Showing 45001 words to 48000 words out of 221574 words

Chapter 16 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

149

nasara a duk inda ka ke."


"Amin Mamy" ya faWa yana raba kansa da ita ya fito zuwa inda motarsa take.

A lokacin Mamy ta ce, "ka yiwa sauran iyayen ka sallama ne?."

Ya Wan yi shiru alamun bai yi ba, Mamy ta ce, "bai kamata ba, ka je ka yi musu sallama."

Ya Waga kai ya ri?e hannun Banisha, Riyya tana bayansa suka nufi bangaren Mama.

Ita da babban Wanta suka same ta, sai Sameer da Janna da suke zaune. Ya shiga da sallama suka amsa, ya ?arasa ya ce, "Mama zan tafi Jeddah."

Ba yabo ba fallasa ta ce, "a dawo lafiya." Ya Waga kai ta kalli babban yayyansu ya ce, "Sai anjima Hamma."

Ya kalle sa ya ce, "Allah ya kiyaye Rehaan."

"Amin."

Ya kalli Sameer da ya wani haWe rai kamar bai san shi ba, sai bai ce masa komai ba ya kalli Janan da ta haWe rai ta kawar da kai.

Ya san fushi take yi dan bata san zai yi tafiya ba, ya Wan saki fuska kaWan ya ce, "Little Jan zan tafi?."

Sai a lokacin ta kalle sa, kafin ta yi magana ya ce, "i'm sorry, zo mu je mota." Bata musa ba ta mi?e suka fita tare. Mama ta buga ?wafa tana gyaWa kai ta ce, "ayi dai mu gani."

?angaren Umma suka shiga suka tarar tana gyarawa Salman farcensa. Yana ganin Rehaan ya zabura zai gudu, ta buga masa tsawa ta ce, "koma ka zauna malam, uban ka ne shi da ka ke rawar jiki in ka gan shi?."

Rehaan shi kansa sai da ya tsorata da tsawar da ta yi, bai ce komai ba ya yi mata sallama ya fita zuwa wajan amarya Abba.? Bai jima a wajan ta ba ya dawo ya shiga wajan Daada, Allah ya taimake sa ya samu bacci take yu. A bakin mota suka yi sallama da ?annensa ya shiga mota suka nufi airport.

Motarsa tana fita, wani da yake tsaye a estate Win gidan ya Wauki waya ya ce, "Motar Rehaan ta fito, kun tabbatar an kwance burkin motar?."

Ya yi shiru alamun ana basa amsa sannan ya ce, "Dakyau, bana so ransa ko lafiya sa ta tsira a wannan lokaci, a tabbatar da ya rasa Waya daga cikin waWannan."

Ya kashe wayar ya yi shiru yana kallon indai motar Rehaan ta bi. In ba mutuwa Rehaan ya yi hankalin sa bazai taSa kwanciya ba.

? ? Rehaan basu yi nisa ba ya ji an tsayar da motar, ya buWe ido ya ce, "ya dai?."

Shams da yake gaban motar ya ce, "Sir burkin naji yana rawa, shiyasa aka samu aka tsaya a nan.."

"Kamar ya kenan?."

"Bamu san ya aka yi hakan ya faru ba, amma yanzu zan yi waya a kawo mota."


"Alright" ya faWa a hankali yana lunshe idonsa.
Ba jimawa aka kawo wata motar, suka canja mota suka wuce airport tsaye.

Washe gari da safe Islaha da wuri ta shirya dan tana so taje wajan aiki, bayan ta shirya tana falo ta gama shan tea Saheer ya shigo da sallama.

Islaha ta amsa sallamar tana kallonsa, sannan ta ce, "ina kwana Hamma."

Saheer da?yar ya ce, "Lafiya. Ina Mama?."

"Bata fito ba."


"In ta fito ki faWa mata na tafi wajan Baffa."


"To. Amma wajen aiki zan tafi, nima babu lallai mu haWu."

"Okay" ya furta yana ya fita.

Haka ta gama abinda zata yi a sanyaye, ta fito tana kallon ?ofar gidan cikin tunani. Motar da suka shiga jiya ta gani, bata ?arasa wajan motar ba, sai da ta kira Safeera take faWa mata ita ta wuce.

Horn ta ji yana yi mata, ta kalli wajan kafin ta ?arasa a hankali dan ta san shine ta buWe ta shiga suka tafi. Ta kalle sa taga ya haWe rai kamar ba Hammanta mai yawan murmushi ba, ko kallon inda take ba yayi balle ta saka ran zai yi mata magana.

"Kina fama da kanki ki ka saka wannan turaren mai ?arfi, kin kyauta."? Ta kalle sa jin abinda ya ce sai ta yi shiru bata ce komai ba.

Sai da suka tsaya Islaha ta kalle shi taga glass Win gabansa yake kallo alamun ta fita babu abinda zai ce mata. Islaha a sanyaye ta ce, "Hamma!."

Ya yi mata banza kamar bai ji ba, cikin shagwaSa ta ce, "Hamma ka yi ha?uri, ka daina fushi dani don Allah." Tsaki taji ya yi bai ce komai ba, ta sake kallonsa ta ce, "Hamma don Allah."

Ya kalle ta ya ce, "bani da mahimmanci a rayuwarki ne kawai, dan haka ki fita ki bani waje."

"ka yi ha?uri" ta faWa hawaye yana sakko mata.

Bata son fushin Hamma ko kaWan, matu?ar ya yi fushi da ita to tabbas ta Sata masa rai da yawa, baya iya fushi da ita sai abin ya ?ure sosai.

Jin tana kuka sai ya sauke ajiyar zuciya, ya Wan tausasa murya ya ce, "in baki faWa min dalilin ki na son a kashe case Win nan ba bazan saurare ki ba, Islaha."

Ta goge hawayenta bata ce komai ba, ya kalle ta ya ce, "za ki jefa min zargi a zuciyata, zan ga kamar da gagan ki ka gudu daman ba sace ki aka yi ba. ShaiWan yana faWa min abubuwa marasa kyau akan hakan, na ?i bada damar da zan Warsa zargina a kan ki, amma in ki ka cigaba da Soye Soyen nan zan zarge ki Islaha!."

"Wallahi Hamma ban san komai a kai ba, ban san shi ba balle na haWa baki dashi ya sace ni, kuma ni ban aikata komai ba."

"Nima ban ce kin aikata wani abu ba, amma in kika cigaba da Soye Soyen nan zuciyata zata amince kin yi, ko meye ya Warsu a raina zan amince kin aikata!."

"Hamma!."

"Islaha."

"Hammana!."

"Islahaaa!" Ya faWa yana jan sunan yana kallonta.

Ta girgiza kai tana langwaSar da kai, cikin sanyi ta ce, "Hammana!."

Ya zuba mata ido na wani lokaci kafin ya ce, "Matar Hamma."

Ta lumshe ido hawaye yana cigaba da zuba daga idonta. Ta buWe ido ta kalle shi ta ga shima ita yake kallo, ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ka bani dukkan yardar ka, wallahi bazan taSa cin amanar ka ba."

Ya taSe baki yace, "kina san dawo a dawo bara bana kenan, indai baki faWa min dalilin ki ba bazan karSa. Zuciyata zata faWa min akwai wani abu mara kyau da ki ke Soyewa."


"Ina da dalili."

"Am all ears."

"Ka yi min al?awari zaka saurare ni."

"Ina jin ki."

"Zan faWa maka dalilina, amma ka bani kwana biyu don Allah."

Ya zuba mata idanu yana kallonta cikin mamaki, da gaske zuciyarsa ta fara Warsa masa abubuwa marasa kyau, da ya yi tunanin raping Winta suka yi, amma yadda take Soyewa sai ya ga ba lamarin rape bane, abin ya girmi haka a tunaninsa.

Saheer zai yi magana ta tare shi da sauri ta ce, "don Allah ka yi min wannan alfarmar."

Ya Waga kai ya ce, "Allah ya kaimu. Jeki wajan aikinki." Ta ?i fita, sai da ta tabbatar ya daina fushin sannan ta shiga.

Tun daga gate take gaisawa da mutane har ciki, haka aka cika table Winta ana gaisawa tana murmushi tana amsa gaisuwa da addu'a.

Bayan mutanen sun watse Safeera da Muslim suks ?araso wajan ta, Muslim ya ce, "Islaha ashe mai keken nan ?o?arin watsa miki acid ya yi?."

Ta Waga kai alamun eh, Muslim ya ce, "amma bashi da kirki, nan yazo ya same ni fa ya ce yaga lokacin da aka sace ki, yana so ya ba da shaida ashe shima mugu ne."

Safeera ta ce, "mugun gaske ma kam."

"Kuma wallahi ya gudu, an nemesa an rasa."

Ita dai bata ce komai ba sai kiran Zainab da ya shigo wayar ta, ta Wauka take sanar da ita su haWu a asibiti dan fita zata yi bata da aiki. Bata jima sosai ba suka fita ita da Safeera zuwa asibiti wajan Baffa.

A can suka tarar da Umman Safeera ita da Mama suna tattaunawa akan abinda ya shafe su. Suka gaisa da Islaha daga nan suka wuce wajan Baffa dan ance sun farka.

Da suka shiga Baffa idonsa biyu amma yana cikin raWaWi, dan a lokacin yankan yake yi masa ciwo sosai, kana ganinsa ka san yana cikin yanayi na zafi da ciwo. Dan haka basu jima a ciki ba, suka koma wajan Kawu suka tarar yana bacci.

Kiran Safeera aka yi a waya ta tsaya tana amsawa, ita kuma ta koma wajan su Umma da Mama. Daga can gefe ta hangosu a tsaye Umma tana mi?awa Mama wata ba?ar leda, sai ta matsa kusa dasu dan ta ji me za a ce, bata sani ba ko akan tafiyar Umma ne, tana so ta ji dan ta sanar da Safeera su yiwa tufkar hanci.

Umma ta ce, "fasko ne kamar yadda ki ka ce, gashi nan nayi komai, visa za a buga min na tafi."

Mama ta karSa ta ce, "kin tabbatar zaki iya? Kar sai na yi asarar kuWi an yi visa da ticket ki ce baza ki je ba."

"Mai zai hana ni zuwa? Wallahi zuwa babu fashi sai dai in bani da rai."

Mama ta saka a aljihun doguwar roga ta ce, "tunda akwai gidan aikin a ?asa ko yaushe za a iya cewa ki fito. Visa ba wahala take yi yanzu ba, dan haka ki zama cikin shiri. Na karanta miki tsarin ko?."

"Na haddace tsaf a kaina."

"Kar a same ki da saSa wani abun. Gidan aikin ki duk wata a kuWin najeria naira rubu Wari biyar za a baki. ?ari uku ta kamfani Wari biyu naki."

"na amince da wannan."

Mama ta girgiza kai ta ce, "tare zaku tafi da Labiba, yadda Babanta yake kwance a nan tsaf zata je ta samo mana abin arzu?i. Itama ta yi komai, lokaci kawai ake jira."

Umma ta ce, "godiya mu ke woman leader."


"Ko kefa, yanzu ki ka fito a mace, da kun zauna namiji yana sarrafa ku bayan ba wata tsiyar ku ke samu ba a wajensa ba?. ?arshen cika bakin namiji fa saki ne, to sai meye dan ya sake ki? Mtsww! A kan ki aka fara saki ko a kan ki za a gama?."

Mama hango ?awarta na ?arasowa, sai ta kalli Umma ta ce, "Jeki kawai Maimuna, za mu yi magana kawai." Umma ta fita a lokacin ta ?araso wajan.

Tana zuwa ta ce, "komai ya kankama kenan ko?."

Mama ta ce, "an sanu biyu, Labiba da babar Safeera."

"Na taSa ki da alkhairi, an kuma samun wani gidan a Jeddah. Albashinsa har ya fi na gidan da Labiba zata je wallahi. Dan a wata Waya miliyan Waya da rabi zasu bayar, ban da alkhairin yau da kullum."

Mama ta zaro ido ta ce, "wayyo Allah, anya bani zan shirya mu tafi ba?."

Ta girgiza kai ta ce, "yarinya suke nema, mai jin turanci, mara ?iba, mai son aiki. In zai yu a samu? mai kyau, ?ar gayu dan basa son ?azama."

Mama cike da zumuWi ta ce, "a ina zamu samu wacce zamu tura musu?."

"Hanan baza ta je ba?."

"Bana tunanin Hanan zata je, dan tana samu a nan sosai. Baza su tafi su biyu ba, saboda babansu."


"Kin ga da ?ar rikon nan ta ki zata yarda itace daidai da abinda aka lissafa, yadda take da shegen iyayin nan da wuri zata yi saurin shiga."

Mama ta taSe baki ta ce, "kar ma ki Sata min rai, mu koma ciki mu cigaba da magana."

Islaha ganin suna tahowa tayi saurin komwa baya, ta yi shiru tana lisssafi a zuciyar ta. Miliyan Waya da rabi za a bayar duk wata, hakan yana nufin zata iya tara kuWin wanda ta aro a ?asa da shekara Waya.

Ta yi ajiyar zuciya tana tunani, ta Wan sauke numfashi cikin tunanin abinda ya kamata ta yi, dan gaskiya sai ta biya kuWin nan hankalin ta zai kwanta. Ya kamata ta yi tunanin da ya kamata, indai zata samu kuWi ta sauke nauyin bashi ko meye zata yi.

Dafata ta ji anyi daga baya, ta juya a firgice tana kallon wanda yake tsaye a bayan ta.....
[6/25, 11:14/ AM] KRBBK: RDB2P20
Nana Haleema

Tana juyawa suka haWa ido da Zainab, Islaha ta Wan sauke numfashi cikin tsoro ta ce, "kin bani tsoro Zainab." Zainab ta bita da kallo, kafin ta rungume ta cikin kewar ta ta ce, "na yi kewar rashin ki sosai Adda Islaha, na yi kewar ki."

Islaha ta ri?e hannunta tana murmushi ta ce, "nima na yi kewar ki Zainab. Ya na ganki haka, akwai matsala ne?."

Zainab ta Wan yi shiru kafin ta ce, "Adda Islaha Mama ce ta saka a sace ki, na ji da kunnena tana waya tana cewa a tabbatar an Wauke ki."

Islaha ta ja hannunta suka zauna a inda babu jama'a sosai, ta kalle ta cikin nutsuwa ta ce, "ban gane ba, yi min bayani yadda ya kamata."

Zainab ta ce, "Ina nufin Mama ce ta saka a sace ki, saboda kina saka mata ido akan abubuwan da take aikatawa."

Islaha ta yi shiru tana tunani cikin ruWani, kenan mutanen da suka sako ta a gaba suna da yawa, tunda ga wata maganar ma ta sake Sullowa daga inda bata yi tunani ba. Bata nunawa Zainab firgici akan haka ba sai ta ce, "faWa min damuwar ki Zainab."

Zainab ta sauke nunfashi ta ce, "Zaman gidan ya yi min zafi Adda, na gaji da zaman gidan wallahi. Abubuwan da ban yi zato ba suna ta faruwa, na kasa tsallake wasu abubuwan."

"Me ya faru?."

"Adda gabaWaya kowa na gidan da kowa na gidan canjawa yake yi, ma'aikatan gidan Mama ta siye su, kowa a ?ar?ashin ta yake, shiyasa ba a taSa jin Sarnar da take cikinsa a bakin kowa ba. Da zarar maganar kuWi ta shiga shikenan sai a canja.."

"Akwai wata mata da ta takurawa Mama akan a kaini gidanta, kullum sai an takura min da maganar matar. Wai in na je za a canja min makaranta, za a yi kaza da kaza. Ni na gaji, da kin yi aure gidanki zan dawo da zama kawai, gabaWaya zaman gidan ya fita daga raina."

Islaha ta Wan yi shiru sannan ta sauke numfashi ta ce, "in aka kai ki gidan me zaki yi a can?."

"Nima ban sani ba, amma kamar ba abin arzu?i zan aikata ba, dan matar kwata-kwata bata kwantan min a raina ba."

Ta girgiza kai ta ce, "kina ji, ki kwantar da hankali ki, babu abinda zai same ki sai alkhairi. Ina tare dake a ko yaushe a ko ina. Ki nutsu ki ji abinda zan faWa miki."

Zainab ta Waga kai Islaha ta ce, "kar kuWi ko wani abu ya ruWe ki kamar Hafsa, ki cigaba da bijirewa, duk abinda za a ce miki kae ki yarda, ki nuna kw bakya ra'ayi. In aka takura ki amince ki je gidan, da zarar an tafi kai ki ki yi min waya ki faWa min inda aka kai ki. Ni kuma a wannan lokacin zan haWa hujja da nake son haWawa akan su Mama da ma'aikatan gidan, in abin nan ya tabbata wallahi sai na yaWa ta a ko ina, sai gwamnati ta san abinda take aikatawa da sunan ri?e marayu."

Zainab ta share hawaye ta ce, "in na bisu babu matsala?."

"Babu komai, Amma kafin ki tafin ki tabbatar kin sanar dani, yadda zan shirya komai na biyo sawun ki."

"Zan yi duk abinda ki ka ce Adda."

"Yauwa Zainab. Allah yana tare dake, bazai taSa bari ki wula?anta ba in sha Allah."

"Allah yasa."

"Amin."

"Adda kayana duk sun yi min kaWan, bani da kayan sakawa sosai."

Islaaha ta dafa ta, tasan yadda ake ?arancin kaya a gidan marayu, ta san yadda kayan sakawa suke yankewa, ta san yadda yaran da basu kai matakin sana'a ba suke rasa kayan sakawa. Wani lokacin sai masu ziyara sun zo sun kawo kaya, a nan ne za a zaSi wanda bashi da kayan sosai a bashi ya rage ko ya ?ara. Ita kanta ta shiga irin wannan yanayin, har ta kai ta kawo tana cire kaya ta wanke da daddare ta shanya,washe gari ta kuma mayarwa jikinta.

_(?an uwa ga wanda Allah ya bawa dama, in an haWa kayan sakawa na bayarwa, a dinga tunawa da yaran da suka tashi a gidan marayu. Kayan yara ko na manya, na maza ko na mata, a dinga taimkawa ba a san inda za a dace ba. Allah ya sa mu dace amin.)_

Islaha ta ce, "Akwai kayan da zan baki, sannan akwai kuWin da zan tura miki, ki shiga kasuwa ki siyi ?ananun atamfofi ki bayar a gidan a Winka miki. Ba su Kamila suna Winki ba?."

"Suna yi Adda."

"To ki bayar a Winka miki, nawa da zan baki ki basu su rage miki. Zan tambayi Safeera ma in tana dasu ta sake haWo miki, indai ina da rai babu abinda zaki nema ki rasa Zainab."

Ta yi murmushi ta ce, "Allah ya bar min ke Adda Islaha, Allah ya baki miji na gari, mai kuWi wanda zai Wauke ni na koma gidansa."

Ta yi murmushi ta ce, "Amin Zeey. Ina auren Hamma zan Wauko ki, kin gama zaman gidan nan in sha Allah." Zainab ta yi murmushi, suka cigaba da hirar gidan, har Zainab ta yi mata sallama ta tafi.

Bayan tafiyar Zainab Islaha ta yi shiru tana tunani, abubuwa uku suna yi mata yawo a cikin kanta, abubuwa uku suna kai kawo a tsakiyar ?wa?wal?war ta. Zainab, Mama da ta da ta saka a sace ta, uwa uba kuWin mutumin da ta Wauko, dan ya fi komai Waga mata hankali a halin da ake ciki.

Ta yi ajiyar zuciya cikin nauyin ?irji, a lokacin Safeera ta ?araso ta zauna, suka Wan cigaba da hira duk da hankalin Islaha baya tare da ita ko kaWan, wani abun daban take tunani.

" " " " " "

*JEDDAH, SAUDI ARBIA*
*AL HAMRA, CORNICHE RESIDENCES.*

Unguwa ce mai kyau da tsari, unguwa ce mai Waukar hankali tun daga kallon farko zaka san ko a cikin ?asar saudia ba ?ananun mutane ne suke zaune a cikin ta ba. Unguwa ce mai cike da tsafta, da tsaro na musamman.

Ko ina na kan titin unguwar al hamra cike yake da cameras saboda tsaro, unguwa ce da take kusaa da ?aton tekun Corniches, babban ocean da yake Waya daga cikin manya manyan ruwan da ake ji dasu a garin Jeddah. Unguwa ce da take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login