Showing 153001 words to 156000 words out of 221574 words

Chapter 52 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

124

haka ta kwanta ba dan tana jin baccin ba.

? ? Mama kuwa tana kashe wayar ta kira Labiba, Labiba tana zaune ita da Aysha, ta ga kiran Mama. Ta Wan lumshe ido ta ce, "Mama ce."

Aysha ta ce, "Allah ya sa ba yarinyar nan ce ta faWawa Mama abinda ya faru ba."

Labiba ta girgiza kai ta ce, "Islaha baza ta faWa mata ba, sai dai in wani abun ne."

Ta Wauki wayar ta saka a kunne ta ce, "Mama ina yini."

Mama ta ce, "lafiya. Ya na ji maganar ki kamar mara lafiya?."

Labiba ta ce, "mura nake fama da ita."

Mama ta ce, "Na ji maganar wai za ki dawo gida, akan me?."

Labiba da mamaki ta ce, "zan dawo gida kuma? In ji wa?."

Mama ta ce, "ban gane in ji wa ba, ba yanzu Ale Musa ya bar wajan ki ba?."

Labiba ta ce, "ni bai zo inda nake ba, rabon da na gan sa tun ranar ya zo ya karSi kuWin nan."

Mama ta ce, "Yanzu muka gama waya dashi fa, ya ce min har riyar dubu takwas ki ka bashi, wai kin gama biyan kamfani kuWin da suka kashe miki."

Labiba ta ce, "Kuma ni ya ce miki?."

"to wacece ?ata in ba ke ba?."

"Ki ka sani ko Islaha yake nufi?."

Mama ta yi Wif tunawa da hakan da Islaha, dan ko kaWan bata yi tunanin ta ba. Labiba ta ce, "Itace ma, ko tantama bana yi Islaha ce."

Mama ta ce, "Islaha! A ina zata samu kuWi kamar wannan? Ko kin haWa ta da mai gidan naki ne?."

"aa Mama, ni bai sake yi min maganar ta ba ma, dan a cikin kwanakin nan ma baya nan ya yi tafiya, bai jimawa da dawowa ba."

Mama ta ce, "taSWijam! A ina yarinyar nan ta samu kuWi irin wanann? Kin ji yadda yake faWa min kuWin da ta samu?."

Labiba ta ce, "Mama in ta so babu abinda bazata samu a nan ba. Nima dan kina yi min addu'a, da yanzu na fi haka."


"Lallai yarinyar nan tantiriya ce, ki ce yawon ta zubar Winta kawai take yi."

Labiba bata ce komai ba, Mama ta ce, "Na yi mamaki wallahi."

Labiba ta ce, "Mama kaina ciwo yake, sai anjima" ta faWa tana kashe wayar.

Nana Haleema.
[7/20, 10:26/ AM] KRBBK: RDB2P68
Nana Haleema.

Bayan Labiba ta kashe wayar Aysha ta kalli Labiba ta ce, "Lafiya dai?."

Labiba ta ce, "yarinyar nan da muka haWu ranar nan, wacce ta raka ni asibiti. Wai itace zata koma nigeria, har ta gama biyan kuWin da aka kawo ta."

Aysha ta buWe ido ta ce, "a cikin wata biyu har ta biya kuWin shekara guda?."

Ta Waga kai Aysha ta ce, "lallai yarinyar tantiriya ce, ki ce har ta fi mu iya harka."

Labiba ta ce, "ni ba wannan ba. Aysha tsoro nake ji, kar na sake yin ciki."

Aysha ta ce, "me zai kai ki sake yin ciki kuma? Wancan Win ma kuskure aka samu, amma yanzu ai na san baza ki sake bari ki yi ciki ba."

Labiba ta ce, "ta ya kenan? Mutumin nan ba ya barina na huta, ni wallahi gabaWaya na fara gajiya."

Aysha ta ce, "kin gaji da kuWin?."

Ta Wago ido ta kalle ta ta ce, "Ba haka bane, kawai ban ji daWi da na yi ciki ya zube ba."

"Au so ki ka yi ki haife sa?."

"A'a."

"To ai murna za ki yi da ya fita da kansa, ba ke ki ka zubar dashi ba ai."

Labiba ta yi shiru bata ce komai ba. Aysha ta ce, "kin ga."

Ta faWa tana nuna mata wasu pills a hannunta. Labiba ta kalle ta ta ce, "na meye?."

"Hana Waukar ciki, babu ruwan ki da fargabar za ki sake yin ciki nan gaba."

Labiba ta zubawa maganin ido sannan ta ce, "ni bazan sha magani ba."

Aysha ta ce, "meyasa baza ki sha ba? Kina so ki dinga Waukar ciki ne?."

"Bana so, amma bazan iya shan maganin tsarin iyali ba. Kar na lalata mahaifata tun ban yi aure ba."

Sai ta bawa Aysha dariya, ta yi dariya son ranta sannan ta ajjiye mata maganin ta ce, "yadda ki ka gani, gashi nan in kin ga za ki sha daidai ne, in baza ki sha ba ma duk Waya." Ta mi?e ta fita daga Wakin ta bar Labiba cikin tunani.

? ?? Washe gari Maleek da matarsa suka dawo, bayan sun huta suna zaune, su Islaha gama gabatar musu da abinci. Bayan sun kammala Islaha ta zauna ta ce, "ina da maganar da zan yi."

Maleek ya ce, "ina jin ki."

Ta sauke numfashi ta ce, "ina so zan bar aikin nan, zan koma nigeria."

Maryam ta ce, "Meyasa za ki koma?."

Islaha ta ce, "ina da wani abu da zan je na yi a can, zamana a nan ya ?are."

Maleek ya ce, "Kin tabbatar babu abinda aka yi miki?."

Ta Waga kai alamun eh. Maleek ya ce, "yaushe za ki tafi?."


"Cikin satin nan."

Ya Waga kai ya ce, "shikenan, in za ki tafi ki faWa min zan nemar miki ticket."

Ta yi murmushi tare da godiya ta tashi ta koma Waki. Duk sai ta ke jin babu daWi a ranta, amma komawar gidan ya fi mata alkhairi akan zaman.

Da yamma ta je Mall ta Wan yiwa mutane masu mahimmaci a gare ta tsaraba madaidaiciya ba mai yawa ba, tana ta shirin tafiya gida a hankali har lokacin babu wanda ta faWawa.

Bayan ta dawo tana shirya kayan Mama ta kira ta, ta Wauka kafin ta yi magana Mama ta ce, "har kin samu dama da saken da za ki biya kuWi gabaWaya baki faWa min ba ko?."

Islaha maimakon ta bata amsa sai ta ce, "Ina yini Mama?."

"ai da ban yini ba da ba ki ji mi ba. Waye ya ce ki ce za ki dawo gida ba tare da na sani ba?."

"Mama na gama abinda ya kawo ni, dawowa gidan...."

"Me ki ka gama da ya kai ki? Me ki ka gama da ya kai ki ?asar?. Yawon watsewar ki ka gama?."

"Mama ni bana yawon watsewa, waWanda suke yi dai suna yi, amma ni babu."

"Kan uba! Ni ki ke faWawa wannan maganar?."

Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, dan ranta a Sace yake sosai.

Mama ta ce, "in ba wayon banzan ba a ki ka samu waWannan kuWaWen masu yawa? Ale Musa ya faWa min duk abinda yake faruwa, ya faWa min duk abinda ki ka bashi da abinda ki ka ce masa."

"Ni gida zan dawo."

"to ki nemi wani gidan, gidana ba gidan ubanki bane balle ki ce za ki dawo ki zauna. Ki san inda za li samu ki zauna, amma ba dai zama a gidana ba wallahi."

Islaha tana sane ta kashe wayar, dan in ta cigaba da jin maganar Mama zata iya zaginta bata san ta yi ba.

Rehaan yana zaune hankalinsa gabaWaya yana kan aiki, ya yi busy sosai, yana ta aiki ko motsin kirki ba ya yi. GabaWaya abin ya yi masa yawa, ya samu sa?o daga kamfaninsa na Englaand, ya samu sa?o daga asibiti, ya samu daga mall da sauran kasuwancinsa.

Ya cillar da wayar jin kansa ya Wau chaji, ya hargitsa gashin kansa yana ji kiran waya yana shigowa amma bai iya Wauka ba, dan bai san me zai ce ba. Dan lokacin rufe ko ina ya kusa, dan ayi lissafi a fitar da zakka.

"Ya dai Mr Busy" Jafar ya faWa yana zama a kusa dashi.

Ray ya Wago ya kalle sa yana lumshe ido, sai kuma ya ce, "Uk, yaushe zaka koma?."

Jazy ya taSe baki kaWan ya ce, "Sai bayan aurena, na gama tattara komai nawa na can yana gida, ni da sake zuwa wata ?asar sai na je honeymoon."

Ray ya ce, "ka taimaka ka je don Allah, abubuwa sun yi yawa a can."

Ya girgiza kai ya ce, "meye amfanin Alex? Na ga shine yake ri?e da komai a can ko?."

"amma ba kamar kana can ba, ban san me zan ce ba."

Jazy ya ce, "Daga nan ka wuce can, dan ni dai bazan shiga ba gaskiya, ni da Uk sai zamu tafi da Riyya."

Ray ya sauke numfaahi mai tsaho bai ce komai ba. Jazy ya ce, "lokacin lissafin ka ya yi."

A fisace ya ce, "ba shiyasa na ce ka je ba, dame zan ji? Da waWanda suke Yola, ko dana Uk?."

"Ka tuna da partnership Win kamfanin nan na France, shima zai shiga lissafi."

Ray ya ji kamar ya sha?o wayan Jazy ya matse sai ya daina numfashi, amma sai ya daure ya shafa kansa yana girgiza kai cikin takaici. Ya san yana cikin yanayi na cakuWewar tunani, amma ya dinga tuna masa da abinda ya manta dashi, yana sane yake tsokanarsa, dan kawai ya fusata shi.

Jazy ya murmusa ya ce, "My billionaire, yanzu dai ka zama mai saurin fusata, da ba haka ka ke ba wallahi. Yanzu da an yi magana sai faWa, ka dinga sassautawa kan ka."

Ya sake yin dariya sannan ya ce, "Haka za ka yi ha?uri, ai daman masu kuWi irin ka kullum a haka suke, ba sa samun lokacin kansu yadda ya kamata. Kullum sune tunani, lissafi da chajawar kai. Kai ka gode Allah, abubuwa suna zuwar maka da sau?i, baka cika rasa lokacin kan ka ba."

Ray ya yi masa banza, yana ji ana yi masa waya bai amsa ba. Jaxy ya ce, "ni na san wannan shekarar ma sai dai ka kimanta kawai ka fitar. Ribar da ta shigo kamfaninka wannan shekarar ta fi ta last year...."

"Hmm dole ?an uwanka su dinga cewa ka yi ?an?anta da samun irin wannan kuWin, gabaWayanka nawa ka ke? Amma kana da abinda ko Abba sai dai ya kalle ka. Yana da kyau ace ka yi aure, ka fasai ka Wora matarka akan wani abun daban, yadda za ka dinga samun sau?in wasu abubuwan."

Ray jin Jazy ya koma maganar hankali sai sauke numfashi ya ce, "Alhamdu lillah!. Amma fa is not easy, kwana biyu gabaWaya kaina a rufe yake. Na shiga Dubai, daga na shiga Madina na dawo nan. Ni shiyasa nake sso ka yi auren ka tafi da Riyya can, sai ta taimaka min da wani abun."

Jazy ya kalle shi yana harararsa ya ce, "baza ka wahalar min da mata ba."

Ya harare sa sai kuma ya ja tsaki ya ce, "dole ta yi, min, bazai yu kai ba ka yi min ba, ita ka ce baza ta yi ba."

Ya yi dariya ya ce, "ina da abin yi ai, ba a ?asan ka nake ba."

"Na fitar da kuWi ina so na bawa mutanen gidan mu, amma bana son ?aramar magana."

Jazy ya yi dariya ya ce, "ka san sai sun yi kuwa, ?an gidan nan naku ko ruwa za ka faWa sai sun ce ka zuba musu ?asa. Amma kar ka fasa, ka yi Win kaine a gaba gaba dasu." Ya girgiza kai bai ce komai ba.

Jazy ya ce, "Bilal ya ce min ana ta sadaka da abinci. Na ce daWina sa Rehaan Mamy akwai hankali kaWan." Ya Wan yi murmushi kawai bai ce komai ba.

Jafar ya ce, "Yauwa, ina housemaid Win nan ta ka? Tana zuwa kuwa?."

Nan da nan annurin fuskar Rehaan ya gushe, ya Wauere fuska bai ce komai ba.

Jafar ya ce, "ina so na ganta ne."

Ya Wago suka haWa ido, Jazy ya ce, "Ya na ga ka Sata rai, dan na ce ina so na ganta shine na haWe rai haka?."

Ya sake tamke fuska ya ce, "ban taSa jin tsanar ko wacce halitta kamar yadda nake jin tsanarta ba. Ko kaWan bana so na tuna na taSa ganinta."

Jazy ya zaro ido cike da mamaki, dan tunda yake da Rehaan bai taSa ji ya ce masa ga wani ko wata da ya tsana ba, ko a film in suna kallo ba ya cewa ya tsani wani actor ko actress balle kuma a zahiri.

Jafar da ya cika da mamaki ya ce, "Meyasa? Me ta yi maka haka da ka tsane ta?."

Ya yi tsaki bai ce komai ba, yana jin tsanarta tana sake shiga jikinsa. Jazy ya ce, "kuma wallahi tana da kirki sosai, na yi binckena kanta. Ni da na ji a gidan marayu ta girma sai na ji ta bani tausayi, shiyasa ka ga na sake da ita har muna hira haka, dan rashin iyaye babu daWi."

"Oh, na Wauka ka shiga jerin mazan da suke tare da ita, kamar Ubaid."

Jazy ya yi tsaki yana binsa da kallon mamaki ya ce, "ko da na shiga cikinsu Win bana tunanin ranka zai Saci kamar haka, ko da ni da ita za ka gani a Waki Waya bana tunanin ranka bazai Saci har haka ba Rehaan. Ni na rasa me ta yi maka da ke ke Sata rai saboda ita, kai ta faWa kamar wata mata mahimmaci a gare ka. Kuma ta faWa min ta zo ?asar nan saboda kai, lokacin da ka sace ta akwai kuWin ka da ta Wauka, ta ce ka duba cctv zaka gani. Wannan kuWin shine ya kawo ta nan dan ta biya ka. Ni kuma nace maya ta koma gida, zan biya ka kuWin ka, kuma already na tura Bilal kuWin."

Rehaan ya Wago ya kalle shi, sai kuma ya ja tsaki ya ce, "wani lokacin wannan Wabi'ar ta ka ta saurin sakewa da kowa haushi yake bani, a haka kamar namiji amma banza ne kai."

Kafin ya yi magana ya ce, "Kawai saboda ba ka san zafin nema bane, shiyasa ka ke abinda ka ke so da kuWin Daddy, shiyasa fitar da kuWi ba ya yi maka wahala. Ni da na san zafinsu ai bazan yi ba."

"Dallah can, har ka faWawa wani kashe kuWi?. Naira miliyan sha bakwai ne fa ba wani abu ba."

"Oh! seventeen millions ka ke cewa ba wani abu ba? Baka zafin nema ba Jazy."

Ya yi dariya ya ce, "dan kana keeping malice da ita ns ya saka ka ce cewa haka, amma ban kama ?afarka a kashe kuWi ba. Kuma na biya bashin da ya saka ta baro gida dominsa."

Ray ya ce, "?arya take yi fa, ta saka ka yi asarar kuWin ka, dan na rantse da Allah baza a dawo maka dasu ba."

Jazy ya ce, "ka ji na ce a dawo dasu ne? Ni dai na biya mata na sauke mata nauyin da take ganin ta Worawa kanta."

Ray ya taSe baki ya ce, "Lokacin da na ganta a diamond hotel, ina ranar da aka ce anyi sata an gudu, har ka ke bani labari?."

Jazy ya ce, "wani Wan siyasa ko?."

"To itace ta yi, a kan idona ta fito daga Wakin, shima ya fito yana cewa ta manta face mask Winta."

Jazy ya zuba masa ido yana kallonsa kafin ya ce, "da gaske ka ke?."

"Ita Win banza na yi mata ?arya? Tun daga nan na santa, nima kuma gashi ta faWa maka ta yi min sata. Na haWu da ita a train da zan dawo daga Madina, har na taimaka mata ganin bata da lafiya, ashe miscarrige ta yi."

Jazy ya zaro ido ya ce, "miscarrige?."

"Na ga record Win ta a asibiti da komai, ta sha wrong medicine ne ya saka cikin ya zube. A ina ta samu ciki? Ko shima ni ne silar da ya saka ta yi?."

Jikin Jafar sai ya yi sanyi dan ya san bazai taSa yi masa ?arya akan Islaha ba. Jazy sai ya ji bai ji daWin maganar ba, da gaske shi tausayi ta bashi shiyasa ya taimake, ta ashe ?arya ta yi masa.

Ray ya ja tsaki ya ce, "ka daina yi min magana a kan wacce bata cikin rayuwata, a bar maganar don Allah, ka daina Sata min rai."

Jazy ya ce, "na yi mamaki ne sosai, ban yi tunanin tana da Soyayyen hali ba, dan ni da zuciya Waya na taimaka mata." Ray ya mi?e ya bar masa wajan, dan shi ko tuna ta ma ba ya son yi ko kaWan.

Nana Haleema.
[7/20, 10:27/ AM] KRBBK: RDB2P69
Nana Haleema.

Islaha a hankali take tafiya da daddare akan titi, titin yana burge ta yadda komai yake cikin tsari, duk da akwai nisa da mall Win amma haka ta ke son zuwa a ?afa saboda kawai titin yana burge ta.

Daidai wani shawarma and home of ta ga Jafar a tsaye, ta Wan yi jimm tana kallonsa dan bata so su haWu, ba dan ya yi mata laifi ba sai dan Wan uwansa da take jin haushi. Ganin bai ganta ba sai ta Wauke kai tana fatan Allah ya sa kar ya ganta, dan bata san me zata ce ba.

A hankali ta ji an ce, "Miss Islaha."

Ta Wan runtse ido kafin ta juyo a hankali, ta kalle sa da murmushi ta ce, "Mr Jafar."

Ya yi murmushi yana kallon ta, ta Wan ?arasa kusa dashi ta ce, "ina yini."

Ya ce, "lafiya lau. Ina zuwa ke kaWai?."

Islsha ts ce, "zan je mall ne."

"Mall Win za ki je da ?afa?."

"Uhum, ina son ganin gari ne kawai."

Ya Wan girgiza kai ya ce, "i through kina Nigeria."

Ta girgiza kai ta ce, "Jibi zan koma in sha Allah."

"Allah ya kaimu. Na tsayar dake, sai kin dawo, a yi min tsaraba." Ta Wan yi murmushi ta juya ta cigaba da tafiya ta a hankali.

Jafar ya tsaya yana tunanin abinda Rehaan ya faWa masa, ya san Rehaan bazai yi masa ?arya ba, dan shi damuwar wani ba damunsa ta yi ba, ba ya shiga lamarin da bai shafe sa ba, tunda har ya faWa Win ya san ta faru.

Amma Islaha bata yi kama da irin matan da yake kwantanta dasu ba, she looks very decent and neat, bata yi kama da abinda yake yawan faWa a kanta. Abinda ya yarda dashi akan Islaha kawai bata da kunya, kuma tana da tsiwa, shima ba ko yaushe ba.

Lokaci na farko da ya ji bai yarda da maganar Rehaan ba, duk da ya san abinda ya faWa masa ya faru, dan bazai yi ?arya akan Islaha ba, amma ba a kan Islaha ba, sai dai in kuskure ko akasi aka samu a kan hakan. In itace wacce yake cewa ta yi sata a hotel da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login