Showing 1 words to 3000 words out of 232724 words

Chapter 1 - JIRWAYE COMPLETE

29 Aug 2026

31

[20/12, 18:05] Dee

ج

asmah

🦂

: JIRWAYE

Khadeejah Bint Ismail (Deejasmah)

Young talented writers association (YOTAWA)

CHAPTER 1.

Bismillahir Rahmanir Raheem, Wassalatu alan Nabiyil Kareem.

Royal Tropicana Hostel Kaduna State University, K

ASU Kaduna, Nigeria.

Zaune take bakin can saman bunk k'afafunta na dangling tana shilla su, tana kuma sake mak'ale wayar da ke kunnenta da alamun wayar da take yi ne yake kai mata duk inda take buk'ata. Knocking k'ofar d'akin aka yi ta tura baki tana

kallon k'ofar da k'yar ta iya cewa '' it is open'' turo k'ofar aka yi aka shigo d'akin wata yarinya ce mai kusan adadin shekarunta irin 22-23 d'in nan ce ta shigo da sallamarta.

Ganin wacce ke saman gadon ne ya sanya ta girgiza kai tana cewa '' Deey

ah-Rhid wai ku ba kwa gajiya ne haba don Allah allow us the single breathe mana''.

Sauke wayar tayi daga kunnenta tace '' says someone da kullum sai tayi sabon saurayi, abeg ajiye jaka ki dafa mana indomie ga shi can na fito da shi''.

''Yanzu

don Allah Deeyah baki dafa indomien nan ba? Da fa yunwa na shigo''.

''Kar ki cije ni Malama gas d'in ne fa ya k'are na kai cylindern wurin Malam Aminu can na ga taki ma babu alamun an yi refilling tunda dai yanzu an kawo wuta ki datse k'ofar and cook

for us kafin su gani''.

''Na ji tohm, amma ki ajiye wayar nan don ba zan iya in ta aiki ni kad'ai ba kad'an daga aikinki kina gama wayar nan na fama ki d'auki system ki fara coding d'in ki ko classes so ki sallame shi kwa had'u da dare''.

Da

riya tayi can k'asan mak'oshi tana cewa '' Ray I'll have to go, Pookie ta shigo''.

''Okay Babe take care''.

''alright, bye '' ta na fad'in hakan ta yanke wayar tana kallon Mufeedah da ke yanka veggies saukowa tayi daga saman bunk d'in tana cewa

'' toh na ajiye wayar me zan miki?".

''Saboda in dinga magana ana amsa ni ''.

''Amma ke yarinyar nan muguwa ce wallahi, ina jin muryar mijina zaki tada ni just saboda in saurari muryar ki mara dad'i''.

''Ke ma kin san k'arya kike yi, mu

ryar nan rud'a maza take yi''.

''D'azu kika ce you are single yanzu kuma kin ce muryarki tana rud'a maza, toh ai dama sai maza ni ina mace mai zan yi da taki? ''.

''Ohon miki '' ta amsa tana murgud'a baki, dariya ta saka tana cewa '' barin je

toilet ni ba zan biye miki ba''.

Toilet ta shiga bata wani jima ba ta fito, Kallonta Mufeen ta kuma yi tana cewa '' hala da ban ce ki kashe wayar nan ba a kan bunk d'in zaki yi fitsarin''.

''Ai ban ce miki fitsari na yi ba''.

''Ohh abun n

e? '' da kai kawai ta amsa mata ta kuma zama a bunk d'in k'asa, y'ar hira suke yi sama-sama har ta gama dahuwar indomien ta juyo musu a plate, fork ta d'auko musu da ruwa ta ajiye a gefen da suke zama su ci abinci. Bismillahi tayi ta fara ci tana kallon Mu

feen da ke cewa '' amma next session d'in room of 2 d'in zamu kama? Ko zamu koma MKR ne?".

''Nima ina wannan tunanin amma ko a can MKR d'in in zasu bamu room of 4 sai mu je saboda dai kin ga su Aysh suna zuwa da exams room of 2 ba zai ishe mu ba''.

''I've been thinking of that, kawai dai na ji Ateey tayi magana ne ''.

''Don't mind Teetee kan me zata yi magana ita da ba ma a school d'in nan take ba talkless of the hostel''.

''But you know she'll definitely talk''.

''Yeah she'

d definitely do but I'll handle that okay?''.

Kai ta gyad'a kawai tana kawar da zancen da cewa '' zaki je weekend d'in ne?".

''I absolutely don't think so, kin ga Friday zan je Founders Friday Saturday kuma akwai Africa's talking ko na je gida I'

d be roaming about weekend d'in will be stressful zaki je ne ke?".

''Yes but ba gida zan je ba , it's about wancan wedding d'in na gidansu Aunty Mami sai kirana take wai in zo na sha ma you'd be available ne mu je tare''.

''Unfortunately i w

on't, ke kad'ai zaki je yanzu''.

''No please, let's do this mu je Kamu on Thursday Friday dinner ne har zaki iya dawowa daga FF d'in naki ''.

''Kin dai san........''

''Please Pookie do this for me kin san i won't be comfortable in muta

ne suka cika yawa''.

''Ke naki da sauk'i ai you know that I hate weddings ''.

''You hate weddings amma kin iya soyayya, next year like this za mu je bikinki''.

''Me I'll just do a low-key wedding babu abinda za'a yi ''.

''Well this is a

lie, Ni dai please mu je Pookie kin ga mutane zasu yi yawa a wurin su yi ta son maka magana and I'm sure you can handle them''.

''Wannan kamata yayi ki yi k'awance da Teetee saboda ita ce ba ta son mutane ''

''Ai ni ba son su bane ban yi tsoro n

ake ji in suka cika waje but ita Ateey fa k'iri-k'iri bata son kowa ya zo ko inda take gaisuwar mutunci ma ba so take yi, ke dai Deeyah kin huta ba ruwanki''.

''Kina son in biki wuri kina zagin min twin''.

''Ba zaginta na yi ba gaskiya na fad'i

duk da ke ba ki son gaskiya indai a kanta ne''.

''Na ji tohm'' ta amsa daga haka ba ta kuma cewa komai ba.

Murmushi Mufee ta saki tana kallonta tana mamakin kalar son da take yiwa twinnien tata wanda ko da alamu ita bata mata kwatankwacin shi.

Tana da dagiya da son a fad'i gaskiya amma ko kusa ba ta son shi kan 'yaruwarta saboda ba ta ganin laifin ta duk abinda tayi duniya dai-dai ne shi yasa ta samu damar taka ta da wulak'antata iya son ranta amma ba ta tab'a damuwa ba, a kaf duniya ba ta jure

raini daga wurin kowa sai ita.

Adeeyah Shamaki Hussein ASH ko kuma kace ASH_Witchie kamar yanda kusan kowa ya santa a social media. The computer scientist, Data analyst and a web develover/designer. Ta wani gefen ma ta k'ware a dark web so akan kirata da

AI specialist don ta iya amfani da sarrafa AI ta hanyoyi da dama. A had'uwar farko da ma wainda ka biyo baya zaka sameta da sanyin hali sosai, fuskar nan kullum a sake take shi yasa take da saurin shiga zuciyar mutane, akwai saurin sabo ga girmama kowa ba

ta da son a raina ta ita ma bata raina mutum duk k'ank'artar shi amma tana da jan girmanta ba kuma ta da girman kai tana da kirki sosai irin wanda ke sa mutane ke mata kallon bata da wayau but tana sane she's just extra kind akwai zurfin ciki ainun sai ta

yi rayuwa da mutum na tsayin shekaru bai san halinta ba saboda tsab'ar k'ok'arin ta na kamewa but duk son mutanen ta bata son taron biki in ka d'auke hackathons d'in da ta kan je da su summit shima wainda suka shafeta ne amma biki kam ba nata bane and do y

ou know why? Saboda she can't just fit into any social circle. Ba ta iya kwalliya irin

na zamani ba, dressing d'in ta da komai irin na old school take yi there's nothing attractive about her duk da tana da kyau da jiki mai kyau amma saboda yanda take dress

ing makes it hardly noticable kullum cikin manyan kimonos masu tsad'a da pallazos wanda duk tsadar su bata iya zab'an color mai kyau she's really outdated ba ta san komai a rayuwar ta ba sai books and her system ko kallo bata yi sai wanda ta san zata k'aru

haka books d'in da ta kan karanta are but technology based. Ba ta san wani abu nishad'i ba in dai ya wuce wanda ake samu a coding, kun san yanda lectures yake very boring duk inda ka kai ga son karatu akwai randa kake jin ba ka jin shiga school or you'd j

ust be not in lecture mode ko anyi karatun ba zama yake yi ba ko? Toh ban da ASH ita she's always looking forward to lectures and she's always serious zata yi wasa da dariya da mutane ne a wajen lecture hall amma da zaran an shiga you are no longer her fri

end sai an fito kuma she can take her time to do tutorial ga course mates d'in ta maza da mata ba ta da wannan k'yashin har juniors d'in ta ma. Ko ba a fad'i maka ba ka san dole kan ta yana ja she's not part of the people da ake kira guru by naci but gifte

d don tsakanin ta da karatu a lecture hall ne da zarar an yi take ganewa karatun da ta kan yi a room ko library is far ahead of abinda ake musu a class. Computer science take karanta amma tana yin side courses online akan AI, data science, cyber security w

ed design programing and the rest. Tana da platforms da ta kan koyar da su daban, so ko da ka gan ta tana duba wani littafin it has to do with her work don currently as a student tana yin freelancing a companyn da dama ciki har da almighty KAD ICT HUB da K

ADA HIVE. Aside karatu or tech she's really boring da ba kowa zai iya zama da ita ba sai wanda ya fahimceta she can be very odd too, she can joke at a time and also be serious at the same time. Zata iya tashi in the morning and won't talk sai rana ta take

ko da ranar ta k'i yin magana she's somehow bi-polar da babu wanda yake gane inda ta dosa sai wainda suka santa.

Sauke idanunta Mufeedah Jumare tayi daga kanta tana girgiza kanta, d'an gyaran murya ta yi don bata son hirar ta su ta tsaya a haka tace '

' wani kaya zaki saka tohm?".

D'an murmushi ta saki tana mai jin son Mufeen har ranta wato a duniya idan akwai wacce zata ce ta fahimci halinta toh Mufee Jumare ne, ta san ta ba tareda ita d'in ta bata dama ba kuma ta kan mata uzuri a lokuta da dama

dubanta tayi tana cewa '' well, I won't decide I'll just flow with the mood of the day''.

''Don Allah baiwar Allah ki rufa min asiri, in kika ce you'd flow d'in nan aka zo you are in your werey green mode and you just dress as you deem fit ki zabga

kimono ki bini biki?".

''You are abusing the color that you were the one who gave it to me, Toh Allah ma ya taimake ki in tashi ina son zuwa wurin bikin if it happens to be otherwise then then sai dai ki tafi ke kad'ai''.

''Ya Rabbi, try t

hat da kin ga k'arshen mood kuwa da sai kin yi tunanin anya Mufee Jumare ne?".

''Fad'a kike yi kawai Madam'' ta furta tana fashewa da dariya.

''Try it you'd see'' itama ta amsa tana dariya cike da jin dad'in yanda ta sake ta bar wancan magana

r da suke yi.

Haka suka k'are cin abincin cike da nishad'i, Mufee tana tsokanarta akan she better be in wedding mood daga yau zuwa Friday don she has to dress like someone going for wedding not the other way round. Ita kuma tana ce mata abinda yake r

anta shi zata yi so kar ma ta dame ta.

Yes, I know what's been running on your mind and it is exactly what's going on mine too.

ASH!ASH!ASH! what's amazing a rayuwar ta and ta yaya ta fara yin soyayya ne bayan most people like her ba su iya shi ba ba m

a su da lokacin ta?.

Yes ita ma da fari bata da lokacin sa but you can't just run away from nature. She's a human after all not an AI robot or her system, her nervous system is working properly so dole ne ta ji feeling but how? That's a question for ano

ther day.

Café 1, Market square, Barnawa, Kaduna Nigeria.

Shigowa tayi da tafiyar nan tata ta catwalk wanda take had'awa da rangaji kamar wata bishiyar turare a tsakiyar bazara, wanda ya taimaka ainun wajen sake bayyana zubin halittar d

a Allah ya mata wanda ko da ta suturce jikinta ba lallai ya b'oyu ba balle kuma careless shigar da tayi da bai yi wani k'ok'ari wajen amsa sunan shi na tufafi ba. Riga da skirt ta sanya na wani d'anyen lace tumeric color wanda aka yi wa wani malalacin d'in

ki kai kace a jikin ta aka d'inka shi duk ya bi ya lafe a duk wani kusurwa da curves d'in da Allah ya azurtata da shi. Siririya ce sosai amma kuma akwai arzikin halitta she's really busty ga hips kamar zasu fasa skirt d'in su fito haka ma mazaunan nata mas

u tudu ne irin matan da

ake kira da agwagwa akwai arzik'in naman cinya don haka kai tsaye zaka sanyata matsayin matan da ake kira da Kiran. Ta gefen halittar fuska ma sai godiya ga ubangijin da ya iya tsara halitta duk da ba za'a ce mata kyakkyawa irin ta

gaban misali ba amma a Nigerian mu zata shiga sahun mata masu kyau ba kuma wai irin wanda akan kira kyan 'yan gayu ba, a'a kyakkyawa ce babu wani abu da ya tawaya ta halittar ta irin matan da ake kira da Gawaniy, sai dai kash duk wannan zubi na halitta da

Allah ya mata ta sauya shi ta hanyar man k'ara hasken fata da ya sauya haskenta daga wankan tarwad'a zuwa fara. Ba kuma iya kalar fatan ta canja ba har da gashin da yake kanta da aka k'arawa Brazilian hair mai matuk'ar tsada wanda in baka sani ba zaka iya

cewa nata ne don human hair ne ta siya ba kuma wig bane ta sanya a'a fixing mata shi aka yi a can k'arshen gashin nata da ya sanya ya zubo kan gadon bayanta ya kwanta ga shi ya ji color mai dark golden brown da grey a ciki, ba iya bayan bane aka shafawa A'

a duka gashin kanta ne zaka iya fad'in kasancewar ba ta d'aura d'ankwalin kayan ba sai siririn gyale na Chantilly da ta yafa a kanta hakan ya sa gaban gashin nan da ya ji wax bayyana kuma colorn shi ya sanya bai b'oye cikin kan nata bai kuma sauka ba balle

ya rufe wanda ke kwance a gadon bayanta.

Kyakkyawar fuskarta kuwa bata shafa komai ba sai glowing take yi kamar zaka sace ta, hancinta sanye da abun hanci na gold dake ta lilo yana d'aukan idanu ga kuma irin na tsakiyar hancin nan da ake cewa in mata

suka saka suna kama da shanu, but in her case ko kusa ba tayi kama da halittar da ake kiran ba don yayi masifar mata kyau fiyeda tunaninka haka kunnenta tun daga farko har k'arshe jere yake da y'an kunnaye mabanbanta har da gefen kunnenta da ya kusa da fu

ska sai da aka saka masa nasa.

Yatsun hannunta ma zubona ne da suka dace da kowani yatsa, haka k'afarta ma da zobe amma a yatsar ta ta biyu sai sarkar k'afa mai hawa uku da ta sanya yana lilo.

Ga wasu uban heells da ta saka, hannun 'yar k'arama

r jaka ce kalar veil d'in ta nude sai wayarta da keyn motarta. Azababben turarenta shi ya fara isar da sak'on zuwanta wajen kafin k'arar takalminta ya biyo baya.

Ateeyah Hussein Shamaki kenan ko kuma kace ''Aesthetic by Teeyah'' A model and also a co

ntent creator, student ce a Greenfield University inda take karantar theatre and performing arts.

A tsakiyar café d'in ta tsaya tana k'arewa tables kallo daga farko har k'arshe da alamun wani take nema aiko sai wani ya d'ago mata hannu harara ta jefa ma

sa tana tura baki sama ta nufi inda yake a zaunen.

Su uku ne zaune a kan table d'in da ya ke table of 4 dukansu maza ne sai ita d'aya da ta zama mace, hannu ta mik'a musu suka gama gaisawa kana ta samu wuri ta zauna tana duban wanda ya fara d'ago mata

hannu tun zuwanta

tace '' Mamu i don't know why you chose this place wallahi, upon all the nice places in city centre center why this?".

Wani ne dake gefe ya cab'e da cewa '' i told him so, traffic d'in da ke stadium roundabout ma kad'ai ya isa ya sa m

utum ya ji had'uwar ta ishe shi''.

''I'm telling you and i was very oblivious of it fa na tsaya a JOS road for that company commercials da na gaya maka and I was stucked in it tun 4 fa look at the time now''.

'' Kai Yassar nan mugun munafiki

ne wallahi, ji yanda kake magana as if ba tare muka zo ba '' fad'in Mamu yana hararar shi, kallon banza Yassar d'in ya masa yana cewa '' amma ai sai da na gaya maka tun lokacin a canja venue ko?".

''Don Allah ku mana shiru mana, ha'an kun ishe mu da

hayaniya what do you want beaut?" Feezy ya furta yana tambayarta, idanu ta juya tana cewa ''Iced Americano will do, and some desserts I think''.

''Babe na fa miki ordern pie, your favorite fillings and ice cream''.

''That'll come later'' t

a amsa tana kawar da kanta, hannu ya kai ya d'ago fuskarta yana cewa '' I'm sorry Sweetest....''

Hararar da ta masa ne ya sanya shi kasa k'arasawa, ya sani a duk duniyar nan fiyeda kowa ba ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login