Showing 132001 words to 135000 words out of 232724 words
aure sun zaci irin na saka ranar nan ne da aka saba, amma ina wannan kaya ne aka kawo kamar har da lefen nan da komai gaba
ɗ
aya. Kaya ne sai da suka cika parkorn Amah da ma wasu da aka
ɗ
aura
kan wasu, drinks kuwa sai a kitchen aka jera su da ruwa da su biscuits da sweets. Su kuwa main na parlorn har da set na akwati wai na Amarya wanda kayan sarauta ne maishi a ciki irin wainda suke kai na baiko bisa al'adar masarauta. Abu dai sai san barka, T
ee sai da ta riƙe baki saboda ganin kayan arziki amma abun mamaki ko ka
ɗ
an ba ta ji a ranta ina ma ita aka kawowa kayan ba kamar yanda ta ji a kayan Ridhwan. Ba ta ji nadamar za
ɓ
an shi ta gudun ma wannan auren ba kamar wancan karon, sai ma murna da take ta
ya ƴaruwarta da irin gidan da ta samu sai fatan Allah ya kawo farinciki kamar yanda itama ta samu a nata auren.
Hakan ya sa ta gane cewa shi so babu ruwan shi da aji ko mulki, inda ba ta son Ridh may be da taji kishin ganin kayan. Amma yau ko kusa ba
ta ji komai ba sai ma hannu da ta kai tana shafa marar ta inda take da tabbacin akwai ajiyar masoyin nata
ɗ
an satittika, fatan ta Allah ya kawo mata shi lafiya su raini kayan su da soyayya.
Masu kawo kaya dai basu da
ɗ
e ba suka tafi bayan an basu tukuici
, su Yaya Balaraba da Aunty Umaimah dai sai da bu
ɗ
e komai suna ta yabawa har da cewa wai Adeeyah akwai ƙashin arziki. Murmushi kawai Tee tayi tana ciro wayarta ta yi videon kayan, direct ta turawa Dee da
ɗ
an short note inda take cewa '' These people don r
eady oo, har da kayan Gimbiya fa suka kawo''.
Lokacin da message
ɗ
in ya shigo Dee tana online meeting ne da Shedrack daga Founders friday, ba ta duba ba sai da ta gama. Ko da ta ga message
ɗ
in wani tunani ne ya fa
ɗ
o mata a rai tuno cewa ko wancan aure
n ita ta tura mata kayan da aka kawo wannan karon ma haka. Murmushi ta saki ta duba kayan kana ta dubi Mufee tana cewa '' zo ki ga ''.
Da sauri ta taho tana leƙa wayar kayan da ta gani sosai ya bata mamaki tace '' Oshey you are gonna be a princess''.
''Kin ji ki da wata magana kuma, princess a ina?".
''Dama tun can Princess ne, you were just very humble to say so it's kind of official?".
''Not that official, but yeah zasu kawo sadaki soon''.
''Allah ya sanya alkhairi ya sa da mu za'a
yi, My Pookie zata auri Prince oshey wani hanin ga Allah baiwa....''
''Do the calms Pookie abeg''.
''Toh mun yi Madam, kai i no go calm down yi min forwarding in turawa su Nazeey''.
''Ke dai wani zubin akwai rawar kai''.
''Ko ma rawan miy
e kice, i no go calm down Kaduna must know say i'm getting my friend married to a prince''.
Tsaki kawai ta saki, instead ta tura mata kamar yanda tace sai ta shiga DM
ɗ
in Scor ta masa message da '' sun fa kawo kaya yau''.
Gani tayi yana typing sa
i ko ga message
ɗ
in shi ya shigo yana cewa '' shi ya dawo ne?".
''Nope, iyaye ne suka shigo''.
''Yaushe aka saka bikin?"
''I don't know, how are you feeling?".
''I don't know Baby, amma zuciyata babu da
ɗ
i anya i can do this kuwa?".....
..
Ji tayi zuciyarta na karyewa amma ba zata bari ta rinjayeta ba, ta yi alƙawari kuma sai ta cika shi don haka da sauri ta fice daga DM
ɗ
in tana kashe datar gaba
ɗ
aya........
Deejasmah
💜🦂
CHAPTER 59
Kamar ƙyaftawar idanu maganar auren Adeey
ah da Musharraf ya kankama daga nan Kaduna har zuwa can Barewan duk da shi dai ango ko a jikin shi balle kuma amaryar da ba don Mufee tana tuna mata da shi ba mantawa suke yi. An kawo sadaki da dukiyar aure irin dai-dai ajin da Affah yake so, sai da ya kir
ata yana kuma shi mata albarka ita dai da Ameen ta amsa masa don ba yanda ta iya sai haka
ɗ
in. Musaddiq ne ya zo har school wurin ta kan maganar shirye-shiryen ta ce masa tayi babu abinda take shiryawa ita dai a
ɗ
aura kawai a wuce wurin, dariya ya ƙyalƙyac
e da shi yana cewa ''kai Aunty Gimbiya, wani irin babu abinda zaki yi? Sai kace wacce za'a yi wa auren sadaka?".
''Uhmm Ya Musaddiq kenan, miye marabar dambe da fa
ɗ
a?".
''Abubuwa da yawa ma, amma kamar baki san wa zaki aura ba ko? Tafidan Barewa
ne fa gaba
ɗ
aya''.
''Ko sarkin garin ne ma Ya Musaddiq, nifa I'm just getting married for getting sake nothing more''.
Duban ta yayi a tsanake da ita da shi bata san wa yafi wani tsanar auren nan ba, shi na shi yace yana da wacce yake so to ita ku
ma fa? Anya ba akwai wanda take so ba? Amma ai ba a da
ɗ
e da fasa wancan auren ba, ba lallai ta samu wanda take so ba. Cikin lallashi yace '' ki daina fa
ɗ
in haka Aunty, auren nan naku yin ubangiji ne in kuka yi haƙuri komai zai wuce''.
''Na yi ma na Ya
Musaddiq, ko baka gani ne?".
''Haka ne amma ki cigaba da haƙuri, akwai Aseobin da muka order daga Atamfa_&_more. Zan kawo su next week in Shaa Allah sai ki raba musu bayan nan in akwai wani abu don't hesitate to tell me kin ji?".
''Thanks'' ta ams
a masa, murmushi kawai yayi ya miƙe tsaye. Rako shi wajen common room
ɗ
in da suka zauna a ciki, sai da ta ga tafiyar shi kafin ta koma ciki. Ko da ta shiga room
ɗ
in su take bawa Mufee labarin za'a kawo Aseobi, ai ko ta dinga ihu tana rawar soko wai yanzu n
e suka san zata yi aure. Kai ta girgiza don ta lura ita damuwarta ba yanda auren zai faru bane, kawai dai ita dai ayi bikin koma miye zai faru ya faru. Toilet ta shige ta bar ta nan zaune tana cewa '' bari in yi creating group ma, wani hashtag zan yi usin
g?".
Ganin ba a amsa ba ya sanya ta kallon ƙofar toilet
ɗ
in, ganin babu kowa a wurin ya sanya ta sakin murmushi don da gangan take yin duk abinda take yi. Ta san in ta nuna zancen auren nan yana damun ta ba zata ta
ɓ
a yin abun arziƙi ba, don tana sane
da yanda shi wancan Muhammad
ɗ
in yake son manipulating
ɗ
in ta in ba wai an samu me shaking
ɗ
in ta bane ba zata shiga hankalin ta ba.
Ko da ta fito ba ta ƙyale da maganar ba sai kuma tambayar ta take yi, ita ko bata tanka mata ba. Da dai tayi shiru sai t
a kira su Nazeey haka suka yi ta shiriritar su kamar yara ƙanana tun tana
ɗ
aure fuska har ta gaji ta saki ta dinga dariya, don ta san ƙawayen nata ba wani hankali ba ne da su.
Kamar yadda yayi alƙawari sati na ƙarewa sai ga shi da kayan niƙi-niƙi a ba
ck seat
ɗ
in motar shi, a manya kwalaye guda biyu ya kawo kayan. Ma'aikatan hostel
ɗ
in ne suka taimaka mata da shi ciki, a ƙofar
ɗ
aki suka ajiye kayan ta musu godiya sosai kafin ta juya suka fita. Musaddiq ne ya sallame su da ku
ɗ
a
ɗ
e masu kaurin da bata san
ko nawa ba ne, yau ma sai da ya kuma rarrashin ta kafin yayi mata sallama ya tafi. Shigar da kayan su Mufee suka taya ta yi ciki kafin ta rufe ƙofa suka farke kwali, Atamfar mix and match ce kalar yayi da aka yi musu mai red da blue a jiki. Tayi kyau ainun
fiye da yanda ta zaci zata gani sai wasu Adire ƴan asali, sannan Mandela. Duka adadi
ɗ
aya ne wato 30-30, kuma an ha
ɗ
a su duka uku an yi wrapping da ƴar cards mai
ɗ
auke da sunan M&A_love story. Ga paper bags a gefe iya adadin kayan duk da same suna a jiki
ga date
ɗ
in bikin wato nan da 2 months da sati biyu masu zuwa riƙe baki suka yi suna kallon kayan. Yayinda Mufee ta duƙufa irgen ku
ɗ
i a cewar ta wajibi ne su san nawa aka kashe a wannan sabga, ba ta biye ta ba don ita ma mamaki ne ya rufe ta. Video ta fara
yi tana turawa Tee tace mata ga kaya fa,da sauri ta kira ta tana cewa '' You don't mean it dear''.
''Ni ma dai i'm really shocked kayan nan sun yi yawa kuma sun yi kyau''.
''Yawwa, nima kyan ne ya saka ni mamaki amma yawan su da kike magana kin
san inda zaki yi aure kuwa? Dee the Barewas are loaded ba ki mamakin yanda Affah ya samu ku
ɗ
in shi? To daga gadon su ne. Ga ku
ɗ
i ga sarauta ga komai Allah ya ba su, kuma shi wannan Musharraf yana daga cikin masu ku
ɗ
in gidan don bai dogara da su completely
ba. Yana nema every blessed day, ke ma nan da 2 years in kika duba networth
ɗ
in ki zaki ga komai ya sauya''.
''But i don't care about that Tee, kwanciyar hankali ya fi min komai''.
''Adeeyah rayuwa tana da ƙalubale ga kowa sai dai na wani ya
ɗ
ara
r wa wani, amma in kika kar
ɓ
e shi da zuciya
ɗ
aya sai Allah ya miki canji mafi alkhairi ya baki ladan haƙuri I'm sure ba zaki ta
ɓ
e ba''.
''Ameen dear, thanks much''.
''What are twins for? Yanzu kin yi lissafin wainda zaki bawa kayan?".
''Uh
mm nope, su dai Mufee ne za'a cire musu nasu sai sauran ban san yanda za'a yi da shi ba''.
''Barin kira Amah mu ji yanda za'a yi, gobe sai in shigo nan
ɗ
in ''.
''To Tee sai kin zo
ɗ
in, Thanks''.
Da haka suka yi sallama, kwashe kayan suka yi
daga ƙasa suka maida shi cikin kwalayen a gefe suka ajiye komai suka cigaba da sabgar gaban su. Ranar kamar almara sai ga ƴan neighboring room
ɗ
in su sun yi knocking ko da ta gansu sai da tayi mamakin ganin su amma ba ta ko nuna ba, ta basu hanya suka shig
a ciki. A bunk
ɗ
in kasa suka zauna su ukun, Raliya da ke da surutu ne ta kalli gefen kwalayen tana cewa '' wai Mufee kin fara pre-order ne?".
Kallon banza ta jefa mata da mamakin gulma irin tasu wai pre-order bayan a gaban su Dee ta shigo da kayan bal
le ma su ce. Da yake ta fisu sanin ta kan tsiya sai tace '' Aa Adashin kayan kitchen na fara in zaku shiga''.
''Adashi kuma? To ki nuna mana sample
ɗ
in kayan sai mu shiga'' in ji Nafisa kamar munafuka.
''Kayan kitchen
ɗ
in ne baku sani ba sai an nun
a muku? To zan tura a group
ɗ
in hostel
ɗ
in nan sai ku gani ''.
''Kai Mufee ke dai an yi ƴar air, wai kayan kitchen'' cewar Aminah
''To ai ban ga dalilin shigowar ki bane da gulma bakin ku, it's better ku fa
ɗ
i abinda ke ranku not beating around the
bush''.
''Mu ba komai we are just asking wallahi''. Fa
ɗ
in Raliya tana ƙyafta idanu.
Tsaki ta
ɗ
an saki tace '' uhmm'' wanda yayi daidai da shigowar kiran Musaddiq. Hayewa kan gado tayi ta amsa tana tambayar shi ya ya koma gida.
''Ai ba yau za
n tafi can ba, akwai abinda zan yi nan Kadunan. Ya kayan?".
''Sun yi kyau sosai Ya Musaddiq, har ina mamakin yanda ka iya za
ɓ
e haka''.
''Ba ni na za
ɓ
a ba, Aunty Munawwarah ce. Sai ma damuwa da ta dinya yi wai kar ku ce bai muku ba''.
Zaro id
anu tayi a ranta tana ayyana yanda har yau bata san ƴanuwan shi bayan Musaddiq ba, kai abu
ɗ
aya da ta sani shi ne su ba yaran Marafa bane. Baban su ya da
ɗ
e da rasuwa shima yaron mai babban
ɗ
aki ne kuma tsohon Sarki kafin babban Yayan su na yanzu ya kar
ɓ
i s
arauta. Ba ma ta san sunan shi ba, ba kuma ta san akwai mace a
ɗ
akin nasu ba sai yau.
Murmushi ta saki mai
ɗ
an sauti tana cewa '' A'a wallahi sun yi kyau, ka cewa Aunty mun yaba muna kuma godiya ''.
''Aunty zata ji, amma kayan sun isa ko sai an ƙ
aro?".
''Komai yayi har sun yi yawa ma, ai ƙawayen ba wani yawa ne da su ba ''.
''Toh haka ake so ai, yanzu dai don Allah ku shirya tsarin bikin da budget
ɗ
in ku sai mu san me ake ciki''.
''Za su yi in shaa Allah''.
''Toh sai anjima ''
Daga haka suka yanke wayar ba ta kuma kallon ƴan
ɗ
akin ba ta juya baya, haka suka ƙarashi zaman kallon su suka fita.
Washegari around 11 Tee ta iso duba kayan ta yi tana kuma yabawa kafin suka ha
ɗ
u ita da Mufee suka yi packaging kayan a bags
ɗ
in,
jera su suka yi kan rug. Tee ta sa wayarta tana ta videon ta, dama tun suna aikin take komai. Suna yi tana cewa Mufee '' nima dai sana'ar ha
ɗ
a ankon nan zan zo in fara kawai''.
Dariya ta saki tana cewa '' kuma zaki yi ciniki tunda kina da mutane ''.
''Sosai ma, dama ina zaune yanzu ba abinda nake yi. Ads ne dai ba'a hana ni ba sai makeup shi kuma ban da lokacin shi yanzu sai covering ''.
''Ai ko to ki fara yanzu da kin yi a biki guda
ɗ
aya shikenan fa''.
''Ai fa kin kawo shawara Mufee, Aest
hetic by Teeyah zai koma Asoebi by Teeyah ''.
''Kar ki wani canja suna, ki barshi a Aesthetic
ɗ
in ki. Ke fa
ɗ
aya kike da sunan nan''.
''Ai ko haka za'a yi, dama ga sabon clothing line da zan fara by the end of the year''.
Ita dai da idanu ta
bisu tana mamakin yanda suka sake da juna haka, mutanen da a da ko magana da juna ba sayi? Shi ne har da wasanni haka? Murmushi kawai ta saki a zuciyar ta tana mai tabbatar da tuban Tee na gaske ne. Da kan su suka cire na friends
ɗ
in ta da aka ce za'a yi
creating group a sanya su ciki, da cousins
ɗ
in su ta gefen Amah sai yaran ƙawayen ta har da Meenalin TK a ciki. Wasu da suka rage ne ta cewa Mufee '' ki cirewa Ramlah da waincan na jiyan suma''.
''Ai ko ba za'a ba munafukan yaran nan ba ''.
''Hab
a Mufee miye a ciki in aka basu, besides ma in muka ajiye babu abinda za'a yi da shi''.
''Toh a cire miki
ɗ
aya ki
ɗ
inka Please kayan sun yi kyau sosai ''.
''Ni dai Aa ba zan
ɗ
auka ba, ki basu please ''.
''Toh naji Aunty Gimbiya''.
Tsaki k
awai ta saki tana kawar da kan ta gefe ai ko ita da Tee me zasu yi in ba dariya ba.
A ranar suka yi tsarin abinda zasu yi da bikin inda bisa shawarar Tee suka ce zasu yi Kamu kawai sai Ladies eve wanda babu ankon shi su zasu fito da shi. Mandelar kuma
ranar yinin biki zasu saka ita
ɗ
ayar kuma in sun je can Barewa sai suka saka a can, don Affah ya shaida mata biki kawai za'a yi a can ta dawo nan ita da mijinta don jere ma a nan zasu yi. Ita da can sai ziyara, ta ji da
ɗ
in hakan don dama ba ta ƙaunar ta k
oma can gaba
ɗ
aya da zama gwara su zauna a nan sa dinga kai ziyara can
ɗ
in........
Deejasmah
💜🦂
CHAPTER 60
A ƙarshen watan aka kawo kayan lefe wainda suke suma gari guda, yanda ka san an kwance dealer daga Dubai. Ba kuma wai a yawa ka
ɗ
ai ba
har da kyau da aji, Ateeyah da aka kar
ɓ
i kayan da ita a yau ma sai da ta yaba da su don su ha
ɗ
u kamar wancan ranar ma ba ta ji ƙyashin ko ina ma nata bane. Ji tayi tana taya ta murna sosai, duk da dai an kawo kayaki masu kwalliya musamman Abayoyin amma sa
uƙin abun ba su
ɗ
in ka mata ko guda
ɗ
aya ba. Sun sako mata gold a wata akwatin da musamman Aunty Munawwarah ta damƙa shi hannun Tee akan ta ajiye shi gudun ƴan kallo su sure shi.
Amah dai duk yanda ta kai ga tsanar auren nan ganin kayan nan sai taji w
ani iri, ba wai kuma don yawan su ko ha
ɗ
uwa ba. Aa ji tayi zuciyarta ta ta
ɓ
u da ganin yanda ƴanuwan shi ke farinciki da ma ita nata, to don me zata takure kan ta bayan ita ma