Showing 222001 words to 225000 words out of 260401 words
faru ba kawai ka zo ka sani a gaba da fa
ɗ
a, kar ka kuma yi mini tsawa, bani yarinyata, kuma Wallahi matarka ta kuma
ɗ
aukar mini ita saina wanka mata mari" ta ƙarasa maganar tare da fizge little daga hannunsa.
Shiru Mami ta yi, ta tuna
watarana da ta ta
ɓ
ha
ɗ
a baki da ƙawarta suka yiwa Abra sharri, har Major ya mareta, ashe haka Abra take ji idan ta yi mata ƙazafi. Wasu hawaye masu fitowa da
ɗ
acin zuciya suka faa sakowa saman kuncinta.
Abbi ya yi ajiyar zuciya ya ce "Ki zo muje falo,
ki ga wani abu".
"Ba abin da zan gani, kaje ka ƙyaleni kawai"
Major ya ce "Abin yana da mahimmanci, ki zo muje".
"Kaje ka nunawa matarka bani ba, ita ya dace taga abu mai mahimmanci daga gareka bani ba".
"Ko da kuwa abin da ya shafi Salman ne k
o Abra?"yai Maganar yana kallonta. Sai kuma jikinta ya yi sanyi, Abbi ya sanya hannu ya janyo hannun Mami zuwa falo.
Afra kuwa tun da ta shigo, tangamemen hoton Abra ne da Salman ya yi mata maraba, babu yadda za'ai ka kalli hoton kace ba ita bace a jiki
.
Jikinta ne ya hau rawa tana nuna wa Salman hoton. Salman ya taka ya ciro hoton ya miƙawa Afra ya ce "This is your sister, we are really missing her" yayi maganar ba tare da ya iya tsayar da hawayen da suka taho masa ba.
Salima kuwa bin su ta dinga yi
da ido, tana son tayi magana, amma ta kasa magana, saboda yadda Salman ke mata kwarjini, sam yaron baya sakar mata fuska a matsayinta na matar mahaifinsa.
"Yanzu ta mutu? Yayata ce ko ƙanwata ce, ko mu biyu ne? Babu wanda ya sani sai Allah, me yasa ban
ha
ɗ
u da ke kan ki mutu ba? 'yar uwata me yasa kika tafi ban ganki ba, a rayuwata ace ko sau
ɗ
aya naga jinina, yanzu idan ba a gano iyayenmu ba fa, shikenan kin mutu kin barni ni ka
ɗ
ai haba 'yar uwata" tamkar mahaukaciya, haka Afra take gunjin kuka, Salma
n ya kar
ɓ
e hoton yana share mata hawaye, ganinta yake ba ta da banbanci da Afransa.
Mami ce ta fito tana hura hanci, hannunta
ɗ
aya riƙe da Little,
ɗ
aya kuma yana cikin na Abbi. Wata irin mummunar fa
ɗ
uwar gaba ce ta ziyarci Mami, jikinta ya hau rawa baki
nta ma haka.
Nema take ta saki Little, Abbi yai sarin kar
ɓ
eta daga hannunta.
"Major me nake gani? Abra ce fa? Abra ce ko baka ganinta ne?".
"Calm down please, ba Abra bace ba kalleta da kyau".
Cikin tsawa ta ce "Ta yaya zaka cemini ba Abra bace, kallet
a fa a kusa da Faris, Abra ba ta mutu ba kenan, ko kuma fatalwa ce" Salman ya taso da sauri ya kar
ɓ
i Little, Mami kuwa gaba
ɗ
aya ta birkice, Abbi ya zaunar da ita, amma ta kasa nutsuwa, sai nuna masa Afra take tana cewa Abra take gani.
Abbi ya yiwa Afra n
uni da ta zo, Afra ta taso ta ƙaraso gaban Mami, aikuwa ta rirriƙeta ta ce "Abrana, Wallahi Major Abra ce kalleta fa".
Abbi ya kalli Afra ya ce "Afra, ga maman 'yar uwakki, ita ce ta riƙe Abra, wannan jaririyar kuma, ita ce wadda ta rasu ta bari, ki gay
a mata ke ba Abra ba ce".
Afra ta riƙo hannun Mami cikin nata, tana hawaye ta ce "Mamanmu, ba 'yar ki ba ce wadda ki ka rasa, amma zan iya cewa 'yar ki ce ta dawo gareki, kamar 'yar uwata nima tsinta ta aka yi, aka riƙeni a wani ƙauye har na girma, mijin
'yar uwata ne yaje ƙauyenmu ya ganni, shima da fari cewa ya yi, ni matarsa ce amma daga baya ya gano, ba ita bace, ni sunana Afra ana ce mini 'yar Baba a garinmu, ni a ƙauye na tashi, Abranki kuma a birni, mijin Abra ya ce ta fini hankali da nutsuwa, da ra
shin hayaniya, ni kuma... Sai kuma tai shiru tana murmushi, a lokacin da hawaye ke zuba daga idonta.
"Major yanzu kana nufin ba Abra na ba ce?".
"Ba Abranki ba ce, 'yar uwatta ce" Nan Abbi ya yiwa Mami bayanin komai.
Mami ta rungume Afra a jikinta
tana wani irin kuka, tamkar zata shi
ɗ
e, Afra ma ta rungumeta tana kuka.
Salima ta ce "Sweetheart, nifa ban gane meke faruwa ba, wannan ba ita ce 'yarka ta hoton nan da aka ce ta mutu ba?"
Abbi ya ce "Ba ita bace, zan miki bayani".
Adnan kam
ko da ya isa garin Kaduna, a Asibiti ya samu masauki, saboda yadda zazza
ɓ
i da ciwon kai suka rufe shi, sai da aka sa masa ruwa sannan ya wuce gida.
Ko da Adnan ya jewa Hajiya Mama da Abba abin da ya faru Abba ya ce "Lallai wannan lamari akwai ban mamaki
a cikin sa, dan haka zuwa jibi insha Allah, zan shirya in je Kano da kai na".
Adnan ya ce "Dan Allah Abba idan ka je kace su bani Auren Afra, zan iya rasa raina idan ba sameta ba".
"In ka rasa ranka Allah ya jiƙanka, ai Nagode Allah da ya sanya yari
nyar ta ce bata sonka, ni dai Adnan ba zan kuma yin jagoranci a nema maka Aure ba, da mahaifiyarka ma ta mutu dangana na yi, kaima in ka mutu Allah ya jiƙanka".
"Abba dan Allah, kai mini rai, na tuba nabi Allah na bika, ba zan sake maimaita kuskuren da
nayi a baya ba"
"Sai kuma kayi Adnan, idan har ina raye babu mai aura maka 'yar uwar Abra, kaje can ka nemi wata 'yar ka aura, amma ba 'yar uwar Abra ba".
Mama ta ce "Dan Allah Yalla
ɓ
ai ka sassautawa yaron nan, kalli yadda ya koma" Abba ya
ɗ
aga mata
hannu ya ce "Wannan yaron ba abin tausayi bane, kuma na gama Magana, kuma idan har ka takura sai sun baka yarinyar nan, zan tona maka Asirin irin riƙon da ka yiwa 'yar su" haka Adnan ya dinga kuka wiwi, kamar wanda uwarsa ta mutu.
"Ok Zuwa next
week nake son Visa don Allah, abu ne na gaggawa ya taso mini, da yake buƙatar in je da kaina"
Hajiya Saudat ta zubawa doctor ido, tana saurarensa, sai da ya gama wayar sannan ta kalleshi ta ce "Wai ni don Allah doctor, sai yaushe zaka bawa iyayen yaron na
n damar zuwa su ganka ne?"
"Sai na dawo daga tafiya"
"Ni ban ma tambayeka ba, ina zaka je naji kana maganar visa?".
Doctor ya gyara zamansa ya ce "Dubai zanje" hantar cikinta ce ta ka
ɗ
a, ta dube shi a firgice ta ce "Kaje Dubai kayi me?"
"Wurin wanda na
ajiye zani, ai kin fi kowa sanin ina da ajiya a can".
"Me kake nufi? Me kake nema a can da babu a nan?".
Bulama ya ce "Abu mafi mahimmanci da kika sa na wofantar, dole in gano alaƙata da yarinyar da nake bincike a kai, dan haka dole in tafi Dubai"
Gaba
daya ta rikice ta ce "Amma ka san zuwanka Dubai na nufin tonuwar Asirinka wataƙila ma da karayar arzikinka?"
"Ban damu ba, ida har abin da na rasa ne zai dawo gareni"
Wayar Hajiya Saudat ce ta fara ringing, jiki na rawa ganin lambar Meenal ce ta
ɗ
aga.
"Muna magana da mahaifiyar Meenal ne?".
"Eh nice"
"Ku zo nan Asibitin Health well, yarinyarki babu lafiya, ana buƙatar sa hannunku ku zo ku biya ku
ɗ
ayi mata aikin gaggawa"
₦
300 kacal, a biya kan a karanta dan Allah 08081012143
[11/17, 2:50 PM
] Abk: A ki
ɗ
ime Hajiya Saudat ta ce. "Wacce Meenal
ɗ
in? Ban gane ba bawan Allah, me ya samu ƴata?"
"Idan kika zo za ki fahimta, amma fa ana buƙatar ku yi gaggawar zuwan, saboda gudun kar a rasa rayuwar ta."
Su
ɓ
ucewa wayar ta yi daga hannunta ta fa
ɗ
i
ƙ
asa, cikin gigita ta ce. "Doctor wai Daughter ce babu lafiya, tana health well ana buƙatar mu je mu saka hannu za a yi mata aiki." Babu yabo ba fallasa ya ce. "Allah ya ba ta lafiya."
"Haba Doctor, ya na ga kamar ba ka damu ba, ƴarmu fa Meenal nake mag
ana a kai."
"Damuwar da nake ciki ta fi ƙarfin wannan, ki
ɗ
auki ATM
ɗ
ina ki je a yi duk abin da ya dace."
Bai jira amsar ta ba ya fice daga
ɗ
akin, zuciyarsa cike da tunanin wanne abu ne yake damun Meenal da har ya kai sai an yi mata aiki ba tare da s
un sani ba? Da kallo Hajiya Saudat ta bi shi cikin bugawar zuciya, mamaki da fargaba sun cika mata fal a cikin ranta, yau Bulama ne take masa maganar Meenal tana cikin mawuyacin hali na ciwo amma ya ka
ɗ
a ƙafarsa ya yi gaba? Shi da ko ciwon kai take kusan t
are suke jinyar saboda yadda yake nuna damuwarsa tare da ba ta kulawa. Lallai dole ta miƙe ta nemi mafita gami da kawar da abin da ya
ɗ
auke masa hankali daga gare su.
Cikin matuƙar tashin hankali ta zari gyalenta da handbag da wayarta dake yashe a ƙasa
ta yi waje zuwa asibitin da aka ce mata Meenal tana can.
Ɗ
akin Abra Abbi ya sa Salima ta gyara wa Afrah, bayan ta gama ta dawo parlour inda duk suke ta ce. "Our new daughter na kammala miki gyaran dakin, sai ki shiga ki kwanta ki huta." Murmushi A
fra dake riƙe da Little ta yi, ba tare da ta
ɗ
ago kanta ba ta ce. "Na gode sosai Aunty." Cikin son cusa kai Salima ta ce. "Haba mene abun godiya don Uwa ta yi wa ƴarta abu?" Murmushi kawai Afra ta yi ba ta ce komai ba, sai shafa fuskar little take cikin ƙa
unar ta da ta mamaye zuciyarta lokaci
ɗ
aya, farinciki mara iyaka take ji a cikin ranta, yau ta ga jininta a duniya, Allah Sarki Baba, dama yana nan ya ga wannan ranar mai cike da tarin farinciki a gare su. Mami kuwa ta
ɓ
e baki ta yi jin abin da Salima ta fa
ɗ
a, Abbi kuwa murmurshi ya yi cikin jin da
ɗ
i ya ce. "Daughter, tashi ki je Antinki ta nuna miki
ɗ
akinki." Cikin girmamawa ta ce. "Toh." Salman dake ta kallon ta ya miƙe tare da
ɗ
auke little daga cinyarta, cikin murmurshi ya ce mu je na raka ki yayata." Da
sauri ta kalle shi cikin mamakin jin ƙato da shi ya ce mata Yaya, shi ma kallon ta yake, hakan ya sa idanuwansu suka sarƙe cikin na juna, da sauri ta janye nata saboda wani irin abu da ta ji ya daki zuciyarta, bayan ya kai ta
ɗ
akin yana ƙoƙarin fita ta ce.
"Ka bar mini ita a nan." Fahimtar da ya yi little take nufi ya sa ya ce. "Kina buƙatar ki yi wanka a yanzu, ita kuma rigima ne da ita, kina ajiye ta za ta iya farkawa tay ta kuka, idan kin yin wankan sai Mami ta kawo miki ita." Gya
ɗ
a masa kai ta yi ba tar
e da ta bari sun ha
ɗ
a ido ba har ya fice, haka kawai ta ji suna mata kwarjini shi da Abbi, shi ya sa ta nutsu kamar ba ita ce Ƴar Baba gagarau ba. Bin
ɗ
akin ta shiga yi da kallo, ƙawatuwar shi da yadda ya tsaru ba ƙaramin burge ta ya yi ba, sai tambayar ka
nta take yi wai wannan ha
ɗ
a
ɗɗ
en
ɗ
akin duk nata ne? Yau ita ce za ta kwana a birni gidan ƴan gayu mai kyau irin wannan, ba don halin kewar su Inna da take ba da sai ta raba dare tana tsallen murna a kan wannan luntsumemen gadon.
"Allah Sarki Innata, na s
an yanzu suna can suna kuka da alhinin tafiyata ita da Yaya Musana." Ta fa
ɗ
i haka a fili ƙwalla na cika mata ido. A hankali ta zauna a bakin gado tana ƙara bin
ɗ
akin da kallo, Adnan ne ya fa
ɗ
o mata a rai, turo baki ta yi kamar yana gabanta, lokacin da ta t
uno yadda yake yi mata magiya akan ta so shi.
Salima ce ta shigo
ɗ
akin bakinta
ɗ
auke da sallama, bayan ta amsa mata ta ajiye wata leda mai
ɗ
auke da kayan bacci a kusa da Afra tare da fa
ɗ
in. "Ga kayan bacci nan idan kika yi wankan sai ki saka." A hankali
Afra ta ce. "Toh na gode, amma na taho da kayana ma suna cikin Mota ba a shigo da su ba ne."
"Okay, bara zan yiwa Honey magana sai a shigo miki da su yanzu, ki saki jikinki kin ji, nan ma gidanku ne, bari na kawo miki abinci.'
Gya
ɗ
a mata kai ta yi t
a ce. "Ina zan
ɗ
ebo ruwan da zan yi wanka da alwala?" Murmushi Salima ta yi ta ce. "Duk akwai a cikin toilet, mu je na raka ki, ki gani." Miƙewa ta yi ba tare da ta ce komai ba, duk wannan kanbanbar da Salima take ba ta wani yi mata ba, sai ta ji ta fi son
farar matar nan mai kama da Salman. A toilet
ɗ
in ma lalacewa ta yi wajen kallon yadda aka ƙawata shi, kasa
ɗ
aurewa ta yi ta ce. "Yanzu nan ne bayin gida kamar wani
ɗ
aki? Ta
ɓ
, ai da ni ka
ɗ
ai na shigo fita zan yi na ce ban ga bayan gidan ba, na saba da namu
na ƙauye ko rufi babu balle siminti." Murmushi Salima ta yi ta nunnuna mata duk abin da ta san zai mata wahalar ganewa da yadda za ta yi amfani da shi. Bayan ta fita ta ce. "Wai aljannar duniya, har da wani fanfon ruwan zafi? To shi daga ina yake zuwa kum
a? Ko ta cikin ƙasa ake dafa shi?"
"Khamal wai me kake nufi da ni a gidan nan ne? Ina cikin damuwar rashin Abra amma mai kama da ita ta zo sai kaita tura waccan matar tana yi mata abubuwa? Alhalin gani a zaune."
"Na sani ko ita ma za ki ce ƴata c
e karuwa ta haifa mini? Ki azabtar da ita kamar yadda kika yi wa Abra."
Cikin hawaye Mami ta ce. "Me ya sa kake son dawo da abin da ya wuce ne? Ai babu wanda ba ya yin kuskure a rayuwarsa." Wani kallo ya watsa mata ya fice ba tare da ya kuma magana ba.
A zuciye Mami ta ce. "Kuma yarinya a gurina za ta zauna ba a gurin wata baƙar yarinya ba, sai dai a yi duk abin da za a yi. Ban da neman fitina yarinyar kusan sa'ar ta amma ita za ta riƙe ta, ita ma shegiyar da neman gindin zama har da wani ce mata ƴarta,
ko a gidan uwar wa ta haifi kamar ta oho?" Ta ƙarashe maganar tare da jan tsaki.
"Doctor me yake damun ƴata da har ya kai a yi mata surgery without knowing us?" Hajiya Saudat ta tambaya a gigice.
"Mu ƙarasa office mana sai mu yi maganar."
"B
a ni da nutsuwar ƙara taku ko nan da can? Please tell me what happened to my daughter?" Ta yi maganar cikin kuka.
Cikin tausawa likitan ya ce. "Ki dai daure mu ƙarasa office
ɗ
in, kin ga nan reception ne, bai dace mu yi magana ba."
Ba ta kuma magana
ba ta bi shi suka tafi. Bayan sun shiga sun zauna ya ce mata. "An yi mata abortion ne, sai kuma aka samu matsala ta samu raptured utherus, mahaifarta ta ragargaje gaba
ɗ
aya, yanzu za a yi mata aikin gaggawa a cire t....."
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraj
j'un, na shiga uku! Meenal
ɗ
in za a cirewa mahaifa? Mahaifa fa ka ce Doctor?"
"Eh, ta sha maganin abortion ne wanda ya wuce ƙa'ida, hakan ne ya janyo mata wannan matsalar, ba don da wata Nurse da take aiki a nan asibitin suka zo ba ma da ba za mu kar
ɓ
e
ta ba."
Gumi ne ya shiga yankowa Hajiya Saudat ta ko'ina a jikinta, cikin rawar murya ta ce. "Doctor, kuma babu wani abu da za a iya yi dole sai dai a cire mahaifar?"
"Babu." Ya fa
ɗ
a a taƙaice.
A dole ba bisa son rai ba Hajiya Saudat ta saka han
nu aka yi wa Meenal aiki, wadda ke cikin mawuyacin halin ciwo.
Ba ƙaramin tashi hankalin Hajiya Saudat ya yi ba da ta ga Meenal, Saboda yadda ta
ɗ
ashe ta yi fari fat alamun babu jini a jikinta, ga wata rama da ta yi kamar wadda ta da
ɗ
e tana jinya, ts
abar galabaita ko magana ba ta iya yi, sai hawaye kawai take.
Washegari bayan Salima ta gama ha
ɗ
a breakfast ta shiga
ɗ
akin Afra don ta taso ta. Tarar da ita ta yi har lokacin tana kwance tana bacci, saboda jiya ba ta yi bacci da wuri ba, kewar Inna
da baƙunta sun hana ta. A hankali ta tashe ta, bayan ta shiga toilet ta fice ta
ɗ
auko mata sabuwar abaya da undies a cikin kayan lefenta, ta ha
ɗ
o da su lotion da powder ta kawo mata. Cikin mintuna ƙalilan Afra ta shirya, kasancewar ta mai kazar-kazar ba ka
mar Abra ba. Sosai ta yi kyau cikin bak'ar abayar da ta haska