Showing 156001 words to 159000 words out of 221574 words

Chapter 53 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

130

yanzu an kamata, tunda ba Soyayyiyar fuska ce da ita ba, tana da Waukakar da baza ta yiwa Wan siyasa sata ya ?yale ta. Kuma shi ba daga gidan Ubaid yake ganin ta ba, a gidan Maleek yake ganinta, hakan sai ya tabbatar masa da kuskure Rehaan ya yi.

Ya kawar da tunanin daga ransa, amma yana ji a ransa sai ya yanke ta a idanun Rehaan, ba dan wani abu ba, sai dan baka dan me gobe zata haifar ba. Ice cream da shawarma ya siya ya koma gida ya tarar da Rehaan yana shirin tafiya aiki, yana tsaye a gaban consool Win falon yana gyara zaman necktie Win wuyansa.

Ya yi kyau cikin black Win suit, ya haWe gashinsa a tsakiya, ga wani luxury watch da ya Waura a tsintsiyar hannunsa. Jafar ya kalle sa ya Wauke kai, ya zauna a kan kujera yana waya da inda ya ba da order kayan da zai saka.

Sai da ya gama wayar Rehaan ya kalle sa ya ce, "kai kaWai ka ke siyayyar ka, ba ka faWa min."

Jazy ya ce, "sau nawa ina faWa maka kana avoiding Wina? Shiyasa na ?yale ka, bikina ne ba naka ba, ni ya kamata na yi duk abinda zan yi."

Ya gyaWa kai ya ce, "bikin ka ne kam" ya faWa yana Waukar wayarsa.

Jay ya ce, "Kaima harda kai, tunda tare za a haWa mu."

Hararar sa ya yi, hakan ya saka ya Wan yi murmushi bai ce komai ya fara cin shawarmarsa hankali kwance.

Rehaan yana sauka Mamy ta kira wayar Jafar, ganin video call ne sai ya gyara zama sosai kafin ya Wauka.

Fukar Mamy ta bayyana kan screen, ganinsa da ice cream da shawarma sai ta ce, "shan za?i, sanyi, ciye ciye duk ka iya Jafar."

Ya Wan yi dariya ta ce, "Ina yini Mamy."

Ta ce, "Lafiya lau Jazy, nima yau na zama Rehaan, na ce Jazy."

Ya yi murmushi Mamy ta ce, "Tunda mu ka yi magana da kai baka ce min komai ba, ya amince da zancen Ikram kuwa?."

Jazy ya ce, "Wallahi Mamy na yi masa, amma ina farawa ya ce shi baya so, Ikram ?anwarsa ce ba zai iya auren ta ba."

Mamy da damuwa ta ce, "Jafar Rehaan ya girma fa, ga arzu?in da Allah ya yi masa, aure ne kaWai ya rage masa. Meyasa bazai amince ya auri Ikram ba? Duk wacce zata aure shi a yanzu dan kuWi zata aure shi, amma ikram mun santa, mun san wacece ita."

"Mamy ko ni na faWa masa, da yana zancen zai yi lissafi za a fitar da zakka nake faWa masa ya kamata zuwa yanzu ya yi aure."

Mamy ta Wan yi jim kafin ta ce, "Ni na fara wani tunani Jazy."

Jafar ya ce, "na me kenan Mamy?."

"Anya yana da lafiya?."

Maimakon Mamy ta ji kunyar tambayar shine ya ji kunya, amma ganin ita ko a jikinta sai ya basar yana Wan murmushi ya ce, "waye ya sanar masa Mamy? Amma na tabbata lafiya lau yake, yana da ilimin da in bashi da lafiya zai nemi magani bazai zauna ba."

"Haka ne kam Jafar. Daman ni ya bawa damar zaSa masa mata, kawai zan zaSa nasa ita, koda zai zo ya ce baya so na san daga baya zai amimce. Zan yi magana da Ikram, in ta shirya aurensa za a yi bayan auren ku."

Jafar ya ce, "Mamy amma da kar a yi gaggawa,? ki bari ya amince Win. Kin san hali, Wan rigima ne."

Mamy ta ce, "?yale ni dashi, bazan zuba masa ido haka ba. Ita wacce Daada zata aura masa bamu san wacece ba, wata?ila tana daga cikin waWanda zasu so su ga bayansa saboda kuWi. Ina so ya samu wacce zai samu peace of mind."

Jafar ya ce, "Shikenan Mamy, Allah ya zaSa mana abinda ya fi alkhairi." Ta amsa da amin ta kashe wayar.

Jafar ya sauke numfashi ya ce, "za a sha rikici dashi kam, kafin ya karSi auren nan za a jima sosai." Ya faWa yana kiran Juwariyya, dan tunda Rehaan ya fita bashi da abokin hira, gwara ya kira ta su sha soyayya.

? ? ?? " " " " " "

Daada tana zaune ita kaWai a falon ta, Abba ya shiga da sallama ya zauna a kan carpwt ya ce, "lokacin da ki ka aika in zo na shiga wanka, yanzu na fito."

Daada ta kalle sa ta ce, "akan maganar yarinyar nan da Muhammad zai aura, an sake komawa kuwa? Tunda ka ce min babanta yana asibiti baka sake cemin komai ba. Ka san da bikin Zuwairiyya nake so a haWa, gabaWaya biki yanzu bai wuce sati huWu ba."

Abba ya ce, "Daada wanda take hannunsa ba mahaifinta bane."

Daada da mamaki ta ce, "waye Win ta?."

Abba ya ce, "Yarinyar a gidan marayu ta tashi, bata san kowa nata ba, tana gidan ne a matsayin ?ar ri?o ba ?ar gida ba."

Abba sai ya ji shiru Daada bata ce komai ba, jin shirun ya yi yawa ya Wago ya ga Daada tana hawaye.

Hankalin Abba ya tashi ya ce, "Daada lafiya,
Me ya faru haka? Na faWi wani abun da ya saka ki kuka ne?."

Daada ta dakatar dashi da hannunta ta ce, "ashe shiyasa ta shiga cikin raina, shiyasa nake jin sonta har cikin jinina, ashe marainiya ce.
Allah sarki, maraya bawan Allah, Allah sarki Ishlaya, sai na sake jin sonta, sai na sake ji dole ma Muhammadu ya aure ta."

Abba ya Wan girgiza kai jin kukan ba wani mai babban dalili bane ya ce, "Zan saka a sake bincikawa in Allah ya yarda. Tunda kina so za a yi in Allah ya yarda, in mahaifin nata ya dawo daga asibitin za a je a same shi in Allah ya yarda."

Ta goge idonta ta ce, "haka nake so na ji, Allah ya nuna mana lokacin." Abba ya amsa ya tashi ya fita.

Abba yana fita ya shiga apartment Winsa, a zaune ya tarar da Mama tana jiransa, ya ?arasa ya zauna ta ce, "ka dawo."

Ya Waga kai ya ce, "Na dawo. Daada da rigima, wai batun auren Rehaan take yi da yarinyar nan. Ni da yake ban mayar da hamkali ba, tunda na saka a ka bincila sau Waya ban sake bincikawa ba."

Mama ta ce, "Tunda ka ga ta dage akwai alkhairi a ciki, gwara ka saka albarka Allah ya sanya alkhairi."

"Maganar auren take yi a na nan da sati uku fa, Kawai sai na je na ce musu nan da sati uku zuwa huWu Wana zai auri ?ar ku?."


"Ai ba wani abun damuwa bane, akwai abinda za a dawata su dashi har a yi auren a wannan lokacin."


"Ba a yi binciken kirki a kanta ba, bazai yu ace daga nemo yarinya a yi aure babu bincike mai ?arfi ba."

Mama ta Wan Sata fuska ta ce, "haka ne kuma" ta faWa dan kar ta musa ya yi saurin gano ta

Abba bai ce komai ba ya mi?e ya shiga Waki, ta bi sa da kallo ta ce, "Wallahi sai auren nan ya yu, sai na tabbatar da auren nan ya tabbata ko da zan rasa wani abu nawa. Bazan bari a yi binciken ba, ni na san abinda zan yi" ta faWa tana tashi ta fita cike da mugunta a ranta.

Nana Haleema.
[7/20, 10:27/ AM] KRBBK: RDB2P70
Nana Haleema.

? ? Riyya suna tare da Ikram da Janan, suan ta zaSen fabrics na biki, ga kaya nan a gabansu a jibge kamar ba a so, ana ta haWawa ?awaye packs Winsu, dan bikin manya ne, bikin ?anwar Rehaan Yola komai na package Win ?awayen amarya kyauta za a bayar, babu batun siyan anko. Bayan kayan sakawa a pack Win, harda kuWin Winki za a sakawa ko wacce a cikin pack Winta.

Janan ta ce, "Ya batun musician Win ne? An gama komai?."

Riyya ta ce, "an gama yin komai, babu abinda ba a yi booking ba. Indian night ma an gama yin komai, kuma ba ki siyi outfit Win ki ba."

Ikram ta ce, "waye ya ganni a kayan india, ban taSa sakawa ba fa."

Riyya ta cee, "kuma dole ki saka. Kin ga nawa nan" ta faWa tana buWe musu wani milk kaya mai kyau.

Janan ta ce, "Wow, amma ya yi kyau. Zai yi miki kyau sosai. Ina na Hamma Rehaan?."

Janan tana faWar hakan gaban Ikram ya faWi, amma bata nuna ba ta ce, "zan so na gansa cikin kayan india, na tabbatar ba ?aramin kyau zai yi ba."

Janan ta ce, "ba ki taSa gani ba? Ni na taSa gani ya saka sau Waya, yana sakawa ya cire wai babu daWi."

Riyya ta yi dariya ta ce, "bara na kirasa yanzu, bai faWa min gift Win da zai bani ba" ta faWa tana Waukar waya ta kira sa ta saka a speaker.

Yadda wayar take yin ringing da bugun zuciyar Ikram, ta Wan yi shiru tana jira ya Wauka amma sai ta katse bai Wauka ba.

Riyya ta ce, "Mr busy, Matarsa ta shiga uku, ko yaushe yana kan waya akan kasuwanci, in ba waya ba laptop, ki rasa inda zai kai kuWi."

Janan ta ce, "ya za a yi ya yiwa matarsa? Ai duk wannan abubuwan nasa sauke sa zai yi a sha love."

Riyya ta yi dariya ta ce, "Kuma fa haka ne." Zata sake yin magana kiransa ya shigo wayar.


Ta Wauka ta saka a speaker ya ce, "Riyya."

Ta ce, "Na kira ba ka Wauka ba."

"Ina ganin kiran, kawai dai na kira ki ne yanzu.
Ya aka yi?."

"Ba ka bani gift ba."

"Wanne gift?."

"For my wedding."

Ya Wan yi dariya ya ce, "oh amarya."

Ta Wan yi dariya kaWan bata amsa ba, sai ya ce, "ni ban san me zan ba ki ba Riyya, amma ki tura min abinda ki ke so."

Ta ce, "ka san me nake so?."

Ya yi shiru bai amsa ba, Riyya ta san jiran ?arshen maganar yake yi sai ta ce, "ni kawai ka zo bikin, shine kyautar da zaka yi min."

"Riyya abun babu sau?i, ina da aikin da zan yi, zuwana zai zama under probability."

Cikin shgwaSa ta ce, "Ni dai don Allah ka zo, bazan ji daWin ace bikina baka nan ba."

Ya Wan sauke numfashi ya ce, "Okay. Ina Kiddo?."

"Tana wajan Mamy."

"ke kina ina?."

"Ina tare da Ikram da Janan."

Ya Wan yi shiru kamar bazai yi magana ba sannan ya ce, "suna ji babu wanda zai yi min magana?."

Janan ta ce, "ni fushi nake da kai, na kira ka har sau huWu baka kira ni ba."

"Sorry Jan, amma kin san bana so a tara min kira."

"Zan kiyaye."

"Good gal."

Ikram ta ce, "Yaya Rehaan."

A hankali ya ce, "Ikram."

Ta ce, "Uhum, ya aiki?."


"Alhamdu lillah, ki gashe da Mummy." Yana gama faWar ya kashe wayar gabaWaya.

Janan ta ce, "wai kuwa yana da budurwa?."

Riyya ta ce, "bashi da kowa, Hamma Jazy ya faWa min bashi da wata budurwa har yanzu. Sai dai wannan aure da Daada take so ta ?a?aba masa."

Janan ta kalli Ikram da ta ?i cewa komai, ta taSa ta ta ce, "Sis kin yi shiru."

Ikram ta Wan yi murmushi ta ce, "Kawai ina tunanin wacce lucky gal ce zata Wauki Ya Rehaan a matsayin miji."

Riyya ta yi yar dariya ta ce, "gaskiya kam sai dai lucky Win. Amma kuma ga shi nan zai yi auren, duk da ba ya so amma dai matarsa ce."

Janan ta kalli Ikram ta ce, "Iky ni wallahi na jima ina ji ina ma ya aure ki, tunda Hamma Jazy ya Wauki Riyya, na san shima zai iya auren ki, nikam ina so ya aure ki sosai."

Ikram ta Wan yi murmushi ta ce, "rufa min asiri, ina ni ina shi?."

Ta harare ta ta ce, "ka ji wata magana, Akwai aibu da kin aure sa ne?."

Ta girgiza kai ta ce, "Babu, kawai na san ba abu ne da zai yu ba."

Riyya ta ce, "zai iya yuwa mana, ki ka san me Allah ya rufe?. Mu zamu so ki aure sa Win, saboda
kowa ya san wacece ke balle azo ana wata magana, ko bakya so?."

Ta kalli Riyya ta ce, "Riyya kenan, Wacce mace ce zata ce bata son Hamma ne? Sai dai in ta san bazata samu ba."

Janan ta ce, "ke kam za ki samu, daman na lura kamar you have stong feelling for him."

Ikramta Wan yi murmushi kawai bata ce komai ba, she wish abinda suka faWa ya zama gaskiya, da sai ta yi azumi guda goma na godiya ga Allah.

? ? ? " " " " " " " " "

Islaha tana ta shirye shiryen dawowa gida, har an siya mata ticket, har ticket Win jirgin da zata hau zuwa Adamawa ta siya.

Ranar da zata bar ?asar tun bayan sallar i'sha ta shirya, da taimakon Sunaira da Maleek ta yi komai yadda ya kamata. A lokacim ta fita zuwa wajan Labiba, dan ta ji ko akwai sa?on da zata kai wa Mama.

Falon gidan babu kowa shiru, Islaha ta Wan zauna tana jira ko za a fito amma ba a fito ba.

A lokacin Aysha ta shigo falon ta ga Islaha a zaune, Islaha ta kalle ta ta ce, "Don Allah ina Labiba?."

Aysha ta ce, "in ki ka shiga ciki, Waki na biyu" ta faWa tana Waukar wayarta ta fita. Islaha ta mi?e ta shiga ciki kamar yadda ta ce mata.

Islaha a hankali take takawa a nutse, gidan ya yi mata kyau sosai, tana ta mamakin su haka gidanjensu yake manya ga kyau.

A hankali ta tuea ?ofar ta shiga da sallama tana kiran sunan Labiba.

Gaban ta ya yanke ya faWi, ta yi saurin ja baya, tana jin kamar wata ta ja tasaboda shock Win da ta ji ya ratsa ta, ta fara zare ido tana so ta tuna abinda ta gani, amma bata so ta gasgata abinda ta gani ba gaskiya ne, ta fi so ta bar shi a hasashe ko mafarki.

Ta jima a haka cikin rashin nutsuwa, kafin ta firgita ta dawo hanlalin ta, ta kalli Wakin sai kuma ta zabura ta bar wajan a guje cikin kuka.

A wannan yanayi ta koma, ta faWa kan gado tan kuka kamar ranta zai fita, ita kanta bata san kukan me take yi ba, kawai dai ta ji tana kuka ne wanda yake zuwa daga zuciyarta.

Abinda ta gani bata taSa gani ba ko a film balle a zahiri, mace da namiji a tare suna aikata wani abu mara kyau bata taSa gani ba ko da wasa.

Ganin da ta yi ya saka zuciyarta ta tsinke, jikinta yana rawa, zuciyarta tana rawa, cikin wani irin yanayi mara daWi wanda bata taSa jin kanta a ciki ba. Ita dai bata san adadin lokacin da ta Wauka a wajan ba, sai ji ta yi an buWe ?ofar an shigo.

Tunda ta shigo ta zuba mata ido kawai tana kallon ta, ganin ta normal da ita kamar ba ita ta gani ita da namiji a Waki ba.

Labiba ta dake ta ?arasowa inda take ta ce, "Kin je nemana, lafiya?."

Wani irin abu Islaha ta ji yana taso mata daga cikin kanta yana mamaye duk jikinta, ji take kamar ta tashi ta sha?e Labiba har sai ta mutu.

Labiba ta ce, "Sai wani kallona ki ke, meye ba?o a abinda ki ka gani Win? Kin saba yi fa, ina jin farar fatarsa ce ta ruWa ki. Amma wannan a wajan ki ai....." Islaha bata san hannunta ya sauka a akan fuskar Labiba ba, sai ganin kanta ta yi a tsaye a kusa da ita tana nuna mata yatsa ta rasa abinda zata ce.

"Kai! Ni ki ka mara?" Ta faWa tana kai mata mari? amma Islaha ta ri?e hannun, ta sauke hannunta tana jin ?yan?yamin Labiba yana shiga zuciyarta.

Kasa ce mata komai ta yi, kawai ta shiga bathroom tana jin fitar Labiba.

Ruwa ta dinga zubawa kanta kamar itace ta aikata, haka ta ji?e gashinta jagab, a sanyaye ta sake shirya ta fito falon tana zare idanunta. Sama sama suka yi sallama da mutanen gidan, duk ta karSi lambobinsu dan zasu dinga gaisawa a whatsapp, aka kai ta har airpot.

Ita dai a sanyaye take yin komai, Sunaira ce mai taimaka mata tana nuna mata abinda bata sani ba, a haka har ta gama komai ta yi boarding.

Sai da ta shiga boarding room sannan ta samu ta sha tea, ta yi tagumi tana tuna abinda ta gani da abinda kunnenta ya ji mata.

GabaWaya ta ruWe ta fita daga hankalinta, ita dai ta san tana zaune kawai sai gani ta yi an fara shiga jirgi. Ta mi?e a sanyaye ta shiga itama ta zauna tana kallon window.

Sai ta fara tunanin ko tana da rabon dawowa ?asar ko babu Allah ne ya sani. Ga shi ta shigo ta fita bata je ta ga ka'aba ba, babban abinda yake yi mata daWi ta shiga madina har ta kwana biyu. A haka jirgi ya Waga zuwa ?asa nigeria.

? ?? A jirgi suka yi sallar asuba, ?arfe tara na safe jirginsu ya dira a Abuja. Bayan ta gama komai ta Wauki kayanta kuma ta zauna jiran jirgin da zai kai ta Adamawa state.

Sai ?arfe sha biyu sannan komai ya zama ready, mota ta Wauke su zuwa inda stairs Win jirgin yake. Awan su uku a sama sannan suka sauka, tun a airport ta canja wasu kuWin zuwa naira, ta yo drop Win taxi zuwa gida zuciyarta tana bugawa, dan bata san abinda zata tarar a wajan Mama ba, bata san yadda zasu kwashe da Hamma ba, wacce irin amsa zata bashi in ya tambaye ta? Ta bashi labarin Rehaan Yola ko kuma ta yi shiru?. Da wannan tunanin aka cigaba da tafiya, tana kallon Yola cikin yanayin kewa.



Ya ku ke ganin Hamma zai karSi maganar Rehaan? Mama zata bari ta zauna a gidan ta? Ana ta shirin auren Rehaan, ya abin zai kasance?
Drama don start=?%?d'?d'?

Nana Haleema
' [7/21, 12:04/ PM] KRBBK: RDB2P71
Nana Haleema.

_Don girman Allah ku shiga Youtube ku yi searching littafin KIRAN RABO, ku danna like ku yi comments a kan ko wanne episode.=?O?
Islaha a ?ofar gidansu Safeera aka sauke ta, daman ta yi canjin riyal

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login