Showing 144001 words to 147000 words out of 232724 words
dafe ƙirjinta a ranta tana ayyana anya ba ta kwafsa ba? Not for
him only but for Shamaki tana jiyo muryar shi a kanta yana cewa '' so nake ki haihu nan da shekara, ina buƙatar tsiro na a gidan Sarautar Barewa don hakan ne ka
ɗ
ai zai dawo min da kimar da na rasa.........''
Kenan wasan
ɓ
uyar da take yi is more of disa
dvantage to her than to him, anya ba kwa
ɓ
arta tana shirin yin ruwa ba kuwa? Wajibi ne ta tashi tsaye ta san inda yake mata ciwo she needs to seduce him into her nest but how?...........
If you ask us na who we go ask oo?
Da gaske fa matsalar Adee
yah Shamaki ne da Scor ji dai yanda suke shirin rikita mata ƙwaƙwalwa da rana tsaka.
Deejasmah
💜🦂
CHAPTER 65
Yanke wayar tayi ta zuba uban tagumi tana wa kan ta fa
ɗ
a kan abinda take yi, meyasa da ya nuna maitar shi a fili ba ta biye masa ta
ba shi abinda yake so ba?. Ko ba ta haka mata suke iya siye zuciyar wanda suke so ba ne, oho ba ta sani ba don ba wai tana zama da matan aure ko sauraren labaran su ba ne. Infact ba ta da experience na rayuwa kan komai bar ta dai ta rungumi system
ɗ
in ta a
gaba ya fiye mata sauƙi than seducing any man to her nest. Ganin babu abinda zai iya fisshe ta ga shi lokaci yana ta ja ya sanya ta miƙewa tsaye, gadon ta fara gyarawa kana ta wuce toilet.
Wanka tayi ta shirya cikin wata atamfa mai gold mai kaloli masu
sanyi da
ɗ
aukar idanu, gyale mai sequence fari ta ciro daga cikin closet tana ta
ɓ
e baki don ita duniya ta tsani atamfa ko wata kala ce tana dai sakawa ne don babu yanda ta iya. Baƙaƙen wedges da ke ajiye a bakin ƙofarta ta zura tana fita waje, a kan dinin
g ta tadda shi zaune yana sanye cikin Moroccan kurta kalar beige an masa irin design
ɗ
in da ta fuskanci yana so. Baƙar dara ce kan shi yana shan tea, yawu ta ha
ɗ
iye har zata fasa ƙarasawa dining
ɗ
in saboda ganin shi da tayi sai kuma zuciyarta ta raya mata
' ke da kike neman kusanci miye na zama nesa da shi?' umarnin zuciyar ta ta bi ta isa wurin shi sai da ta ja kujera ta zauna kafin ta dube shi a hankali tace ''barka da safiya ''.
Kallon tsaf yayi mata daga sama har ƙasa cikin abinda bai fi 30 seconds b
a kafin a ƙasan maƙoshi ya amsa da '' Kin tashi lafiya?" Ya ƙarashe da wata murmushin takaici ta gefen baki.
''Lafiya'' ta amsa masa irin yanda yake mata kafin ta yi serving kan ta, a hankali take cin abincin tana shaƙar ƙamshin shi da ya cika wurin.
Take ranar da ya kwana
ɗ
akin ta ya fa
ɗ
o mata a rai, tana tuno yanda
ɗ
akin ya kama ƙamshin duk kuma yanda ta tsani ganin shi zata iya bada shaidar akwai son ƙamshi irin wanda ba ta ta
ɓ
a ji ko a jikin Scor ba. Duk da hakan amma ta fi son na shi don yana sau
kar mata da natsuwa da sukuni, ba ta jin akwai namijin da yake da effect a kan ta kamar shi.
Cikin sanyin ta take cin abincin, yana kallon ta ta ƙasan idanun shi yana observing duk wani abu da take yi. Amma ba lallai ka iya cewa ga abinda yake yi ba sab
oda yanda ya maze kamar ba kowa a wurin, abinda yayin ko ba ƙaramin kuma tsinka mata zuciya ya kuma yi. Idan ko kallo ba ta ishe shi ba ta ina zata fara janyo kan shi gare ta kenan? Sai dai ba ta da me bata amsa don haka ta daure ta fuskanci gabanta.
Su
n da
ɗ
e kafin su gama cin abincin shi ne ma ya riga ta gamawa ya miƙe ya nufi
ɗ
akin shi, hakan ya bata damar ƙarasawa cikin sauri don har da zaman shi a wurin ya sa ta jin wani iri. Kusan ten minutes sai ga shi ya dawo da wata alkyabba a hannun shi, zama ya
yi kan cushion alamun ita yake jira. Ko 2 minutes ba ta ƙara ba ta miƙe shi ma ya tashi tsaye yana bu
ɗ
e mata alkyabbar wai ta sa. Rigar nan tana
ɗ
aya daga abubuwan da ta tsana a gidan sarautar nan, a ha
ɗ
a ka da kaya masu masifar nauyi kana zaman-zaman ka a
mma ya ta iya hakan nan ta saka tana tsayawa a gaban shi. Karon farko da hakan ya faru da su sai ta ga tayi ƴar kucila a gaban shi, shima kamar ya lura da hakan amma sai ya cije ya nuna mata hanya.
Jerawa suka yi a ranta tana lissafin ko ina Sailuba t
a shiga yau oho? Ta ji shirun yayi yawa,amma ba ta tanka ba in ta dawo zata saka a kirata. Daga bakin parlorn su zuwa wurin parking duk inda suka bi zubewa ake ana gaishe su, tana lura da bai amsawa itama tun da tayi biyu uku bakin ta ya gaji don haka tayi
shiru kayan ta sai hannu kawai take
ɗ
agawa.
Seat
ɗ
in baya aka bu
ɗ
e musu suka shige a natse, ta zauna gefen shi tana jin ƙirjin ta yana bugawa sosai don kusancin su da juna. Shi ko ko a jikin shi waya ma yake amsawa can ƙasa ba ta ko jin me yake fa
ɗ
i,
sai kawai ta maida kallon ta ga cikin gidan tana ƙare masa kallo irin yanda ba ta samu chance ba a farkon zuwan ta cikin shi.
Duk da ba ta ta
ɓ
a shiga gidan wata sarauta ba a rayuwarta amma based on pictures da take gani a media zata iya cewa masaraut
ar Barewa daban take a tsarin masarautun gargajiya. Don komai na su daban ne gine-ginen da ma tsarin su, duk da akwai gargajiya mai yawa a ciki amma kuma tsarin zamani ya shigo ciki sosai kai tsaye zata ce masarautar wayayyu ce irin na gaban kwatance. Ga b
ishiyoyi ta koina na gidan an ba su ruwa sai ƙamshin ƙasa ke tashi, ga koina a share yake tsaf in ka
ɗ
auke ganyayyaki da suka fa
ɗ
o.
Sun wuce
ɓ
angarori da dama kafin suka iso wani wurin da zata ce ya fi ko'ina na gidan ga fadawa nan da barori cikin shi
gar su na kullum, a can gefe driver yayi parking kafin su kai ga fitowa wani daga cikin baran gidan ya taho da sauri ya bu
ɗ
e musu ƙofar. Shi ya fara fita kafin itama ta fito, kamar yanda suka jera
ɗ
azu haka yanzu ma suka shiga wurin.
Shiru kake ji in
ka
ɗ
auke ƙarar AC da yake tashi da wani ƙamshin da bata san ko na humidifiern da ke girke a kusurwa ko diffuser ba ne ko air freshener ba, ko ma dai na miye akwai kwantar da zuciya sosai. A gaban wata sliding door ya tsaya ita ma ta ja tunga sai da ya nemi
iso aka ba sa izini kafin ya tura ƙofar bayan ya cire takalman shi, itama cirewa tayi irin yanda ta yi ta bi shi a baya.
Ba fada suka zo ba don babu fadawa a ciki ko ƴan fada, sai dai tace
ɓ
angaren sarki ne ko ma tace turakar shi inda yake ganawa d
a iyalin shi. Ƙaton parlor ne mai
ɗ
auke da ha
ɗ
a
ɗɗ
un royal chairs da curtains sai wani ƙaton bookshelf daga gefen dama, hagu kuma ƙofofi ne. Walls
ɗ
in
ɗ
akin na
ɗ
auke da hotunan sarakunar masarautar har zuwa kan shi, zaune yake hakimce kan kujera sanye da ku
san kalar kayan Musharraf amma na shi farare ne tas sai jar hular dara da ya sanya. Kallo
ɗ
aya ta masa ta san suna kama sosai da shi tundaga tsayi da ma kauri, sai yanzu ta gane inda Shamaki ya samo kalar tsawon shi. Gadon masarautar su ce, mazan su manya
ne irin sankata-sankatan nan wainda da muna yara muke kira da jariran samudawa. Haka za baƙin su kusan iri
ɗ
aya ne da su, baƙaƙe ne irin sosai
ɗ
in nan amma kuma mai kyau ne. Su Musharraf kuma da Musaddiq ba su kai su ba shima har da gyaran da sukewa jikin
su ya sanya hakan. Kwarjinin shi ne ya
ɗ
ibe ta tayi saurin zubewa a gaban shi cikeda girmamawa.
Shi ya fara gaishe shi ya amsa fuska sake kafin itama ta mara masa baya, da murmushi ya amsa yana cewa '' matso gabana ƙanwata''.
Kunya ne ya rufeta a
mma ta daure ta matso don ta tuna an gaya mata sarakuna ba sa son maimaita magana sau biyu. Sai dai kan ta a ƙasa ta ƙaraso inda ya nuna mata, wanda yayi dai-dai da shigowar Fulanin shi da sallama. Duka amsawa suka yi sai da ta ƙaraso suka gaishe ta kafin
tace '' idan ku kenan Musharraf?''.
''Wallahi Anty ina ta son shigowa baƙi ne ake ta yi shi yasa ''.
''Nima haka nake cewa da sai sun shirya komawa tukuna ya kawo ta mu yi sallama, a rabu ba wata sabo a tsakani?".
''A yi afuwa ranka ya da
ɗ
e''.
''Ai dole in yi, ka kaita ciki kuwa?".
''Yanzu za mu je in shaa Allah ''.
''Masha Allah, kina ji ko ƙanwata? Nan gidan ku ne kar ki bari wani ya gaya miki otherwise. Yanda yake da iko da gidan nan haka kike da shi, in ya miki ba daidai ba k
ar ki ji tsoron gaya min okay? Allah ya muku albarka ya kawo zuri'a
ɗ
ayyiba ''.
Fulanin ce ta amsa ita dai godiya ta dinga bin shi da shi, musamman da ya sanya aka kawo mata wata ƙatuwar package
ɗ
in da bata san miye a ciki ba. Sun
ɗ
an ta
ɓ
a hira dukan
su ita dai ba baka sai kunne, ko an saka ta a ciki bai wuce eh ko a'a ba. Sai can kusan 1 hour kafin suka baro wajen na shi, tana tafe a hanya tana lissafi shi sarkin bai da izza irin ta Musharraf sai dai akwai wani authority da yake
ɗ
auke da shi. He comma
nds the room without even trying, akwai hikima da taushin harshe a yanda yake magana. In dai haka sauran ƴan gidan za su kar
ɓ
eta ba zai mata wani wahala ga samun abinda take muradi ba, tana a duniyar tunanin ta suka iso
ɓ
angaren Mammah.
Shi ma ya ha
ɗ
u
kamar wancan da suka baro amma ya fi shi nesa kusa ba, kamar wancan sai da aka musu izini kafin jakadiyarta ta musu iso kafin ta fita ta bar su. Suna shiga ko matar ta tashi zaune tana mata maraba da shigowa, ajiyar zuciya ta sauke ta ƙarasa gabanta bisa
isharar da ta mata. Cikin sake fuska kamar irin sun sabar nan take mata hira, babu izzar da aka ce mata tana da shi. Shi kan shi mamakin yanda ta mata yake ta yi, don ya fi kowa sanin halin Mammahr ta shi. Suna a zaunen Muneerah ta fito da kara
ɗ
in ta tana
ganin ta ta taho da sauri ta rungume ta tana cewa '' Aunty Adeeyah barka da zuwa''. Sai kuma ta kalli Musharraf tana cewa '' Mai girma Tafida barka da safiya ''.
Harararta yayi yana cewa ''sai yanzu kika ganni halan''.
''Kai Yaya wallahi in na g
a Auntyn mu mantawa nake da kowa, ya cika kishi ''ta ƙarashe tana wa Dee ra
ɗ
a a kunne. Murmushi tayi tana cewa '' Au haba?'' da irin muryar da ta mata magana. Mammah ce tace '' Ke dai Munee ba ranar da zaki canja hali sai hayaniya kike mata a kunne ba zaki
barta ta sha ko ruwa ba''.
''kai Amah ƙawance fa zan ƙulla da ita, in kina cewa ban da natsuwa ai sai ta fasa ƙawancen da ni''.
''Waye zai yi ƙawancen da ke?" Mammah da Musharraf har suna ha
ɗ
a baki wurin tambayar ta, dariya ta saki tana cewa '
' Aunty Adeeyah mana, kuma Allah Mammah sunana Moon ba Munee ba''. Harararta tayi tana cewa '' to an ji ke kuma Adeeyah kar ki biye mata ''.
Murmushi ta saki kawai bata ce komai ba. A nan kam sun da
ɗ
e sai azuhur ma suka shiga wurin mai babban
ɗ
aki, a
nan ta ga tarairayar jika da kaka. Don tsohuwar rungume ta tayi da Muneerah ta tsokane ma ba ta amsa ba sai cewa tayi wai bata ta
ɓ
a zaton zata rungume ta a jikin ta irin yau ba, wani sanyi ne ya cika mata zuciya da ta tuna ita fa kakar ta ce amma ba su sam
u wannan gatan ba saboda son mulki. Shanyewa tayi kawai bata nuna ba, sai yamma suka baro wurinta ana ajiyeta ya bar gidan gaba
ɗ
aya. Haka ta koma ciki da tarin kayan da aka ha
ɗ
o mata daga can
ɗ
in su Sailuba suka kai mata ciki.
Ita ka
ɗ
ai ta koma ciki b
a abinda take yi sai flipping channels daga wannan zuwa wannan, gajiya tayi ta bu
ɗ
e kayan da ta zo da shi. Na mai martaba alkyabba ne guda uku da turaruka masu tsa
ɗ
a sai Qur'ani da wani book wai atomic habits. Murmushi ta saki tana maida su cikin closet, s
u Mammah dai wasu ha
ɗ
in kayan gyaran jiki ne ta bata da ma turaruka. Wanka tayi ta zura wata abaya tana jiran a yi magrib, har aka yi Isha'i bai shigo ba da ta idar da sallahr abinci ta
ɗ
an tsakura ta ci ta shiga ciki ta kwanta shiryawa tayi cikin tank top
fara da pj pants masu taushi ta kwanta. Ba ta kulle ƙofa ba tana tsumayin zuwan mijin ta..............
Deejasmah
💜🦂
CHAPTER 66
Sai dai tun tana zura idanu wa shigowar shi har tayi bacci ba ta ji motsin bu
ɗ
e ƙofa ba, ta zaci irin in ta farkan
nan zata gan shi sai dai wayam kake ji babu kowa sai wutan da ta bari a kunne. Tsaki kawai tayi tana miƙewa ruwa ta sha ta yi fitsari kafin ta kashe hasken ta koma ta kwanta cike da takaicin ƙin shigowar ta shi, don a cewarta in bai shigo ba ta yaya zata i
ya samun damar seducing
ɗ
in shi zuwa ga gareta. Haka ta kwana da haushi ta farka.
Yau ita
ɗ
aya ta wuni tsuru kamar mayya in ka
ɗ
auke Sailuba da take
ɗ
an shigowa time to time, ita ma ta gaya mata Tafida ne yace bai son tana yawan zirga-zirga tsakanin s
u. Kai kawai ta gya
ɗ
a tana mamakin kalar izzar Musharraf mai saka ka takaici, lumshe idanu tayi tana lissafin yanda zata iya surviving a cikin gidan nan a haka.
Wayarta ta
ɗ
auka ta kirawo Amah sun da
ɗ
e suna hira da ita har take gaya mata Tee ba lafiy
a, mamaki ne ya kama ta don ko jiya sun yi waya ba ta gaya mata ba. Ai ko tana yanke wayar Ridh ne ma ya
ɗ
auka yake shaida mata wai tana bacci, zaro idanu tayi tana cewa '' Wai ciwon sosai ne?".
''A'a har da dai gajiyar biki ne, don suna dawowa ta far
a a tsaitsaye. Daren jiya ne ko bacci ba mu yi ba''.
''Toh fa, dama in ce ban sani ba mun yi magana da ita da safe fa jiyan. To Allah ya ƙara sauƙi I'll call later In Shaa Allah ka gaishe min da ita sosai''.
Okay ya amsa suna kashe wayar ta samu da
mar yin gulmar da yake cikin ta '' Ridh ne da
ɗ
aukar waya? Ahhh har sun fara soyayyar ta su kenan?" Sai kuma ta ce '' to ai dama suna son junan su sani ne shi bai yi ba he thought it was me, to ko ma dai ciki ne da ita?".
Ba ta da me ba ta amsa sai ka
wai ta ajiye wayar da maganar ma gaba
ɗ
aya, amma lokaci zuwa lokaci ta kan yi murmushi in ta tuna Tee tana tareda wanda yake kulawa da ita. Ta godewa Allah da ba ita ke gidan nan ba da zuciyarta ta jima da karyawa, don Tee is not as strong as she shows. Ta
kan nuna she's cold, mean and non-chalant but har ga Allah she's very soft behind the facade she carries. Haka za tana da masifar tsoro ta yanda ba ka tsammani, duk da shima ta kan nuna ba ta da shi amma in da ita ke gidan wannan cold-hearted obnoxious man
da yanzu tana cikin wani yanayi wanda ba zata iya mata fata ba. A fili tace '' Allah ka ƙara ha
ɗ
a kan bayin ka, ka kauda fitina tsakanin su''.
Sai kusan rana ta ha
ɗ
u da Musharraf shi ma lokacin fita zai yi kuma ya na ta waya, bai kalleta ba ita ma ba
ta dubi inda yake ba duk da zuciyarta mai son yin biyayya tana ta kwa
ɓ
arta kan hakan. Yana fita ta koma cikin
ɗ
akin ta ta zauna, ba ta son kallo don ba gwanar shi ba ce ita ga shi kuma ba wai an kawo mata system
ɗ
in ta bane