Showing 120001 words to 123000 words out of 232724 words

Chapter 41 - JIRWAYE COMPLETE

29 Aug 2026

100

irin na har abadan nan shiyasa itama take masa hauka.

Sabeer Katchalla dai ganin ba ma ta shi suke ba sai kallon juna suke ya sanya shi miƙewa ba tare da ya musu sallama ba yayi wucewar shi, tana ganin ya tafi ta bu

ɗ

e murya tace '' This is stalking

scor in case you don't know and i can sue you for that''.

''Go ahead dear, sue me kin ji ko?".

Harara ta jefa masa tana maida kan ta kan waya, shi ko yanda ta yin sai ya sanya shi murmushi. Ko da aka kawo mata tean sai ya amsa ya fara sha baya

n ya sake bada ordern wani, ba ta tanka masa ba sai danna waya take yi ba ta san abinda ya sa ta cigaba da zama a wurin ba da ta yi tafiyar ta in ya so ya ci kan shi shi

ɗ

aya. Gyaran murya yayi yana cewa '' I love this dress, that's how my woman should dre

ss like''.

''Ashe ma, so you have a woman ban sani ba'' ta ƙarashe sarcastically.

''Yes, kuma tayi kyau sosai. Anya ba zan shiga gida yau ba? In ya so kafin shekara ta ƙare an yi bikin mu".

''Ga ka ga hanyar gidan nan Scor sai ka dawo''.

''I hate sarcasm Trouble''.

''And i love it''.

''And i love you'' shima ya furta yana kallonta cikin idanu.

Kawar da kai tayi ba tareda ta yi magana ba, a haka har waitress

ɗ

in ta dawo Mocha latte ta kawo mata da wani cookies

ɗ

in. Kallon shi tay

i tana cewa '' idan ban sha fa?".

''I know you like it so much, and chocolates too''.

Tura baki tayi ta fara sha a tsanake, shikuma yana morewa kallon ta. Ko da ta kammala ba ta iya tashi ba sai da Amah ta kira tana tambayar tana ina. Ce mata tayi

yanzu zata dawo, tana miƙewa ta

ɗ

auki bag

ɗ

in ta. Shima tashi yayi ya rako ta har wurin motar ta, sai da ya ga tashin ta kafin ya shiga tashi ya bar wurin.

ATEEYAH

Ranar ta ga tarairaya daga wurin Ridh kamar zai lashe ta, ya kai ta wata duniyar so

mai tsayawa a rai da fasa zuciya. Sai da ta ji kamar ta fi kowace mace dacen samun masoyi, wanda shi ma kusan hakan take a wurin shi. Bai ta

ɓ

a zaton zai ji da

ɗ

in rayuwa da ita, he fantasized his whole life da DeeDee komai na rayuwarsa ita ce. Sai dai a ya

nzu yanda take shayar da shi mamaki take yin dai-dai da tsarin shi ya sanya shi gane da ita ka

ɗ

ai ya dace a rayuwar nan ba wata ba, har ma yake tunanin inda Dee ya aura anya zai iya samun abinda yake samu yanzu kuwa?.

Kullum ya fita he's looking forwa

rd to going back to her, duk wani motsin shi ita ce a naniƙe a ran shi. Ko patient yake dubawa zancen shi matar shi ne ke masa yawo, tana fita sai ya yi mata imessage yana tambayar yanda take. Streaks ko ya zame sabo kamar irin ƴanmatan nan da basu da wani

damuwa sai shi, ko me take yi sai ta tura masa haka shima. In kuma suka koma gida suna maƙale cikin juna, sun

ɗ

auki komai da kowa sun ajiye shi behind them.

Wasu are in love ooo.

Months later.

Rayuwa na cigaba da tafiya same pattern babu ab

inda ya canja na daga rayuwar Dee sai abinda ba a rasa ba, Scor yana nan sai dai ya rage zuwa wurin Dee sai dai kiran waya shima ba kowani lokaci ba musamman da aka koma school. Shi ma kuma ya koma bakin aikin shi, tunda shekarar ta fara ya bu

ɗ

e sabon Tech

hub

ɗ

in da bata san da shi ba duk kuma iya ƙwaƙwar ta ya ƙi fa

ɗ

a mata tayi fushin har ta haƙura ta sauko. Ta fannin soyayyar shi kuwa zuwa yanzu ta yarda ta fa

ɗ

a son shi sosai, duk da bata nuna masa ko a magana amma fa ta daina hararar shi in yazo wurinta

a hostel ko ya

ɗ

auketa suka fita yawon restaurants

ɗ

in da suke yanzu. A wannan tsukin ko Adeeyah bata sanarwa ba balle Amah, a sirrance take kayanta amma tabbas wanda akewa ya san ana yi duk yanda ta kai ga boyewa.

Ko waye ma ai dole ya sani

Ba

yawa ayi manage kaina ciwo yake yi, may be gobe a samu biyu in shaa Allah.

Deejasmah

💜🦂

CHAPTER 52

Yau tana tashi da safe gidan Tee tayi niyyar zuwa, don haka tana wanka ko breakfast ba tayi ba ta zura hijabinta dogo kan riga da wandonta. S

allama ta wa Mufee ta ja motar ta zuwa gidan. Kamar wancan ranar da mai gadin ya tsura mata idanu da mamaki yau ma haka ya mata, ita dai murmushi ta saki tana

ɗ

aga masa hannu tayi shigewar ta. Knocking ta yi a ƙofar kafin ta tura ta shiga da sallama, babu

kowa a parlorn sai dai a gyare yake tsaf ga kuma dining a shirye sai ƙamshi ke tashi. Wayarta ta zaro tana ƙoƙarin kiran Teen, na Scor na shigowa. Kallon lokaci tayi tana cewa ''safiyar taka ta yi ba''.

Sai da ta tura baki kafin ta

ɗ

aga ba tareda ta

yi magana ba, murmushi ya saki yana cewa '' good morning Trouble ''.

''Ni fa ban son sunan nan, besides ni ya kamata in ke kiran ka haka not the other way round''.

''Kin san me ya sa nake kiran ki hakan? Hana ni bacci fa kike yi Trouble ko nim

a ina hana ki ne? ''.

Lumshe idanu tayi ta bu

ɗ

e tace '' kana hana ni da kiran wayar ka mana, ko ban kasa don Allah ba na kasa don damun ka''.

''Ki ji tsoron Allah Trouble, ke da kike kashe wayar ki in ta kira ban samu''.

''In ban kashe ba da

mu na zaka yi''.

''Ni nake damun ki ko Trouble?".

''Isn't it obvious? Na ji ka so excited this morning what's up''.

''I'm not excited, talking with you is what's exciting me''.

''Uhmm, yayi''.

''Kina ina haka?".

''Ka fi kowa s

anin inda na je Scor, shiyasa ma ka kirani''.

"Da na so ne ki fa

ɗ

i da kan ki, but meyasa kika je?".

''Gidan sister na ne fa''.

''I know but it is also that guy's house''.

''Kana ma da bakin magana sai kace ba kai ka hana ni zama a gidan ba'

'.

''Ƙaddara dai, not me''.

''Kar ka ƙullawa ƙaddara sharri Scor, ka sani''.

''Well ni ne, and I'm so glad i did''.

Shiru ta masa bata tanka ba sakamakon jiyo muryar Tee tana cewa '' wallahi ba wani nan, wayon kan ne ban sani''.

A ca

n ƙasa shi kuma yana cewa '' Allah Bae ba abinda kike tunani zan miki ba, magana fa zan gaya miki''.

''Ka fa

ɗ

i a nan ai ina jin ka......'' Maganar ce ta maƙale sakamakon ganin Dee zaune, da sauri tace '' Ashe da gaske kike?".

''Eh mana, muna ƴar

wannan wasan da ke ne?".

Ta ƙarashe tana duban ta, wani soft crop top kalar pink ne a jikinta mai crow neck sai wandon shi irin mai mannewar nan a jiki same colour. Ba yau ta saba ganinta cikin wannan kayan ba saboda ko a can gida ba ta da kayan da ya

fi su amma na yau sai ya bata kunya don ta san mijinta tayi wa kwalliya. Ita ko Tee kallon Ridh da ya tsaya a corridor tayi ƙirjinta yana bugawa, ba ta son ya fita ko ka

ɗ

an Dee ta gan shi a yanayin da yake babu ko riga. Shi ma ya gane kallon me take masa

don haka da sauri ya koma ciki ita kuma ta ƙaraso tana cewa '' I thought yanda kika saba min kika yi, how far?".

''Fine ya gidan?" Kafin ta amsa ta maida zancen ta kan Scor tana cewa '' have to go okay?".

''Zan zo anjima in kin dawo''.

''Gid

an mu zan wuce daga nan''.

''Ko ma ina ne zan zo ni dai''.

''Bye'' ta furta ba tareda ta amsa masa ba ta dubi Teen da sai yanzu ta ga yanda tayi kyau sosai, ko da yake ta kwana biyu bata ganta ba tunda tayi resuming school ba su ha

ɗ

u ba.

''Am

arya mai capacity'' ta furta tana murmushi.

Ji tayi maganar ya nushe ta a take wannan mafarkin ya kuma fa

ɗ

o mata a rai, da sauri tace '' abeggi wata amarya a nan, matar cushe dai kin san ance wai ba ma daraja''.

''I've told you time without number

ki daina kirawa kan ki wannan sunan, kina da darajar ki da kima and nobody is in the position to say otherwise''.

''Haka dai kike cewa''.

''Akwai wani abu da yake faruwa ne tsakanin ku Ateeyah? Is he treating you somehow?".

Kai ta girgiza ta

na cewa '' No kawai dai hankali na ba a kwance yake ba Dee, ji nake kamar yana tare da ni ne akan dole. Ko kuma yana tarayya da ni saboda ina da fuskar ki da kamannin ki''.

Hararar ta tayi tana cewa '' A'uzubillahi wani irin magana kike yi haka Tee?".

''Ba zaki gane me nake magana a kai bane Dee, kin ta

ɓ

a jin kina tareda mutum amma zuciyar shi tana wani wuri?".

Kai ta girgiza tana cewa '' Hasashe ne amma ba gaskiya ba, in kina zargin hakan then it means that you have to work for it. Abu

ɗ

ay

a ne ba zan yarda ki

ɗ

auka ba, shi ne yayi degrading

ɗ

in ki ko wulaƙanci bayan nan kuma.....''

''He's not doing such, kin san ma ni ba'a haife ni da jure wulaƙancin

ɗ

a namiji ba. You know it like i do''.

''Na sani, to yanzu fa?".

''Ba laif

i''.

''To ki cirewa ranki damuwar komai, zaki ga yana miki abinda ya dace in shaa Allah''.

''Uhumm, ya mutumin ki fa? Oh my gosh barin kira Ray ya fito lokaci na ƙurewa baki yi breakfast ba ko?".

Murmushi kawai tayi yayinda ita kuma ta miƙe

zuwa cikin

ɗ

akin bayan kamar minti uku sai ga shi ya fito da jallabiya, gaisawa suka yi irin yanda suka saba idan suka ha

ɗ

u yanzu kafin suka nufi dining. Sai yanzu ne take ganin wallan zuwanta gidan nan, meyasa ba ta bari zuwa anjima ba sai tazo may be ma

ya fita time

ɗ

in. Duk sai taji ta a mugun takure haka shi ma, gaba

ɗ

aya breakfast

ɗ

in babu da

ɗ

i ita ta fara miƙewa ta wuce

ɗ

akin Dee. Kwanciya tayi tana lissafin rayuwa, da yanzu fa ita ce matar shi ko? Oh rayuwa da ƙaddara ababe ne masu cikeda tarin ƙaluba

le.

Shi ma bai da

ɗ

e ba ya fita sai lokacin ta fito suka fara hira da Tee, wanda ko da wasa ba ta yarda zancen Scorpion ya shigo ciki ba duk yanda ta tambaya sai ta goce mata don bata son a yi judging

ɗ

in ta kan son da take masa ko ka

ɗ

an. Ba ita ta t

afi ba sai can yamma, direct gida ta wuce Amah ka

ɗ

ai ta samu a zaune tayi nisa cikin tunani tana ganinta ko sai da ta zabura tana cewa '' why do you come today? Affahn ku ya kira ki ne?".

Kai ta girgiza tana cewa '' wani abu ya faru ne Amah?".

''

Sai wani abu ya faru kafin in tambaye ki? Answer me my friend'' ta furta da

ɗ

an tsawa kamar ba ita ba.

''Sorry Amah bai kira ni ba''.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauke tana cewa '' Alhamdulillah, to maza ki zo ki koma mun gode da ziyara''.

''Am

ah what's going on? Kina tsorata ni''.

''Kina ji ko? Ki koma school idan Affahn ku ya kira ki kar ki yarda ki ce masa you are free kin ji ko?".

''Innalillahi Amah, something is going on and you don't want to tell me''.

''Zan miki voicenote

ta WhatsApp and explain everything, yanzu dai please ki tafi kar ya zo ya same ki''.

Kai ta gya

ɗ

a tana miƙewa tsaye tace '' toh Amah''.

Itama miƙewa tayi suka nufi ƙofar barin parlorn tana cewa '' Allah ya miki albarka Adeeyah''.

Suna isa par

king lot motar Affah ta shigo gidan, runtse idanu tayi tana maimaita salati cikeda jin komai yana kwance mata. Ita ko tsayawa tayi ƙyam tana exchanging kallon daga kan shi zuwa ita, har suka yi parking.

Mudi ne ya bu

ɗ

e masa mota ya fito, kallon su yayi

yanda suka yin ko ba a fa

ɗ

a masa ba ya san guduwa suka kusa yi amma sai ya maze yace '' kin zo gidan kenan?".

''Eh Affah, dama mun je wani summit ne a Zaria shi ne na tsaya mu gaisa yanzu zan koma''.

''Ai neman ki nake yi mu je ciki'' yana fa

ɗ

in

haka yayi shigewar shi ya bar su nan tsaye. Ƴar musayar kallo suka yi tsakanin su kafin suka mara masa baya kamar kajin da ƙwai ya fashewa a ciki. A kan kujerar parlor suka same shi zaune, Amah ta zauna gefen shi ita kuma ta zauna ƙasa tana gaishe shi. Am

sawa yayi yana tambayar ta ya makaranta, kafin ya

ɗ

aura da cewa '' da baki zo ba ma da na sanya Mudi yaje ya

ɗ

auko min ke anjiman nan don akwai magana mai muhimmanci da nake son mu yi da ke''.

Ya ƙare yana duban matar shi take kamar ba ta wurin,

ɗ

an mur

mushi ya saki zargin shi yana tabbata. Ta ji hirar shi da me babban

ɗ

aki

ɗ

azu, shiyasa take masa haka amma bai nuna mata ba sai cewa da yayi '' well yau dai dole ki kwana a nan, don gobe kuna da aiki sosai''.

''Wani abu zai faru ne Jarmai?".

''Eh

Turai, gobe zamu yi baƙo ne a nan gidan In shaa Allah''.

''Baƙo kuma?".

''Eh MUSHARRAF ne zai zo wurin Adeeyah''.

''Waye Musharraf kuma Affah?".

''Mijin da zaki aura in shaa Allah''.

Gabaki

ɗ

ayan su ne suka zaro idanu suna kallon

shi a tsorace........

Deejasmah

💜🦂

CHAPTER 53

BAREWA EMIRATE

Ƙ

ishingi

ɗ

e take kan kilisa tana duba saƙo a wayarta a kayi sallama, amsawa tayi tana kallon mai shigowa. Jakadiya ce ta ƙaraso gabanta cikeda girmamawa tace '' Allah ya taimaki

Zakanyar Barewa barkan ki da hutawa''.

Kai ta gya

ɗ

a mata tana mai cigaba da kallon wayar ba tareda ta amsa ba, sai can kuma tace '' Barka''.

''Zakanyar Barewa, Yarima Musharraf yana neman iso''.

''A ce masa ya shigo''.

''An gama uwargijiya

ta, ki huta lafiya '' tana fa

ɗ

in haka ta tashi ta fita.

Ko minti uku ba tayi ba wani matashi ya shigo

ɗ

akin dogo ne sosai sankacece, bai da kauri sai manyan ga

ɓɓ

ai. Baƙi ne sosai amma hutu da gyara sun sa kalar skin

ɗ

in na shi yin kyau sosai, amma fa ak

wai kyau da zubin halitta kamar shi yayi kan shi. Sanye yake cikin kaftan kalar sky blue an masa Moroccan design da ya dace da kayan, kan shi sanye cikin dara baƙa. Idanun shi kuma eyeglasses ne mai farin kwalba.

Zama yayi a gabanta yana dubanta yace

'' Barka da yamma, Mammah''.

''Sai yanzu ka ga damar shigowa?" Ta tambaya tana duban shi.

''Ki yi haƙuri Mammah'' ya amsa yana duƙar da kan shi.

''Meyasa kake son

ɓ

ata min rai ne Musharraf? Uhmm magana guda

ɗ

aya ana ta faman yin ta sai kace ƙa

ramin yaro?".

''Mammah ki gafarce ni, an saka ni a tsaka mai wuya ne. Kin hore mu da cika alƙawari komai wahalar shi, amma....''

''Amma me? Kana son cewa ni ke son saka ka karya alƙawarin da ka

ɗ

auka ne ko me? Meyasa ka fiya taurin kai ne?".

''Ki yi haƙuri''.

''Ba haƙuri nake son ji ba, so nake kace ka amsa maganar Takawa kawai''.

''Na amsa, in Shaa Allah ''.

''Gobe ka shirya kace ka gan ta a Kaduna, Musaddiq ya raka ka''.

''In shaa Allah''.

''Yawwa Babana, Allah ya m

aka albarka ka ji''.

Ameen ya amsa mata a ƙasan maƙoshi ƙunci yana game masa rai, kallon shi tayi tausayin shi yana kama ta. Ta san shi

ɗ

in mai biyayya ne amma fa akwai kafiya musamman kan abinda yake so, tunda yace bai son yarinyar nan akwai wanda yake

so tanƙwara shi zai masa wahala. Shiyasa ta

ɓ

ullo masa ta wannan hanyar don ta san lallashi ba zai ta

ɓ

a yi mata ba. Duban ta yayi yana cewa '' zan shiga wurin Mai babban

ɗ

aki in kin min izini''.

''Na maka izini

ɗ

an Albarka, ka gaishe min da ita nima

zan shiga zuwa da safe''.

Da kai ya amsa mata yana miƙewa tsaye ya furta na bar ki lafiya, da idanu ta bi shi har ya fita. Tafiya yake yi cikeda zafin rai ko kallon gaban shi bai yi ta da

ɗ

i, balle ya amsa gaisuwar da barori ke bin shi da shi ba. Da sall

ama ya shiga wani

ɓ

angare bayi suka zube masa, ko kallon su bai yi ba balle ya amsa. Tana kan kujera sanye da gilashin ƙara ƙarfin idanu ta

ɗ

ago tana kallon shi.

''Ho Janare wa ya

ɗ

ano harsashin ne?".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login