Showing 6001 words to 9000 words out of 232724 words

Chapter 3 - JIRWAYE COMPLETE

29 Aug 2026

44

yanke kiran.

Ajiyar zuciya ta saki tana kwashi kayakinta ta bubbuga pillown da Mufee take kwance, idanu ta bu

ɗ

e cikeda bacci tana cewa " what?".

''I'm off".

''Ba dai ha

r 9

ɗ

in ta yi ba?".

Kai ta girgiza tana cewa '' zan tsaya PG ne''.

Ohh okay ta amsa tana miƙewa, ƙofa suka nufa ita ta fita tana ce mata bye ita kuma ta datse ƙofar.

Turus ta ja tsaya sakamakon ganin wata mota a bakin hostel

ɗ

in na su, sai kuma

ta basar ta hanyar fara duba cikin bag

ɗ

in ta kamar irin ta yi mantuwar nan. Cigaba da tafiyar tayi har ta zo gaban motar, wanda yayi dai-dai da fitowar mai ita.

Matashin saurayi ne wanda ya tara duk wani suffar maza a tattare da shi, baƙi ne irin mai

ƙ

yallin nan wanda hutu ya sake fiddo da kyan jikin na shi. Sanye yake da hoodie da wando kalar blue sai crocs baƙi yana sakin mata murmushi. Ɗan tura baki tayi tana cewa '' really? Rhid?".

''Toh ya kike son in yi Bae? Jiya how many calls na miki wayarki

na DND ba kuma ki kirani back ba ya kike so in yi in ba in zo ba?" Ya amsa a mugun shagwa

ɓ

e kamar wani yaro, lumshe idanu ta yi tana bu

ɗ

ewa tace '' but in da ban fito ba fa?".

''Then I'd wait har sai sanda kika fito or Mufee, it wasn't like na san le

cture hall

ɗ

in ku da sai in je can''.

''You really are impossible'' ta amsa tana

ɗ

an sakin murmushi, shi ma murmushin ya saki yana cewa '' ba ki yarda zan iya binki lecture halls

ɗ

in ku ba ko?".

''Not even that, but how could you wait for me all da

y? Work fa?".

''i'm off today'' ya amsa yana lumshe idanu.

''Off?".

''Yeah, call fa zan yi yau and I'll have to rest da rana''.

''Oh okay, ni kuma ina da class by 9''.

''And it is almost 9, oya hop in lemme drop you off at the venue''.

''Nan kusa ne fa, and zan tsaya PG hostel in amshi power bank

ɗ

ina''.

Kai ya girgiza yana cewa '' okay lemme walk you''. Hannu ta kai tana dafe goshinta cikeda jinjina nacin shi ta murgu

ɗ

a masa baki juyawa tayi ta

ɗ

ayan hannun ta shiga cikin motar,

murmushi yayi ya shiga driver's seat ya tada motar suna tafe suna hira ka

ɗ

an-ka

ɗ

an PGn dai da bata je ba kenan don NB ne venue

ɗ

in a nan ya ajiyeta ba shi ya tafi ba sai kusan 15 mins after 9 shima don ta matsa ne. Shi ma sai da ya kafa shara

ɗ

in she should

call him da rana kafin, bu

ɗ

e motar ta yi da gaggawa ta fita don ta ga shigar lecturern na su kusan 10 minutes kenan.

Sallama tayi masa ta fita tana jin shi yana mata tsiya wai tana tsoron lecturern kar ya hanata shiga class, ita dai bata tanka ba don b

urinta ya tafi. Ƙofar hall

ɗ

in ta nufa ai ko kamar yanda tayi expecting a tsattsaye ta ga students

ɗ

in da ya hana shiga class don dama policyn shi in dai har ya shiga babu wanda zai shiga bayan shi. Wa'inda ke tsaye ko suna ganinta suka fara kiran sunanta

'' ASH''

''Witchie''.

Tsayawa tayi tana duban Saka

ɗ

a

ɗ

i da ke gefenta yana dariya yana cewa '' be like say im go let us enter''.

''You think so?".

''Yes, ke zaki shige mu biyoki a baya''.

Ta

ɓ

e baki tayi tana cewa '' or rather in juya hostel

kawai ba, You know say I no like wahala''.

''We know, let's give it a try'' ya furta da sauri sauran da ke gefenta suma suka ha

ɗ

a baki wurin cewa '' Please''.

Idanu ta rintse ta bu

ɗ

e kana ta wuce gaba tana

ɗ

an tura ƙofar da aka rufe

ɗ

in sai dai ba

ta shiga ba sai kanta ta tura, da sauri duka students da lecturern suka zubo mata idanu. Idanu ya

ɗ

an bu

ɗ

e yana kallonta ya kuma kalli front seat da ta saba zama bata nan. Nan ko yace '' That's why the class seems a bit off, ashe ASH was not in class what

happened? Why are you late?".

''It was.....''

Bai jira ta gama magana ba yace '' never mind, you can enter and the others too'' da sauri ta furta thank you sir, cikeda sakin ajiyar zuciya don ya taimake ta inda ya barta sai ta ƙarasa ma bata san me

zata ce ba. Shiga ciki suka yi da sauran ƴan wajen suma suna ta fa

ɗ

in thanks sir wanda yake annoying lecturern, bayan sun zazzauna ne ya koma podium

ɗ

in shi yana cewa '' y'all know why I did let them enter right? It's because she's never late in my class

always punctual and attentive'' students da yawa ta

ɓ

a baki suka yi duk da sun san gaskiya ya fa

ɗ

i amma ai hakan bai shafe su ba, ganin ba su bawa hirar muhimmanci ba ne ya sanya shi ajiye ta yana cigaba da lectures

ɗ

in da ya fara mostly yana tsayawa asking

questions which he's directing it to Adeeyah and as usual tana ba shi amsa har ma tayi explanation fiye da yanda yake yi ma.

Ta fito daga class

ɗ

in ta na ƙarshe by 3pm ne ta tarda 2 misscalls daga Amah, murmushi ta saki da mamakin kiran nata sai ta b

ayar da hakan da cewa ko wani abun zata gaya mata da ta manta. Kiran ta mayar tana tafiya towards PG hostel

ɗ

in da ta so zuwa tun safe amma zuwan Rhid ya hana ta. A daidai lokacin ne kuma Amahn ta amsa kiran, gaishe da ita tayi ta amsa itama tana tambayart

a class

ɗ

in ta na ranar Alhamdulillah ta amsa tana sauraron maganar Amah dake cewa '' You have to come home this weekend, your Affah Insists ''.

''But Amah...''

''No Buts Love just do as you are told''.

''Okay Amah but sai Saturday zan samu dama

r zuwa in shaa Allah sai in dawo Monday early morning ''.

''I'd tell him so, bye bye then'' tana fa

ɗ

in hakan ta yanke wayar, numfashi ta ajiye haka nan take jin fargabar ha

ɗ

uwarsu da Affahn nasu musamman da ba ta san dalilin shi na kafewa akan sai ta zo

gida ba.

Power bank

ɗ

in nata ta amsa ta wuce hostel

ɗ

in su, kamar jiya yau ma Mufee ba ta dawo ba. Sai dai bata kwanta ba couscous ta dafa ta ci nata kafin ta jawo system

ɗ

in ta tana aiki rabi kuma tana waya da Rhidwan da ya sata gaba da kiraye-kirayen

wayar shi, ba ta da yanda ta iya dole ta

ɗ

aga tana amsawa lazily wanda hakan da take yi ba ƙaramin kashe shi yake yi ba.

Viaducts Apartments, Auckland New Zealand.

Ɗ

un

ɗ

in

ɗ

akin yake ba ka ganin haske sai hayaƙin da ya kaure

ɗ

akin wanda yake fitowa

daga sigarin da ake sha, yayinda karan shi ma yake bada

ɗ

an haske. Zuƙa

ɗ

aya aka yi wa sigarin ya ƙare akan ash tray ya ajiye sauran karan babu komai, lightern da ya kuma kunnawa ya ƙara lighting wani tabar hakan ne ya

ɗ

an haska fuskar shi da ba lallai ka

gane kalar shi ba.

Kira ne ya shigo wayar shi dogon tsaki ya saki yana kallon gefen shi, sunan Snake ne yake yawo kan screen

ɗ

in. Hannu ya kai ya

ɗ

aga rejecting yayi yana maida kiran, wanda babu

ɓ

ata lokaci wancan

ɗ

in ya

ɗ

aga ba tare da yayi magana b

a yace ''Uhmm?".

Wata magana da aka fa

ɗ

a daga can gefen ne ya sanya shi cewa'' what the heck Sna?!''.

Ƙ

ara bayani aka masa ta can hannun yayi shiru yana sauraren abinda ake cewa sai da ya kammala bayanin ne ya iya cewa '' that means that you didn't d

o your work well, and it was your fault''.

''I don't care Sna you know quite well I don't accept failure, so you have to make up for that''.

''It's just that we were squared we never expect anything like that''.

''Who the hell he is?''.

''It's not a he Scor but a she,mace ce ''.

''What the fuck?!" Ya furta yana zabura cikeda takaicin jin wai mace ce ta

ɓ

ata masa aikin da ya yiwa mugun tanadi, duk yanda Snake

ɗ

in ya so masa bayani Scorpion

ɗ

in bai ko saurare shi ba saboda masifar da

yake cin shi abu

ɗ

aya ne kawai ya iya fa

ɗ

a masa '' Find her!!!".

Yana fa

ɗ

in haka ya yanke wayar yana sakin wani kalar haki a jiggace yayi jifa da wayar a bayyane ya furta '' how dare she?! How dare someone decode what I encode?!" Ya ƙarashe da ƙaraji ka

mar mai shirin fasa

ɗ

akin...........

CHAPTER 3

Kamar yanda suka yi shirin tafiya kamun a ranar ta Alhamis suna dawowa daga classes

ɗ

in su na ranar suka fara shiri inda da taimakon Mufee Adeeyah ta shirya cikin Buobou gown na lace baƙi da adon milk wa

nda Amah ce ta siyan musu same color da Ateeyah sai dai ita an mata riga da skirt kamar yanda ta fi ƙwarewa a sakawa ita kuma tayi Buobou don ba ta son kayan da zai matse ta ko ka

ɗ

an.

Sosai kayan ya fito da kalarta da take ji fair haka don ba fara ba ce

tas amma ba ruwan tarwa

ɗ

a ba ne tana dai tsaka tsakiya, a kamammin fuska duk da tana kama da TeeTeen amma ta fita kyau ainun musamman ma da ya zama ba ta lalata skin colorn ta ba tana nan a yanda take ba ta shafa kowani kalar mai sai Nivea da Stella showe

r gel

ɗ

in da take wanka kuma na Oriflame ne mara sa haske. A ƙyale-ƙyale na rayuwa kuma babu wani abinda yake burge ta a jikinta ma babu wani abun da zai iya burge kowa duk da tana da dirin da ko makaho ya shafa zai iya tabbatar da hakan amma kalar suturar

ta kan

ɓ

oye hakan. A komai na rayuwa she's exactly the opposite

of TeeTee wata sa'ilin ma in zaka ha

ɗ

u da su daban ma ba lallai ka lura cewa suna yanayi ba, don ita gashin da TeeTeen ta ƙara saboda DeeDeen ta fita ne amma ita kuma locking nata gashin tayi

tun tana secondary school. Sai dai in ya mata tsufa a warware a sake wani duk bayan 2 weeks kuma take zuwa a wanke a gyara mata shi amma ko kusa ba ta kitso har ji ma take yi wani lokacin kamar a yanke mata shi.

Amma yau Bouboun da ta sanya ya mata kya

u ainun musamman da Mufeen ta zauna ta yi waxing gaban gashin ya kwanta sosai, sannan ta mata

ɗ

auri simple amma ya

ɗ

an bayyana gaban gashin sai gyalen Chantilly da ya hau da kayan sosai. Sai dai a duk kyan da tayi da magiyar da Mufeen tayi akan ta saka was

u ƴan wedges nata ƙi tayi don tace ta barta da crocs

ɗ

in ta su zata saka, babu yanda ta iya haka ta ƙyaleta jakar ma don ta dame ta ne ta riƙeta zama tayi a bunk tana jirar Mufee ta kammala sai ga kiran Rhidwan cikeda yatsine ta

ɗ

aga don duk da tana son sh

i ta tsani nacin kira da zuwa.

Yanzun ma abinda ba ta son ya sanar mata wai yana cikin school ya kusa hostel

ɗ

in su, cikeda tura baki tace masa ai za su fita ne ai ko yace in sun shirya sai ya sauke su a wajen bikin. Ji tayi kamar ta ce ya koma ba sai

ya ƙaraso ba , dama ce masa tayi sun riga da sun tafi amma yanzu ba dama tunda yana hanya.

Mufee da ke

ɗ

aura

ɗ

ankwali ne ta dubeta tana cewa '' what?".

''Rhid ne zai zo wai'' ta amsa not able to hide her annoyance.

Dariya ta saki tana cewa '' Ni

fa ina son wannan soyayyar taku as, one time sweet and lovey dovey but another time kuma you'd be acting as if he's forcing himself on you bayan it's so obvious that he loves you ''.

''Na ji Malama ki yi ki shirya, he'd be here any moment''.

Uhmm ta

furta yanzu kam ta ƙoƙarta ainun wurin ha

ɗ

iye dariyarta tana jinjina kai tabbas Deeyah and Teeyah have quite something in common.

Cigaba da

ɗ

aurinta tayi har sanda ya iso Deeyahn ce ta fita tana shaida mata yana waje waiting for them. Fita tayi ita kum

a ta ƙarasa ta rufo musu

ɗ

akin tana binta a baya.

Tun da ta fito yayi tsaye cur da idanun shi yana kallonta kai kace wacce aka canjawa halitta, she looks as exactly kamar ran da ya fara ganinta kyakkyawa da kyawawan takunta da ke kuma haskaka yanayin

ta zai iya cewa tundaga ranar bai kuma ganinta irin haka ba but be just doesn't care not because bai son ganinta a hakan but because bai son ya nuna mata kamar kwalliyan ta ya kawo shi yanda yake kallon nata kuwa ya kuma sakawa ta na jinta very self-consci

ous karon farko a rayuwarta she isn't someone that gives a damn about how she looks amma a yau ta ji kamar ta tsaya ta tambayi mutanen da suke a gefen ta '' how does she looks?".

Inda Allah ya taimake ta bata kai ga tambayar ba ya ba ta amsa da '' Ya Il

ahiy,Bae you look so gorgeous ''.

Ɗ

an duƙar da kai tayi tana sakin ajiyar zuciya all the weirdness da take ji yana sauka a hankali, murmushin da ba ta san yana ƙara mata kyau ba tayi tana

ɗ

an juya masa idanu ba tare da ta sani ba. Wani shegen murmushi y

a saki yana ciro wayar shi yana

ɗ

aukarta hoto, ji tayi kamar ana wani ma ya

ɗ

auketa amma ta rasa ta ina mai

ɗ

aukar yake waige ta fara yi sai dai babu kowa a gefen nata. Dawo da kallonta tayi kan shi tana jin duk excitement

ɗ

in ta na guduwa don a duniya ta

tsani ta jita somehow watched, sosai canjin nata ya ba shi mamaki sai dai kafin ya kai ga fa

ɗ

in wani abu Mufee ta fito sai kawai ta saki ajiyar zuciya tana nufar ƙofar motar bin ta yayi ya bu

ɗ

e mata ta shiga ta zauna daidai da isowarta wajen jin suna gaisa

wa ya sanya ta tuna ' wai ashe fa ba su gaisa ba'.

Sai da ya tada motar kafin ta iya gaishe shin ya amsa a ƙasan maƙoshi yana tambayar ta inda suka nufa, Ahmadu Doka ta amsa masa a hankali.

''Ta wurin MTN office?".

''Yeah ta nan''.

''Ta s

inger za mu fita kenan'' ya furta yana jan motar zuwa gate, hira suke yi ƙasa-ƙasa inda ba ta wani ja da nisa ba ta sake saboda tabbas Rhid gwanin iya kawar da damuwa ne da

ɓ

acin rai without even trying hard to do that.

Ficewar su daga harabar hos

tel

ɗ

in ya sanya shi fitowa daga ma

ɓ

oyar shi dake nan tsakanin Royal Tropicanan da kuma PG yana sakin ajiyar zuciya, kallon gefen shi yayi ya tabbatar babu wanda yake wucewa gyara p-cap

ɗ

in shi yayi yana sakin wani makirin murmushi a hankali yace '' Su kum

a dukan su mayun maza ne kenan? But what's the relationship between her and this guy and who even is he?".

Wannan tambayar kan shi yayi mawa amma kuma sai ya ji kamar wani assignment ne ya ƙaru a kan wanda aka ba shin, wani machine da ke parke na dispat

ch riders ya nufa ya haye yana mai lissafi a kan shi. Bai bi su ba don bai cikin aikin shi for that day don task

ɗ

in da aka ba shi kawai ya nemo wacece twin

ɗ

in Teeyah Hussein Shamaki ne nothing more nothing less, a yau kuma ya samu duka information

ɗ

in da

yake nema a kan ta har ma da ƙari tabbas tips

ɗ

in shi na ranar sai ya fi na kullum. Jan machine

ɗ

in shi yayi zuwa

ɗ

ayan assignment

ɗ

in don an tabbatar masa da yau TeeTeen zata fita kuma har location

ɗ

in inda zata jen an tura masa.

Seems like we too h

ave a stalker

😶

.

Around 4:30 suka iso venuen kamun inda ake yi a cikin gidan su amaryan, wurin ya ha

ɗ

u ainun musamman yanda aka yi decorating wajen ga ƴan mata sun ci ankon adire sai kaiwa suke da komowa. Su na zuwa Aunty Mami ce ta musu iso cikeda

jin da

ɗ

in zuwan nasu don akwai ta da son mutane sosai kuma bikin ƙanwar mijinta ake yi ga shi ba ta da ƴanuwa da yawa a Kadunan duk sauran suna can Zaria wainda suke garin duk sun zo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login