win gidan kamar hasken rana, da wata ?aramar mage da take yawo a wajan.

Takaici ya mamaye mata zuciya ta buga kanta a jikin bango tana kuka, tana ji kamar ta samu wu?a ta dinga cakawa kanta har sai ta mutu, ga waya a hannunta amma ta zama babu amfani, gata a gidan da babu kowa amma bazata iya fita ba.

A wajan ta zame ta kwanta tana kukan rashin mafita, sanyin falon ya fara yi mata yawa, ta cure a waje Waya ta haWe kanta da guiwa tana kuka mai tsuma zuciya. Tun tana kukan cikin daWin rai har ta gaza, ta koma sauke numfashi, tana sake curewa waje Waya saboda sanyin da yake ratsa ko ina na jikinta.

Ta mi?e ta sake kallon window ta ga gidan shiru babu motsin kowa. Gabanta ya faWi, ta tafi tunanin yanzu ita kaWai ce a gidan mai uban girma?. Hawaye ya sakko mata, ta koma ta zauna ta rasa abinda yake yi ma daWi.

Bata san adadin lokacin da ta Wauka a wajan ba, duk da sanyin da take ji haka take zaune a wajan, tsoro da tashin hankali ya cika mata zuciya, tunanin waWanda suka sace ta ya hanata sukuni. Bata san lokacin da bacci ya Wauke ta ba.

? ? ? ? ? ? Washe gari.

"Yauwa Hanan, don Allah turo min Islaha in kin shiga gida."

Hanan ta kalli Sadik ta ce, "Islaha bata kwana a gidan nan ba."

Ya kalle ta da mamaki ya ce, "kamar ya bata kwana a gidan ba?."

Hanan ta ce, "eh, jiya kwata-kwata bata dawo gidan nan ba, ni na yi tunanin ma a asibiti ta kwana."

Sadik ya zuba mata ido yana kallon ta, kafin ya janye idanunsa ya ce, "ni ban gane ba, kina nufin bata dawo gida ba gabaWaya?."

Hanan ta ce, "na faWa maka na yi tunanin tana asibiti tare da Mama."

Sadik ya ce, "wata?ila tana can Win, na kira wayar ta bata shiga kwata-kwata. Bara na je na duba."

Zai kunna motar kenan sai ya ji Hannan ta ce, "to ai ga Maman ma."

Ya dakata yana kallon Mama da ta sauka daga napep,? ya tsaya yana jira ta ?araso ya ji ko Islahan tana can. Mama tana zuwa wajen ta ce," Sadik ka ganni ko? Na dawo gida na Wan kimtsa sai in koma, na bar Sa'ida a can. Ya batun kuWin aikin, An samu kuwa?. Nima yanzu zan Wan tattaro wani abun sai a haWa dashi."

Sadik ya ce, "ana kan haWawa Mama. Islaha tana can ne?."

Mama ta ce, "Islaha bata je ba, na yi tunanin tare za ku tafi da ita."

Hanan ta ce, "ba a asibitin ta kwana ba?."

Mama ta ce, "tun jiya da daddare da ta bar asibiti bata koma ba har na fito."

Hanan ta ce, "to wallahi ba a gida ta kwana ba, dan kwata-kwata Islaha bata dawo gidan nan ba."

Mama ta kalli Hanan ta ce, "to wajan ?awarta fa? Wata?ila ai tana can ko?."

Jin hakan sai Sadik ya Waga kai yana ajiyar zuciya ya ce, "eh gaskiya ne, bara na aika gidansu Safeeran."

Mama bata ce komai ba ta shiga ciki shi kuma ya ?arasa ?ofar gidansu Safeera Hanan ta bi bayan sa.

Kafin Hanan ta ?araso Safeera ta fito, ganinsa sai ta yi murmushi ta ce, "Hamma Sadik barka da zuwa."


Ya ce, "Barka dai Safeera. Ya gida?."

"Lafiya lau, ya mai jiki?."

"Da sau?i. Ina ?awar taki?."

"Yanzu zan tambaye ka na ce tana ina, na ga ban gan ku tare ba."

Sadik gabansa ya faWi ya ce, "kina so ki ce ba tare ku ka kwana ba?."

Safeera ta girgiza kai ta ce, "ni rabona da ita tun a wajan aiki, da ta tashi ta ce min ta wuce asibiti. Na kira wayar ta jiya wajan tara na dare amma wayar bata shiga ko kaWan."

Sadik ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!."

Safeera ta firgita ta ce, "me ya faru? Ina Islahan take?."

Hanan ta ce, "Islaha bata kwana a gida ba, hasalima ba a san inda take ba."

Safeera ta zaro ido waje ta ce, "kamar ya ba a ganta ba, kamar ya ba a san inda take ba? Ku yi min bayani."

Sadik ya ce, "abinda ki ka ji shine gaskiya, bamu san inda Islaha take ba. Dalilin zuwan mu nan mun yi tunanin kuna tare."

"Innalillahi! To ina ta je? Ko tana orphanage?."

Sadik ya kalle ta ya ce, "tana zuwa can ta kwana ne?."

"Gaskiya tunda ta bar gidan bata taSa kwana ba. Na shiga uku, ina Islaha ta tafi?. Bara na kira Zainab ?anwarta ta gidan na ji ko suna tare" ta faWa hannunta yana rawa ta kira Zainab ta saka a speaker.

Daga can Sangaren Zainab ta Wauka ta ce, "Adda Safeera ina kwana?."

Safeera cikin rashin nutsuwa ta ce, "lafiya. Zainab kuna tare da Islaha ne?."

Zainab ta ce, "A'a, ina ta nemanta nima, ko a waya na kasa samunta."

Safeera ta ce, "Na gode" ta faWa tana kashe wayar.

Safeera ta kalli Sadik ta ce, "ina Islaha take? A ina ta kwana?" Ta faWa hawaye yana sakkowa akan fuskarta.

Sadik ya ce, "kwantar da hankalin ki Safeera, zamu ganta in sha Allah."

Safeera ta fashe da kuka ta ce, "Islaha bata kwana a wani wajen sai a Hamma Sadik, bata zuwa ko ina. A ina ta zauna haka, Ina ta je?."

Ya yi ajiyar zuciya bai ce komai ba, dan abin ya Waure masa kai, ya rasa inda Islaha ta shiga, duk inda ake tunanin taje bata can. A lokacin Saleem ya ?araso wajan yana kallonsu.

Ganin yanayin da suke ciki ya saka ya ya ce, "Sadik lafiya na gan ku haka?."

Sadik ya ce, "Islaha ce ba a gani ba, tun dare jiya ba a sake samunta a waya ba. Kuma duk inda muke tunanin zata je ta kwana bata nan."

Saleem ya zaro ido ya ce, "ban gane ba, wacce Islaha kenan?."

Safeera ta ce, "Islahata, Islahata ce ba a gani ba. Ina ta shiga?" Ta faWa cikin kuka mai tsanani tana kallonsa.

Saleem ya ce, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Ba a san inda take ba, kuma bata faWawa wani zata je wani waje ba?."

Sadik ya ce, "da zata je zata faWa min, tunda yanzu ko yaushe muna tare."

Kira ya shigo wayar Sadik, ya duba ya ga Saheer ne, ya kalle su ya ce, "Ga Saheer yana waya, na tabbata ya neme ta bai same ta bane shiyasa ya kira ni."

Saheer ya Wauka ya saka a speaker, Saheer ya ce, "Sadik kuna tare da Islaha ne? Tun jiya nake kiranta bata shiga kwata-kwata. In kuna kusa haWa ni da ita don Allah."

Sadik ya sauke numfashi ya ce, "Ba ma tare, amma in mun haWu zan faWa mata sai ta kira ka."

"Yauwa kar ka manta don Allah. In ka je asibitin ka Wauko min hoton Baffa ka turo min. Zuwa jibi zan dawo in sha Allah."

Sadik ya ce, "to, ina zuwa" ya faWa yana kashe wayar.

Sadik ya kalle su ya ce, "tabbacin wani abun ne ya samu Islaha, dan da akwai inda zata je da zata faWawa Saheer ko Safeera."

Saleem ya ri?e haSa cikin tashin hankali ya ce, "abu kamar wasa, Islahan ce ba a gani ba?."
Safeera dai kuka take yi kamar ranta zai fita.

Sadik ya ce, "ba tsayawa zmau yi a nan ba, mu je mu bincika ko zamu same ta a wani waje, in ta kama mu bada cigiya."

Saleem ya ce, "gaskiya ne kam, mu je mu duba."

Safeera ta ce, "nima zan je."

Saleem ya ce, "ki koma gida, duk abinda ake ciki zan faWa miki."

"A'a, ina so in je, don Allah mu tafi tare."

Suka nufi motar Sadik, Saleem ya bar tasa a wajan suka shiga suka tafi, Hanan ta shiga gida.

Hanan ta shiga ta faWawa Mama abinda yake faruwa. Mama ta ce, "ban gane ba a ga Islaha ba, ina ta je?."

Hanan ta ce, "wallahi ba a sani ba. Duk inda ake tunanin zata je bata nan."

"Ikon Allah, har gidan marayun bata can? Akwai yayyenta da suka yi aure fa, duk zata iya zuwa gidansu."

"An kira iya wanda aka sani, amma bata nan."

Mama ta Wan yi shiru ta ce, "to ina yarinyar ta je? Gashi dai bata kwana a waje balle na ce harka ce ta yi kyau, duk tsiya da iskancin sai ta dawo. Gaskiya akwai alamar tambaya a lamarin nan, akwai abinda ya faru."

Hanan ta Wan yi shiru, duk da basa shiri da islaha amma ta ji babu daWi akace ba a ganta ba.

? ?? Su Saleem asibitin suka je, suka ?arasa wajan ma'aikata suka yi musu bayani abinda ya faru, suka nemi ganin cctv amma suka hana suka ce sai an zo da hukuma. Dole haka Sadik ya koma ya kai report wajan hukuma mafi kusa, aka basu Wan sanda Waya suka taho sannan suka amince aka shiga camera room Win.

?aki ne babba, Waki ne mai Wauke da tv guda biyar, ko wacce da inda take haskawa. ?akin kamar Wakin camera turawa, komai ana gani a tv.

Wanda yake aiki a wajan ya ce, "ina ku ke sm gani?."

Sadik ya ce, "Jiya da daddare, misalin ?arfe takwas na dare. Wajan asibitin nan mu ke so."

Bai musa ba ya danna ya dawo da lokacin, suka fara ganin abinda yake faruwa. Sai ga fitowar Islaha daga asibitin ta mi?e hanya tana tafiya.

?an sandan ya ce, "camera ta gaba."

Ya saka ta gaba inda ta Wan tsaya cikin tsoro kafin ta cigaba da tafiya. Tana shiga wajan duhun ya kalle su ya ce, "daga iya nan cameras Win mu suka daina aiki."

Sadik ya ce, "wayyo Allah, don Allah babu wata ma'aikata ko bank a nan kusa da zasu iya Waukar mana abinda faru?."

Ya girgiza kai ya ce, "gaskiya babu. Asibitin nan ne kawai a wajen nan."

Kowa ya yi shiru cikin tunani, basu da yadda suka iya dole suka fito daga Wakin. Suna fitowa wayar Saleem ta yi ?ara, ya duba ya ga Muslim ne sai ya Wauka.

Muslim ya ce, "Saleem ba ka shigo bane? Chairman yana ta faWa kai da Islaha ba ku zo ba."

Saleem a raunane ya ce, "Muslim wallahi Islaha ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login