Showing 207001 words to 210000 words out of 221574 words

Chapter 70 - RAGAYAR DUTSE BOOK 2 COMPLETE

Unknown   

25 Aug 2026

145

ki da rafar daloli, yau kuma ga ki da naira miliyan hamsin. Islaha kina so kaina ya tarwatse ne?."

"Ai na faWa maka abinda zan yi ko? Ban Soye maka ba na faWa maka saboda gudun zargi. To shi na aikata, ga kuWi nan sun zo ni kuma na ?ulla yarjejeniya."

"Na shiga uku ni Sadik!...." ya faWa yana dafe kansa tare da juya musu baya.

Sai kuma ya waiwayo ya ce, "Islaha ba mafarki bane ba wannan, rayuwa ce ta zahiri wacce take faruwa a gaske ba a mafarki ba. Ki Wago kai ki kalle ni da kyau, a gabanki nake a tsaye ba a cikin mafarki nake ba..... Ki daina raina min hankali, ki faWi abinda zai yu don Allah. Wanne irin mutum ne zai Wauki wannan kuWin ya ba ki saboda auren contract."

Islaha ta ce, "Na dai faWa maka gaskiya, ka daina yi min tambayoyi akan wannan abun da ya riga ya zama tarihi, abinda na sani shi nake faWa maka. In ba ka yarda ba ga Safeera nan, a gaban idanunta aka yi komai, wata?ila in ita ta faWa maka baza ka ?aryata ba."

Safeera ta ce, "Hamma Sadik a gabana aka yi komai, har takardar yarjejeniyar na karanta. Ta ?ulla aure na wata biyar saboda kuWin fansar Hamma."

"in aka je yarjejeniya ana nufin yarjewa akan abinda kowa yake da ra'ayinsa. Na ji ita akan Hamma ta yi, shi kuma akan me ya bata kuWin dan ya aure ta?."

"Mahaifinsa. Zai aure ta saboda mahaifinsa" Safeera ta ta bashi amsa tana kallonsa.

Ya kalli Safeera ya ce, "wai waye wannan mutumin ne? Waye wanann da akan mahaifisa sai yi aure ta harda wannan kuWin matsayin na yarjejeniya?."

Islaha ranta ya fara Saci ta ce, "bazan tsaya na tsara maka ?arya ba, in ma abinda ka ke tunani na je na aikata babu wanda zai bani waWnanan kuWin a lokaci Waya saboda na bashi kaina. Abinda nake so da kai kawai ka amince, a je a yi abinda ya kamata."

Ya kalle ta ya ce, "Ba ki amsa min ba, waye shi?."

Islaha ta ce, "In na faWa amfani me hakan zai yi?."

Sadik ya ce, "Ki faWa min."

Islaha ta Wan yi jim tana tunanin ta faWa ko kar ta faWa, ta kalle shi ta ga ita yake kallo alamun yana jiran amsa, ta sake tafiya dogon tunani kafin ta ce, "Rehaan AbdulAziz Yola, wanda ka fi sani da Ray!.

Nana Haleema.
[7/29, 12:06/ PM] KRBBK: RDB2P95
Nana Haleema.

Sadik sai da wayar hannusa ta kubce ta faWi ?asa saboda yadda sunan ya ratsa kunnensa ya shiga har ?wa?walwa. Safeera ce ta du?a ta Wauko masa wayar, tana murmushi tana aiyana inda shine ya gansa ido da ido da bata san ya zai firgice ba.

Sadik ya zuba mata ido yana kallon ta cikin rashin sanin abinda zai ce mata. Sunan Ray kawai yake maimaita a ransa, da Raay ta ?ulla auren contract take nufi ko me? Da Ray zata zauna a matsayin miji da mata ko kuma dai wasa take yi masa?

Ya kasa magana sai tunani yake yi, duk da ta faWa masa sunan mahaifin wanda za a yi auren amma ko kusa bai kawo Rehaan bane. Ya Wauka sauran yaransa ne tunda ance yana da yara da yawa, bai yi tunanin babbar giwar ne da kansa ba.

Sadik ya kalle ta ya ce, "Ray fa ki ka ce?."

Islaha ta nuna masa Safeera ta ce, "ka tambaye ta, a gabanta aka yi komai."

Ya kalli Safeera ya ce, "Da gaske shine ko AI ne?."

Ta Wan yi dariya kaWan ta ce, "shine. Yadda ka shiga wannan firgicin haka nima na shiga, lokacin da na haWa ido dashi sai da na ji kamar ba a duniyar nake ba. Mr Ray da muke gani a tv da magzine, shine na zauna a falonsa har na haWa ido dashi. Har ya yi mata magana da yaren da nake ji, ban Wauka ya iya wani yare in ba turanci ba, sai gashi na ji ya yi har zan ba da shaidar ya iya ko ina. Rehaan shine wanda ya saka hannu Islaha ta saka hannu, shine ya tura kuWin da aka turo maka."

Sadik ya karSi wayarsa a hannaun Safeera, ya duba bank name Win wanda ya turo kuWin, amma sai ya ga sunan kamfani ne kuma bai yi kama da sunan Ray ba.

Ya kalli Safeera ya ce, "Bank name Win ba nasa bane."

Safeera ta ce, "Kaima kamar ba mai ilimi ba, ta ya zai turo maka kuWi da kansa? Sai dai ya saka a tura."

Sadik kalli Islaha yana girgiza kai ya ce, "Abokina ya yi ha?uri, ko da ya dawo daga hannun masu garkuwa Islaha kin fi ?arfin....."

Islaha dakatar dashi a fusace ta ce, "kar ka ?arasa!."

Ta nuna kanta da yatsa ta ce, "Har abada ni matar Hamma ce, babu wani namiji da zan kasance a ?ar?ashinsa a matsayin mijina sai Hamma. Auren wata biyar ne kawai, daga ya ?are kowa zai kama gabansa kamar ba a zauna ba. Na auresa saboda Hamma, kuma zan zauna da shi saboda Hamma, zan dawo saboda Hamma. Zan dawo a Waura mana aure da Hamma, mu zauna a matsayin ma'aurata kamar yadda muke mafarkin halam, shi kuma ya je ya cigaba da rayuwarsa kamar yadda yake yi!" Ta faWa cikin fushi tana kallonsa.

"Amma Islaha ko da ace kun rabu za a ce ex wife Win Ray ce, iya wannan matsayi da ki ka samu na ex Winsa babban mataki ne a duniyar nan. Kuma ta ya zai sake ki? Ni bana hango rabuwa a zaman ku."

"Na faWa maka auren wata biyar ne kawai, ya san mahimmacin rules tunda a turawa yake rayuwa, ya san meye contract marriage tunda a cikin masu yi Win yake zama ko yaushe. Bazai karya Waya daga rules Wina da na ba shi ba, zai yi komai base on yadda muka gina auren ni da shi, bazai taSa breaking ko guda Waya ba, dan ya san illar yin hakan. Zan kiyaye rules Winsa, shima zai kiyaye nawa, lokaci yana yi komai zai ?are."


Sadik ya girgiza kai ya ce, "Islaha ya kamata ki tuna, bayan contract akwai aurensa a kan ki. Mu musulmai ne, ba a kan contract mu ke gina aure ba balle mu ce da an yi canceling shikenan auren ya ?are. Dole sai ya sake ki ta hanyar furta miki ko ya rubuta miki."

Islaha ta ce, "Na san da wannan, kuma zai yi Win kamar yadda na faWa maka."

"Yanzu yau laraba, jibi kenan Waurin auren ku dashi?." Ta masa Waga kai alamun eh.

Sadik ya ce, "Baffa ya sani?."

"ya sani, amma bai san batun yarjejeniya ba. Don girman Allah ka yi min al?awari babu wanda zai sani, daga kai sai Safeera ne ku ka san maganar nan, don Allah ka ri?e min amana. Ko Hamma ne zai dawo kar ka faWa masa, ni zan san abinda zan ?ir?ira na faWa masa amma ba aure ba. Kuma ko da wasa kar ka faWawa wani ka san Rehaan ya yi auren contract dani ko da wata, wallahi bana so a san da auren nan kamar yadda ba ya so."

Sadik ya ce, "Na yi miki al?awari babu wanda zai sani in sha Allah."

Ta ce, "Sai batun waWanda za a kira domin kuWin fansar Hamma, Baffa suke kira yanzu ba kai ba, ya za a yi yanzu?."

Sadik ya ce, "ni suka fara kira kafin Baffa, zan kira su gobe, sannan zan je a ciro kuWin a bank sai a kai musu. In Allah ya yarda Saheer zai fito lafiya."

Ta Waga hannu sama ta ce, "In sha Allah." Sadik har lokacin bai fita daga shock ba, ya kalle ta alamun yana son yin magana amma ya ga ta haWe rai alamun babu tambaya, dole ya yi shiru ya shiga mota yana tunani akan wannan lamari mai Waure kai.

A gidansu Ray shagali bikin kawai ake yi, masu henna ma daga india suka zo aka yiwa amarya da ?awayenta ds iyayen amarya. A ranar suke yin indian night kamar yadda suka saka shi a cikin jerin event Win da zasu gabatar.

Ango da amarya sun sha kwalliya a cikin kayan india, kowa ya kalli Riyya ya san jininsu ce, shima Jay da yake yana da haske da kyau sai ya zama kamar Wan india Win. Kowa in ya kalle su sai ya sake kallo saboda kyau, ita kanta Mamy Win shigar india ta yi, kowa na wajan shigar india ya yi dan kyauta aka raba kayan.

Mama da Umma ne suka ce baza su saka ba, sai suka saka lafaya kawai amma basu naWa sari kamar sauran mutane ba. Rehaan ma kayan india ya saka, irin rigar nan tasu mai Wan tsaho har guiwa.

Yana zaune a kame a wajan, har ya fi amarya da angon farin jini dan shi kaWai ake haskawa. Cikin lokaci kaWan hotuna da video suka zaga duniya, ana ta yaba kyau da tsarin bikin dan ya ?ayatar sosai.

Umma da Mama sai taSe baki suke yi, suna ganin yadda ake Sarin kuWi a wajan dan dukkansu da kuWin india suke li?i ba naira ba.

Lokacin da Riyya ta je ta ri?o hannun Yayanta ya shigo kan stage wajan ya Wauki ihu, iya Mamy ne dasu a kan stage Win sai Jazy da ya zama Wan family Mmay shima.

Gently Mamy take taka rawar india, shi dai yana tsaye yana murmushi yana ri?e da hannun Banisha da take kusa dashi. Sai daga baya ya fara yiwa Mamy li?i da kuWin da bai san adadinsu ba, Mamy ta ruungume su aka yi musu hoto.

Daga nan aka kira mawa?in daga gayyata tun daga ?asar india har nigeria. Mawa?in da india take ji dashi, mawa?in da india suke mararinsa, mawa?in da bollywood take ji dashi, mawa?in da mu kan mu ?an nigeria wa?o?insa suke burge, wato arijit sight. Aka chase aka raba abubuwa masu yawa, sai ?arfe Waya na dare aka tashi kowa ya tafi.

Mama da Umma suna zaune basu tashi ba, duk da sun gaji amma sun ?i tafiya, amma saboda gulma suna zaune sai sun ga ?arshen abin.

Mama ta ce, "Abu babu tsari, wai indian night. An cuci ahlimu da aka Wauko mana wannan."

Umma ta ce, "ni ba wannan ba, wai ina matar Rehaan Win ne? Ita meyasa ba a yi bikin da ita ba?."

Mama ta ce, "?yale jinin matsafa, kin san da yake ba son auren yake yi ba, bazai bari ayi biki dashi ba. Ni kuma wallahi sai na tabbatar da auren nan saboda cikar burina."

Umma ta ce, "Haushin yaron nan nake ji, da ace mutuwa a hannuna take da yanzu na kashe shi kowa ya huta. Komai ace Rehaan, komai shi? Yaran mu sun zama koma baya, ba a yin komai dasu sai shi?. In ki ka Wauki waya ki ka duba kafafen yaWa labarai, gabaWaya akansa ake magana yau. Shirme!" Ta faWa tana mi?ewa ta fita.

Mama ta bita da kallo tana murmushi ta girgiza kai ta ce, "duk yadda zan yi na mallake yarinyar nan ta zama yar Wakina sai na yi, ba a banza na tsaya kai da fata a aurota ba, ina da shiri na musamaman akan hakan. Zan ri?e ta da kyau, zan jawo ta a jiki, zan nuna mata ?auna, yadda duk abinda na ce tayi akan Rehaan zata yi, duk wani sirrinsa zai zama yana tafin hannuna."

Ta sake yin dariya ta ce, "Mu je zuwa, yanzu ne za a fara kafcen, da ba a yi komai ba."

Washe gari.

Saheer tunda ya ji labarin za a kawo kuWin fansarsa sai jikinsa ya yi sanyi, duk sai ya damu yana tunanin in ya tafi wa zai bar wa amanar sa Sudais ya bar masa? Kuma Allah ya sani ba ya so su Black su yi nasara akanta, ba ya so wani abu ya shiga tsakaninta da mai garkuwa da mutane da sunan mijinta. Duk da mijinta ne na aure, an Waura aure da sadaki da shaidu, amma rashin mafita ce ta saka aka amince dashi.

Kwana biyu ta Wan sa ki jiki, duk bata magana har lokacin amma in suka bashi abinci suka ya bata tana ci kaWan, kuma shi kaWai ne yake yi mata magana ta ji. GabaWaya sai ya ji ya damu, ba dan ba ya son komawa gida ba, sai dan bai san ya rayuwarta zata kasance a wajen ba.

?arar machine Win ArWo da ya ji ya saka shi ya Wago ya kalli ArWo da ya sauka daga kan machine Win, ya zauna a inda ya saba zama yana kallon su Waya bayan Waya ya ce, "Ban kawo ku nan na ajjiye ku ba, ban kawo ku nan dan mata su dinga dafa mu ku abinci kuna ci ba. Duk wanda ?an uwansu baza su kawo kuWi ba za mu daina ganin ku, ?an uwanku kamar ba sa son ku."

Kowa ya yi shiru babu wanda yake magana, ya kalli Saheer ya ce, "Kai yau mu ka yi zasu kawo kuWin ka, ga shi akwai inda zan je na dawo. Sai dai in sun kawo su tafi, ka bi bayansu daga baya."

Saheer dai ba shi da bakin magana, wannan kashe kashe da yake yi kamar suna kashe sauro bazai bar ka ka yi magana ba. A take ya saka aka fito da mazan ciki, suka yi musu dukan tsiya aka yi video aka turawa ?an uwa, shi kuma ya tashi ya fita.

Kamar yadda Sadik ya shirya haka shirya kuWi ya ta fi dajin da kwantance da suka dinga yi masa, su da kansu suka faWa masa inda zai tsaya, ya je wajen ya tsaya, suka ce masa zai ga mai jar riga kawai ya bi bayansa, haka aka yi yana ganin mai jar riga ya bi sa, daga nan aka hau machine aka tafi sansaninsu.

Islaha da Safeera ne kaWai suka san an tafi kai kuWi, ko su Baffa basu san me yake faruwa ba, ba a so su sani saboda kar su tambayi a ina aka samo kuWin.

Islaha tunda Sadik ya tafi gabaWaya bata da nutsuwa, duk ta ruWe saboda tashin hankali har rama ta yi, tunda Sadik ya tafi bata iya zama ba kai kawo take yi. In ta gaji ta huta ta kuma mi?ewa tana cigaba da tunani.

A ranar gidan su Rehaan a ranar aka haWawa Riyya grand kamu, babu yadda Jafar bai yi da Rehaan ba amma ya ?i zuwa.

An shirya kamu a babban Wakin taron da ake ji dashi a garin Yola, an kashe kuWi masu nauyi, anyi harkar gold, social media ta san ana bikin ?anwar Rehaan Yola. Amarya ta yi kyau, ta samu gift ma su yawa marasa adadi.

Gidan su Rehaan suna can suna shagali, islaha kuma tana tunani, har dare babu Sadik babu labarinsa. Hankalinta ya tashi, ko abinci ranar bata ci ba, gani take kamar Sadik Win bazai dawo ba.

Nana Haleema.
[7/30, 11:15/ AM] KRBBK: RDB2P96
Nana Haleema.

Sai sha Waya na dare sannan ta ga Sadik yana yi mata waya, ai ko hijjab bata tsaya sakawa ba ta fita a guje ta gansa a harabar gidan a tsaye.

Ta tsaya tana kallonsa ganinsa shi kaWai, shima ya gaji kuma wahala ta bayyana a tare dashi sosai. Ta ?araso ta ce, "Hamma Sadik ya ake ciki, Ina Hamman nawa?."

Sadik ya kalle ta kamar yadda take kallonsa, ita kuma gani ta yi duk ya firgice, ruWewa da tsoro sun bayyana ?arara akan fuskarsa. Sadik Ya ce, "sun ce sai gobe ko jibi za su sako shi."

"Kamar ya? Daman in aka ba da kuWi ba ranar mutum yake dawowa ba?."

"Ban sani ba Islaha, ban taSa zuwa inda suke ba sai yanzu. Daji ne Islaha, ban taSa shiga daji ba sai yau, wajen kamar ba a duniya yake ba."

"Ka ga Hamma Saheer?."

Ya Waga kai ya ce, "na gan shi."

Hawaye ya sakko daga idonta, ta saka hannu ta rufe bakinta ta ce, "basu kashe sa ba?."

Ya Waga mata kai yana murmushi ya ce, "yana nan da rai, kuma zai zo ya ganki. Wai shugaban nasu ne ba ya nan, shiyasa baza a ba da shi ba. Duk yawan kuWin nan sai da na irgasu, a haka ma ban gama ba kawai na ce musu na gama ne."

Islaha ta zube a wajan ta yi sujjud shukur tana farin ciki da murnar Hamma yana da rai, sai ta mi?e ta ce, "Yanzu sai gobe ko jibi?."

Ya Waga kai ta dafe kai ta ce, "meyasa basu ?yalesa yau ba? Kar su karSi kuWi su hana mu shi."

"Za su bayar in sha Allah."

"Ya Hamma yake, Ya rame ko?."


Sadik ya yi murmushi yana kallonta ya ce, "Samun mace mai ?aunar mutum tsakani da Allah kamar ki za a jima, ?arnin irin ku ya jima da ?arewa, waWanda suke saka rayuwarsu a hatsari saboda wanWanda suke so ya jima da shuWewa. Har abada Saheer bazai samu wacce take sonsa kamar ki ba, har abada Saheer bazai samu masoyiya kamar ki ba, har abada Saheer bazai samu mai ?aunarsa da zuciya Waya kamar ke ba. Na jinjina miki sosai, kin sadaukar da farin cikin ki da rayuwarki gabaWaya saboda shi, Allah ya bar ?aunaa."

Ta yi murmushi tana goge hawaye ta ce, "Hamma ya wuce komai a wajena, Hamma ya yi min abinda babu wanda ya yi min shi a duniyata. Ya Wauko ni kuma ya ri?e ni, ya taimake ni ya kaini matakin da ban yi tunanin zuwa ba. Duk ahinda? zan yi masa ban faWi ba, kuma ban saka masa ba."

Ya Waga kai ya ce, "Gaskiya ne wannan. Ina so na faWawa Baffa saboda kar ya yi asarar da kadararsa ya siyar, amma ban san me zan ce ba."

Islaha ta ce, "Ka samu dabarar da zai daina cewa zai siyar Win."

Ya Waga kai ya ce, "zan san abinda zan yi in Allah yarda, Baffa yana nan?."

"Yana ciki."

"bara na je na same sa, shi da Maman." Islaha bata ce komai ba, ya wuce ya shiga ciki itama ta bi bayansa.

A nan ya samu Mama a zaune suna tattaunawa akan batun siyar da kadarorin da aka saka a kasuwa. Kamar dare bai yi ba, dukkansu idanunsu biyu ana lissafa abubuwan da ya kamata a siyar.

Bayan sun gaisa Baffa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login