Showing 15001 words to 18000 words out of 221574 words

Chapter 6 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

122

labarin waye Rehaan, daga wannan lokacin baza ki sake cewa waye ni ba. Babu inda zaki je sai na ga dama, kuma babu wanda zai san kina nan. If i like, zan bar ki ki shekara a nan, babu abinda aka isa ayi min" ya faWa yana fita daga record Win, sai kiran Jazy ya shogo wayarsa.

Kamar bazai Wauka ba sai kuma ya Wauka, Jazy ya ce, "Ray wacce yarinya ce a guest house?."

Ray ya Wan yi tsaki ya ce, "ni bani da pravicy ne? Komai sai ka sani?."

Jafar ya ce, "ka bani amsa kawai, wacce yarinya ka sace?."

"Bai shafe ka ba."

"Ya shafe ni malam, ka faWa min ko in kira Mamy na faWa mata ka fara kawo mata gidan ka."

Ya Wan yi tsaki ya ce, "ina ruwanka da sanin wacece?."

Jazy ya ce, "ya zama dole na sani, ina so na san yaushe ka samu gut Win kawo mata gidan ma? Yaushe ka samu courage na fara aikata wannan shirmen?. Infact me ka Wauko ta ka yi da ita?."

"Ciki, ko ban kai nayi bane?."

Jazy ya yi dariya jin amsar da ya basa, duk da ya san Rehaan ba mutum ne mai dirty talks ba, tunda ya faWa ya san yana da dalilin sa. Jazy ya ce, "ka kai ka yi ciki, kana da lafiyar da a rana zaka iya yiwa mata goma ciki. Dan ka kawo ta dan ka yi mata ciki tsaf zaka iya."

Ray ya yi banza bai amsa ba, Jazy ya ce, "i'm not joking Ray. Wacece yarinyar da ka saka a ka Wauko maka?."

"Wata ce."

"me zaka yi mata?."

"ba ka ce na fara iskanci ba? Ciki zan yi mata."

"Ray ba wasa nake yi ba, ka faWa min."

"Nima ba wasa nake yi ba."

"Please."

"Kana magana kamar wani Yayana, ka yi magana a tausashe mana, ka daina Waga min murya."

"Okay my bad. Wacece?."

"She is the girl from that hotel, she is the one I told you to find for me."

Jazy ya ce, "Okay ina jin ka, itace wacce ka ke nema. Meye na Wauko ta? Me zaka yi mata?."

Rehaan ya ce, "I brought her here so she would know who I am. She always keeps asking who I am. I want her to know who Rehaan is."

"is that all? Shikenan dalilin naka?."

Ya yi masa banza bai amsa ba, Jazy ya ce, "wannan shine dalilin da zai saka ka Wauko yarinya daga gaban iyayen ta? Ka san halin da iyayenta zasu shiga saboda raahinta?."

"Ina ruwana da iyayenta? Ni abinda yake gabana kawai na sani. Ina so na tabbatar mata da ni waye, ina so ta san ina da ikon da zan yi mata duk abinda naga dama babu wanda ya isa ya hana ni."

Ya Wan dafe kai yana lumshe idanunsa ya ce, "Ina so ta san zan iya barinta over a year a nan babu abinda zai faru, ina so ta san in na kashe ta na kashe banza!....." ya ?arasa faWa cikin sanyi.

Kafin Jazy ya ce wani abu Rehaan ya ce, "Yadda take a gidan nan, in na so a ciki zan yi nata kabarinta babu wanda zai san tana ciki. Who is she? Ta san waye ni? Ni take kallo tana faWawa maganganu marasa daWi, kuma sai na zuba mata ido ina kallonta?!" Ya faWa cikin fusata, amma da yake muryar ?an gayu ce dashi in ba sanin halinsa ka yi ba baza ka taSa cewa faWa yake yi ba.

Jazy jin yadda yake faWa ya san ransa ya Saci akan abinda yarinyar ta yi masa, kuma tunda har ya Wauki mataki abin ya taSa ransa sosai.

Ya san shi mutum ne wanda zaka zage sa a gaban idonsa ma ya Wauke kai kamar bai ji ba, bai cika mayar da ?arami abu babba a wajansa ba. Yana da ha?uri da kawar da kai, duk abinda zaka yi masa sai ya ga dama zai Waga kai ya kalle ka, kawai baya so ka shiga rayuwarsa, yadda bai shiga taka ba, kaima ka ka shiga tasa.

Tunda ya ji ya fusata har ya yi hukunci ya san ta taSa masa rai, kuma ya yi mamaki sosai. Dan karo na farko kenan da wani abu ya taSa haWa sa da wata mace har ya yi mata irin wannan hukucin. Ray ba shi da saurin fushi ko kaWan, yana da ha?uri, yana da kawaici, amma in ya yi fushin sai ka gwammace bai yi ba.

Jazy ya ce, "kwantar da hankalin ka Ray, na san ta Sata maka rai, amma meye na sakawa a Wauko yarinya ?arama don Allah?. Wannan ba girmanka bane, in sunan ka ya fita a kan wannan lamarin ka san abinda zai faru ko?."

"So what? Babu wanda ya isa ya yi min wani abun, kaf danginta babu wanda zai iya ja dani. In na kashe ta na kashe banza, haka zan binne a nan, ta ko na bawa kare ya cinye namanta."

"Amma ha??inta ai yana kanka, shi kuma akwai wanda zai rama mata ko?."

Ray ya yi masa shiru bai tanka ba, dan ko me Jazy zai ce wallahi bazai bar Islaha ba sai ya ga damaX Jazy ya ce, "don Allah ka ?yale ta tayi tafiyar ta. Wannan abun ba girman ka bane wallahi, ka ?yale ta rashin sanin waye kai ne ya saka ta yi maka rashin kunya har ta ce waye kai, amma nan gaba ko kuWi aka bata akace ta yi baza ta yi ba. Please, allow her to go."

Ray ya yi tsaki ya ce, "So is that all you have to say to me? Should I hang up now?."

Jazy ya ce, "calm down Mr Ray, don't do anything that will ruin your reputation, don't smeer yourself with black paint. Don Allah, ka ?yale ta ko dan iyayenta, na tabbatar suna can gida suna nemanta. Ko Mamy in ta ji ka Wauke yarinyar mutane kawai dan ka nuna mata who you are zata yi maka faWa."

Ray ya Wan yi shiru kamar ya ji nasihar, sai ya kuma yin tsaki ya ce, "i don't have your time" yana faWa ya kashe wayar ya cillar da ita gefe yana shafa fuskarsa da hannayensa, yana ji kamar a lokacin take yi masa rashin kunya, ya yi alwashin sai yarinyar ta san waye shi kamar yadda take tambaya.

Babu wanda ya taSa kallonsa ya ce masa waye kai, a ko ina girmama shi ake yi in yaje waje, kafin ya je sunansa ya riga shi zuwa. Amma sau biyu suna haWuwa tana raina masa hankali, in ya ?yaleta ma ai bai nuna mata capacity da yake dashi a Nigeria ba. Zai nuna mata yana da ikon da zai saka a Satar da ita gabaWaya, kuma in ta Sata ta Sata kenan har abada, ko cigiyar ta baza a sake yi ba.

? ? ? ******

Sadik yana komawa asibiti bayan sallar magrib Mama da Adda Sa'ida da Labiba suka fito daga reception zuwa waje.

Adda ta ce, "Sadik ya labarin Islaha, an ganta ko an samu labarinta?."


Ya Wan yi shiru yana girgiza ka ya ce, "wallahi babu labari Adda. Kawai an samu wani ya faWa yadda abin ya faru, ya tabbatar mana da Wauke Islaha aka yi."

Adda ta ce, "innalillahi! Aka Wauke ta Sadik?."

Ya Waga kai ya ce, "tabbas, a gaban asibitin nan kaWan aka yi garkuwa da ita."

Mama jikinta y yi sanyi matu?a, ta kalle sa ta ce, "yanzu me ?an sandan suka ce?."

"Sun bamu tabbacin za a yi bincike, duk abinda yake akwai zamu ji. Yanzu muna jira mu ji ta inda za a Sullo, in an yi waya an nemi kuWin fansa to masu garkuwa da mutane ne, in ba ayi waya ba kuma wani ne ya Wauke ta bisa dalilin kansa."

Adda ta ce, "daman islaha ta tara ma?iya akan aikin jaridar nan da take yi, wata?ila ta tsayawa wani ko wata a rai."

"tabbas kuwa, dan har an kama mace Waya, wata yarinya ce da ta yi i?irarin sai ta ga bayanta."


"Ka ji ko? Kai innallahi wa'inna ilaihir raji'un!. Saheer ya sani?."


"Ya sani, mun yi dashi da gobe zai taho ma, to na ga gwamnatin ?asar ta hana kowa fita saboda matsalar tsaron da ake samu, kin ga shima an rufe dashi sai lokacin da suka buWe zai samu damar fitowa."

Labiba ta ce, "Allah ya bayyana Islaha."

Suka amsa da amin duk jikinsu ya yi sanyi, Mama da bata ?aunarta ita kanta ta ji babu daWi jin an yi garkuwa da ita, abin bai yi mata daWi ba ko kaWan.

Adda ta ce, "ya batun kuWin aikin Baffa? An dace?."

"Wallahi Satan islaha ne ya Wauke min hankali, amma in Allah ya amince za a dace, komai zai zo da sau?i in sha Allah."

Adda ta ce, "Allah ya sa. Nima zan turo maka wani abu da yake hannuna, sai a san abinda za a yi."

Ya Waga kai kawai bai ce komai ba, dan jikimn a sanyaye yake akan Satan Islaha, ganin abin yake yi kamar wasa.

? ? ? ?? ******

Kyakykyawam mari ya sauke nata akan kuncinta, Ummi ta fasa ihu ta koma jikin mahaifiyarta tana kuka sosai.

Mahaifinta ya ce, "shashasha mara hankali, tunda nake ban taSa shiga police station ba sai yau. Ke kin san furuci akan sai kin ga bayan mutum? Kin san girman kuskuren da ki ka aikata kuwa?."

Yayanta da yake tsaye ya ce, "wallahi akan wannan maganar sai ta yi zaman gidan yari."

Abba ya sake fusata matu?a ya kalle ta ya ce, "meya kai ki, waye ya aike ki furtawa wani sai kinga bayansa?."

Ummi tana kuka a jikin babarta ta ce, "kuskure ne Abba, wallahi ni ban faWa da niyar zan aikata ba."

"Yanzu sai ki fito da yarinyar, sai ki faWa mana uban da ki ka saka ya sace ta."

Ta Wago tana kuka ta ce, "wallahi Allah ni ban saka ayi mata komai ba, ban yi mata komai ba Abba. Tun daga lokacin ban sake tunawa na yi wata magana ba sai Wazu."

Abba ya ce, "?arya ki ke yi, tunda ki ka ce sai kin ga bayanta ke kika saka a sace ta, dan haka ki fito musu da yarinya."

Ta fashe da kuka ta ce, "wallahi ban saka a sace ta ba!."

Cikin faWa Yayanta ya ce, "wannan ke kika sani, kotu bata san ba ke bace tunda kin furta. An samu shaida kuma kema kin amsa da bakin ki, iya wannan ya ishi kotu tura ki zaman gidan yari."

Mamanta ta ce, "ke waye ya aike ki? Waye ya faWa miki ana wasa da irin wannan maganar?."

Ta share hawaye ta ce, "wallahi sai dai in wani ne ya yi amfani da kalamaina ya aikata, amma wallahi ni ban aikata komai ba."

Abba ya girgiza kai ya ce, "wannan ke kika sani, abinda hukuma ta sani kin fi kowa hannu a Satan yarinyar nan, kuma koda ta bayyana case Win bazai mutu ba, ko ya ya wai abun ya same ta za a ce ke ce."

Yayanta ya ce, "Abba in ta rasu fa? Ai tana mutuwa a hannunsu wallahi ita ta kashe ta, gidan yari zata tafi a Waure ta Waurin rai da rai."

Ummi cikin kuka ta ce, "na shiga uku! Wallahi ban yi komai ba. Ni haushi take bani ne kawai, na riga ta fara aiki amma tazo ta mamaye komai, ba a saka mu yin komai sai ita. Mu da muka rigata zuwa ba a yi mana abinda ake yi mata, akan idanunmu ake Waukaka, ta koma kamar bamu rigata fara aiki ba."

"Ranar ma katin gayyatar Mr Ray aka bata, kuma ni chairman ya yiwa al?warin zan yi hira da duk wani babban ba?o, amma sai bai bani ba ya bata. Shine na ji haushi na tare ta har na faWi maganar, amma wallahi Allah ban saka ayi nata komai ba."

Abba ya fusata ya ce, "rufe min baki ko na Salla ki, daman ba?in ciki ki ke yi nata kenan ko? Hassada ce take damun zuciyarki ko?."

Yaya ya ce, "ga illarta nan ta fara gani yanzu, dan wallahi babu mai fitar dake a case Win nan sai Allah, ki yi addu'a dan da?yar baki yi zaman gidan kaso ba. Kin ga sai ki ?ara hankali, nan gaba kar ki sake furtawa wani kalma makamanciyar wannan balle ki ce sai kin ga bayansa."

Ita dai kuka take yi sosai ta ce, "Abba ka bani dama na gudu Lagos, don Allah."

Yaya ya harare ta ya ce, "ai in kika kuskura ki ka gudu kin ?arawa wutar fetur wallahi, dan duk inda ki ke sai an nemo ki kuma baza a sassuta miki ba. In kina wannan tunanin ma ki daina, shashasha mara hankali."

Shi dai Abba bai ce komai ba ya bar wajen saboda Sacin rai, Ummi ta cigaba da kukan rashin mafita, sai dai ta yi alwashin in har aka rufe ta to wallahi sai ta zama silar da za a kulle Muslim, sai dai ayi mutuwar kasko, a mutu har liman, baza a a rufe ta ita kaWai ba wallahi.
[6/17, 11:58/ AM] KRBBK: RDB2P07
Nana Haleema

Islaha bacci ta yi mai tsaho har asuba tana bacci, sai bayan an yi sallah sannan ta mi?e tana ri?e wuyanta da ya ri?e, sannan ga bayanta ya ri?e sosai saboda kwanciyar kan kujera. A hankali take sake kallon Wakin tana tuna abinda ya faru, ita dai ta san ta tare masa hanya daga nan bazata iya tuna komai ba.

Wani tunani ya Warsu a ranta, ta mi?e a firgice tana duba jikinta, tana tatttaSa wuyanta da fuskar ta amma bata ji wani canji da zai nuna an yi wani abu da ita baz Ga kayan jikinta a yadda ta kwanta, alamun ba a taSa su ba, babu alamun an buWe wani Sangare na jikinta. Sai lokacin ta yi ajiyar zuciya, hankalin ta ya Wan kwanta, tana sauke ajiyar zuciya a hankali.

Tana dafe da kanta, ta duba wayar ta taga lokacin sallar asuba ya yi, ta mi?e a sanyaye ta nufi inda ta yi alwala jiya da niyar sake yi.

Kayan jikinta duk sun dame ta, musamman undies Winta har wani zafi take ji a jikinta saboda yadda suka yi dauWa, duk ta ?yamaci kanta.

A haka ta shiga banWaki sai kawai ta haWa da wanka, ta yi wanka ta cire undies Win ta fito dasu a hannunta, ta tsaya tana kallon kayan ta rasa me zata saka. Ta san dai bata da kayan sakawa, su Win ne kawai. Rashin mafita ya saka ta mayar jikinta amma bata mayar da undies Win ba, dan gaskiya baza ta iya mayar dasu jikinta ba, musamman pant Winta, yafi komai damunta. Ta jawo bedside drawer ta cilla undies Win a ciki, ta kalli undies Win da ta saka da niyar duk ranar da zata bar gidan zata Wauke abinta. Ta kalli kanta tana tunanin anya ma kayan zasu yi sallah.

Tunawa bata da mafita ya saka ta fito ta dawo inda aka ajjiye ta tayar da sallar asuba jikinta a snayaye.

Ta ji daWin jikinta, babu ciwon kai kuma zazzaSin ya sauka gabaWaya. Ta jingina da kujera tana lumshe ido tana tunanin halin da Baffa yake ciki, tana tunanin halin da masoyinta yake ciki. Ta san zuwa yanzu Hamma ya san an sace ta, ta san yana can cikin tashin hankali mai tsanani. Wayar ta ta Wauka amma still no service, ta cillar da wayar a wajan tana sauke numfashi a hankai.

Kallon abincin jiya ta yi, duk suna wajan babu abinda aka taSa, kuma Allah ya sani yunwa take ji, ta daure ta Wauke kai daga kallon abincin ta rufe ido, tana ji kamar ta dinga dukan kanta har sai ta daina jin takaicin da yake damun zuciyarta.

A hankali ta ji an buWe ?ofar, ta juyo tana kallon wanda ya shigo. Baturen Chef ne, Waure da apron a ?ugunsa sai wata maid a bayansa.

Ta zuba musu ido tana kallo suka Wauke abincin jiya, suka ajjiye mata sabo suka fita basu ce mata komai ba itama bata ce ba. Ta yi banza da abincin, ta rufe ido cikin rashin sanin abinda ya kamata ta yi.

Har gari ya yi haske Islaha bata motsa ba, sai ma gyara zama da ta yi a wajan. Sai da ta ji zata kashe kanta sannan ta ?araso ta zuba tea ta sha, bata sake kallon komai na wajan ba ta kwanta a kan carpet hawaye yana zuba a idanunta.

Rehaan kuwa da ya farka lokacin sallar asuba sai da ya dubata ta camera record Win wayar sa, bai Wauko ta dan ta yi rashin lafiya ba, dole ya so ya ga ya take tunda ya san ta suma. Da ya duba ya ga yadda take bacci sai ya ja tsaki ya ajjiye wayar.

Bayan an idar da sallar asuba bacci yayi mai aji, hakalinsa a kwance kamar bai Wauke ?ar mutane ba, ya jima sosai yana bacci dan har rana ta fito bacci yake yi.

Sai gab da sallar azahar ya tashi, ya shiga ya yi wanka ya shirya cikin ?ananun kaya, ya kwance gashinsa ya sauka har wuyansa. A lokacin ya Wauki wayarsa daidai lokacin kiran Jazy yake shigowa.

Ya yi tsaki ya share bai Wauka ba, ya fito falon tare da sakkowa ?asa cikin takun isa da ?asaita.

A kan kujerar dining ya zauna, babu abinda ba a ajjiye masa akan dining ba, komai yana ajjiye yana jiransa kamar banza.

Kiran wayarsa da aka sake yi, ya zubawa wayar ido ganin Jazy yana yawo a kai,ya Wan girgiza kai ya Wauka Jazy ya ce, "na san daman zaka ?i Waukar wayata, kuma bazan fasa faWa maka gaskiya ba Ray, ajjiye yarinya a gidan ka babban hatsari ne wallahi."

Bai kula shi ba, dan bashi da lokaci bashi amsa, dan bazai Wauki maganar sa ba sai ya yi maganinta. Jazy yana ji yana wasa da cokali ya san abinci yake ci, dan ya san lokacin cin abincinsa ne, dan shi yafi damuwa da yin lunch akan breakfast ko dinner.

Jazy ya ce, "malam kana ji ina magana fa." Nan ma ya yi masa banza bai ce komai ba.

Jazy ya ce, "Wallahi zan haWa ka da Mamy. Allah in na sake yin magana ka yi shiru sai na kira Mamy na faWa mata,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login