Showing 216001 words to 219000 words out of 232724 words
Bai matsa ba don ya san matsayar ta ya fita yana tambayar
ɗ
akin da yake Musaddiq ya raka shi.
Da yake
ɗ
akin VIP ne ak
wai ciki da kuma ƙaramin parlor ya sanya a parlorn ya tarda Hajiya Maijiddah tana waya, ganin shi ya sanya ta ajiye wayar tana gaishe shi. Tambayar shi me jiki yayi ta amsa tana narke fuska alamun tausayi, kana ta miƙe tana cewa bari ta masa iso. Zama Musa
ddiq yayi shikuma ya nufi ƙofar kamar zai tura ƙofar sai kuma ya tsinkayi muryar ta tana cewa.
''Ga fa baƙin mugun can yazo duba ka sai ka san me zaka yi, don ban son ya fahimci kana magana''.
Kana ya jiyo shi muryar shi can ƙasa yana fita alamun
ya samu matsala irin sosai
ɗ
in nan da vocal cords
ɗ
in shi yana cewa.....
Deejasmah
💜🦂
CHAPTER 95
''Ki ce masa ina bacci'' ya amsa yana fitar da numfashi da ƙyar.
''Ka san dai nacin mutumin nan ba zai bar shi ya tafi ba, dole sai ya gan k
a
ɗ
an wahala kawai''.
''Kin san na tsani ganin mutumin nan kamar yadda na tsani mutuwa ta, so I'll close my eyes har ya zo ya tafi ''.
''Ohon maka dai koma mi zaka yi ni dai kar kayi magana ne damuwata, don yanda ka kwana zaburar nan kana wani ki
ran sunan Masarauta kamar ita kake bautawa ai aka ji asirin mu sai ya tonu''.
''Baaaaa abinda zai faru, kar ki bar shi ya......''
Kasa jurewa yayi ya hanka
ɗ
a ƙofar ya shiga ciki,a zabure duka suka kalle shi. Hajiya Maijiddah ta bu
ɗ
e baki zata yi
magana da yake Shamakin na gaske ne yayi saurin
ɗ
aga mata hannu yana cewa '' fita ki bani wuri da
ɗ
anuwana zan yi magana''.
''Ba inda zan je kana ganin ba shi da lafiya haka nan in bar ku ku.....''
''Kar ki damu ki je kawai dama ai ranar wanka ba
'a
ɓ
oye cibi na gaji da
ɓ
oyewa abun yana cizona a zuciya gwara a yita ta ƙare''.
Sai da ta kalle su kafin ta fita daga
ɗ
akin, kamar ta la
ɓ
e jikin ƙofa ta ji me zata tattauna sai ta ga Musaddiq zaune yana kallon su. Tsaki ta ja kawai ta fita daga
ɗ
akin d
ama abinda yake so kenan,sai yayi locking parlorn yana kuma maida wayarshi jikin ƙofar don ta na
ɗ
ar masa abinda suke cewa.
Wani kallo Shamaki yakewa
ɗ
anuwan nashi da yake kwance, hannun shi
ɗ
aya da alamun bai aiki haka ma ƙafafun shi a sandare suke. H
annu
ɗ
aya dai ya saka yana dafe kai da shi da alamun sara masa yake yi, inda ace da ne da sai yaji tausayin shi ainun amma abinda ya ji da kunnen shi ya sanya shi girgiza kai kawai yana cewa '' ka ga yanda ka ƙare ko?".
''And so what? Ai bai kai wanda
ka ƙare da shi ba. Ba mulki ba
ɗ
an'uwan ka da yake jin zai iya bayar da komai na shi kan ka, kai ko burin ka ka cutar da shi. Ka bar gani na a haka zan warke in koma can gidan, kuma wallahi ba zan haƙura ba sai na tabbatar daga kai har zuriyar tsohuwar ca
n kun wulaƙanta''.
Shamaki da shock bai gama fitar shi bane yace '' kake ganin zaka kuma samun damar da ka samu da? Toh waye ma yace maka zaka warken
ɗ
in?".
''Ba a haife ni don in ƙare a wulaƙance ba, ni ne Zakin Barewa don sarauta aka haife ni''
.
''Shiyasa ka fito daga tsatson baiwa ai, ga shi kuma zaka ƙare ba wan ba ƙanin ba ka samu riba a duniya ba ta lahira kuma sai yanda hali yayi''.
''Ƙarya kake yi, kai ne sakarai da bai san komai ba kayi asara ba ni ba. Kalle ni da kyau Hashimu n
ake ciwon idon ku kai da Habibu, na hana shi zaman lafiya na jaza masa ciwon da shi ya zama ajalin shi....''
Ai da wata kalar sauri ya dira gaban shi yana riƙe kwalar rigar shi yace '' kai ne ka siyar masa da company? Kai ne''.
''Yes nine me zaka
iya yi? Nace me zaka iya bayan nayi komai ne da saka hannun ka, kai ne ka bani makullin komai na shi ni kuma na sarrafata yanda nake so''. Ya ƙare a wahale don namijin riƙo ya masa ba wai na wasa ba. Sake matse masa wuya yayi kamar me shirin kashe shi yan
a cewa '' sai na zama ajalin ka, kai ka kashe min
ɗ
anuwa''.
''Ban kashe shi ba, kawai nayi accelerating tafiyar ta shi ne, atleast na taimaki yaran shi'' ya kuma furtawa da ƙyar.
Sake masa wuya yayi yana dafa bango ƙirjin shi na masa zafi yace ''
why? Me muka maka?".
''Tambayata kake yi? Bayan kun san komai, kawai rashin adalci ya sa kuka ƙi gani. A gidan da aka raine ni bamu da maraba da bawa, eh Baba shi ya haife ni amma saboda ta tsatson baiwa na fito bai bani darajar da ya baku ba. Babu w
ani kulawa ko kyautatawa,komai na shi ku ne. Ya kai ku makaranta masu tsada a wajen ƙasar nan ni kuma a nan nayi karatu,nisan da nayi shine Kano jami'ar Bayero. Ya baku muƙamai ni kuma ko dogarin shi ya fini daraja, ya
ɗ
auki sarauta ya baka and you did wor
st than he did. Ka tattare komai a ƙarƙashin ka, ko
ɗ
an'uwan kan da kake iƙirarin son ma baka duba ba balle ni karan ka
ɗ
a miya. Ya mutu ban da gado haka na ƙare gallafiri sai alakoron da kuka bani and you are asking me why? Ko shi Habibun da na shigewa gab
a aka maka juyin mulkin da me ya ƙare ni? Sarautar Marafa fa kawai ya bani sai kace wani shege ba ma Galadima ko wani muƙami mai daraja ba,sai maida ni bawan da yayi na mai kula masa da dukiya. Uban mu
ɗ
aya amma a suna ne kawai ku ka
ɗ
ai ne kuka san da
ɗ
in s
hi and you are asking me why?".
Ya ƙarashe maganar tashi cikeda
ɓ
acin rai, da sauri Affah ya kalle shi yana zaro idanu jin yanda yake magana da
ɓ
acin rai. Kai tsaye zuciyar shi ta fara tuno masa komai kamar a lokacin yake faruwa, sai kuma ya tuno rayuwa
r da yayi da na shi yaran wanda kusan hakan ne. Ya fifita guda kan guda ya fi bawa Ateeyah kulawa yana ganin itace zata shigo gidan sarautar har ya samu biyan buƙata, sai gashi nan komai ya juye masa ba yanda ya zata ba. Yanzu irin zafin da Marafa yake ji
shi take ji? Yanzu yanda Mahaifin su ya zamewa Marafa a suna haka ya zamewa Adeeyah? Gwara ma Marafa an san
ɗ
an baiwa ne kuma ba sa sarauta amma kuma ba'a ce kar a basu duk wata soyayya da ta cancance su ba amma ita fa? Ba ta samu ko taro daga gare shi na
soyayya ba, amma kuma ba ta fasa masa biyayya ba sai ma fatan da take yi har yanzu ya dube ta irin wanda yakewa Ateeyah. Kaicon shi da ya tafka kuskure saboda son abun duniya ga shi nan bai kai shi ko'ina ba, kallon Marafa yayi yana cewa '' ka ji tsoron Al
lah ka tuba, Allah ba'a ba shi silly excuse kuma bai yafe laifin wani kan wani. Ka yi sanadiyar rushewar zufar Habib saboda kishi bayan ba da dukiyar da kake hange ya gina ta ba, da zafin nama ya assasa komai da kuma zuciya mai kyau. Ya
ɗ
auki amana ya baka
ka ci, in ka manta barin tuna maka hukuncin wannan munafunci ne a addinance kuma Allah ya yi alƙawarin wuta gare su. Sai yanzu na tuna dalilin da ya sa aka gaza tracing
ɗ
in information
ɗ
in companyn, kamar allura haka ta zille masa. Sai na gaba ka yi ƙoƙar
in shiga zumunci wanda Allah da kan shi ya tsinewa mai yanke zumunci, ba zan ce maka komai ba zan barka da Allahn da ya halicce mu ya saka mana doka. Ya sa ka gyara in kai mai shiryuwa ne''.
Yana fa
ɗ
in haka ya juya ya fita daga room
ɗ
in dama asibitin
gaba
ɗ
aya, tafiya kawai yake yi bai san inda yake jefa ƙafar shi ba. Komai ya kwance masa nadama mara amfani yana rufe shi.
DeeDee da Amah dai basu san me yake faruwa ba suna can suna hira da ƴanuwa, ga shi an ha
ɗ
e da Mammah ana hirar wasshe gamo. Sa
i da aka yi la'asar ne ya kirawo ta kan ta shirya yanzu za su wuce, ba a ko yi 15mins ba ya shigo ya sake duba ta da jiki sai duƙar da kai yake yi yana jin kamar kowa ya san kuskuren da ya tafka. Musaddiq da ya saurari komai ne ya kai su airport sai da ya
ga tashin su kafin ya koma a hanya yana ta saƙe-saƙe. Tabbas sun yi kuskure suma sun yanke hukunci ga Kawun su suna ganin duk abinda yake faruwa laifin shi ne ashe shi ma Abien su da na shi laifin, don me zai yarda a tun
ɓ
uke
ɗ
an uwansa saboda yayi gado? Ta
bbas bai da maraba da Ateeyah da ta so a
ɗ
auke ƴaruwarta saboda ta samu Ridhwan. Tabbas da mulki da sarauta akwai santsi a cikin su in aka biye su za'a shiga taraddadi da fangan-fangan ga shi nan suna gani ba wai sai a nesa ba. Giyar mulki masifa ce ta shi
ga tsakanin ƴanuwa ta farraƙa su irin farraƙawa ta har abada, an rabu ba zumunci. Ko da yake ma
ɗ
ai
ɗ
aikun gidajen sarauta da na masu mulki ne akwai zumunci, duk an saka son abun duniya a lamarin shiyasa yanzu ma duk ta rage kwarjini an
ɓ
ata komai. Shiyasa
yake godewa Allah da yanda Musharraf ya tsaya musu akan bu
ɗ
e kamfanin su, don su dogara da kan su. Da yanzu suma suna nan zaune jiya i yau a ƙare da attacking ƴanuwa don a samu sarauta, kaicon wannan lamari kaico.
Sai dare da yaje kwanciya yake turawa
Musharraf audion, murmushi yaji da ya saurara don dama ya san za'a yi haka amma bai san a kusa haka komai zai faru sai ga shi nan kamar almara komai yazo da sauƙi. Ba sai sun saka baki ba balle a ce sune, hamdala yayi wa Allah yana turawa Musaddiq thumbs
up.
Washe gari aka sallameta da sassafe suna komawa Innani ta ha
ɗ
a ruwanta mai zafi a toilet ta gashe ta don tace ita dai wankan da ake mata bai mata ba, dole sai da tayi nata. Ita kanta Deen taji da
ɗ
in wankan baccin ta ta sha ma'ishi, tana tashi ta h
a
ɗ
a ta da abinci wai kar ta lalace don jego take yi bambancin kawai bata shayarwa ne. Nan ne dai suka samu matsala don ba wani son abincin da take cusa mata take yi ba, gwara ma dafaffiyar madarar da take bata shi kam tana son shi har ƙosawa ma take yi a k
awo shi yammacin ranar sai ga Munawwarah da Ateeyah da ma Ridhwan. Taji da
ɗ
in zuwan su don nan suka tare wurin ta, Moon ma nan ta tattaro ta dawo suna ta shaƙiyancin da suka saba. Ko da dare da Ridh zai tafi accommodation
ɗ
in da ya kama musu ji tayi kamar
kar su rabu amma gudun kar ya fasa barin ta
ɗ
in ya sa ta bi shi tunda gobe zai tafi. Sai daren ne suka yi waya da mijinta a tsanake wanda ta fuskanci yana cikin nisha
ɗ
i yau, ko da ta tambaye shi cewa yayi sai ya dawo zata ji komai. Murmushi kawai tayi suka
cigaba da hira da shi, sai kusan 10 kafin suka yi sallama.
Washegari Ridh ya koma ya bar Tee a nan, ji suka yi kamar an tsoma su a aljanna. Musamman da Lami ta
ɗ
auke mata kula da Rushdah musamman ma cikin dare don haka take samun bacci sosai sai gari
ya waye ake dawo mata da ita, ai kam tace ta ga wuri ba zata koma ba sai tayi arba'in biyu. Mijinta dai yace bata isa ba ta dai yi sati
ɗ
ayan da tace ta koma gida, haka ta dinga tura baki amma ba yanda ta iya ba dai ta tafi a kwanakin da ya
ɗ
iban ba sai d
a ta ƙara 5 days kai kafin ta tafi don shima ta san yana buƙatar su ne sosai. Dee taji tafiyar nan a ranta don tayi bonding da ƴaruwarta a kwanakin irin wanda basu yi ba a da, su kwana
ɗ
aki guda su tashi tare. Su tattauna matsalolin su su kashe su rufa bab
u wanda ya ji balle ya gani, ko ita kanta tayi kyau sosai abun ta har ta kan manta da naturen yanda haihuwar tazo mata sai in nononta ya ciko ne take tunawa da hakan kuma bata bari ya dame ta sai irgar kwanakin dawowar mijinta da yanzu ya bar Brazil yana D
oha ba kuma zai kai da
ɗ
ewar can ba zai dawo. Innani tana lura da yanda take yi na lissafin mijinta ta barta ne tayi ta gama don tayi alƙawarin ba zata bari ta koma yanzu da
ɗ
anyen jiki ba haka nan..............
Deejasmah
💜🦂
CHAPTER 96
Kwana biya
r kawai yayi a Doha ya tattaro kayan shi zuwa Nigeria, wanda zuwan ya zame masa kamar a kan ƙaya yake. Ji yayi kamar yayi tsalle
ɗ
aya ya gan shi a gida gaban matar shi, a duniyar shi bai ta
ɓ
a jin
ɗ
okin ganin wani ba kamar yau. Gani yayi tafiyar ma ta ƙi ƙa
rewa, cikin ikon Allah jirgin su ya sauka a Lagos ta Nigeria around 4 am. Flights masu zuwa Barewa ya duba daga nan
ɗ
in sai dai babu sai Kano ko Kaduna, tsaki yayi kawai don dole ya siya ticket mai zuwa Kaduna. Shi kuma ba zai ma tashi ba sai goman safiya,
tsinuwa ne kawai bai yi ba haka nan ya fita daga airport
ɗ
in ya shiga wani madaidaicin motel kusa da airport
ɗ
in. Wanka yayi yai sallah kafin ya
ɗ
an kwanta, tsabar yanda ya saka abun a ran shi 8:30 ya farka. Room service yayi order ya ci abinci kafin ya s
hirya ya tattaro kayan shi ya koma filin jirgin, sanda ya isa ma ana ta wani clearance
ɗ
in don haka sai ya bi queue
ɗ
in aka masa ya shiga ciki. Sai 11 jirgin su ya tashi zuwa Kaduna, inda shi kam yana sauka babu
ɓ
ata lokaci suka kuma yin boarding wani zuwa
Barewa.
Musaddiq ne ya
ɗ
auko shi da suka sauka wurin 3 na rana, kai tsaye part
ɗ
in Mammah ya sauka. Ya ga tarba ta musamman wannan karon ba kamar sauran zuwan da yake yi ba,nan nan aka dinga yi da shi sai da aka kira sallahr la'asar kafin suka fita shi
da Musaddiq zuwa Masallaci. A can ma ko da aka idar da sallah haka su Takawa suka rufe shi da barka da zuwa, suna jajanta masa rashin da aka yi masa. Da murmushi ya amsa su kawai yana alla-alla su ƙyale shi ya wuce wurin matar shi bai samu wannan damar ba
sai kusan 5 da Takawa ya fara shigewa ciki ya bar su nan, a gaggauce ya ma Galadima sallama ya wuce sashen mai babban
ɗ
aki.
Tun da jini ya
ɗ
auke mata ta fara gyaran jiki bisa jajircewar Innani, wani kalar gyara ake mata na ƴan gata ciki da waje. Ita
kan ta ta fara jin gyaran a jikinta sosai, ga wani kyau da ta ƙara ga kuma ƙamshi da ya game mata jiki. Ba kuma iyaka wannan aka tsaya ba Innani da kanta take zama tana karanta mata dabarun zama da miji ba
ɓ
oye-
ɓ
oye ba komai, tun tana jin kunyar wasu har t
a saki jikin ta don taji abubuwa ne da zasu taimake ta sosai. Musamman ta gefen magana duk da tana da sanyin murya Tee ce tata take da zaƙi sosai, amma tata ta fi da
ɗ
i ta koya mata yanda zata kuma maida maganar ya zame mata makami. Hakaza ta mata karatu ma
i girma kan tsaftar ciki da waje da ma muhalli, don har cewa tayi.
''Kin san inda abinda ake so ake samu ko? To da wallahi sai kin kwance wannan
ɗ
aure-
ɗ
auren na kan ki don ni ban ga amfanin shi ba''.
''A kwance me? Duka-duka fa da biki nayi shi ai
ba zai ma kwancu ba''.
''Ki ji ƙazanta bikin ki da kuke neman shekara
ɗ
aya shi ne zaki ce bai da
ɗ
e ba? Ina iska zata shiga ciki''.
''Ba wata ƙazanta a nan ina zuwa ana wankewa fa, ko nima ina wanke kayana a gida bai wari. Ba ki san nawa na kashe ma
sa bane shiyasa''.
''Kika kashewa wannan
ɗ
an iskan abun ku
ɗ
i da yawa? Lalacewar tayi yawa kam''.
''Gayu ne fa''.
''Allah ya raba mu da wannan gayun kam'' ta amsa har da murgu
ɗ
a baki kamar yarinya.
Dariya tayi tana cewa '' Ameen, besides m
ijina bai ta
ɓ
a complaining ba so