Showing 3001 words to 6000 words out of 260401 words
dan fitar da su daga cikin sarƙaƙiyar dajin, yayin da wasu sojojin ke ta kwaso gawarwakin'yan uwansu da aka kashe.
"Khamal" aka kira sunansa, da sauri ya juya ga
nin Jamil kwance cikin jini, anyi masa harbi kusan guda uku, jikinsa na rawa yace "Jamil" Jamil ya girgiza kai yace "Khamal ina maka fatan tsira da ranka, kaje wajan matata kace ta yafe min, wlh ban san adadin ƴan matan da nayi mu'amala dasu ba, yanzu haka
ina
ɗ
auke da Hiv, ina da tabbacin matata ma tana dashi, bata san hawa ba bata san sauka ba, na
ɗ
ora mata mugun ciwo" Khamal ya Girgiza kansa yace
"Kayi salati" Khamal ya fara salati Jamil yana maimaita wa, a nan jikin Khamal Ubangiji ya
ɗ
auki ran Jamil.
...
Kwanan su wajan uku, cikin dajin gaba
ɗ
aya kuma sun kwashe ƴan matan an fita da su, a kwanaki ukun nan, kullum se sunyi musayar wuta da 'yan bindiga.
sojojin duk sun ƙare, se wanda ba'a rasa ba, da gudu Major yake tafiya ganin wata budurwa yashe a
ƙasa, kafin ya Ƙarasa wajanta yaji ance
"Kaiiii" Aka daka masa tsawa da karfi, Juyawa yayi ya ware idanunsa ganin wani riƙe da bindiga zai harbeshi, Denial ya tare harbin hakan yasa aka harbi Denial a ƙirji...
Captain ya zaro bindiga ya fara Harb
in
ɗ
an ta'addan , sai daya kashe shi sannan ya nufi wajan Denial yace "Mene yasa haka Denial?" Denial ya girgiza kai yace "Kai na musamman ne, gwara na mutu kai ka rayu, bana fa
ɗ
a maka ba? Daman nasan mutuwa zan, kada ka manta da abinda na baka, a cikin mu
akwai maciya amanar ƙasa, amma kai da gaske kake naka aikin, Khamal na baka amanar iyali na.. zaka iya, nasan zaka iya ka kula dasu"
Yana fa
ɗ
in hakan rai yayi halinsa, wani irin ihu Khamal ya saki mene yasa haka ke faruwa? Su sojoji a haka rayuwarsu z
ata ƙare ne? Sunyi shiri na gaske akan fa
ɗ
an nan, amma kamar 'yan ta'addan sun san da zuwansuz duk sun samu nasarar kashe zaratan sojoji masu ƙoƙari, ciki har da makusantan abokansa, Miƙewa ya yi, gaba
ɗ
aya jikinsa jini ne kayansa duk sun yage, ga yunwa, ƙ
ishirwa.
Yana zaune a ƙasa yaji shawagen Helicopter, da alamar General ne ya ƙaraso,yasan
ɗ
auki gaggawa aka kawo musu, kasa Miƙewa yayi har sai da wani soja yazo wajansa ya
ɗ
aga sa, yana fa
ɗ
in "Komai yazo ƙarshe Captain"
Sauran gawarwakin aka kwashe
zuwa cikin wata babbar motar sojoji, raguwar 'yan ta'addan da sojojin suka kama suka
ɗ
aure, suma aka zuba su cikin mota, suma sauran mutanen da suka tsitstsinto anyi garkuwa da su, a wata mota aka zuba su, Khamal ya miƙe ya na tafiya a hankali, kamar dag
a sama kunnansa ya fara jiyo masa kukan ƙaramin yaro, tsaye yayi, yai shiruu, jin kamar ba kuka bane yasa ya cigaba da tafiya. yana ƙoƙarin sanya ƙafarsa cikin mota, ya ƙara jiyo sautin kuka, a wannan karon kuma ya tabbatar gaskiya kunnansa ya jiyo masa,
kuka ne da gaske, fasa hawa motar yai, sauran sojojin na kiransa amma be kula ba, a hankali yake tafiya jiki a sanyaye da ƙyar yake
ɗ
aga ƙafarsa saboda wahala, ganin baiga kowa ba sai ya fara tunanin ko aljanu ne? Ko kuma kukan wata dabbar ce, wani kukan
ya sake jiyowa da sauri ya juya zuwa inda yake jin kukan, ya ƙara nausawa cikin dajin, ware idanunsa yayi kan ƙaramar yarinyar dake zaune a ƙasa ta ƙanƙame jikinta waje guda, Idanunta rufe da alama gaba
ɗ
aya a firgice take, Khamal ya ware idanunsa akan yar
inyar gaba
ɗ
aya ba zata shige shekara uku ba (3Years) fara ce sosai kamar buzuwa kamar kuma Balarabiya, tafi kama da ruwa biyu (Half-caste) domin gashinta wanda yafi ƙarfin kanta ya sauka har ƙasa kasancewar a zaune take, farar fatar jikinta tayi baƙi sosa
i, ga raunuka a jikinta..
Sosai Khamal ya girgiza da ganin ƙaramar yarinya a cikin jejin nan, sai ya fara tunanin ko dai Aljana ce?ko a cikin matan da akai kidnapping take, Samun kansa ya yi da cewa
"Ke" shiru tayi masa sai kukanta take tana ƙanƙame
jikinta, cikin rashin sanin cewa yarinyar nada ƙarancin ji a kunnanta yasa Khamal ƙara cewa "Kee" nan ma tayi masa shiru.
"kada ka kuskura ka
ɗ
auki yarinyar nan, ita ba kidnapping
ɗ
inta mukai ba, ita tamu ce, rainonta za muyi, 'yar mu ce" Cewar wani m
utum da ke tsaye, hannunsa riƙe da bindiga.
Captain Khamal ya kalli mutumin sai kuma ya kalli Yarinyar, kana yaja baya ka
ɗ
an yace "To me zan da ita tun da taku ce?" Ya fa
ɗ
a yana Juyawa, mutumin ya sunkuya zai
ɗ
auki yarinyar kenan yaji saukar bullet a b
ayansa, ihu ya saki yana fa
ɗ
uwa ƙasa, cikin zafin zuciya Khamal ya fisgo Yarinyar yace "Keeee...." Sai a lokacin taji saukar muryarsa a kunnanta, fararen idanunta ta
ɗ
aga, wanda yasa zuciyar Khamal bugawa, Yarinyar ta washe bakinta ta nufi wajan Captain Kh
amal tace
"Abbi..." Ta fa
ɗ
i hakan tana ƙanƙame ƙafafuwan Khamal, “Abbi?” Khamal ya maimaita a zuciyarsa a fili kuma sunkuyawa yayi ya
ɗ
auki yarinyar a kafa
ɗ
arsa, kai tsaye ya nufi in da motocin su suke da ita yana ƙoƙarin shiga cikin mota yaji saukar
wani abu mai kama da kibiya ko mashi a gefen cikinsa, a hankali kuma yaji zafin saukar abu a jikinsa tsananin azaba yasa sam bai kawo cewa harbinsa akai ba, ƙafarsa ya
ɗ
aga da ƙyar yana sauke Yarinyar muryarsa na rawa yace
"Shiga ciki" watsa hannunta
tayi tace "Abbi" alamar bata gane zan can nasa ba, da hannunsa yayi mata alamar ta shiga cikin motar, sauran sojojin na ciki basu san meke faruwa ba, bayan ta shiga cikin motar Khamal ya
ɗ
aga ƙafarsa da ƙyar zai shiga cikin Motar ya ƙara jin saukar wani ha
rbin a gefen cikinsa...
😂😁
Ya kuka ji salon Bright pens?..... Daban ne... Share share share as so much as you can!.
#Nimcyluv
#Zee kumurya
#Ayushercool
[9/30, 8:55 PM] Abk: *
✷
DARE DA HUDU
✷
*
_Bright pens of
✍
🏾
_
Nimcyluv
Ayushercool
Zee kumu
rya
Ƙ
irƙirarren labari me, ba mu yi shi dan cin zarafin wani ko wata ba, idan yai kamanceceniya da rayuwar wani ko wata Arashi ne.
Littafin DARE DA DUHU haƙƙin mallakar mu ne, bamu yar da a juya shi ta kowace siga ba, ko a sashi a wata kafa b
a ba tare da izinin mu ba.
BISMILLAHIRAHMANIRAHIM
ELEGANT ONLINE WRITER'S
P2.....
Jin sautin harbin da ya sake tashi ne, ya sa yarinyar fitowa daga cikin Motar da sauri ta tsaya tana kallon Captain.
Jini ne ya shiga zuba a gadon ba
yansa, ga na cikinsa da yake zuba shi ma, cike da jarumta irin ta soja yake ƙoƙarin tsayuwa kan ƙafafunsa, ya kuma ƙoƙarin ya yunƙura ya
ɗ
aga ƙafarsa, sai dai yaji jikinsa yai masa nauyi, ga wani danshi da yake ji ya jiƙa masa kaya, sai a lokacin ya fuskan
ci harbi ne, a nan take duhu ya maye gurbin hasken ranar da ya haska dajin a idon Captain, a hankali yai baya ji kake timm ya fa
ɗ
i ƙasa.
Sam ba ta san me ya faru da mutumin ba, wanda ya kar
ɓ
o ta a hannun wa
ɗ
an nan mutanen, sai dai ta zuba masa many
a manyan idanunta, sai jujjuya ƙwayar idanunta take a kansa.
Sautin Wani harbin ne ya kuma tashi, cikin azama wani soja ya fito daga cikin Motar, ya danƙi yarinyar ya kwantar da ita flat a ƙasa, ya shiga danna nakiyar ta sa bindigar shima a saitin in da ƙ
arar harbin ke tasowa.
Sautin Command
ɗ
in Commander Land army ya jiyo nesa ka
ɗ
an da in da suke, yana bawa tawagar sojojin umarni, cikin dakakkiyar muryarsa dake amsa kuwwa a dajin, tare da ƙarar motocin sojojin na yaƙi, hakan ya tabbatar masa, da an tur
o wasu sojojin domin kawo musu
ɗ
auki.
Nan da nan ƙarar harbi ya sake cika dajin, tamkar za'a tsaga dajin.
Tai lamoo a ƙasa, duk wannan ba ta kashin, da ƙarar bindigogin da ke tashi, can ƙasa ƙasa take jiyo sautin ka
ɗ
an ka
ɗ
an a cikin kunnenta.
Gaba
ɗ
aya hankalinta yana kan mutumin nan da ya
ɗ
akko ta, da yake kwance a ƙasa, ba ya ko motsi.
Ba tare da tunanin komai ba, ta miƙe zata nufi in da yake ƙasa a kwance, sojan nan da ya kwantar da ita flat a ƙasa, ya fizgota cikin tsawa yace "Lay down befor
e they shoot you" shiru tai tana son gane me yake cewa.
Ya sake kwantar da ita a ƙasa, hellcopter nan kuwa tuni ya tashi ya fara shawagi a sama, suna communicating da sojojin dake ƙasa.
An kwashi kusan awanni biyu ana wannan musayar wuta a tsakanin '
yan ta'addan da kuma sojojin, wanda a ƙarshe Allah ya bawa sojojin nasarar fatattakar maharan, suka kashe na kashewa.
Sai bayan da ƙura ta lafa, sannan Lieutenant Faruk ya migirna a hankali, saboda harbin shima da akayi masa a dantsensa.
Cikin jaru
mta ya miƙe tsaye, sai dai jiri ne ke
ɗ
ibar sa, saboda jini da yake zubarwa a dantsen nasa, yana tashi ita ma yarinyar ta tashi tsaye, sannu a hankali ya ƙarasa in da Captain yake kwance a sume cikin jini, ya durƙusa ya
ɗ
ago shi, tare da kara kunnensa a sa
itin zuciyarsa, can ƙasa ƙasa yaji bugun zuciyarsa alamar yana da rai.
Bin su kawai take da ido, tana sake zura kai tana kallon Captain da idanunsa ke rufe.
Tawagar sojojin da suka shigo dajin kawo musu
ɗ
auki ne suka fara
ɓ
ullowa, suna ta tattara gawar
wakin 'yan uwansu, da wanda a kaiwa rauni.
Cikin hanzari suka ƙaraso in da su Captain suke. Lieutenant Faruk na zaune rungume da Captain a jikinsa, Chief Commander yace "Are you ok?"
Faruk yace "Yes sir, but Captain K Buba needs first aid, he is seri
ously bleeding"
"Is he alive?" Ya sake tambayarsa.
"Yes, but am not sure"
Nan da nan aka
ɗ
auki Captain zuwa inda aka kwantar da wanda suke buƙatar taimakon gaggawa, wan
ɗ
anda akaiwa rauni.
Nan Army doctors, likitocin sojoji suka rufu akan Captai
n dan ceto rayuwarsa, aka fara ƙoƙarin cire bullet
ɗ
in dake cikinsa.
Sun yi nasarar cire na bayansa, amma na cikinsa ba su samu cire shi ba, sukace sai an koma can Barack za'a iya cire shi a Asibiti. Nan su kai ƙoƙarin tsaida jinin da ke zuba a jikinsa.
Lieutenant Faruk ma an cire masa bullet
ɗ
in da ke damtsensa, an saka bandage an nanna
ɗ
e masa hannun.
"Hey, what this little baby is doing here?" Chief Commander ya fa
ɗ
a yana nuna yarinyar da Captain ya tsinta.
Faruk yace "Captain ne ya tsinto ta"
.
"Is she among the victims?"
Faruk yace "No, I don't think so, maybe she was kidnapped too, I don't actually knows where she belongs to"
Ita dai bakunan su kawai take bi da kallo, Tare da son fuskantar me suke fa
ɗ
a.
Mota daban aka ware, aka ta
ra gawarwakin sojojin da suka rasa rayukansu akan ceto wannan
ɗ
alibai da akai garkuwa da su (may the gentle soul of the fallen heroes, rest in perfect peace).
Aka samu wata motar aka saka wan
ɗ
anda suka ji rauni, tana ganin an
ɗ
auki Captain ita ma ta miƙ
e ta bisu, dan kar su
ɓ
ace mata, aka saka shi a mota ita ma ta fara ƙoƙarin shiga Motar.
"Hey, Carry this girl with you" Commander yai maganar yana nuna wani soja.
Ganin ya danƙi hannunta zai shiga da ita wata motar ya sa ta fashewa da kuka.
"Shut
up!" Yai mata tsawa, duk da ba ta iya jin sautin abunda ya fa
ɗ
a sosai amma ba ƙaramin razana ta yai ba, gaba
ɗ
aya tsoron su ya shige ta, har ta fara tunanin ko irin mutanen da suka sato ta ne.
Lieutenant Faruk ne ya ƙaraso, ya kamo hannunta suka shiga
wata Motar, sai leƙa window take, tana nunawa Faruk motar da aka saka Captain a ciki, bai kula ta ba ya jingina da jikin kujera tare da lumshe ido.
A daidaita sahu ce ta tsaya a ƙofar wani Babban Asibiti, mutane sai shiga suke suna fita, tare da
salallami, fuskokinsu duk babu da
ɗ
i.
A gigice wata mata ta sakko daga cikin adaidaita sahun, hannunta
ɗ
auke da wani yaro da bai fi shekaru hu
ɗ
u ba, jikinsa sai rawar sanyi yake, haƙoransa na datsewa.
Bayan ta sallami mai a daidaita sahun, cikin gudu_gud
u sauri_sauri ta shiga cikin Asibitin, ta nufi
ɓ
angaren Accident and emmrgency, wato sashen bada taimakon gaggawa.
Teburin Nurses ta nufa hannunta riƙe da yaron tace "Bayin Allah dan Allah ku taimaka min, yaro na kawo".
Ɗ
aya ta
ɗ
ago ta kalleta tace "Ba
mu da gado"
Cikin tashin hankali tace "Dan girman Allah ku duba min yaron nan, kar shima in rasa shi, duk 'yan uwansa babu sai shi ka
ɗ
ai ku temaka dan Allah"
A fusace wata Nurse tace "kinji mace, muka ce miki ba mu da gado, ko ransa a hannunmu yake?
In Allah ya ga dama kar
ɓ
ar shi zai yi, ko kina so ko ba kya so, wa
ɗ
anda kike gani a kwance ma sallamar su za muyi, likitoci yajin aiki zasu tafi, in kina da ku
ɗ
i kuma zaki iya kai shi Asibitin ku
ɗ
i a duba shi"
Cikin kuka tace "Wanne zan kai shi wanda z
an samu likita a dubamin shi"
Nurse
ɗ
in tai murmushi ta ce "yanzun nan aka kira likitan da yake duba marasa lafiya a nan, duk ranar Talata yske zuwa, kuma awa uku kawai yake ya tafi, doctor G.Y ya tafi Asibitinsa, ki je ki same shi a can sai ya fi duba
miki yaron yadda yakamata, a bashi duk abunda yake buƙata".
"Au dama ba'a shiga yajin aikin ba?" Ta tambaya tana rarraba ido.
Nurse
ɗ
in ta ce "eh ba'a shiga ba tukuna, amma ai na gaya miki bamu da gado ko? Kuma ana shirye-shiryen tsunduma yajin aikin
likitoci"
"To shikenan, ina ne Asibitin nasa?"
Suka kwatanta mata Asibitin, haka ta kuma fitowa da yaron, cikin tashin hankali ta tafi in da aka kwatanta mata.
G.Y BULAMA HOSPITAL AND MERTERNITY, shine a rubuce a katafaren ginin, Manyan m
otoci na ta shiga suna fita a cikin harabar Asibitin.
Tana rungume da yaron ta shiga cikin Asibitin, kai tsaye ta nufi in da wasu Nurses ke zaune tace "Sannunku, dan Allah mara lafiya muka kawo" tai maganar tana nuna musu yaron da ke hannunta.
"Kuna
da file a nan ne?" Wata Nurse ta tambaya.
"A'a, Wallahi mun je Asibiti uku duk sai ace mana ba gado, a na ƙarshen ne aka ce mana wai yajin aiki likitoci za suyi, shine aka kwatanta mana nan"
"To ai Hajiya sai kun bu
ɗ
e file sannan likita zai ganku"
Ta ce "To nawa ne bu
ɗ
e file
ɗ
in?"
"Naira dubu biyar ne, single file"
Turus tai, dan ku
ɗ
in hannunta dama dubu bakwai ne, sun ƙarar da biyu a yawon Asibitoci.
Dubu biyar
ɗ
in kenan ta rage a hannunta, a sanyaye ta ce "To a bu
ɗ
e mana"
Haka ta biya
ku
ɗ
in nan, aka bu
ɗ
e musu file, bayan an bu
ɗ
e aka ce su biya dubu uku ku
ɗ
in ganin likita.
Ta kalli Nurse
ɗ
in ta ce "Wallahi suke nan a jikina, ki taimaka min baiwar Allah, kar in rasa
ɗ
ana, dan Allah ku duba shi"
"Baiwar Allah, ba fa Asibiti na bane,
kuma ba Asibitin gwamnati bane, haka ƙa'idar Asibitin take.
Ta koma gefe kawai ta fashe da kuka.
Wani dogon mutum ne fari sol, ya fito daga wani
ɗ
aki jikinsa sanye da farar rigar likitoci, Nurses na biye da shi sun riƙo masa files, ganin mace ta saka
ɗ
a a gaba tana kuka ya sa ya tsaya ya kalleta ya kalli yaron ya ce "Lafiya baiwar Allah, baki san akwai marasa lafiya a kwance ba kika ware murya kina wannan kukan?"
Cikin kukan ta ce "dan Allah likita kai min rai, ka dubamin yaron nan, dubu biyar
ɗ
in
kenan na biya ku
ɗ
in bu
ɗ
e file, kuma yanzu ance sai na biya na ganinka dan Allah ka dubamin shi".
Ɗ
an shiru yai yana kallon ta, daga bisani ya durƙusa ya tatta
ɓ
a yaron, ya bu
ɗ
e idon yaron, sannan ya miƙe tsaye yace "ku biya naira dubu hamsin, kwantar da
yaron za'ai ya galabaita sosai"
Daga haka bai kuma cewa komai ba, ya fara tafiya.
Take hawayen idonta suka bushe jin an ambato dubu hamsin, dan basu da ita ba su da dalilinta, dan Mai_ gidanta
ɗ
an aca
ɓ
a ne.
Jiki na rawa ta
ɗ
akko 'yar ƙaramar wayar
ta mai madannai, ta nemi lambar mijin nata, cikin kuka tai masa bayanin halin da ake ciki.
Yace "ki kwantar da hankalinki, kice su yi masa duk abun da ya dace, zan bada jinginar babur
ɗ
ina, in kawo ku
ɗ
in.
Allah sarki