Showing 186001 words to 189000 words out of 232724 words

Chapter 63 - JIRWAYE COMPLETE

29 Aug 2026

92

bata san adadin kuma kowa da na shi kayan takaicin. Sai ta gwammaci zaman gidan na farko akan na waincan, duk da dai ba kai tsaye ta fito take mata zancen ba a sakaye take komai cikeda kulawa da ƙoƙarin son nuna itama ba ta da son kai.

Moon wurin 2 ta zo ta kawo mata wasu kayan da wayarta, da ta tadda miss calls fin 10 daga su Amah, Mufee da Tee. Mufeen ta fara kira inda take mata ƙorafin inda ta ajiye wayarta. Cewa tayi '' ya na can cikin

ɗ

aki ne, ya garin kun gama defense

ɗ

in?".

''Mun gama alhamdulillah, kin san jiya fa an sa rana''.

''You don't mean it dearest, kai Alhamdulillah babe ina taya ki murna Allah ya bar ki da mai ƙaunar ki ya ba ku zaman lafiya ya kauda shai

ɗ

an''.

Kai ƙarshen maganar tata yayi dai-dai da shigo

war Scor cikin

ɗ

akin bayan shi Musaddiq ne da ledoji a hannu, kawar da kai tayi gafe tana jin me Mufeen take cewa cikeda excitement. Idanu tayi rolling tana cewa '' da

ɗ

in auren me son ki kenan dearest, Allah ya ba mu danshin ku''.

''Ke fa kin cika zol

aya wallahi, ke ma ga yaya Tafidan ki nan kuna kashe mu da soyayya ''.

Tsaki ta saki ƙarami tuno cewa duk mutanen duniya kowa yana rayuwar aure normal ba wani matsala ko damuwa sai wanda ba'a rasa ba amma banda ita, don gaba

ɗ

aya rayuwarta a cuƙurƙude t

ake rabon da ta samu farinciki mai

ɗ

orewa ta manta. Ko Tee a yanzu haka ta fita zaman natsuwa da kwanciyar hankali ba ma ita ba, amma miyasa hakan ya faru da ita kawai kamar ba a duniyae mutane take ba. Jin Mufeen na cewa '' You there?" Ya sanya ta sakin a

jiyar zuciya tana cewa '' yes but i have to go right now, I'm so happy for you Pookie Allah ya sa da mu za'a yi ''.

''Alright, ki cewa Moon ta kyauta ta bar ni a gantale tun tafiyar ku''.

''Za ta ji saƙon ki tabbas'' ta amsa tana dariya ta yank

e kiran tana ajiye wayar kan pillow ba tare da ta kuma duban wainda suka shigo ba.

Musaddiq ne ya gya

ɗ

a kai yana danne dariyar shi, dama tun ranar farkon da ya ha

ɗ

u da ita ya san tana da masifar taurin kai irin na su na gado. Don haka sai yace '' barka

da rana Aunty Gimbiya ya jiki?".

Haushin shi take ji tuno duk abubuwan da suka faru, tana da yaƙinin shi ne Snake don haka ba ta ga me tanka masa zai haifar ba. Sai dai ta danne ganin Moon hankalin ta yana kan su ta kuma san halin ƴan kayanta don haka

tace '' lafiya lau, Ya Musaddiq'' daga haka ba ta ƙara cewa uffan ba. Shiru ne ya ratsa

ɗ

akin ba mai cewa uffan sai Scorpion da ya tsare ta da idanun shi duk da ƙasa-ƙasa yake kallon ta amma ta san zuwa yanzu ta san in ita yake kallo ko akasin haka. Kamar

ha

ɗ

in baki ƙannen shi suka miƙe suka fita aka bar

ɗ

akin daga ita sai shi da yake tsaye hannun shi dafe da ƙugun shi, sanye yake da wani farin tissue mai taushi sosai fuskar nan a cunkushe yace '' ba ki iya gaisuwa ba ne?".

Kamar tayi banza da shi sai

kuma tace '' ai ban san wanda zan gaisar ba ne''.

''Ohh really? Look Adeeyah ni fa ba sakaran namiji ba ne da zai

ɗ

auki duk wani ƙananun shirmen ki a gaban ƙannina ba ne, you must learn how to respect me''.

''Respect is a reciprocal, it is earne

d not owned kuma in ya zube bai kwasuwa. So ban san ta ina kake son in fara ba''.

''Haka kika ce?" Ya tambaya yana cije lips

ɗ

in shi.

Ko

ɗ

ar babu a ranta tace '' yea, kuma a shirye nake da in tabbatar maka da hakan''.

''Yayi miki kyau '' ya ju

ya ya fita cikin tafiyar ƙasaitar da sai yanzu take tuna yanda Scorpion shi ma yake taku. Dafe goshin ta tayi tana cewa '' amma ni

ɗ

in nan an yi wawiya duk wani ilimin da nake da shi ya tashi a banza tunda ga abu a gabana na gaza gane miye''.

Wayart

a ta

ɗ

auka tana kiran Amah, wanda kai tsaye take tambayar ta ko tana lafiya yau bata kira ta ba gaba

ɗ

aya. Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa '' wallahi Amah ba wani da

ɗ

i nake ji ba, jiya a asibiti muka kwana amma yanzu da sauƙi ba kamar da ba ''.

''Alla

h sarki Baby, yanzu ya jikin naki?".

''Feeling much better, sun ma ƙi saki na ne amma ba abinda yake damu na yanzu ''.

''Ki bari dai su sallame ki don kan su yawwa''.

''In Shaa Allah Amah, ya Affah?".

''Yana lafiya, yanzu ya rage abubuwan

da yake yi yana ganin kamar zai iya convincing

ɗ

ina ne''.

''In Shaa Allah ma hakan ba zai yiwu ba Amah, na ma kusa dawowa ai''.

''Toh Allah ya dawo da ku lafiya, ki kira ƴaruwarki itama ba ta wani jin da

ɗ

i kin san in cikin nan ya tsufa sai a h

ankali ''.

''Yanzu zan kira ta''.

''Toh sai anjima Allah ya ƙara sauƙi ''.

''Ameen ya rabb '' ta amsa tana yanke kirar, sai da ta sauke ajiyar zuciya ta iya kiran Tee, ringing biyu ta

ɗ

auka tana cewa ''Dee''.

''TeeTee me yake damun ki h

aka na ji ki wani iri ne?".

''Muscles pain ne yake damuna sosai,yanzu haka sun bani bed rest ne ma''.

''Subhanallahi, sorry dear me. Allah ya ƙara afuwa''.

''Ameen, ke fa naji muryar ki wani iri''.

''Nima ba wani jin da

ɗ

i nake yi ba, jiya

a asibiti muka kwana ''.

''Subhana, amma ya kike ji yanzu?".

''Da sauƙi sosai, muna sa ran sallama ma''.

''Okay then, Allah ya ƙara sauƙi ''

Ameen ta amsa suka yi sallama da juna tana jin haushin da yake cin mata rai yana raguwa ko ba do

n komai ba don ciwo ya wuci wasa.

Tafida dai tunda ya fita bai kuma shigowa

ɗ

akin ba saboda mugun haushin da ya cika masa rai, itama tafi son haka don ba abinda zai canja mata zuciya a yanzu dai haka ba ta sani ko a gaba ba. Ba ta ko bu

ɗ

e kayan da ya

kawo mata ba sai da Mammah zata zo da dare ne ta kawo mata abubuwan buƙata.

Yau ma tare suka kwana kamar jiya, sun yi hira sosai cikeda sakewa amma ko kusa ba a kuma tada zancen tsakanin ta da Tafida ba. Da safiya around 11 aka sallame su, Musaddiq ne

ya zo ya maida su gida. Wanda bisa shawarar Mammah Turakar Mai babban

ɗ

aki aka nufa da ita kai tsaye, wanda hakan ba ƙaramin da

ɗ

i yayi mata ba don dama tana ta tunanin yanda za'a yi ita da shi in aka ce ta koma can

ɓ

angaren nata. Sauran ƴan gida kuma aka c

e musu jinya take yi nan gudun ƙaramar magana, Mammah da kan ta taje sashen da Moon sai da aka tattaro kayakin da zata buƙata tas suka tafi da su can ba tareda mai ita

ɗ

in ya san wainar da ake toyawa ba..........

Deejasmah

💜🦂

CHAPTER 84

4 ya s

higo gidan cikeda gajiya da son ganin ta don tun

ɗ

azu sun yi waya da Musaddiq ya shaida masa ya dawo da ita gida, hakan ya sa yana shigowa hanyar

ɗ

akin ta ya nufa sai dai wayam ne ya masa barka da zuwa ba kowa a

ɗ

akin kai ko ƙamshin da ta ke sakawa in ta n

a ciki ma babu balle na turaren ta. Juyawa yayi zuwa

ɗ

akin shi wai ko can ta nufa shi ma dai duk

ɗ

aya har gwara nata ma akan na shi don ash trayn da ya tara tikar sigarin shi tana wurin bai

ɗ

auke ba. Sake komawa nata yayi ya fara duba ta a toilet labarin

ɗ

aya ne, closet

ɗ

in ta ya bu

ɗ

e nan ko idanun shi ya fa

ɗ

a kan kayanta da aka rage su ba laifi kuma babu suitcase

ɗ

aya. Cije baki yayi wato yarinyar nan ta tafin dai da gaske ko?.

Tsaki ya saki yana fita daga

ɗ

akin, hanyar na Mammah ya nufa cikin

ɗ

acin rai

. Yau ko iso bai jira an masa ba ya afka

ɗ

akin duk da ya san abinda ta tsana kenan, tana zaune kan kilisa tana lazumi tun idar da sallahr la'asar ta dawo wurin ta zauna. Sai ganin

ɗ

an malamin ku tayi kwatsam a kan ta, wani kallo da ta jefa masa ya sanya ji

kin shi yayi mugun sanyi zama yayi a gabanta yana gaishe ta cikin saukar da murya.

Ba ta amsa gaisuwar shi ba sai da tace '' ka kawo min takardar tata?".

Kai ya girgiza yana cewa '' ni fa Mammah ba zan ta

ɓ

a sakin ta ba, bori take yi zata gama kayanta

ne ma ta sauko. Kuma ma ai bata buƙatar takardar tunda tayi gaban kan ta ta kwashe kayanta ''.

''Ba gaban kan ta tayi ba, tana wurina don na mata alƙawarin ba zata koma wurin ka ba. So wajibi ne ka bi umarni na nima tunda ita me zama da kai

ɗ

in ta

gaji da halayen ka ''.

''Wai Mammah ta ce miki ina mata wani abu ne? Ya ma za'a yi ki yanke hukunci without listening to both sides haba Mammah ta.....''

''Kai ne zan ce sai na tsaya na ji me ka aikata? Sai kace ban san halin ka kamar yunwar ciki

na ba? And to answer your question ba ta gaya min komai ba, sai dai kai zaka iya fa

ɗ

i sai in maka adalci''.

''Amma Mammah......''

''Kai Malam ka ishe ni da kiran suna, Mammah, Mammah Mammah haba ka kiyaye ni fa''.

''Allah ya huci zuciyar ki'

'.

Ba ta tanka ba jin haka ya sanya shi sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi ya miƙe yana cewa '' ki huta lafiya '' har ya fita bata

ɗ

ago ta kalle shi. Sai da ya fita ne a kan harshen ta tace '' ba ka da gaskiya yaron nan ko ka

ɗ

an''.

Yana fita ya tsure

sama da kallo ya rasa me yake masa da

ɗ

i, bai san inda zai bi ya ga haske ba. Wurin Takawa ne last hope

ɗ

in shi amma ya san shi ma maganar Mammahn yake ji, sai dai abinda ya sani shi ne tana jin na shi itama akwai girmama juna da fahimta tsakaninsu duk da u

wa da

ɗ

a ne. Wanda ba komai ya kawo hakan ba face yawan biyayyar Sarki Mujahedeen, ga yawan haƙuri kamar Abien su sam duniya bata masa zafi ba. Mai bi masa Muwaffaq ma haka sam bai da kwarafniya daga kan Munawwarah ma akwai biyayya haƙuri ne bata da shi so

sai, sai shi da ya fi kowa fitina a kaf gidan ya sani shi da kan shi ma Musaddiq da Muneerah kam ai sanyi ƙalau ne mutanen nan. Tuno yayyin shi ya sanya shi sakin ajiyar zuciya yana jin kamar ya samu mafita wa kan shi, ya tabbatar in yaje za su goya masa d

a baya har sai matar shi ta koma masa. A ƙafa ya kuma takawa zuwa cikin gidan sarauta wurin Takawa don ya san yanzu ya fito masallaci yana hutawa, a nan kam sai da ya nemi iso aka masa kafin ya shiga da sallama.

Takawa da ke zaune gefen shi fulani ce d

a kan ta take serving

ɗ

in shi peppered soup ya amsa sallamar yana cewa '' maraba da kai Tafida shigo ciki, yanzu muke zancen ka''.

Ji yayi wani ƙwarin guiwa ya kuma zuwar masa ya ƙarasa ya zauna gaban su ya fara gaishe da yayan na shi. Amsawa yayi cikin

sakin fuska ya gaida Fulani itama da ta amsa tana cewa '' Tafida amma tare kuke jinya kai da Adeeyah hala? Duk ka bi ka rame haka''.

''Ba abinda nake gaya miki ba kenan, duk ya rame ina ce an sallame ta ma?" Ya ƙarashe tambayar idanun shi kan

ɗ

an'uwan

na sa cike da kulawa.

''An sallame ta, akan haka ma na zo mu yi magana'' ya furta hakan yana sadda kai ƙasa. Fulani ce ta miƙe da sauri tana cewa '' barin ba ku wuri tohm, Allah ya taimake ka'' ba ta ko jira me zai fa

ɗ

i ba ta wuce ciki ta bar su nan

su biyu. Sai da ya ga fitar ta kafin ya juyo da kallon shi gare shi yana cewa ''me yake faruwa ne?".

''Mammah ce ranka ya da

ɗ

e''.

''Me tayi?".

''Cewa tayi wai sai na saki Adeeyah''.

''Subhanallahi, saboda me?".

''Ita yarinyar ce ta

ke wannan maganar, ni kuma gaskiya ba zan iya ba''.

''Akwai abinda yake faruwa a tsakanin ku ne?".

''Babu amma ban san me ta gayawa Mammah ba, yanzu haka tana can wurin ta ta riƙeta''.

''Ashha, amma abu bai yi da

ɗ

i ba. In an yi Isha'i sai mu

shiga wurin ta da Muwaffaq da kai har ma da Mai babban

ɗ

aki sai mu ji ko me yake faruwa okay? Kar ka damu in shaa Allah yau matar ka zata koma wajen ka''.

''Nagode ran ka ya da

ɗ

e''.

''Ba komai, zauna mu ci abinci''.

Shi ya sake serving yaya

n na shi don wanda aka saka masa ya huce, shi ma yayi ma kan shi suka fara cin naman yana ƙara lallashin shi.

Ana idar da sallah suka nufi sashen mai babban

ɗ

aki da niyyar roƙonta ta sa Mammah ta bashi matar shi, sai dai suna shiga abinda suka fara c

in karo da shi ya ba su mamaki su duka DeeDee ce zaune kan carpet ta jingina da cushion tana cin gya

ɗ

an da Innanin ta saka a dafa mata. Zaro idanu duka suka yi suna kallon ta musamman ma shi da ya ga ta kuma yi masa kyau, cije lips yayi yana kuma ƙureta da

idanu.

Gaishe ta suka shiga yi ta amsa fuska a sake, itama Dee gyara zama tayi tana jan veil

ɗ

in Boubou gown

ɗ

in jikinta ya kuma rufeta da kyau tana cewa '' barka da dare ranka ya da

ɗ

e''.

''Yawwa, barka Adeeyah ya jikin naki?".

''Alhamduli

llah da sauƙi''.

''Allah ya ƙara sauƙi, ya sa kaffara ce''

Ameen ta amsa tana juyawa kan Galadima suka gaisa ba tareda ta kuma kallon shi ba, gya

ɗ

a kai yayi cikeda takaicin abinda take masa.

Innani ce tace '' lafiya kuwa? Na gan ku haka?".

Taka

wa ne yayi gyaran murya yana cewa '' actually mun zo bayar da haƙuri ne, gare ki da ma Mammah akan abinda yake faruwa tsakanin Musharraf da Adeeyah''.

''Wani abu yana faruwa ne? Ke ƴar nan akwai abinda ya faru ba ki gaya min ba?" Ta tambaya idanun ta

kan Adeeyah.

Ajiyar zuciya ta sauke tana girgiza kai tace '' ni ma ban sani ba, Innani''.

''Ƙarya kike yi'' ya ca

ɓ

e cike da masifa.

Mammah da shigowar ta kenan don ta duba Deen jiyo masifar da ake yi ko sallaman ta ba a ji ba ya sanya ta cewa ''

miye yake faruwa a nan?".

Duka suka juya suna duban ta, ba ta jira amsar su ta shigo

ɗ

akin da kyau tana samun wuri gefen Adeeyah ta zauna. Mai babban

ɗ

aki ta fara gaisarwa ta amsa fuska sake kafin ta juyo tana amsa gaisuwar yaran nata da suka zauna tsi

t ana kallon kallo, sai kuma ta dubi Dee tana amsa ta da kulawa tana tambayar ta jikin ta. Kana ta kuma maimaita tambayar ta, wato uwa daban ne ko da kasantuwar Takawa a sarki sai da ya rusuna kafin cikin taushin murya yace '' akan abinda ke faruwa tsakani

n Musharraf da Adeeyah ne, muke son ki yi haƙuri ki janye zancen saki tunda yana son matar shi ''.

''Yana son matar shi ya zalunce ta har ta nemi saki a tsakanin su? Ga shi ka tambaye shi in ina da sa hannu a lamarin nan, ita ta fa

ɗ

i ni kuma ba zan ta

uye ta ba''.

Ta ƙarashe tana hararar shi kamar idanun ta za su fa

ɗ

o ƙasa, sauke kan shi yayi tsoro yana kama shi don yana jin kamar asirin shi ne ya tonu. Kallon ƴan

ɗ

akin ne ya koma kan Dee da ke jin kamar ƙasa ta dare ta fa

ɗ

a ciki kafin Takawa yace ''

Subhanallah Adeeyah me yake faruwa ne da zafi haka? ''.

''Ba komai'' ta amsa muryarta yana rawa, cewa yayi '' wani irin babu komai kuma kin ta

ɓ

a ganin mace ta nemi saki ga mijinta babu komai saboda jin da

ɗ

i?".

''Ni kawai ba zan iya zama da shi b

ane, ya san abinda ya aikata ya fi kowa sani''.

Shiru ne ya kuma kara

ɗ

e

ɗ

akin kowa yana kallon shi kamar sun ga baƙon halitta kafin Takawa yace '' kai Musharraf me yake faruwa?".

Kasa magana yayi ya fara kame-kame '' uhmm.....Wallahi.....Taka....wa n

i.....''

''Kai ban son shiririta a nan ka gaya min me yake faruwa, akwai sa'an ka a nan ne?".

''Ku yi haƙuri'' ya amsa yana duƙar da kai, don bai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login