Showing 27001 words to 30000 words out of 260401 words
bulala akan fatar gadon bayanta.
Ihu ta saki da dukkan ƙar
finta tana kiran sunan Abbi, bata ta
ɓ
a tunanin akwai azaba irin wannan ba, saukar bulalar ya gigita Abra Khamal Khamis ƙwarai, har wani irin shi
ɗ
ewa take na rashin sabo!.
Na'ima tace "Yadda ki ka rabani da farin ciki na, ki kai sanadiyyar shiga tsakani
na da mijina, haka zaki dauwama cikin gidan nan ina gana maki azaba kala kala, wacce zata saka da ƙafarki ki fice ki bar min gida na,
Gidana nawa ne, da ga ni, sai Mijina sai kuma yaran da zan haifa masa, bana buƙatar kowa cikin rayuwarmu, zuwanki ya rugu
za min dukkan wani burina, ba zaki ta
ɓ
a jin da
ɗ
i ba in dai a gidan nan ne, mufuka, Algungumin".
Tai Maganar Kamar ta na yi da sa'arta.
Yadda Na'ima ke kumfar baki zaka
ɗ
auka da wata ƙatuwar mace, sa'arta take wannan ihun, ba da little Abra da ba ta wu
ce a goyata. A. Abra kasa kuka tayi sai sakin ajjiyar zuciya kawai take, bayanta yayi kwance da zanan bulala, ta kasa ko
ɗ
aga kai ta kalli Na'ima.
Tana bala'i da kumfar baki ta wanke wa Abra kashin, tare dayi mata wanka. Na'ima ta kalli Abra kafin da
ɗ
a
n ƙarfi tace "Tsinanniyyar yarinya, Allah ya isa tsakani na dake, wlh da ƙafarki zaki bar gidan nan" Abra bata san me Na'ima take fa
ɗ
a ba, hakan yasa bata ma fahimta ba, wani irin tsoron Na'ima ya kama Abra, tsoran dake neman sanyata cikin mugun hali, da s
on raunata mata ƙaramar ƙwaƙwalwarta.
Kama gashin kanta tayi da ƙarfi, cikin tsanar Yarinyar tace "Keee!!"
Abra ko motsi ba tayi ba, sai jikinta kawai take tsuma da karkarwa na azaba.
"Kika sake, naji kin fa
ɗ
awa Abbi wannan maganar sai na yanka ki" N
a'ima ta fa
ɗ
i maganar cikin kunnen Abra, tana nuna mata wuyanta da hannu.
“A...Abbi jani" cewar Abra wanda ilahirin jikinta rawa yake, Na'ima ta figi hannunta zuwa bedroom tana fa
ɗ
in "Abbin uwarki, ko na Ubanki? Baki da Uba a gidan nan Wallahi zan tabbata
r dana gur
ɓ
ata wannan muguwar fuskar taki. Kura da fatar Akuya!" Abra bata fahimta, da alamar yarinyar ta gama gigita da Na'ima, a haka Na'ima ta shirya Abra cikin Pria shirt short dress. Red colour, ta
ɗ
aure mata tulin sumar kanta da ribbon.
Yadda Na'i
ma taji ana knocking ƙofar ta, yasa tayi saurin Miƙewa tare da gogewa Abra Fuskarta tas, ta nemi perfume ta fesa mata, hannunta ta saka ta
ɗ
auki Abra tana gasa mata mintsini a haka ta nufi ƙofa da ita.
Tana bu
ɗ
e ƙofar taga Captain Khamal tsaye sanye cikin
ƙana nan kaya masu kyau, sai
ɗ
aukan idanu yake.
Na'ima tai murmushi, tace "Man, ina son yarinyar wallahi ta shiga raina daka jiya zuwa yau" tai maganar dan kar ya fahimci wani ab7
Ganin Khamal yasa hankalin Abra tashi, ta shiga miƙawa Abbinta hannu
tana son zuwa gareshi.
"Haba Daughter, nifa Mami ce mene yasa kike gudana" Na'ima ta fa
ɗ
a tana rungome Abra. Kafin ta
ɗ
aga idanunta zuwa ga Khamal tace. "Ina jin babu da
ɗ
i, yadda Abra bata son na
ɗ
auke ta, ba na jin da
ɗ
in ƙyuyar nan ta ta." kwantaccen M
urmushi Khamal ya saki tare da saka hannunsa ya amshi Abra dake hannun Na'ima, Abra ta ƙanƙame Khamal kamar zata shige jikinsa sai ajjiyar zuciya take saki.
A nutse Captain Khamal ya kalli Na'ima yana kashe mata idanunsa yace "Bata da yarda, kin san Ub
a yafi gaban wasa, shiya sa tafi yarda dani akan kowa"
“Uba yafi gaban wasa?” shine kalmar da ya nemi zautar da tunanin Na'ima, tunanin da ya sanya ta ƙara ninka ƙudirinta akan Abra, cikin fuskewa tace "I see, ka fahimtar da ita cewa nice mahaifiyarta,
bana son yadda take guduna ina son yi mata riƙo irin na uwa da ƴa, ina nufin A good mother, who stands by her child, ba zan ji da
ɗ
i abinda yake cikina ya fito duniya har ya girma ba, ace Abra na guduna ina son nunawa, Ɗa na ko Ƴa ta cewa Abra ita ce babba"
Kalman Na'ima sunyi tasiri a zuciyar Kham, wani farin ciki ya kamashi cikin nuna kulawa ya bawa Na'ima side hug yace.
"Kada ki damu, rashin sabo ne da kuma yadda ta tsinci kanta, zan yi ƙoƙarin fahimtar da Ita"
Murmushi Na'ima tayi da saurin kuma
tace.
"Oh, i almost forget bari naje na ha
ɗ
a mata something Liquid, tai breakfast"
Yace "thats good, I don't want my girl to starve" yai maganar yana sake rungume Abra tare da juyawa zuwa part
ɗ
insa.
Na'ima tace "Yanzu ta fara zama da yunwa" Khama
l dake ƙoƙarin bu
ɗ
e ƙofa, ya juya gaba
ɗ
aya yace "magana ki kai?" Na'ima ta bu
ɗ
e idanunta tace "Nace bani 10 minutes" ta fa
ɗ
a tana saurin shigewa cikin kicthen.
A hankali Khamal ya fara ƙoƙarin sauke Abra, wata gigitacciyar ƙara ta saka tana ƙanƙame shi
tare da
ɓ
oye fuskarta a jikinsa, jikinta na rawa tace "Abbi"
Kallonta Khamal yake, He is trying to understand, what scared her.
Zama ya yi da ita saman Royal bed
ɗ
in sa, cikin nuna kulawa yace "Daughter" ya fa
ɗ
a yana kallon Fuskarta, ganin Idanunta y
a yi jaaa sosai, Fuskarta ta kumbura alamar tayi kuka yasa, da sauri Captain ya kamata a jikinsa yace "Mene ya baki tsoro? Waye ya saki kuka Abra Khamal?" Yai maganar yana
ɗ
aga muryarsa dan ta ji me yake fa
ɗ
a.
Abra babu damar magana, sai
ɓ
oye jikinta ta
ke a jikinsa tana ajiyar zuciya, Tsam-tsam Khamal ya rungume ta a jikinsa, yana jin tausayinta na kamashi. Bai yarda da ƙwaƙwalwar Yarinyar ba, baya son ta samu “Depression” saboda alamu duk sun nuna a firgice take, Kamar ma wani abu ne ke tsorata ta, ƙar
a rungumeta yayi a jikinsa jin yadda take ta sauke ajjiyar zuciya!
"I'm sorry Daughter, Abbi is here with you" ya fa
ɗ
a yana shafa kanta.
Kwanciya tai lamooo, a jikinsa bayan wani
ɗ
an lokaci, ya ji Saukar numfashinta a ƙirjinsa, hakan yasa ya
ɗ
an
ɗ
agota
sai a lokacin ya lura bacci tayi, gaba
ɗ
aya a firgice take, kwantar da ita yaso yi, amma Abra taƙi sai ma sa ka masa kuka da tayi.
Kwanciya ya yi saman gadon, ya
ɗ
ora ta a jikinsa yana bubbuga bayanta alamar rarrashi, a nutse ya yi kissing cheeks
ɗ
inta,
Muryar can ƙasa yace.
"Ba zaki ta
ɓ
a kukan rashin iyaye ba, zan baki kulawa, Soyayya, tattali, zan yi maki dukkan abunda Uba na gari ya dace ya yiwa yaransa, zan bada ke ga miji na gari wanda zai so ki Love forever, love without deception insha Allah."
Ya fa
ɗ
i Maganar yana shafa sumar kan Abra, wata irin soyayya ya kewa yarinyar, wacce baya tunanin ko
ɗ
an cikinsa zai iya yi masa irin wannan Soyayyar. Ya kuma fahimci cewa ha
ɗ
uwar jini ce Abra ta kasance kyauta a gareshi ( A gift from God).
Zameta yay
i daga jikinsa yana gyara mata kwanciya tare da ja mata duvet ya lullu
ɓ
e mata jikinta, ya jima yana kallon yadda take sauke numfashi a wahale kafin ya juya zuwa waje.
A dinning area, ya samu Na'ima tsaye, tana shirya breakfast, tayi adonta kamar kullum
cikin doguwar rigar Abaya, fuskarsa babu walwala yaja Kujera ya zauna, without looking at her direction. Murmushi tayi cikin ƙasa da murya tace.
"Ya na ganka kai
ɗ
aya? Where's my Daughter?"
A kasalance yace "Mene ya samu Abra Khamal?"
Dam! Zuciyar
Na'ima ta buga, bata ƙaunar yadda Khamal ke maƙala sunan Abra da nasa, gani take babu wanda ya cancanci wannan sunan irin (Biological Child)
ɗ
in sa.
"Wani abu ya samu Abran bayan na kawo maka ita?" gaba
ɗ
aya ya
ɗ
aga kansa ya kalli Na'ima kafin yace.
"
Na fuskanci ta yi kuka, a launin Idanunta na gane" Na'ima taja Kujera bayan ta kammala ha
ɗ
awa Captain breakfast ta du be shi sosai kafin tace.
"Oh, ina son fa
ɗ
a maka daman,
ɗ
azu tayi kashi a ƙasa kasan daman ba yarda take dani ba, saboda na
ɗ
auke ta zuw
a Part
ɗ
ina, na wanke mata tare dayi mata wanka shine take ta kuka"
Jinjina kansa yayi tare da fara yin breakfast, ba tare da yace komai ba, sai da ya kammala ya miƙe tsaye, a tare suka dawo Main Parlo shi da Na'ima, tana ta fa
ɗ
a masa how she loves Abra.
Murmushi kawai Captain keyi, feeling so happy ƙasa tayi da Murya tace.
"Ya kamata ai mata shopping, na kayan sawa masu kyau sosai"
"Nawa zai isa?" Captain yace kai tsaye idanunsa akan plasma yana kallon News.
"200k, zai Isa komai da komai Man" Kallo
nta kawai yayi ba tare da yace komai ba.
iya satin biyun nan da Abra tai a gidan Captain Khamal, tas ha Wahala sosai wajan Na'ima, bata barin alama guda
ɗ
aya wanda Khamal zai fahimta, kasancewar baya gari yaje bada Wasiyyar da Captain Denial da Jamil s
uka bari.
Hakan yasa Na'ima ta samu full Chance na azabtar da Abra Khamal Khamis.
Da Yamma misalin 4:15 Motar Khamal ce ke tafiya akan titin Railway Quarters Nasarawa kano, kai tsaye motar a gida mai number 15 ta tsaya aka fara danna Horn, cikin sauri
Mai gadi ya bu
ɗ
e musu gate
ɗ
in, ana yin
parking da Motar, Captain Khamal Khamis ya fito, saboda yadda yaji zuciyarsa na bugawa, da sauri ya nufi cikin gidan, gaba
ɗ
aya hankalinsa ya tashi tun daka Main Parlo kunnansa ya fara jiyo masa sautin Muryar Abra.
Tsaye ya yi yana son sanin inda kukan ke tasowa, da sauri kuma ya nufi kitchen a gigice yace. “Na'ima!!!!” Khamal ya dakawa Na'ima tsawa, tsawar daya sanya tayi saurin sakin cokalin hannunta, wanda ya yi jajir saboda gasa shi da tayi a jikin Gas!
Yadda
jikin Captain Khamal ke rawa, haka na Abra ke rawa, Na'ima kam hatta
ɗ
an dake cikinta sai daya motsa, bata ta
ɓ
a tunanin zai dawo cikin wannan satin ba, ko
ɗ
azu sun yi waya amma bai ce mata yana hanya ba.
Dawowar ta sa tazo mata unexpected, wanda yasa N
a'ima ta kasa controlling kanta, tsoro ya kamata musamman yadda taga idanun Khamal na fitar da wani irin ruwan Masifa.
Da gudu Abra ta Ƙarasa wajan Khamal, tana saka wani irin kuka tare da zaro harshenta waje wanda ya yi jaa sosai, Khamal ya durƙusa tar
e da saka hannunsa ya
ɗ
auki Abra, Gam! Gam! Abra ta riƙe Khamal tana sauke numfashi a wahale, cikin taƙaici Captain yace.
"Na'ima? Abun da na gani, gaskiya ne Ƙona mata harshe ki kai With spoon? Ke mahaukaciya ce? Me wannan yarinyar tayi Miki? ashe ƙarya
ki kai baki shirya amsar Abra matsayin ƴa ba?"
Shiru tayi masa, gaba
ɗ
aya Khamal yayi kanta cikin hargaginsu na sojoji yace "Ba magana nake maki ba?"
Tace "Na fa
ɗ
a maka bana sonta, bana sonta yaya zan kuma.....," Marin daya sauke mata ya tilasta wa Na'
ima ha
ɗ
iye sauran maganganun, cikin fusata yace.
"You are evil, Na'ima!... Nayi nadamar bar maki Abra, Whatever happened to her ke ce sila, ba zan yafe Maki ba"
Cikin kuka Na'ima tace "Dama na san wannan shegiyar yarinyar 'ƴar kace, wacce karuwa ta hai
fa maka, wallahi sai na kasheta ba zan ta
ɓ
a zama da ƴar karuwa a cikin gida na ba"
Tana fa
ɗ
in hakan ta nufi inda wuƙa take ganin hakan yasa Khamal ya goya Abra a bayansa, ita kuma ta ƙanƙameshi, bai tsaya jiran komai ba ko tunanin cikin dake jikin ta ya
sake
ɗ
auke ta da mari, sai da ya jera mata mari har uku cikin
ɗ
aga murya yace.
"Abra ƴa ta ce, jina ce, nina na haife ta, nina samar da cikinta tare da karuwar da kike magana, tun da baki da hankali ba ki san me kike ba, Abra Khamal Khamis is my biologica
l Daughter! Kuma zan kawo karuwar da ta haifa min ita a matsayin mata taci gaba da riƙe ta..." Yana fa
ɗ
in hakan yayi waje, kai tsaye motarsa ya nufa Driver na ganinsa ya bu
ɗ
e masa mota ya shiga
ɗ
auke da Abra wacce take ta sauke ajjiyar zuciya na azaba.
Wani irin ciwo ne ya tasowa Na'ima, ba tare data shirya zuwansa ba, wata irin ƙulewar mara, da ciwon baya ne taso mata gadan gadan. ba tare da zato ko tsammani ba, nan take kuma wani ruwa ya fara bin ƙasan ƙafarta, idanunta har rufewa suke saboda kalman ƴ
a, da karuwa da suke mata kai kawo a kunne! Da gaske Khamal yake Abra 'yar sa ce? Wani gefe na zuciyar Na'ima ya tambayeta. Tuna shaƙuwa mai ƙarfi dake tsakanin Abra da Khamal yasa, marar Na'ima ƙara ƙullewa wayarta ta
ɗ
auka a ki
ɗ
ime jin kamar abin cikinta
zai faso ta cikinta ya fito, cikin kuka tace.
"Na shiga uku, zan mutu wallahi ƴarsa ce" Aunty daga can cikin wayar tace.
"Meke faruwa kuma yanzu Na'ima?" Na'ima na durƙushe dafe da cikinta tace "Duk abinda kika ce min nayi, na ƙona mata hannu na ƙona ma
ta harshe da cokali, yau ma ina shirin ƙona mata harshe sai ga shi ya dawo" Aunty ta bu
ɗ
e idanunta With shock tace "mene yasa wani lokacin daƙiƙiyar ƙwaƙwalwa ce take Na'ima? Ba nace idan yana nan babu ruwanki da yarinyar ba?"
Na'ima na kuka tace "Baya
nan, ban san yau zai dawo ba..." Ƙara Na'ima ta saki ba tare data ƙarasa maganar ba, Anty tace "Lafiya kike ihu kuma?"
tana yarfe hannu tace "marata ce za ta fashe Antyy, please Anty kizo na shiga uku...." Jifa tai da wayar jikinta na rawa tana ha
ɗ
a g
umin azaba, da wani irin ciwo da ba ta ta
ɓ
a jin irinsa ba, da ma kwana kusan biyu mararta na mata ciwo, amma da yake ta saka bala'i a ranta ba ta damu taje Asibiti ba.
Mintuna talatin da wayar da su kai, Anty Suwaiba ta ƙaraso cikin gidan hankali tashe,
tun daga tsakiyar Main Parlo ta fara jiyo kakarin Na'ima tana nishi.
Hankali a tashe tace "Ina kayan haihuwar suke, mu tafi Asibiti wannan ai kin kusa haihuwa?"
Da ƙyar Na'ima tace "Cikin
ɗ
akina, kan mudubi" da sauri Anuty ta nufi
ɗ
akin Na'ima bat
a sha wahalar ganin kayan ba, tana
ɗ
akko wa suka ci karo da Granny a Parlon.
Kallon tsaf Granny ta yiwa Anuty Suwaiba kafin tace "Ya na ganki duk a hargitse kamar wata ta
ɓ
a
ɓɓ
iya Suwaiba?"
Kafin Suwaiba tace komai Ammi dake bayan Granny wanda zuwansu
kenan tace "Badai haihuwa Na'ima tayi ba Suwaiba?"
"Haihuwa za tayi, Asibiti zamu tafi" Anty ta fa
ɗ
a a gajarce tana nufar kitchen
ɗ
in.
Granny ta bu
ɗ
e baki sosai tana girgiza kai tace "To mene ya kawo Bazawara gidan Kamalu kuma? Ina da labarin baƙin
halin matar nan, yaza tazo tayi kane kane a gidan jikana kamar ita yake Aure?" Ammi dai ba tace komai ba, tabi bayan Anuty Suwaiba zuwa kitchen
ɗ
in.
Se dai miƙewar da Na'ima za tai, tai nishi se ga jariri.
Ammi tace "Iko se Allah, tun farko be kamata
ta zauna a gida ita ka
ɗ
ai ba ga watam haihuwa ya kama".
Ammi ta amshi jaririn hannun Subawai wanda yake ta tsala ihu, tai waje ta ba su guri, cotton da zaiton ta
ɗ
auka ta shiga goge masa jiki, cikin ikon Allah kuma mahaifa ta fa
ɗ
o, Anuty ta gyara wajan
tass, Na'ima ta haihu a kitchen saboda 5sabar jaraba.. a ranta tana jinjina rashin kirki irin na Khamal Khamis.
Na'ima wacce ta fito wanka yanzu ta shirya cikin atamfa sai kuka take tana fa
ɗ
in "Ammi kin gani ko? ya gwammace ya
ɗ
auki yarinyar yayi waje
da ita, akan ya kai ni asibiti, Duk abinda muka tsara a rayuwar mu amma Zuwanta ya fara lalata komai, wlh ba zan iya ba"
Ammi da take riƙe da kyakykyawan jaririn Na'ima wanda ya kwashe kamarta tas, babu abinda ya
ɗ
auka na khamal sai kyawawan fararen ida
nunsa, amma kamar yaron da Na'ima ta
ɓ
aci.
Ammi tace "kiyi haƙuri, bani da bakin baki haƙuri Na'ima, amma bai dace ki dinga danganta Abra da Khamal ba, Khamal da ya iya riƙe kansa tun lokacin samartaka, tsayin shekaru mene zai sa kice wannan yarinyar
ƴ
arsa ce? Da Khamal zai ajjiye shege da tun yana saurayi zai ajjiye ba yanzu daya yi Aure ba.
Ba ina kare Khamal ba ne, Saboda rayuwa ta sauya Mutane na iya canzawa a kowane lokaci, balle rayuwa irinta sojoji d suke cu
ɗ
anya da mutane daban daban.
Naima
tace "Har mari na yayi akan gantalliyyar yarinya da babu wanda yasan Wacece ita, yanzu fa kiransa akai aka ce masa na haihu, haihuwar da yake ta burinta kalli yadda yayi watsi da komai? Bai damu da
ɗ
an sa da yanzu duniya yake buƙatar jin
ɗ
umin jikinsa ba,
Nasan Khamal sai ya nuna bambanci tsakanin Shegiyar da
ɗ
an daya haifa Wallahi ba zan iya ba" Na'ima ta ƙare maganar cikin kuka, Granny