Showing 81001 words to 84000 words out of 221574 words

Chapter 28 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

129

Ta sauke ajiyar zuciya ta kira lambar Safeera, wayar ta shiga dan ta saka kati sosai a layinta.

Wayar tana ta yi ba a Wauka ba, ta sauke ajiyar zuciya ta rasa wanda zata kira. Kallon lambar Baba take yi abinda ya faru yana dawo mata a ranta, ta rufe ido ta buWe ta nemo, dan baza ta iya kiransa ba, sai ta kira lambar Atika. Bata jima ringing ba Atika ta Wauka, Umma ta ce, "Atika kina jina."

Daga can Sangaren Atika ta ce, "Ina jinki, Hajiya Maimuna mutanen makka da madina. Ya ki ke?."

Umma ta sauke numfashi ta ce, "lafiya lau, kowa lafiya?."

"Lafiya ?alau. Ya aka yi wayar ta shigo? Na ji ance fa layin nigeria ba ya yi."

"Eh da yake na saka kati sosai a wayar, kema kuma yanzu zasu Wauki katin wayar ki."


"Allah sarki. Ai da kati sosai a wayar tawa,
Wazu na saka na dubu uku shiyasa ta shigo."

"Na kira Safeera bata Wauka ba, ban yi magana dasu ba tunda nazo. Don Allah ki duba min su."

Atika ta ce, "kar ki damu zan duba miki su in Allah ya yarda. Da fatan komai lafiya dai ko? Aiki ya samu ko?."

Umma ta Wan taSe baki cikin wani irin yanayi ta ce, "Aiki ya samu kan Atika, ina kan yin aikin ma yanzu."

"haka muke fata. Kin shiga masallacin annabi?."

"Ban je ba, amma zan je in sha Allah."

"Ayi mana addu'a, Allah ya biya mana bu?atun mu na alkairi."

"Amin. Don Allah ki duba min su, in kin same su ki kira ni."

"Kar ki damu ?awata, ki Wauka kamar kina Nigeria, wallahi zan kula miki dasu sosai, zan yi komai dan na samar musu da nutsuwa."

Sai hankalin Umma ya kwanta, ta yi murmushin jin daWi ta ce, "na gode sosai." Daga haka suka yi ssllama ta kashe wayar.

Tana son kiran ?an uwanta na Katsina amma tana jin shakkar aikata hakan, dan ta san bata shuka abin kirki ba, babu wanda zata iya tunkara a halin yanzu.

Ta yi ajiyar zuciya, ta mi?e tsaye da?yar tunawa da kayan wanke-wanken da ta bari a kitchen, ko zasu shekara ita zata wanke babu abinda zai ragu sai ma ya ?aru. Ta shiga banWaki, bata jima ba ta fito tana goge ruwan fuskar ta.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Hasbuhallahu wa'imal wakil! Na shiga uku Maimuna!"

Ta faWa a tare cikin tsananin firgici da tashin hankali wanda bata taSa tsintar kanta a ciki ba.

A guje ta koma banWakin tana sauke numfashi ?irjinta yana up and down, ta rufe ta buWe cikin firgici, ta Wan daki fuskar ta ta tabbatar ba mafarki take yi ba, da gaske ne ba wasa ba.

Bata san ta fara hawaye ba sai Wuminsu ta ji akan fuskar ta, tashin hankalin da ta gani dole ya saka ta zubar da hawayen da bata shirya zuwan su ba.

Tunda take a duniya bata taSa ganin namiji tsaye a haka a gabanta ba, ko mijinta da suka kwashe shekaru sama da ashirin da wani abun bata taSa iya tsayawa ta kalle sa muraran babu suttura, haihuwar uwa da uba ba, saboda kunya mai tsanani. Yau ga wani wanda ba muharamin ta ba, tsaye a gabanta babu suttura ko kaWan a jikinsa yana yi mata murmushi, yana nuna mata jikintsa ta sigar iskanci.=??

Ta dafe ?irji dan har lokacin ?irjinta bai daina bugawa, ta jingina da ?ofa hawaye yana cigaba da sauka daga idanunta cikin tsananin Waci da tashin hankali. Da tana da damar goge abinda ta gani daga ?wa?walwar ta da ta goge, da ta rufe ido shi take kallo a idanunta.

Tana jinsa a kusa da ?ofar banWakin yana bugawa yana yi mata magana cikin yarensa, bata jin me yake faWa amma ta san ba kalaman kirki yake faWa ba.

Umma hawayenta ya ?aru, ta rufe bakinta da hannunta cikin wani irin yanayi da tashin hankali. Bata san ta zame ta zauna a wajan ba, bata san lokacin da ta Wauka a wajan ba ta dai san ta jima a wajen a zaune tana kuka.

Ni dai Umma ta bani dariya>?#?>?#?

Nana Haleema
' [7/3, 2:04/ PM] KRBBK: RDB2P35
Nana Haleema

Sai da ta gaji da kanta sannan ta mi?e a sanyaye ta buWe ?ofar, ta fito tana le?owa kamar munafuka, ganin ba ya Wakin ya saka ta yi ajiyar zuciya tana takowa a hankali ta fito tsakiyar Wakin.

Har lokacin abinda ta gani bai daina yi mata gizo ba, har lokacin abinda ta gani da idanunta bai daina yi mata yawo a kanta ba. Ta rufe ido ta buWe tana kallon daidai inda ta gan shi a tsaye da abinda yake nuna mata.

Tsoron gidan ya mamaye mata zuciya, a haka ta buWe ?ofar ta fito tana le?e cikin ruWewa. A sanyaye take takawa? ta koma kitchen ta fara wanke kwanukan a tsorace.

?arar rufe ?ofar kitchen Win ta ji, ta waigo a hankali ta gansa a yanayi irin na Wazu, yanayin yanzu har ya fi na Wazu muni, kuma yana tsaye ?yam?yana kallon ta.

Umma ta ?walla ?ara ta gudu daga wajan tana kuka, ya biyo ta yana kallon ta yana murmushi yana yi mata magana cikin larabci.

?ar tsere suka shiga yi a kitchen Win, tana gudu yana binta yana maganar da bata san me yake faWa ba, gashi babu wata suttura da ta suturta jikinsa, ita kuma firgici da tashin hankalinta ninkuwa suke yi.

Ba ta yi tsammani ta ji ya cafko hannunta, ya haWa ta da jikinsa yana cigaba da yi mata murmushi kamar zai yi mata kiss.

Umma ta yi dogon salati ta gigice, ta ja jikinta da ?arfi ta fizge, ta fita daga kitchen Win a guje ta afka Waki ta rufe ?ofar tana kuka mai sauti.

Jikinta karkarwa yake yi, ta rasa abinda ya kamata ta yi sai kuka da take yi kamar ranta zai bar gangar jikinta.

Lokaci Waya zazzaSi ya rufe ta ruf, ta kashe ac ta hau kan gado ta rufe jikinta tana cigaba da zubar hawaye.

Ta kasa baccin kuma ta kasa mantawa da abinda ya faru, jikinta ya cigaba da karkarwa na tsahon lokaci tana a haka. Tana ji ana kiran sallah amma baza ta iya tashi ba, a haka har aka idar ta fara jiyo hayaniyar yaran gidan alamun sun dawo.

Dukan ?ofar ake yi da ?arfi tana jin muryar masifaffaiyar matar gidan tana magana ita dai ta kasa motsawa, tana cikin bargo zazzaSi ya rufar mata a jikinta.

Can anjima ta ji muryar Shafa tana cewa, "Maimuna taso ki buWe, Shafa ce."

Jin hakan ya saka Umma ta diro daga gadon ta zo ta buWe cikin rawar jiki. Hajiya Shafa tana shigowa Umma ta kulle ?ofa a firgice.

Hajiya Shafa ta bita da kallo ta ce, "Lafiya? Me ya same ki ki ke wannan rawar jikin?."

Umma bata ce komai ba saboda tashin hankali, Hajiya Shafa ta ce, "wai meye haka ki ke yi? Kin kama kin rufe ?ofa kamar gidan ki, suna ta buga miki ?ofa kin ?i buWewa, shine suka je suka nemo ni aka ce na zo nayi miki magana. Kar ki haifar mana da matsala fa, kar ki aikata abinda za a Waure ki a ?asar nan wallahi."

Umma ta kasa cewa komai sai rawar jiki kawai take yi, ta kasa buWe baki ta ce komai. Hajiya Shafa cikin tsawa ta ce, "ki yi magana mana, meye wannan na rawar jikin?."

Umma tana jan numfashi ta ce, "ni dai a canja min gidan aiki, bana son gidan nan, don girman Allah a canja min gida ko a mayar dani Nigeria."

Ta bita da kallo ta ce, "ban gane ba, ban gane a canja miki waje ba. Meye ya faru?."

Umma ta ce, "nidai bazan iya ba, a canja min gida don girman Allah, bazan iya zama a gidan nan ba, wallahi bazan iya ba. Gida zan tafi, bazan iya zama a nan ba."

Hajiya Shafa ta bi Umma da harara ta ce, "to uban meye ya saka baza ki zauna ba? Ki yi min bayani yadda zan fahimta, meye ya faru?."


"Mai gidan nan nake gani tsirara yana shigowa, har bina kitchen yake yi babu komai a jikinsa, yana jawo ni jikinsa yana taSa ?irjina, yana ?o?arin sumbatata. Ni dai bazan iya ba, a canja mim waje, bazan iya zama a nan ba wallahi" ta faWa jikinta yana rawa, jikinta yana karkarwa.

Hajiya Shafa ta ja tsaki ta ce, "wani abun ya yi miki?."

"Na faWa miki ya taSa min jiki."

"Ina nufin komai ya faru?."

"Allah ya kiyaye, Allah ya yi min tsari da wannan saSon."

Hajiya Shafa ta ce, "Tunda komai bai faru ba meye na Waga hankali? Dan yana shigowa tsirara ai ba wani abun ya yi miki ba, jikinsa ne ko?."

Umma ta kalle ta ta ce, "babu komai a jikinsa fa, sannan dambe mu ka dinga yi dashi, yana bina ina guduwa."

Hajiya Shafa ya ce, "sai me? Ai bai yi miki komai ba ko?."

Umma ta yi sak tana kallonta cikin sabon yanayi, jikinta yana yin sanyi ta kasa cewa komai.

Hajiya Shafa ta ce, "bana son ?auyanci Maimuna, ki daina wannan shirmen kamar wata ?aramar yarinya. Yau ki ka saba ganin namiji babu kaya ko me?."

Umma dai ta kasa magana sai kallo kawai take binta dashi, dan ta kulle mata baki, bakin ya rufe ruf ta kasa magana.

Hajiya Shafa ta ja tsaki ta ce, "ki nutsu, daga yin kwana Waya har ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????sun fara yi min complain a kan ki, ki nutsu in ba haka ba zaki kore ki wallahi."

Umma ta ce, "ni dama zasu kore ni Win."

"A kore ki Win mana meye ya dame ni? In aka kore ki sai ki san inda zaki zauna, nan ba Nigeria bace da zaki je ki kama hayar gida kara zube. Sannan kuWin da aka kashe miki aka kawo ki sai kin biya, wallahi ko sisi baza a yafe miki ba, in ba haka ba hukuma ta raba ku. Kuma in ki ka bar gidan nan ki ka aikata wani abu mara kyau aka kama ki wallahi baza ki tsira ba. In zaki nutsu ki nutsu, nan ba a Nigeria ki ke ba, uban ki zasu ci wallahi."

Umma ta dafe kai muryar ta tana rawa ta ce, "yanzu haka zan cigaba da zama? Ga aiki kamar jaka, daga jiya zuwa yau aikin da nayi ban san adadinsa ba. Ni dama a iya aiki abin zai tsaya da sau?i, zan jure na cigaba da yi tunda ni na kawo kaina. Amma wannan lamari ya girmi aikin da? wahalar sa, namiji magidanci kamar wannan yana yawo a gabana babu kaya ai dole hankalina ya tashi. In ya faWo min cikin dare fa?."


"Kema sai ki faWa masa, sai meye?Ai ba yau ki ka fara haWuwa da namiji ba."

Umma ta zuba mata ido kawai bata ce komai ba, dan har wani zafi take ji a jikinta, zazzaSin da ya rufe ta gabaWaya ya sauka saboda tashin hankali. Har gumi take ji yana tsatstsafo mata, maganar Hajiya Shafa ta fi Waga mata hankali.


Hajiya Shafa ta ce, "ki dakatar da wannan shirmen, ki saki jiki ki yi aiki. Tunda ki ka zo baza ki samu ?anci ba sai kin gama biyan bashin kuWin da yake kan ki, yanzu a ?ar?ashin kamfani ki ke, dole ki nutsu. Zan kira Alhaji Musan, zan faWa masa ya yiwa waWanda suka yi miki hanya magana, bazan Wauki wannan shirmen ba wallahi, na gaji da kawo ?ara."

Umma dai bata ce komai ba dan an kulle nata baki. Hajiya Shafa yi tsaki ta ce, "ki fito ki yi musu aiki, ki daina wanna Wari Warin, ba jin yaren ki suke yi ba. In kina Warare jiki zasu zargi baki da gaskiya, in suka yi miki wani abun ke ki ka jiyo" ta faWa tana yin gaba.

Umma dai tana tsaye kamar an dasa ta a wajan cikin tashin hankali, Hajiya Shafa ta juyo ta ce, "ki zo mu je."

Umma ta tako a hankali ta biyo bayanta cikin yanayi na ruWewa da tashin hankali.

" " " " " " " "

Mamy tana zaune tana waya da yan ?asar su, bayan ta gama wayar Abba ya kira ta ya ce ta zo yana neman ta. Mamy tq mi?e ta nufi apartment Winsa ta same sa a zaune.

Ta ?arasa ta zauna ta ce, "gani Abba."

Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Daada ce."

Mamy ta Wan murmusa ta ce, "akan maganar Rehaan ko?."

Ya Waga kai ya ce, "ta ya ki ka canka?."

Ta yi murmushi ta ce, "indai har aka ce Daada to tabbas na san maganar Rehaan ce. Me ya faru?."

Ya yi murmushi sannan ya ce, "akan auren sa da yarinyar can ne, ta matsa a kai sosai ma kuwa. Dan yau ta ce min ko ta mutu na tabbatar ya auri yarinyar, hakan shine zai saka ta kwanta a kabarinta lafiya."

Mamy ta ce, "ikon Allah! Wai a ina ta san yarinyar nan haka?."

Ya girgiza kai ya ce, "Ke dai ki bar girma Nadira, Daada ta girma shekaru sun ja, shiyasa take fama da rigima kala kala."

Mamy ta ce, "to yanzu kun yi magana da iyayen yarinyar ne?."


"Na faWa min ance mai ri?onta yana kwance a asibiti, da wa zan yi magana?."

"To sai ka faWa mata hakan ko?."


"Na faWa mata, ta sake maimaita min ko bata da rai na tabbatar an yi auren nan. Tana son yarinyar, kuma ita take so Rehaan ya aura. Ko yau ta mutu, gobe a Waura musu aure."

Mamy ta yi murmushi ta ce, "To me zamu ce tunda Daada ce ta yanke? Sai mu yi fatan Allah ya sa ta gari ce."

Abba ya ce, "Amin ya rabbi. Zan saka a yi min bincike mai ?arfi a kanta.

Mamy ta ce, "ni wallahi Ikram nake yi masa sha'awar aure, yarinyar tana da hankali sosai, kuma ni na lura kamar itama tana son shi."

Abba ya yi dariya ya ce, "za a ki saka a maimaita Juwairiyya da Jafar kenan. Ke kin san yadda aka kai ruwa rana akan auren nan, yanzu in aka sako maganar Ikram da Rehaan ai babu zaman lafiya."

Mamu ta ce, "Inda zai amince Win da sau?i, yadda ta amince dana Riyya shima zata amince."

Ya yi murmushi ya ce, "indai har Rehaan Win zai amince da Ikram Win sai ya aure su duka, Ikram itace tamu, mun san halinta ta san namu. Ita kuwa wannan bamu san daga ina take ba."

Mamy ta Wan taSe baki tana jin takaici a ranta ta ce, "ni tun kafin tazo ma bana sonta, sam bata yi min."

Abba ya Wan buWe ido ya ce, "akan me? Yarinyar da baki santa ba zaki ce baki so bata yi yi miki ba?."

Ta yi shiru bata ce komai ba, Abba ya girgiza kai ya ce, "Saboda Rehaan baya so ko?."

Mamy ta kalle sa ya ce, "Na san halin ki ai, duk abinda yake so shi ki ke so, abinda baya so kema bakya so. Kefa koda kina son abu, da ya kushe sai ya fita daga ranki. In kuma bakya so, shi kuma yana so sai ki so kema."

Ta Wan yi murmushi dan tasan haka Win ne, ko me Rehaan yake so tana so, in baya so bata so.

Abba ya ce, "yanzu dai kin san dole nayi abinda mahaifiyata take so ko?."

Ta girgiza kai ta ce, "gaskiya ne."

"To ki ba da haWin kai akan auren nan, na fahimci Daada da gaske take, babu wasa ko rikicin tsufa. Ki yi ha?uri."

Mamy ta girgiza kai bata ce komai ba, amma ko kusa bata son auren nan, haka kawai yarinyar bata yi mata ba, bata santa bata taSa ganinta ba, amma tana jin ?inta a ranta, saboda tana ganin ta silarta za a yiwa Wan da ta fi so a duniya dole, bata taSa yiwa Wanta dole akan komai ba, amma akanta za a yi masa dole. Wannan dalilin ne ya saka Islaha bata yi mata ba.

" " " " " " " "

Mama tana tsaye a Waki ri?e da waya ta ce, "ina jin ki, ya ake ciki yanzu?."

Daga wayar aka ce, "an tabbatar min da yarinyar nan ta tafi ?asar waje aiki, kin ga tayi daidai da wacce mu ke nema."

"Aikin gwamnati ko na kamfani?."

"Aikin gidan turwa mana. Aikin da ake lalata rayuwar mata, shi nake nufi."

Mama ta buWe ido ta ce, "da gaske ki ke?."

"Wallahi da gaske nake. An tabbatar min da yarinyar bata ji, tana Wan taSa abubuwan zamani. Dan gidan da take zaune ma babu tarbiyya, ana yiwa mai ri?onta take da woman leader. ?a?anta ne jarinta, sune suke fita su kwana a waje su kawo mata kuWi, kuma itama a gidan take."

Mama ta ?yal?yale da dariya ta ce, "ina zuwa."

Ta faWa tana kashe wayar, bata Sata lokaci ba ta kira lambar malam, suna gaisawa ta ce, "Malam akan batun auren Rehaan da yarinyar nan, ina so a yi aikin da ko ba yaso sai an yi auren nan ta ?arfi da yaji."

Malam ya ce, "kar ki samu damuwa. Ki Wauka kamar an yi wannan aikin an gama, in kin ga ya tsallake auren to zai iya tsallake mutuwarsa."

DaWi ya mamaye zuciyar Mama, cikim farin ciki da jin daWi ta ce, "yauwa Malam, yarinyar tayi daidai da ra'ayina, tayi daidai da wacce nake nema. A taimaka ayi aikin nan Malam, in ba a yi auren ba hankalina bazai taSa kwanciya ba."

Malam ya ce, "kar ki damu Hajiya Saddi?a, wannan ?aramin abu ne, kawai ki Wauka an gama. Dan wallahi sai an yi auren nan, auren nan babu fashi."

Mama ta ce, "zan turo da abin sakada a rabawa almajirai, sannan akwai naka ka yi cefane." Daga haka suka yi sallama ta kashe wayar.

Mama cikin farin ciki ta ce, "dakyau! Kai wannan lamari ya yi min daWi, bana so Rehaan ya auri mace ta gari domin hakan ma amfaninmu ne. Dole na tabbatar da auren nan ya yu, ko koda zai mutu akan ba ya so sai dai ya mutu, amma auren nan kamar an yi sa an gama!!" ta faWa cikin nishaWi, dan ita kaWai ta san amfanin da hakan zai yi mata.

Mu je zuwa. =؃? [7/3, 2:05/ PM] KRBBK: RDB2P36
Nana Haleema.

Kamar yadda Umma ta faWawa Atika bata yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login