Showing 15001 words to 18000 words out of 232724 words
idarwa ta kuma kwanciya kan dadduman da ke tsakanin bunks
ɗ
in su don ita akwai son baccin ƙas
a musamman da rana ko da asuba, nan ma ba ita ta bu
ɗ
e idanu ba sai to 8 shi ma ƙamshin suya ne ya tashe ta. Miƙa tayi tana kallon source
ɗ
in ƙamshin Pookien ce zaune tana suyan pancakes, mittsike idanunta tayi tana cewa '' what on earth is this aroma?".
Juyowa tayi ta dubeta tana cewa '' good morning ma, what happened to it?".
''It is heavenly ma, sorry good morning kin sani ina salivating this early morning ''.
''It is not that early hala kin manta kina da fita ne da safen nan''.
''Ban manta
ba girl, kin san na gaji a kwanakin nan ne''.
''Sai ki tashi ki yi wanka, akwai ruwa a kettle''.
''Sai da ke ƴar ƙunar baƙin wake inda admin
ɗ
in ta fa
ɗ
o mana room fa?".
''There ain't no way da zata fa
ɗ
o mana, it is locked fa she has to knock kafin t
a shigo and before that I'd have took care of it yanzu dai ki juye ki saka min kafin su yi wanka''.
Miƙewa tayi tana zare hijabinta toilet ta fa
ɗ
a ta ko da
ɗ
e a ciki don tana da da
ɗ
ewa a toilet yanda ka san mai shirin canja fata, sai can ta fito shirin
ta ne bai da wahala don daga mai wani short kimono da palazzo ta
ɗ
auko na material mai taushi kalar Burgundy da beige very matured color kuma bai da hayaniyar rigar ciki mai turtled neck ta saka a ciki baƙa ta saka wandon da ke nan kamar skirt saboda fa
ɗ
i
, hula ta sanya baƙa kafin ta zauna pancake din Mufee ta zuba mata ta amsa muttering thanks.
Nutella ta
ɗ
auko daga locker
ɗ
iba take tana sakawa kan pancake
ɗ
in tana ci, lumshe idanu tayi tana cewa '' no one can cook like my pookie''.
''Haka dai kike
fa
ɗ
i, but you too can cook''.
''Kar ƙi yaudare ni, you know that I cook because it is a necessity not that I love it, masu girki because they love it sai ku ai ''.
Kai ta gya
ɗ
a don ta san gaskiya ta fa
ɗ
i duniya Adeeyah na girki ne don ya zame mata do
le bayan nan kam ba ta yi, a darare da yawa ma ta gwammace ta
fita su ci ko ranar da tayi musu golden yam da safiya saboda ta ga har ta tafasa ne kuma zata fita da safe inda ba ta tafasan ba ma tea kawai zata sha ta fita.
A natse taci tana ci tana mat
a santin da
ɗ
in da yayi har ta gama tissue ta zara ta goge bakinta tana ƙara maimaita thanks, kafin ta miƙe kimonon ta
ɗ
auka ta
ɗ
aura kan rigar ciki jersey veil cream ta sanya wanda ko kusa bai hau da kayanta ba ina ma laifin ace ta saka baƙi tunda rigar ci
kin baƙi ne? Amma ita ko ta kula jakarta ta kullum ta
ɗ
auka tote bag ita ko an ci sa'a ta
ɗ
auki baƙa ta zura crocs masu taushi baƙaƙe lips balm ta shafa, ita dai Mufee sai kallon ta take yi ba daman ta ce gyara don ta san ba gyarawan zata yi ba.
Syste
m
ɗ
in ta ta saka da sauran kayan buƙatun ta ta juyo tana cewa '' ki fa je gidan Aunty Fatee Kar ki zauna ke ka
ɗ
ai kin ji?".
Kai ta girgiza ta ce '' ba zan je ba kin ji ina da test fa Monday, zan tsaya in yi karatu''.
''Ahh kar ki tafi kam, Allah ya
bada sa'a see you on Monday''.
''Thanks, good luck with your stuffs don't forget to greet Amah and Affah for me''.
Kiran sunan Affahn ya sa ƙirjinta bugawa tuno cewa jiyan ba ta kira shi ba kamar yanda Amah tace,
ɗ
an daurawa tayi tana cewa '' in s
haa Allah, we'd talk'' water bottle
ɗ
in ta da ta cika da ruwa ta
ɗ
auka ta fita.
Yau dai Rhid bai zo ba ta tabbatar bai ko tashi ba don haka napep ta tara drop ya kai ta can IT central cikin ung sarki inda ake yin taron Africa's talking na month
ɗ
in, s
anda ta isa ana forming groups ne don haka ba ta shiga ba instead wuri ta samu a reception ta fara kiran Affah kamar kullum yau ma kadaran-kadahan ya amsa sai dai bayan gaisuwan ya tambaye ta ko zata zo
ɗ
in ta kuma tabbatar masa in shaa Allah daga haka ya
yanke, maida akalar kiran ta yi ga Amah ita kam sun jima suna waya har take shaida mata da zuwan TeeTee mamaki ne ya kamata don sammakon yayi mugun yawa a sanin da tayi mata amma sai bata tanka ba sai ma ta
ɓ
a baki da tayi tana cewa ita ma zuwa Asr tana gid
an.
Daga haka sallama suka yi don har an fara shiga, miƙewa tayi da energyn ta ta shiga cikin hall
ɗ
in. Reserved seat
ɗ
in ta ta nufa bayan sun gaisa da Hafizee an bata tag
ɗ
in ta, zama tayi tana duba presentation
ɗ
in ta, ita ce tayi facilitating hackath
on na ranar hatta price
ɗ
in ma ita ta saka. Sosai participants
ɗ
in sun yi ƙoƙari duk da sun samu nasarar hacking
ɗ
in mutum biyu ne kawai suka iya decoding message
ɗ
in ta ukun macece tana tsaka da yi ta ci karo da Virus.
Dubawa tayi tai grading sannan a
take ta ba su price
ɗ
in su, dama abinda ya kawo ta kenan sai kawai suka yi hotuna da winners da ma sauran
participants ta wuce gida don haka nan zuciyarta ke raya mata akwai matsala tun da har Affahn da kan shi ya mata zancen zuwan nata wanda abu ne da ba
kasafai yake yi ba sai in akwai maganar da yake son yi da ita. Yanzu ma dai napep ta ƙara yin drop zuwa can cikin layout
ɗ
in rigachikun-mamadi, za'a iya kiranta da sabuwar unguwa amma ta masu da shi don GRA ce sosai manyan mutane ne kawai a wajen infact ƴa
n siyasa da ƙusoshin Gwamnati sun fi yawa a wurin.
A ƙofar wanii ƙasaitaccen gida mai matuƙar kyau da ƙawa yayi parking, ku
ɗ
in shi ta ba shi ta fita da idanu ya bita da kallo a ran shi yana ƙissima ko dai wurin wani tazo ne a gidan don ko kusa ba tayi k
ama da ƴar gidan ba. Sai dai wannan ba damuwar shi ba ne wayar shi ma ya ciro yayi dialing wata number,
ɗ
agawa aka yi daga can gefen ba tare da an yi magana ba cewa yayi '' Yalla
ɓ
ai yanzu na ajiye ta a ƙofar gidan Hussaini Shamaki''.
Shiru yayi yana sau
raren umurnin da ake ba shi sai da aka gama ya iya cewa '' toh yanzu kuwa''. Yana fa
ɗ
in haka ya ja keken shi ya bata iska don shi dai ya gama na shi aikin sai wani jiƙon kuma. Don dama yau musamman ya fito domin ta, a zahiri ne ta tare shi amma a ba
ɗ
ini su
suka tsare ta don tun safe yake bibiyarta har ta isa can zaman jiranta ya zauna yi har ta fito sai da ta fara neman keke ne yayo u-turn ya dawo ya
ɗ
auketa shi yasa ko da ta gayi inda zai kaita bai musa ba ku
ɗ
in ma da ya fa
ɗ
a mata inda ta taya ko nawa ne h
aka zai
ɗ
auketa bisa umurnin da aka ba shi.
Knocking ta yi securities
ɗ
in da ke bakin ƙofar suka bu
ɗ
e ganin ta tsaye sai suka fara washe baki don duk da ba ta da yawan magana tana da kirki sosai fiye da kowa na cikin gidan har da ma Hajiyan ta su, gai
sheta suke yi ta amsa fuska a sake ta nufi cikin gidan da yake kuma amsa sunan sa kai daga gani ba sai an fa
ɗ
a maka ba ka san na wani babban ƙusan ne a gwamnati duk da dai gidan ya fi kama da na masu sarauta ko siyasa saboda girma da tsarin shi ga securiti
es ta ko'ina.
Tura entrance door
ɗ
in tayi ta shiga cikin parlorn da sallama a bakinta babu kowa a cikin shi sai ƙamshin turaren da yake tashi ga kuma sanyi da ra
ɓ
ar AC, ratsa shi tayi ta shige na gaban shi nan ma babba ne duk da bai kai girman na farkon
ba a nan ne kuma akwai staircase mai matuƙar kyau wanda ya dace da komai na parlorn da aka wa Royal English style with art decor. Ƙasan deep brown wooden floor ne sai wall
ɗ
in da ya kasance na marmara not marmara da kuka sani but na stones masu matuƙar da
raja su kuma sun yi gold haka sai suka yi contrasting da kujerun da suke ainihin Royal marasa hayaniya kalar brown light su da sauran kayan furnitures
ɗ
in duka colorn su
ɗ
aya bayan nan kam wooden doors
ɗ
in irinsu guda da floor
ɗ
in. Nan
ɗ
in ma babu kowa sai
TV dake ta
ɓ
a
ɓ
atun ta ita
ɗ
aya, hanyar kitchen da take jin motsi ta nufa a bakin ƙofa ta tsaya tana kallon mahaifiyar ta su da ke zuba soy sauce a shinkafa tana juyawa yayinda kitchen
ɗ
in da
ɗ
ume da ƙamshi wanda abu ne da ta riga ta sani babu wacce ta kai
Amahn ta iya girki ko da akwai ita dai bata san ta ba.
''Here's the world's best cook''
ɗ
in da ta furta ne ya sanya ta waigo a mamakan ce don ba ta san yaushe ta shigo ba ganinta ko sosai ya sanya ta
mamaki ai ko ta bu
ɗ
e baki cike da shauƙi tace ''
My baby!!" Sosai matar take kama da ita a fuska da komai har da skin colorn su, sun fi Ateeyah hasken fata yanzu ma don mayukan da take shafawa ne da sunan skincare suka canjata ta koma wata fau haka.
Ƙ
arasawa ciki tayi da sassarfa ta rungume ta a ƙasan
maƙoshi take furta '' I've missed this soul''. Itama cewa tayi '' I've missed you too, shine kika ce min sai Asr?".
''Na gama abinda zan yi ne fa tun 12:26 shi ne kawai na taho''.
''Glad You do, we'd then be having our lunch together''.
''Yes
Amah, lemme make the salad ''.
''No need of you sweetie, go and freshen up kafin nan ya kammala''.
''I'm not that tired Maa, zan ha
ɗ
a sai in yi wankan Please''.
''Alright Baby'' ta furta tana murmushi, itama shi ta sake tana zare veil
ɗ
in t
a da shi da jakar ta ja kujera
ɗ
aya ya
ɗ
aura a kai, har da kimonon tata. Kayan salad
ɗ
in ta ciro ta fara aikin su suna yi suna hira cikeda shaƙuwa, cikin ƙanƙanin lokaci kam suka kammala suna gamawa ko Amah ta tarkata ta sai da ta wuce
ɗ
aki bayan ta kirawo
ɗ
aya daga cikin ma'aikatan gidan ta gyara wurin da suka
ɓ
ata.
Staircase ta haye da kayanta a hannu,
ɗ
akin farkon da ke a sama ta gani a bu
ɗ
e. Zuciyarta ne ta raya mata ta wuce amma saboda matsayin shi a gare ta sai ta gaza shiga ciki tayi wani dogon
corridor ta wuce sai ga ta ta iso wani
ɓ
angare mai girman gaske wanda da alamu yana da separate hanya ta waje, glass doorn da ya raba su ta tura ta shiga da sallama a bakinta.
Wani dattijon mutum sankacece ne zaune a kan kujera, baƙi ne sosai irin ma
i ƙyallin nan amma akwai kyau kam ba laifi don kusan ma ba su
ɗ
auko kyan na shi ba ma
ɗ
an dai kawai baƙi ne ga tsawo sosai bai dai da ƙiba sai dai ba siriri ba ne ba. Gefen shi kuma Ateeyah ce zaune tana nuna masa wani abu a wayarta suna dariya, shigowar t
a ya sanya duk fuskar su canjawa ko sallamar ta ma Affahn ne ya amsa fuskar nan ba yabo babu fallasa.
''Yaushe ki ka zo?" TeeTeen ta tambaya tana kallonta sheƙeƙe kamar yanda ta saba.
''Yanzu'' ta amsa ta kai tsaye tana ƙarasawa gaban mahaifin na s
u duƙawa tayi kamar yanda kullum ta saba masa with so much respect tace '' Barka da gida Affah an wuni lafiya?".
''Lafiya lau Adeeyah, ya makaranta kin zo lafiya?".
''Alhamdulillah''.
''Masha Allah'' ya amsa daga haka bai kuma cewa uffan ba sa
i idanu da ya tsira mata kamar mai bincike, yanda yake kallon nata kuma duk sai ya saka ta ji ƙirjinta yana bugawa don ta san kallon shi ba wani Alkhairi ba ne ai ko kamar yanda ta hasaso cewa yayi '' me ya ha
ɗ
a ku da Ateeyah?" Ya tambaya babu alamun wasa
a tattare da shi.
Ɗ
agowa tayi a tsorace tana kallon ta wani makirin murmushi ta saki, cije lips ta yi tana cewa '' babu''.
''Babu? Shi ne zata gan ki a wurin biki tana miki magana ki ka share ta? ''.
''Affah ban share ta ba ita ce fa......''
''Ita ce me? Ko zata miki ƙarya ne uhmm? Tukunna ma who do you ask da zaki je gidan bikin?''.
Yawu ta ha
ɗ
iye da ƙyar tana mai sake duƙar da kan ta cikeda baƙin cikin da ya gaza
ɓ
oyuwa a kan fuskarta, sai dai ko kusa ba ta tanka ba sai ma rintse id
anu da ta kuma yi.................
Yanda ta yin ko ya kuma baƙanta masa rai ai ko ya shiga sauke masifar shi ba ko ƙyaƙƙautawa, Amah da take shigowa ne ta ƙaraso da sauri tana cewa '' kayya Jarmai daga zuwan ta?".
''Daga zuwan ta ma kike cewa? Ba
yan jiya kina ji ko ka
ɗ
an ƴaruwarta ba tayi bacci ba sakamakon abinda ta mata? Yau ma tun safe ta taho nan
ɗ
in cikeda damuwa amma kike cewa don me?''.
''Kana fa
ɗ
in haka kamar ba ka san halin Ateeyah ba? Ya zaka fara fa
ɗ
a ba tare da bincike ba?".
''Wani bincike kuma za'a yi kina ganin zata mata ƙarya ne? Da yake ita ba ta laifi a wajen ki ko?".
''Ba ta laifi a wajena kuma? Ba zaka yi haka da ni a nan ba maza ku tashi ku fita ku bamu wuri ana magana kun tsare mu da idanu ku tashi na ce!!" Ta ƙara
she a tsawace.
Da ko sauri Deeyah da dama kamar a kan ƙaya take ta miƙe, da kayanta da ke cuƙurƙu
ɗ
e a hannu ta fita ita ko Teeyah sai da ta gama kumbura baki kafin ta fita tana ƙunƙuni da harara ta rakata sai da ta fita kafin ta dawo da idanun ta kan mi
jin nata cikin ƙoƙarin ta na danne fushin da take yi kowace rana................
Chapter 7
Su na fita ta maida idanun ta kan shi shima kallon nata yake yi yana mai jiran me zata fa
ɗ
i sai dai ba ta ko tanka ba, instead juyawa ma tayi zata fita da sa
uri ya kamo hannunta ya riƙe. Rintse idanu ta yi da sauri yace '' me kuma Jarmai sarkin laifi ya aikata?".
Sai da ta nisa kafin ta iya cewa '' Ni ban ce ka yi komai ba ai''.
''Haba Turai, na fa san ki kamar yunwar cikina. Na san me shirun ki yake nuf
i''.
''Toh ni dai ban ce ka yi komai ba kawai dai na ga rashin dacewar tuhumar ta daga shigowar ta gidan ko hutawa ba ta yi ba''.
''Kin san dai ban da jimirin yin shiru ina kallon ta ban fa
ɗ
a mata abinda ke raina ba ko?".
''Ai ba a hana ka ba, ya
dai kamata ne a kullum ka zama mai bincike kafin yanke hukunci sai dai kash duk abinda ya shafi Ateeyah ba ka iya aiwatar da hakan kamar ba ka san ko wacece Ita ba''.
''In kina fa
ɗ
in wainnan maganganun sai in dinga mamaki Turai, ke ma fa na da
ɗ
e da fa
himtar duk abinda Tee zata fa
ɗ
i ba yarda kike yi da shi ba. Komai Dee ta yi shi ne gaskiya''.
''And that's because na san su waye yarana ne, na san halin kowa a cikin su a wani karatu ne ya zama Deeyah ta aikata laifi don kawai ba ta wa ƴaruwarta maga
na ba da ta ganta. Well aje ma a tayi laifin ka sani ko ba ta gan ta ba ne? Ko kuma ita ce tayi mata maganar ba ta tanka ba which I'm sure inda ita ce ba zata kawo ƙara ba sharewa zata yi''.
''In aka yi magana ki ce ba ki goyon bayanta while it is so ob
vious that's what you were doing''.
''Shiyasa fa ban saka baki a duk abinda zaka musu ko yanzu ma abinda ya sa na yi maganar saboda na ga daga zuwan ta ne fa ko hutawa ba ta yi ba ai sai ka saka son zuwa gidan ya fita a ranta''.
''Dama ai ba son zu
wan take yi ba''.
''Ni dai Please ka bar maganar