Showing 117001 words to 120000 words out of 232724 words
yawan turo kaya Nigeria ya nufa, akwai sanayya tsakanin su da shi don haka bawan doguwar gaisuwa ya
shaida musu mai yake son yi wato yana da saƙo amma suna da yawa zai yi zuwa uku da motar shi kafin ya gama kawowa. A take suka bashi mota
ɗ
aya akan su tafi sai ya kwaso kayan, ya ji da
ɗ
in hakan sosai don haka tare suka koma da shi can. A wannan karon ko s
un kwaso duka, ko da ya je can sun yi weighing kayan aka saka su a manyan boxes na wurin sukayi sealing da labelling kafin ya biya ku
ɗ
in service suka ba shi expected date da kayan zasu bar wurin zuwa Nigeria don bai zo da sa'a ba 2 days kenan da tura wasu
can
ɗ
in sai nan da 12 days zasu tura na shi. Shi dai bai damu ba don as long as kayan sun bar wurin shi tohm hankalin shi ya kwanta, ranar yayi baccin tsanake don bai ƙi ma a ranar FBI su kawo hari ba as long as basu samu kayan shi ba da sauƙi. Sai da ya k
wantar ne ya turawa Dee message
ɗ
in baya nan, ta karanta amma bata yi replying ba dama ya san ba zata yi ba shima bai jira ba ya koma ya kwanta.
Sai da safe ne ya ga wautar tura mata inda yake da yayi don a yanda ya san ta da mugun kaifin basira yanzu
zata hada pieces
ɗ
in su bata abu guda, zata iya turawa DIA fa. Kai ya girgiza yace she can't, wankan shi ma ya sha ya fita ya zaga gari sai dare ya dawo. Duk da bai da abun yi a ƙasar bai dawo ba sai da ya tabbatar an turo da kayan shi ya
ɗ
au saiti a tsak
iyar ruwa kafin ya tattaro sauran komatsan shi yayi sallama da Agent
ɗ
in shi ya dawo gida Nigeria.
Shigowar dare yayi Snake ya je ya
ɗ
auko shi, tun a hanya yake jera masa tambayoyi kan Adeeyah tun yana amsawa har ya masa shiru. Dan dole ya ƙyale shi
don ya san halin ƴan kayan shi akwai rikici, ya kuma san me yake nufi da komai amma bai ga damar tanka masa ba. Washegari ta kama Saturday ya ji haushi sosai amma ba yanda ya iya sai ma wani kira da aka masa a gida dan dole ya tafi, amma bai da
ɗ
e ba kwana
uku yayi ya dawo ranar Wednesday da yamma. Ai ko alhamis ya dirarwa Adeeyah tana fitowa daga office, yau bata
ɗ
auko mota ba napep ta hau don ta gaji da driving shikuma drivern su baya nan yana off. Tsaye take a kan titi yau dogon jilbab ta sanya kalar tume
ric, wando baƙi ne a jikinta sai takalmin ta slides na Sketchers Ash. Sunhat ne a kanta sai eyeglasses photochrome tana rataye da jakarta a baya, ji tayi mutum ya tsaya a gefen ta da sauri ta
ɗ
ago kai idanunta suka sauka kan shi yana mata wani munafikin mu
rmushi........
Deejasmah
💜🦂
CHAPTER 50
''Hey dear'' ya furta a daidai san da idanun su suka ha
ɗ
u.
Tura baki tayi tana cewa '' what are you doing here?".
''Babu, just passing by and i happened to see then i decide to say hi''.
Danne da
riyar da ya ciyo ta tayi tana cewa '' uhmm, nice to sannun ka''.
Daga haka ta sa hannu tana tare abun hawa, duban ta yayi yace '' don't you missed me?".
Kai ta girgiza tace '' why would i?".
''Oh my Trouble, i see you look good by the way i
approved of this hijab''.
Cije baki tayi ta san da gangan ya fa
ɗ
i haka don hijabin da ta sanya
ɗ
aya daga cikin wainda ya kawo ne, da ta san yau zai zo da bata sanya ba. Abinda ba ta sani ba ko kusa bai gane hijabin ba, don ba shi yayi shopping
ɗ
in ba
order yayi yace a ha
ɗ
a masa colors don bai san wainda zasu iya mata ba.
Kuma cewa yayi '' come lemme drop you home''.
''Ni in shiga motar ka? Har abada in shaa Allah, ni
ɗ
an matsa min please''.
''Meyasa ba zaki shiga ba?".
''Ka fi kowa
sanin dalili, motar ka ai lahira ce in ka ganni a can kuma kai ni aka yi''.
''Ohh '' ya furta yana dariya, kallon ƙasan idanu ta masa tana ƙarewa fuskar shi kallo ta glass
ɗ
in ta. A take ƙirjin ta ya buga na abinda ta gani, kamar silicon idanun ta suk
e gane mata don ba ya ko motsi ma. 'hakan yana nufin all these while fuskar roba yake yawo da ita? To shi Snake fa? Anya su ƴan biyu ne ko dai siblings or friends?'.
''Ya zamu yi kenan ban son kina tsayuwa a ranar nan Trouble'' ya furta yana ƙoƙarin yat
sine amma fuskar bata motsawa ko ka
ɗ
an. Sai yanzu komai yake dawo mata ƙwaƙwalwa tabbas su ba wawaye ba ne inda ace fuskar su ce ta ainihi ba zasu yarda su sake mata ita tana ganin su kullu yaumin ba. Amma ba zata nuna masa ta sani ba har sai ta bar wurin
nan kuma a take wani ƙaimi yazo mata rai, zata cigaba da pretending
ɗ
in nan wurin nuna masa tana son shi har zuwa ranar da zata san asalin fuskar shi. That's all she need wajen tona masa asiri ba wani linking
ɗ
in shi da su Snake ba, in har ta san fuskar sh
i to sunan shi mai sauƙi ne bincike ma zai zame mata kamar shan ruwa ba wahala.........
Gyaran muryar da ya mata ne ya katse ta daga tunanin da ta tafi, ajiyar zuciya ta sauke ta dube shi. Ita yake kallo idanun nan ƙyar a kanta yace '' tunanin me kike
yi ne? Hope it's mine Trouble?".
''It can never be you keep hoping'' ta ƙarashe tana murgu
ɗ
a masa baki. Yanda ta yin sosai ya bashi dariya amma ya danne yace '' Rana yana yi fa Trouble".
''Kana gudun in maka ihu ne Scor?''.
''I trust you, n
a san ba zaki iya ba''.
''Ka ga ni kuma ba zan iya yarda da kai or decisions
ɗ
in ka ba, balle har in shiga abun motar ka so ka tafi kawai'' ta ƙarashe tana tare napep
ɗ
in da ya taho gabanta tace '' Kawo '' kafin ya kai ga motsawa ta shige tana jan aji
yar zuciya.
Kallon keken yayi yana cije lips
ɗ
in shi, tabbas yarinyar nan bata san shi ba ne da har zata dinga yin gangancin ha
ɗ
a hanya da maza. Sai ya fasawa wani baki kafin zata san ko shi waye, kai ya girgiza yana ƙwafa ya shige motar shi ya ja ya
bar wurin.
Ranar yini tayi tunanin da sai da Amah ta tambayeta ko akwai abinda yake faruwa ne? Amsa
ɗ
aya ta bata cewa tana lafiya kawai period
ɗ
in ta ne yazo duk bata jin da
ɗ
i. Ko kusa ba ta yarda ba amma sanin ba ta da takamaiman hujja ya sanya ta ba
rta a haka, da sannu za ta san me yake faruwa a ƙasan ranta kafin nan kuma ba zata zafafa wurin sanin ba ko ka
ɗ
an. Ko da suka zauna cin abinci Shamaki ma sai da ya lura da yanda take yi, karon farko bayan dawowarta gidan da yake tambayar ta rayuwarta a han
nun wainda suka sace ta.
Abu
ɗ
aya da ta tanada don shi ta fa
ɗ
a masa, wato wani wuri suka kai ta cikin daji ba ta san fuskar su ba. Sai ya tambaye ta ko sun ta
ɓ
a mata wata magana kan shi ko wani na shi? Kai ta girgiza tana cewa '' ko
ɗ
aya, da alamu ma
basu san ka ba Affah. Har yanzu na gaza gane dalilin su na
ɗ
auke ni, su ba ku
ɗ
i suke so ba ba wani abu ba''.
''Saka su aka yi su
ɗ
auke ki ai, akan hakan mu ke ta bincike. Kina ji ko Adeeyah? Rayuwar duniyar nan cike take da macuta kala-kala kar ki y
arda da kowa kin ji ko?".
'Uhmm da haka ya yi deserting Tee ta ji bata son kowa sai shi
ɗ
aya' ta fa
ɗ
i a can ƙasan ran ta, amma a fili murmushi ta saki tana cewa '' in shaa Allah Affah''.
Amah ce ta jefa masa wani kallo kana ta maida kan ta zuwa D
ee tana nazartar ta, mamakin yanda take yin murna da maganar da Affahn na su take yi. Sai kuma wata zuciyar ta kwa
ɓ
e ta kan cewa '' ya za'a yi yarinya ba zata ji da
ɗ
i ba mutumin da bai kulawa da ita ya fara dubanta da kallon so?".
Yawu ta ha
ɗ
iye don b
ata da me bata amsa amma ta ƙudurce ba zata amince da duk wani shirin shi kan ta ba, zata yi yaƙin sunkuru har sai ta kai ga yin nasara shammatar shi zata yi ta yanda ba zai ta
ɓ
a tsammani ba. Don haka sai tayi murmushi kawai tana shan ruwa.
ATEEYAH
Tun ranar da Ray
ɗ
in nata ya kama ta tana waya da Beta sai ya zamana kamar an canja mata shi, a kwanakin yana yawan zaman hira da ita ya tambaye ta ya ranar ta ya kasance shi ma ya bata labarin na sa in details. Bayan nan ga son yawan ta
ɓ
a jikin ta, ba w
ai yana nuna mata a zahirance ga abinda yake nufi ba ne. A'a ya na son zama gefen ta ne a hankali kuma suna cikin hirar kafin ta ankara sai ta jita a jikin shi, ba ta ta
ɓ
a yunƙurin ƙwacewa ba don ba sabon abu bane a wurinta kawai dai tana jin effects
ɗ
in t
a
ɓ
awar tashi a kowace ga
ɓ
a ta jikin ta. Tana son shi sosai kuma tana son abinda yake muradi a tare da ita.
A yau ma hirar suke yi tana ba shi labarin wata lecturern su da ta sa wata yarinya a gaba, wai bata son ta kuma ƙiri-ƙiri take nunawa ashe wai y
arinyar budurwar mijinta ne basu sani ba sai da ya zo
ɗ
aukar ta daga school suka kici
ɓ
us ta fito class.
''Amma mijin bai da kirki, yana sane da inda matar shi take aiki ai ko zaka nemi yarinyar kar ka kuskura ka bita school don akwai high chance na ha
ɗ
u
wa da ita ko wanda ya san ta'' ya furta fuskar shi na bayyana
ɓ
acin rai.
Murmushi ta saki tana cewa '' that's what i said, it made me wonder why men are doing this ''.
''In mijin ki ne ya zaki yi?" Ya tambaya yana duban ta.
Kallon shi tayi
idanun su ya sarƙe cikin juna kafin a hankali tace '' wucewa ta zan yi kawai, i won't create a scene for myself in muka ha
ɗ
u a gida we'd deal with it ''.
Duƙowa yayi yana brushing mata kiss kafin a hankali yace '' why would you not? Ko don baki son n
aki mijin ne?".
''It has nothing to do with i love my husband or not Ray, I've lost my pride to the man that should be protecting it. I should have atleast my self respect and esteem to walk away, kar in yi losing
ɗ
in shi again a gaban
ɗ
alibai and cow
orkers''.
''That's good, but you didn't answer my question ''.
''Ray ba fa maganar so muke yi yanzu ba, ko kai kana sona ne?" Ta amsa masa tana saƙale yatsun su wuri
ɗ
aya, wani murmushi ya saki yana ha
ɗ
e lips
ɗ
in su wuri
ɗ
aya don amsar tata ba da
baki ya kamata ba a aikace ne and he's more willing to show her a lokacin. Lamarin da ya kai su ga matakin mallakar junansu a mafi tsadar yanayi, a ranar ya tabbatar Ateeyah ta shi ce shi
ɗ
aya ba su raba da wani ba balle ya samu ragowa. Shi ko daman an
ɗ
a
n ta
ɓ
a shan minti a waje sai da ya ha
ɗ
u da Adeeyah ne komai ya canja, ya
ɗ
aina ta
ɓ
a ƴar kowa sai ga shi Allah ya taimake shi tashi ta iso wurin shi lafiya.
ADEEYAH
Rayuwar su ta cigaba da tafiya same routine babu abinda ya canja zata je aiki ta d
awo, Scor zai kirata a ƙalla sau uku ko hu
ɗ
u a rana tun tana basarwa har ta fara
ɗ
agawa su yi fa
ɗ
a su shirya ko yayi fushi the following day sai ya kira. Ba dai ta daina shigar ta ba shima bai daina mata comments da kashedi ba, wanda shine yake yawan ja mu
su fa
ɗ
a a tsakanin su. Duk yanda ta kai ga shaidawa kanta pretending take yi masa zuciyar ta kan yi rawa kan hakan, duk da bata san me take ji a kan shi ba kuma bata fasa tunawa kan ta cewa shi maƙiyinta ne ta gaza.
Duk events
ɗ
in da aka saba yi a Dec
ember ta je ba tareda tsoro ko shakka ba, da yawa ma idan taje ya kan mata message na yana alfahari da ita ko abinda ta fa
ɗ
in ya mata da
ɗ
i. Hakan ke kuma saka ta jin komai yana tsinke mata, ta rasa yanda yake sanin inda take bayan komai nata akwai tsaro ma
i ƙarfi akai. Ba dai ta tambaye shi ba don ta san ba zai ta
ɓ
a fa
ɗ
i ba itama ba ta shiryawa amsar ta shi ba don haka shiru shi ne ya fiye mata alkhairi.
Yau ta fito daga Stone techhub inda tayi wani 2-days intensive training wa ƴan secondary school aka
n ethical usage na internet, har zata shiga mota sai kuma ta kalli JSeen tea place. Haka nan zuciyarta ta bata shawarar shiga ta
ɗ
an yi ordern wani abun ta ci, duk da an basu abinci a wurin treats ma mai kyau amma kawai ta ji kwa
ɗ
ayin wani abun an gaya mat
a tean wurin akwai da
ɗ
i duk da ita ba wai gwanar shi sosai bane. Outdoor ne wurin don haka seat ta ja ta zauna, waitress ce ta kawo mata menu ta ajiye a gabanta. Green tea ta yi order da cookies, wucewar waitress
ɗ
in da kamar 5mins wani ya ja kujera ya zau
na. A firgice ta
ɗ
ago tana kallon wanda ya zauna a tunanin ta ko Scor ne a take idanun ta ya fa
ɗ
a kan wani matashi.
Fari ne dogo mara ƙiba gashin kan shi an masa aski low cut, bai da gemu ko ka
ɗ
an sai saje. Sanye yake da jumper blue color mai taushi k
an shi ba hula, cikin seconds ta masa kallon ta
ɗ
auke tana maida shi kan screen
ɗ
in wayarta. Murmushi ya saki yana mata sallama, amsawa tayi ba tareda ta dube shi ba. Cewa yayi '' ran ki ya da
ɗ
e da fatan ban yi laifi ba na zauna ba tareda izinin ki ba''.
''Kafin ka zauna ya kamata ka tambaya ai not now''.
''My apologies, na so tambayar ki but i was carried away by your beauty and i lost my manners in the process ''.
''I see'' ta kuma fa
ɗ
i ba ta dube shi ba.
''I'm Sabeer Katchalla''.
'Another S' ta furta ƙasan maƙoshi.
''Pardon?'' ya tambaya a nashi zaton ko da shi take yi.
''Cewa nayi Masha Allah ''.
Ji suka yi an ja kujerar gefenta da ƙarfi da sauri suka kalli wurin, karaf idanun ta suka fa
ɗ
i kan wanda ta zaci gani
ɗ
azu
. Shi
ɗ
in ne da kan shi ba saƙo ba cikin shigar shi ta kullum, Hoodie, pcap, wando, takalmin Sketchers sai eyeglasses
ɗ
in shi. Zama yayi har lokacin idanun shi sarƙafe da nata ya bu
ɗ
e baki a hankali yace............
Deejasmah
💜🦂
CHAPTER 51
''N
a da
ɗ
e ko?" Ya tambaya irin taren nan suka zo wurin ba biyota yayi ba.
Ba ta iya amsawa ba don mamaki hakan bai ko dame shi ba sai juyawa da yayi kan Sabeer da ke zaune yana cewa '' ohh my, seems like we have a company''.
Miyau gayen ya ha
ɗ
iye don
kai tsaye ya gane me yake faruwa a wurin, tare ta ke da saurayin ta ko kuma yace tana jiran shi ne a wurin. Kai ya gya
ɗ
a yana cewa '' Uhmm'' don bai san me zai ce masa ba, ga shi duk da ya sanya glasses masu duhu yana jin kaifin idanun shi a kan shi. Baki
ya ta
ɓ
e yana kai hannun shi kan nata da ke ajiye kan table ya sarƙafe da na shi, duban shi ta kuma yi can ƙasan maƙoshi tace '' what's this Scor?".
''What does it looks like Baby?" Shima ya maida mata tambayar ta da tambaya, he's just hating all of th
is wai wani namiji gaban macen da ta kasance mallakin shi yana mata kallon maita. Lallai gayen nan da alamu sai ya ƙwaƙule masa idanu tukunna zai san ko waye shi. Ga ƙarin takaicin yanda take tambayar shi me yake yi, don bai kuma sace ta ba ne ya kai gidan
shi