Showing 210001 words to 213000 words out of 221574 words

Chapter 71 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

109

ya ce, "Sadik tun Wazu nake yi maka waya."

Sadik ya ce, "ina can wajan ?an sanda ana maganar yadda za a fito da Saheer ba tare da ko sisi ba, kuma da alamun nasara in sha Allah."

Mama ta ce, "Sadik ni ban yarda da wanann maganar ba, kawai a samu kuWin nan a basu."

Baffa ya kalle ta ya ce, "kina dasu ne?."

Sai ta yi shiru bata ce komai ba, Baffa ya kalle sa ya ce, "Kana ganin hakan zai yu?."

Sadik ya ce, "In Allah ya amince, a cigaba da addu'a kawai. In sha Allah Saheer zai dawo gida ba tare da ko sisi ba."

Baffa ya yi masa addu'a sannan Sadik ya tafi, da a gajiye yake sosai, yana so ya je ya huta.

A take Baffa ya kira Islaha ya bata labari mai daWi, bata nuna masa ta sani ba, sai ta nuna ta ji daWin maganar yadda zai yi tunanin da gaske take, a haka kowa ya kwanta, duk mutanen gidan babu wanda yake cikin walwala da jin daWi.

Washe gari
Friday.

Jazy yana ta shirin Waurin aure, ya saka lafiyayyar luxury shadda fara mai kyau da Waukar ido, yana tsaye a gaban mirror yana Waura agogon hannunsa, sannan ya Wauki hula ya saka a kansa yana kallon kansa. Ya yi murmushi dan shi kansa ya san ya yi kyau, ya kalli Ray da tunda ya saka kayan ya koma ya zauna ko magana bai sake yi ba.

Jazy ya kalli agogo sannan ya kalle sa ya ce, "Ray lokaci yana tafiya, tun Wazu ka zauna ba ka tashi ka gama shiryawa ba."

Rehaan ya kalli Jazy kamar mai tunani, suka haWa ido ya ga Jazy Win ya yi kyau sosai, sai mi?e tsaye yana ajjiye wayar hannunsa.

A tsakiyar kansa ya naWe gashinsa, ya Wauki hula ya saka ya rufe gashin gabaWaya babu ta inda ya fito, ya saka agogo yana kallon babbar rigar da Jazy ya saka aka Winka masa, ya Wauka ya saka yana kallon kansa.

Ray ya murmusa dan ba sai ance ya yi kyau ba, shi kansa ya san ya yi kyau, bazai iya tuna rabon da ya saka babbar riga a rayuwarsa ba. Ko bikinsu Sameer bai saka ba, ya saka dai manyan kaya amma bai saka babbar riga ba. Kayansu iri Waya ne sak da Jazy, hatta takalmin ?afarsu iri Waya ne, sai banbancin hula da agogo da lins.

Jazy ya ce, "Ma sha Allah! Angon Islaha, ka yi kyau sosai."

Rehaan ya haWe rai, murmushin da yake yi ya gushe daga kan fuskarsa, ya Wan harari Jazy amma bai ce komai ba.

Jazy ya ?yal?yale da dariya ya ce, "Wallahi kyaunka na yau na daban ne dana kullum, ka y??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i kyau sosai ba tsokanar ka na ke yi ba. Dole na yi mana selfie, na yi posting ko zan samu likes da comments, ka san yin hoto da irinka sai mai sa'a" ya faWa yana Wauko wayarsa.

Ray ya matsa daga wajean alamun bazai yi hoton ba, Jazy ya ri?o shi ya ce, "Dallah ka kalla, tarihi ne fa."

Bai ?i ba ya kalli camerar Jazy ya ce, "ka yi dariya mana, Yayan matata."

Sai ya yi murmushi jin sunan da ya kira shi dashi, Jazy ya Wauke su hoton duk sun yi murmushi kuma ya yi kyau sosai, kowa annuri da kyaunsa ya bayyana a cikin hoton.

Rehaan camly ya ce, "ba ka da tarbiyya, Yayan matar ta ka ka raina haka."

Jazy ya yi dariya ya ce, "my billionaire."


A lokacin wayar Jazy ta fara ringing, da ya duba sai ya ga sunan Abba ne hakan ya saka shi ya Wauka.

Yana sakawa a kunne Abba ya ce, "Jaafar kuna tare da Rehaan ne?."

Jazy ya ce, "Eh Abba."

"Kuna cikin gida?."

"A'a muna guest house."

"Ku yi hanzari ku zo nan kafin ku je masallaci, kuna zuwa gidan ku shigo main palour ba sai kun shiga ciki ba. Ku yi sauri." Jazy ya amsa ya kashe wayar.

Jazy ya ce, "mu je in ji Abba, ya ce mu je yanzun nan." Ray bai ce komai ba ya Wauki wayarsa suka fito daga Wakin.

A harabar gidan ya tsaya yana amsa waya, security guard Winsa suka ?araso suna yi masa barka da fitowa. A lokacin Mansur driver Rehaan ya fito da tsaddiyar sabuwar motar Rolls Royce 2026, aka ajjiye ta a wajen ana jira ya gama wayar ya shiga su tafi. Jazy ne ya ?arasa kusa da motar yana yiwa Ray magana, aka buWe musu sabuwar motar suka shiga baya suka tafi gidan.

Kamar yadda Abban ya ce a main falo Win suka shiga da sallama, mutanen ciki suka amsa suna kallonsu, su kuma suka shiga ciki suka zauna.

Sameer ne da Zayyad da Baba, sai Alhaji Rufa'i, Daddy, Abie, Baffa, da Kawun Saheer da malamin da yake Waura auren ?an gidansu. GabaWaya mutanen falon basu fi su goma ba, sai goro alewa da suke a ajjiye a wajen.

Sai Ray da Jazy suka zauna sannan Abba ya ce, "Yauwa, za mu fara Waura auren Rehaan a wajan nan kafin mu tafi masallaci."

Zayyad cikin mamaki ya kalli Abba ya ce, "Abba ba a masallaci za a Waura ba?."

Abba ya ce, "a nan za a Waura na Rehaan, na Jafar ne za a yi a masallaci. "

Rehaan dai tunda ya sauke kai ?asa bai Wago ba, yana ji ana hidimar Waura aurensa bai ce komai ba, yana ji ko wanne Sangare yana gabatar da kansa a matsayin wakili, yana ji ana zancen sadaki ana tambayar shaidu sun shaida. Yana ji yana gani aka Waura aurensa da Islaha akan sadaki naira miliyan Waya, aka bawa Baffa sadakin Islaha. Ji yake jinin jikinsa kamar ya daskare ya daina zagawa, ya kasa Wago kai saboda yadda yake jin jikinsa ya yi sanyi sosai. In ya tuna aurensa aka Waura da Islaha sai ya ji kamar a tashi duniyar, sai ya ji kamar kowa ya mutu a bar duniyar babu kowa.

Bayan an Waura auren Abba ya kalli Baffa yana? murmushi ya ce, "Alhaji Mustapha mun gode, Allah ya saka da alkhairi."

Baffa ya yi murmushi ya ce, "Amin. Allah ya tabbatar da alkhairi a cikin auren, Allah ya sa ya zama silar farin cikin kowa."

"Amin ya Allah."

Abba ya kalli su Jafar ya ce, "Zayyad ku je masallacin gamu nan, an bar mutane suna ta jira." Duk suka mi?e suka fita, aka bar Rehaan da Daddy a zaune.

Abba ya ce, "Alhaji Mustapha ga Rehaan...."

Abba juyo ya kalli Rehaan ya ce, "Rehaan ga mai ri?on matar ka, kuma uba a gare ta. Ka yi masa godiya akan karamci da haliccin da ya nuna mana. Ba tare da ya san mu ba ya Wauki ?arsa ya bamu, bai san kai ne za ka auri ?arsa ba, amma ya amince da zuciya Waya. Ka yi masa godiya."

Rehaan ya Wago ido a hankali ya kalli wanda aka muna masa, ya rasa me zai ce, dan shi bai ga abin godiya a auren Islaha ba. Amma sai ya daure ya ce, "an gode" ya faWa a ta?aice dan babu yadda zai yi.

Baffa ya yi murmushi ya ce, "Babu komai, Allah ya sanya albarka a cikin auren, Allah ya Worar da zaman har aljanna."

Duk aka amsa da amin ban da Rehaan da ya ja bakinsa ya yi shiru.

Baffa ya ce, "Na san ka san marainiya ce, a gidan marayu ta girma, bata san kowa na ta ba. Islaha yarinyar kirki ce, yarinya ce ta gari mai tarbiyya da sanin ya kamata. Yadda take yin Wawainiya dani ko ?a?an dana haifa basa yi, yadda take yi min biyayya ko ?a?ana basa yi min. A ko yaushe ina ji a raina ina ma ni na haifi Islaha, ina jinta kamar jinina, ina ji kamar Waya daga cikin yaran da Allah ya bani. Ka ri?e ta hannu biyu, na tabbatar da baza ka taSa danasanin aurenta ba, sai dai ka yi alfahari."

Daddy ce, "Duk mun shaida, tarbiyyarta ce ta saka Daada ta ganta, ta burge ta har mu ka zo wannan matakin. In sha Allah ?arku ba zata yi danasani ba, baza ta yi hawaye ba, baza ta yi maraici ba. Zata rayu cikin farin ciki da walwala, za a maye mata gurbin ku da zata baro ta dawo nan."

Baffa ya ce, "Allah ya tabbatar mana da haka."

Duk suka amsa da amin kafin Abba ya kalli Ray ya ce, "ka je masallaci, ga mu nan." Ya mi?e a hankali ya fita ya bar su.

Bayan sallar juma'a aka Waura auren Riyya da Jafar, bayan an Waura auren anata hotuna kafin a tafi reception, Ray dai yana killace dan ba hayaniya yake so ba, duk inda ya yi masu tsaron lafiyarsa suna bin bayansa. A haka aka watse daga reception, ya wuce guest house dan Jazy ba dawowa zai yi ba.

Nana Haleema.
[7/30, 11:15/ AM] KRBBK: RDB2P97
Nana Haleema.


Baffa bayan ya koma gida ya shiga har falon Mama ya samu Mama ta ita kaWai a zaune ya ce, "Ina Islaha?."

A daidai lokacin Islaha ta shigo da sallama, kafin su ji sallamar ta ta Mama ta ce, "Ta tafi yawon ta zubar, ko ta Satan Saheer ba ta yi, sai ?aryar Hamma."

Islaha ta ce, "Gani Baffa."

Baffa ya juya yana kallon ta yana murmushin jin daWi, ji yake kamar ya sauke nauyin da Allah ya Wora masa, ji yake ya sauke ha??in da Allah ya Wora masa a matsayin uba.

Islaha ta dur?usa a gabansa Baffa ya ce, "Kina da sa'a Islaha, ke mai sa'a ce gaba da baya. Duk mai nufin ki da sharri ko waye shi sai dai ya koma kansa, Allah ya yi miki abinda babu wanda ya isa ya ?wace sa daga hannunki, alkhairin da ki ke nema ya ba ki, da ya tashi ba ki sai ya ninka ya kuma ninkawa. KarSi nan" ya faWa yana mi?a mata.

Ta saka hannu ta karSa tana kallon kuWin ganinsu sa yawa. Baffa yana murmushi ya ce, "kin san meye wannan a hannun ki?."

Islaha ta ce, "A'a Baffa."

Baffa ya murmusa cikin jin daWi ya ce, "sadakin auren ki ne."

Gaban Islaha ya faWi, ta buWe ido waje ?irjinta yana bugawa da ?arfi. Ta kalli kuWin ta kalli Baffa da yake kallonta, ta sake Wauke kai tana jin wani iri a jininta, ga wani irin yanayi da take ji yana manaye ko ina a jikinta.

Mama ta yi tsaki ta ce, "Sadakin auren mahaukacin har wani abin murna ne? Mahaukaci ne fa wanda aka bata, sai meye dan ya aure ta?. A banza zai kashe ta kuma ya kashe banza, babu abinda aka isa ayi ranta ya tafi a banza. Ni tunda dai bata auri Wana ba ko waye ta aura bai dame ni ba, Saheer dai ya fi ?arfinta wallahi."

Baffa bai kulata ba ya ce, "Islaha kin yi shiru."

Gabanta faWuwa yake yi, da farko bata yi tuannin zata ji irin wanna faWuwar gaban ba tunda ta san a yadda aka gina auren, amma sai ta ji tsoro yana mamaye mata ?irjinta, fargaba da sanyin jiki suna yi mata dirar mikiya lokaci Waya.

Cikin sanyin murya ta ce, "Har an yi auren?."

Baffa ya yi murmushi ya ce, "An Waura. Yanzu ke matarsa ce halak malak, sun ce min gobe zasu turo da motoci a Wauke ki, tunda babu bikin da za ki yi sai ki tare a gidan ki gobe."

Ta wara ido tana kallon Baffa jikinta har rawa yake yi ta ce, "Baffa gobe kuma?."

"Ko kina da shirin da za ki yi ne?."

Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba. Baffa ya ce, "na riga na amsa musu, amma in akwai abinda za ki yi sai a faWa musu."

"Shikenan Baffa."

"Na faWawa Yayar ki, za a zo ayi miki ado irin na amare, bai kamata a kai ki a haka ba."

Islaha ta ce, "ba sai ta zo ba Baffa."

Baffa ya ce, "Haka za a yi auren na ki babu kwalliyar amare?."

Ta yi shiru bata amsa ba dan gaskiya babu abinda zata yi. Baffa ganin haka sai ya ce, "Shikenan, ki je ki haWa komai na ki, yau Allah ya Waga darajar ki daga ?asa zuwa sama. WaWanda suke ganin ki a wula?ance zasu fahimci sun tafka kuskure, zasu gane sune a wula?ance ba ke ba."

Islaha ganin Baffa zai fita sai ta ce, "Baffa kuWin."

Ya kalli kuWin ya ce, "Sadakinki ne, ke za ki ri?e."

Ta bi kuWin hannunta da kallo ta sake kallon Baffa ta ce, "Baffa ka bar su a wajan ka."

Ya yi murmushi ya ce, "Ha??inki ne Islaha." Daga haka ta fita ita kuma ta sauke numfashi tana kallon kuWin.

Ta kalli Mama da take tsaye tana kallon ta, ta Wauke kai tana mi?ewa tsaye. Mama ta bita da kallo ta ce, "Amaryar mahaukaci! Yau Allah ya yi zan rabu da ala?a?ai daga cikin gidana, sai a je can a ?arata. Ko banza za ki dinga kwana a ac kina cin kaji."

Islaha ta haWWiye yawu bata ce komai ba ta raSa gefen Mama zata wuce Mama ta ce, "daman na rantse, babu ke babu Saheer, kuma rantsuwata bata faWi a ?asa ba. Ki je ki ?arata da mahaukacin ki, a bi wani sarkin, Saheer kam ya fi ?arfin ki wallahi." Bata tanka ba ta shiga Waki, ta rufe ?ofar tana jingina da bango ta lumshe ido.

Ta buWe idanunta ta kalli kuWin hannunta, tana ayyana sadakin aurenta ne a hannunta, aurenta kuma ba da Hamma, da wanda ta fi tsana a duk duniya. Ta juya kuWin a hannunta, tana tuna wanda ta aura a zuciyar ta.

Ta yi tsaki a bayyane ta ce, "igiya uku ta aurensa ta hau kaina." Ta dafe kai cikin takaicin da ta ji yana mamaye ta, ta cize bakinta tana ji kamar ta zane kanta saboda takaicin da ya cika mata zuciyarta.

"Rehaan!"

Kalaman da ya faWa mata a ?asar saudia suna yawo a kunnenta, ta runtse a bayyane ta ce, "na yi saboda Hamma, na yi saboda Hamma ya kuSuta, na yi saboda rayuwar Hamma ta dawo, saboda shi ne kawai, ba dan ya isa ba. Na yi komai domin shi, kuma zan dawo gare sa in sha Allah" ta faWa dan ta kawar da tunanin da yake damun zuciyarta.

?wan?wasa ?ofar ake yi a hankali, Islaha ta bar jikin ?ofar ta buWe ?ofar suka haWa ido da Safeera. Islaha ta bata hanya ta shiga, sannan ta mayar da ?ofar ta rufe. Islaha bata ce komai ba ta ?arasa gefen gado ta zauna, ta zame Wankwalin kanta, ta ajjiye kuWin akan cinyarta tana ji duniyar tana juya mata.

Safeera ta ce, "ya dai?."

Ta Wago ta nuna mata kuWin ta ce, "an Waura auren."

"Shine ya saka ki a damuwa?."

"Ina ji kamar ban kyauta ba, sai yanzu nake jin na tafka kuskure babba. Jikina yana bani kamar...." Sai ta kasa faWa ta dafe kanta.

"Islaha komai ya riga ya faru, wannnan tunanin da ki ke yi duk ihu ki ke yi bayan hari. Yanzu ke matar Rehaan ce, kamata ya yi ki fara tunanin abinda zai biyo baya, ba wanda ya riga ya wuce ba."

"Ya zan yi, ina ji kamar ban kyautawa Hamma ba, ban kyautawa rayuwata gabaWaya ba."

"Hmm kina son maimaita magana Waya Islaha, ke ki ka ce za ki iya yin komai saboda shi. Yanzu kuma kin yi saboda shi Win, meyasa ki ke damun kan ki?."

"Zan iya yin komai saboda shi" ta sake maimaitawa don Safeera ta tabbatar."

Safeera ta dafata ta ce, "ki saka a ran ki wannan Win ma saboda shi ne."

Ta Wago idanunta da suka fara cikowa da hawaye ta ce, "ya zan yi in Hammma ya dawo, da wacce fuska zai karSi maganar nan?. Aure na yi fa, duk da auren contarct ne, amma kafin ya fahimce ni ni kaina na san za a sha wahala" ta girgiza kai tana Waga hannu sama ta ce, "Allah ka taimake ni Hamma ya fahimce ni, Allah ka sa kar ya yi min mummanar fahimta."

Safeera ta ce, "Haka za ki faWa masa ya fahimta, komai zai yi daidai in sha Allah. Ki daina damun kan ki, komai ya riga da ya faru, danasani akan abinda ya wuce Sata lokaci ne Islaha. Na farko baza ki dawo da abinda ya wuce ki gyara ba, sannan tunaninsa Sata miki rai kawai zai yi, tunda ba ki da magani. Kuma auren nan na suna ne, tunda za ku zauna matsayin ma'aurata amma ba wai na gaske ba."

Islaha ta girgiza kai ta ce, "Baffa yana zancen gobe zan koma gidan, ni wallahi komai ya fice min daga rai" ta faWa tana kwnaciya da baya cikin wani irin yanayi.

"Daman ai a can za ki zauna, tunda a matsayin matarsa ki ke yanzu."

Ta yi ?aramin tsaki ta rufe ido ta ce, "bana son maganarsa wallahi, ban san haka na tsane sa ba sai yanzu."

Safira ta yi dariya ta ce, "taimakon ki ya yi dai, ba dan shi ba da ynzu an kashe Hamma har lahira."

Banza ta yi mata bata ce komai ba tana sa?awa da warwarewa. Itama Safieera bata ce komai ba suna zaune a wajen har aka yi sallar la'asar, a nan suka yi sallah ta sake komawa ta zauna tana buga tagumi cikin sabon yanayin da take jin jikinta.

Safeera ta katse shirun ta ce, "Amma bakya ganin Mama zata faWawa Saheer kin yi aure?."

Islaha ta mi?e zaune sosai tana gyara Wankwalin kanta ta ce, "ko shakka babu, Mama sai ta faWa masa. Kin san halinsa da saurin Waukar zafi, kafin na samu ya fahimce ni ma babban aiki ne wallahi."

Safira ta ce, "dole zai birkice, tunda yana da kishi, kuma magana ake ta kin auri wani. Amma daga baya komai zai zama ya yi daidai in sha Allah. Duk inda wanda ka ke so yake, in aka ce ya yi aure dole za ka ji zafi da kishi a ranka."

Islaha bata ce komai ba suka jiyo hayaniya daga falo, da sauri suka mi?e suka fita falon suka ga Baffa ne sai su Mama da suke a tsaye.

Baffa ya ce, "Islaha an saki Saheer, yanzu haka yana asibiti tare da Sadik!."

Nana Haleema.
[7/30, 11:15/ AM] KRBBK: RDB2P98
Nana Haleema.

Wani irin dumm ta ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login