Showing 201001 words to 204000 words out of 260401 words
Meenal a ƙofa a tsaye, jin hayaniya ya sanya ta fito, bai ko kalleta ba ya wuce yana huci.
Meenal ta ƙarasa shiga
ɗ
akin ta kalli Mummy ta ce "Mummy me ke faruwa ne? Wace takadda da hotun
a Daddy ya ke magana a kai?".
"Ke kar ki dameni dan Allah, koma
ɗ
akinki"
Ƙ
urawa Mummy Ido ta yi, ta ga gaba
ɗ
aya gumi ya rufeta, alamun tsoro da rashin gaskiya suka bayyana ƙarara a fuskarta.
"Mummy dan Allah ki gaya mini".
"Get out from my sig
ht, ki koma
ɗ
akin ki na ce" ba shiri Meenal ta bar wurin, tana tunanin meke faruwa haka?
Sintiri Hajiya Sauda ta shiga yi a
ɗ
akin, tana jinjina kai tamkar ƙadangaruwa. "Kafin ka binciko komai, zan sake bunneka doctor, ba bu abin da zaka iya ganowa!' ta
fa
ɗ
a tana sauke ajiyar zuciya.
Hajiya Mama ta kira Adnan a waya, ta ji ko ya sauka lafiya, suka ta
ɓ
a hira, har ta tura masa hotunan Aishatul Humaira ta waya, kamar yadda Mami kan tura mata.
Adnan ya ƙura mata izanu, ji yayi zuciyarsa na son ga
nin Aishatul Humaira, rabon da ya ganta tun tana kwalba, tun da aka tafi da ita bai sake zuwa ya ganta ba, wata irin soyayyar yarinyar ta mamaye zuciyarsa, musamman yadda kammaninta suka juue zuwa na Abra sak, wanda kyakykyawan hanci Bulama irinsa ne
ɗ
o
ɗ
ar
a fuskar Aishatul Humaira.
Nan ya barwa zuciyarsa cewar zai je Kano ya ga Little Abra.
Kwanansa biyu a garin, ya je ofishin 'yan sanda na yankin, ya ga DPO, domin fara gabatar da aikin da ya kawo shi, daga nan kuma ya tafi Kano.
Ba ƙaramin mama
ki Mami ta yi ba da ganin Adnan, sam bai sanar da zuwansa ba, ita abin har mamaki yake bata, yadda ko ta waya baya neman ya 'yar ta sa take ciki, sai dai ta yi masa uzuri, kasancewar tun da Abra ta rasu, yake kwance ba lafiya, dan a yanzu ma ya rame da yaw
a, ya ƙara duhu sai idanu.
Mami ta yi masa kyakywar tarba, tare da yi masa ya jiki.
"Jiki da sauƙi Mami, ya Mamana?".
Mami ta ce "Ai na
ɗ
auka ka bar mini ita gaba
ɗ
aya ne, baka sonta?"
Adnan ya sunkuyar da kai ya ce "Mami ya za ayi in ce bana s
onta, ina gujewa abin da zai sa in dinga tuna Abra ne kawai, yanzu haka ina cikin wani ƙauye a katsina, na tafi aiki, Mama ce ta turo mini hoton ta,naji lallai ina son in zo in ganta".
Mami ta ce "Allah sarki, ai sai haƙuri mu cigaba da yi mata addu'a,b
ari in
ɗ
auko maka ita".
Ta shiga
ɗ
aki ta
ɗ
auko masa Little Abra, wadda ta ke ta bacci, ya ƙura mata idanu kamar zai cinyeta, tayi girma yanzu kamar ba wadda aka ciro a kwalba ba.
Ya
ɗ
agata yana cigaba da kallonta, amma sai lanƙwashe wuyanta ta ke tana
tura baki, alamar bacci bai isheta ba.
"Like Mother like daughter" ya furta yana tuna Abra, tuni idanunsa suka cika da hawaye.
Mami ta ce "Ayi haƙuri dai, Ai mata Addu'a".
Adnan ya jinjina kai sannan ya ce "Abbi ba ya gari ne?".
Mami ta
ɗ
an kwa
ɓ
e baki ta ce "Eh".
"To, ga siyayya can na mata, kuma ina ganin tun da ta ƙara girma, ai mata hakika".
Mami ta ce "Tun yaushe aka yi mata hakika, ai kana wannan rashin lafiyar aka mata komai, taron suna ne da bai yiwu ba, tunda ga abin da Allah ya sa
ukar"
Adnan ya ce "Haka ne, Allah Ya rayata ya jiƙan mamanta".
Mami ta amsa da Ameen.
Adnan ya kwaso uban kayan da ya sayowa Aishatul Humaira.
Mami ta ce "Da ka yi shawara da ni ba zaka sayo wannan kayan ba, ta na da kaya da duk wani abun buƙat
a, da ga can
ɓ
angaren ku sun kawo, nan ma duk an mata komai, madara kawai tana da gwangwani kusan Ashirin, diapers da komai duk akwai".
"Lallai wannan 'ya 'yar gata ce, bakoma Mami ai alhakina ne nima na yi mata".
Sai bayan azahar sannan Adnan ya y
i haramar tafiya, kamar kar ya tafi, ji yake kamar ya ce a bashi 'yar sa ya tafi da ita.
Ba yadda ya iya haka ya yi sallama, ya tafi, sai dai ko da ya wuce ta ƙofar sitting room
ɗ
in da yake zama su yi hira da Abra, sai da gabansa ya fa
ɗ
i, ya tuna yadda ta
dinga nuna masa soyayya a wannan lokacin.
Jiki a sanyaye haka ya baro gidan su Abra.
Bai isa katsina ba sai dare, tun a hanya ya sai 'yan kayan da zai buƙata, da abin da zai ci ya kwana a wani Hotel, dan ba zai iya shiga wannan ƙauyen da daddare ba.
Sai washegari da safe, sannan ya fara shirin tafiya ƙauyen.
Har ya gama shiri, ya ga dacewar yakira Abba, ko ba zai amsa ba ya gaishe shi.
Sai dai yadda Abban ya amsa gaisuwar ne, za ka tabattar da haryanzu Abba yana fushi da Adnan.
A sanyaye ya s
higa motarsa, ya cigaba da tafiya.
Yaran garin kamar ba su ta
ɓ
a ganin mota ba, da zarar Adnan ya yi parking
ɗ
in mota, suke zuwa su kewaye motar suna kallo, saboda haka mai gari ya sa aka samo wuri na musamman da yake ajiye motar, gudun kar yaran su mata
illa.
Da yake har yanzu gajiya na damun Adnan, dan haka a
ɗ
aki ya wuni, salla ce kawai take fito da shi.
Bayan la'asar ya ga dacewar ya zazzaga garin, ya jefi tsuntsu biyu da dutse
ɗ
aya, ya ga ta ina zai fara bincikensa, kuma ko Allah zai sa ya sake g
anin Abra.
Sannu a hankali ya nausa cikin ƙauyen yana zagawa, sai ya ga wurin ya burgeshi, dan haka ya cigaba da kutsawa yana zagaye, har ya bar in da mutane suke.
Tafiya ya yi sosai mai nisa, wurin ba kowa sai bishiyu da kukan tsuntsaye, ga manyan bis
hiyun fruit kala kala a wurin.
Can ya hango wani tafki, ruwan ciki garai da shi, dan haka ya nufi wurin yana son ganin girman ruwan, sai ya tuna zamansu a Dubai, yadda Abra ke son ruwa, kuma tana tsoronsa.
Kamar Aljana, haka zalika kamar a yadda ya gan
ta wancan lokacin, ta juya bayanta, ta zuba su a cikin ruwan, tana ta ka
ɗ
a ƙafafuwan ta a ciki.
Da wata irin gaggawa, ya nufi in da take zaune.
Jikinta ya bata a na tsaye a bayanta, ga kuma ƙamshin turaren da ba zata ta;a mantawa da shi ba ya daki ha
ncinta.
Ba tare da ta waigo ba, ta tashi da sauri, aikuwa gabanta ya fa
ɗ
i da ta ga Adnan a tsaye kamar gini.
Juyawa ta yi zata taka da gudu, dan ba ta gama yadda mutum ba ne, wannan mutum haka mai siffar shago.
Yana gano nufinta ya danƙota, ya ja
ta gefe, jikinta ne ya hau rawa "Ka ga dan Allah ka cika ni".
"Abra, wai har yanzu ba ki gane ni ba? Na san loosing memory ki ka yi".
"Allah ya sawwaƙe, kana nufin na haukace fa kenan, to Wallahi ni ba mahaukaciya ba ce".
"Abra dan Allah ki saurar
eni"
"Kai karka sake kirana da wannan sunan, wani suna kamar babur, kamar burabusko, ni ba sunana kenana ba, dan Allah ka cikani kar Inna ta gane Namiji yata
ɓ
a ni"
"To ai ni mijinki ne Abra"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ko dai aljani ne ya
aure ni ban sani ba?"
Ƙ
ara matso da ita jikinsa ya yi, yana ƙare mata kallo, duk da yamma ta ti sosai, Abransa ta fi wannan fari da ja, amma wannan ma fara ce tas, dan ba ta samu hutu bane, Abransa muryarta a hankali take yin ta, wannan kuwa muryar ta
a tsaye take, cike da tsiwa da rashin kunya. Abra ta fi shagwa
ɓ
a a kan duk al'amuranta, wannan a tsaye take da ƙwarinta.
Mutsu mutsun ƙwacewa take yi, tana ta kurma ihu.
Adnan ya ce "Zan cika ki, amma muje in ga gidanku, zan magana da ke"
Ta ce "T
o, na yadda".
Adnan na cikata, kamar ya saki tattabara, ta watsa da gudu, ta nemi hanyar barin wurin.
Littafin ku
ɗ
i ne, don biya ku tuntu
ɓ
e mu ta wannan lambar. 09047871750
[11/9, 11:32 AM] Abk: Ƙoƙarin kamo ta ya yi, amma yadda take gudu kamar
mai fukafukai ya sa cikin sakanni ta
ɓ
ace wa ganin shi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da shafa sumar kansa, lallai wannan aikin da ya zo yi ba ƙaramin Alkhairi ya zamo a gare shi ba, bai ta
ɓ
a tunanin zai ƙara yin farinciki a rayuwarsa ba, amma ganin wannan h
alittar mai kama da Abra da acting
ɗ
inta ya fara saka shi cikin nisha
ɗ
i. Ya yarda Abransa ta tafi ta bar shi wannan ba ita ba ce, amma tsananin kamar da suke yi idan ba wanda ya yi wa Abra mugun sani ba idan ya ga wannan zai ce ita ce. Saboda yadda komai n
asu yake iri
ɗ
aya, ido, dogon hanci da dogon baƙin gashi, cikakkiyar gira da
ɗ
an ƙaramin bakinsu gami da jerarrun fararen haƙora, hatta hannu da ƙafarsu duk iri
ɗ
aya ne. Banbancin su kawai Abra ta taso a birni gidan hutu, ita kuma wannan yar ƙauye ce. Murm
ushi ya kuma yi a karo na biyu ya juya ya tafi don aiwatar da abin da ya kawo shi, zuciyarsa cike da addu'ar Allah ya sa ya kuma ganin ta a yau.
"Wai don Allah ƴar Baba yaushe za ki yi hankali ne ki san kin girma? Sau nawa nake ce miki ki daina fa
ɗ
o
mana gida da gudu kamar wani filin ƙwallo"
Zama ta yi tana haki tare da turo baki gaba ta ce. "Wai Inna ba ki san me ya faru ba za ki fara yi mini fa
ɗ
a, ba ke ba ce kullum kike cewa kar in bari Namiji ya ta
ɓ
a ni ba?"
Inna ta ce. "Eh ni ce."
"T
o wannan mutumin da na ce miki ya biyo ni jiya yau ma shi na ƙara gani a bakin teku, ya riƙe ni yana kira na da wani suna kamar babur, wai don Allah in daina gudun shi."
Ido a waje Inna ta ce. "Wane shi? Me yake nema a gurin ki? Ɗan gidan waye a garin
nan? Don ba zai yiyu ba sai mun je an kira iyayensa an yi wa tufkar hanci, akan me zai dinga ta
ɓ
a ki?"
"Kai Inna ya na ga duk kin tsora ta?"
"A'a, kar na tsorata? Na san mugun nufin shi a kan ki?"
"To Inna daga ganin shi ba
ɗ
an garin nan ba ne,
irin yan gayun nan ne yan birni, sai ma kin ji ƙamshin da yake mai da
ɗ
i." Ta ƙarashe maganar tana murmushi.
Tsaki Inna ta yi ta ce. "Ko ma
ɗ
an ina ne ba ruwana, bari Musa ya fito daga wanka mu je gidan mai gari". Ganin da gaske Inna take sai Ƴar Baba t
a ce. "To ƙarya ma nake yi duk abin da na ce miki." A ƙufule Inna ta
ɗ
auki mafirficin kaba za ta kwa
ɗ
a mata tana fa
ɗ
in. "Ja'irar kashi, wato kin mayar da ni kakarki ko?" Kafin maficin ya sauka a jikinta ta kwasa da gudu ta yi
ɗ
aki tana dariya. Musa da ya f
ito daga bayan gida a lokacin shi ma dariyar yake. Yana ajiye bokitin hannunsa ya ce. "Wani lokacin Inna kamar ba ki san halin ƴar Baba ba, ta zo ta zauna ta tsara miki zance na ƙarya, ke kuma ki hau kai ki ta banbanmi, sai kin gama ta ce ƙarya take." Inna
ta ce. "Na daina yarda da ita ai, ja'ira kawai, Allah ya shirya mini ke."
Ita kuwa tana shiga
ɗ
akinta ta yi tsalle ta fa
ɗ
a kan katifarta, haka kawai ta ji mutumin da take ha
ɗ
uwa da shi ya tsaya mata a rai, ta rasa me ya sa kuma da Inna ta ce za ta ka
i ƙarar shi gurin mai gari ta yi saurin cewa ƙarya take, ita da take jiran ƙiris mutum ya yi mata abu ta kai shi ƙara. Tsaki ta ja a fili ta ce. "Ƙila ma aljani ne,
ɗ
an baƙi kawai, bai san ma ni na fi son farin mutum ba, ta ƙarashe maganar tare da murgu
ɗ
a
baki. Tunowa ta yi wata ƙawar su ta haihu jiya, hakan ya sa ta miƙe ta fice daga
ɗ
akin don zuwa ganin
ɗ
a.
"Inna zan je na ga jaririn Atine." Ta yi maganar tana saka takalmi.
"Ki bari a yi Sallah mana, ko kuma gobe da safe kya je."
Diddira ƙafa
ta fara yi tare da fa
ɗ
in. "Don Allah ki bar ni na je, duk su Lantana fa suna can tun
ɗ
azu."
"Allah ya tsare." Inna ta fa
ɗ
a a takaice, don ta san idan ta hana ta ma zama zata yi ta cika musu kunne da ihu, don ba ƙaramin aikinta ba ne.
Bayan Magriba
Abbi ya sauka a Kano, direct gidan Ammi ya wuce, saboda ta kira shi akan tana son ganin shi. Bayan sun gaisa Ammi ta gyara zama ta ce. "Babana,
ɗ
azu matarka ta kira ni tana ta kuka akan wannan auren da za ka ƙara, don Allah ka tausaya mata ko
ɗ
aga bikin na
n ne a yi mana, ka ga har yanzu tana cikin alhinin rashin Abra, wallahi tausayi take ba ni, duk ta bi ta
ɗ
aga hankalinta." Cikin ladabi Abbi ya ce. "Ko shekara za a ƙara akan Auren nan idan aka tashi yi sai Nai'ma ta ƙara
ɗ
aga hankalinta Ammi, kuma kin ga
babu da
ɗ
i biki saura kwana biyar sannan a ce za a
ɗ
aga saboda wani dalili mara ƙarfi, an riga an gama buga IV an raba, yarinya sun fitar da anko sun yi komai, sai a
ɗ
auke mu ƙananun mutane." A sanyaye Ammi ta ce. "Shikenan, Allah ya tabbatar da Alkhairi ya
ba ku zaman lafiya, Allah ya ba ka ikon yin adalci a tsakanin su."
"Amin Ammi, bari na ƙarasa gida don sauka ta kenan na ce driver ya fara kawo ni nan, idan na je na yi wanka na huta zan je gidan Iman, ta dame ni akan za su yi Mother's day da sauran su
."
"Da ka rabu da su Babana, muna cikin alhinin mutuwar Granny da Abra babu wasu bidi'ebidi'e da za mu yi."
"Na mata maganar hakan ni ma, amma ta ce mini ai ba ki
ɗ
a za a yi ba, kamar walima abin zai tashi, za a ci a sha ne kawai."
Ammi ta ce.
"Toh shikenan, Allah ya kai mu."
Ya amsa da Amin tare da miƙewa ya yi mata sallama ya tafi.
Sai kusan isha'i ta baro gidan Atine, tana tafe ita ka
ɗ
ai cikin sauri ta ji ta yi karo da mutum. Cikin masifarta ta bu
ɗ
e ba ki za ta yi magana amma maga
nar ta kakare, sakamakon ganin wanda ba ta yi zato ba. Adnan ne shi ma ya dawo daga inda ya je, hannunsa riƙe da torchlight yana haska hanya. Duk da ba ta kalli fuskarsa ba amma ƙamshinsa ya sanar mata shi ne.
"Innahu Sulaimanu wa'innahu bismillahirrahm
anirrahim." Ta fa
ɗ
a tare da ja baya cikin tsoro da fa
ɗ
uwar gaba, don zuwa yanzu ta fara tantamar anya ba aljani ba ne? Duk inda ta yi sai sun ha
ɗ
u.
"Angel!"
Ya fa
ɗ
a cikin murmurshi tare da haske fuskarta. Turo baki ta yi ta ce. "Wai kai a ina ka san
ni ne? Don Allah ka daina bibiya ta, ni fa ban san ka ba ban ta
ɓ
a ganin ka ba."
"To ai yanzu kin san ni ko?" Ya yi maganar yana ƙoƙarin kamo hannunta."
"Na shiga uku! Wai da wa Allah ya ha
ɗ
a ni ne?" Ta yi maganar tare da tattare siket
ɗ
inta ta mann
a da gudu. Da kallo ya bi ta har ta
ɓ
ace wa ganin shi, zuciyarsa cike da mamakin yadda ta ƙware a iya gudu haka.
"Who is she?" Ya tambayi kan shi cikin rashin sani, yana son sanin wacece ita da gidan da take da tarihin rayuwarta, don kamar su da Abra ta
fi ƙarfin a ce kama ce kawai, sai dai in da wata alaƙar, domin hatta muryar su iri
ɗ
aya ce, yadda suke magana ne kawai ya banbanta.
Kamar kodayaushe cikin gudu ta ƙarasa gida, tana tafe tana murgu
ɗ
a baki da zancen Adnan a cikin ranta. Labarin na cin ta
a rai amma ba ta fa
ɗ
a wa Inna ba, saboda
ɗ
azu ta riga ta ce mata ƙarya take.
Nai'ma na zaune a main parlour ta yi tagumi abun duniya duk ya bi ishe ta Abbi ya yi sallama fuska babu walwala. Ba ta amsa masa ba sai ma ha
ɗ
e rai da ta yi. Kallon yadda t
a rame ta lalace ya yi, sai ya ji tausayin ta ya tsirga masa, takaicin ta na kiran Ammi da ta yi ya fara gushewa daga cikin ransa. Jakar hannunsa ya ajiye tare da zama a kusa da