Showing 210001 words to 213000 words out of 260401 words

Chapter 71 - Dare da Duhu complete

"Kai, wannan ai nice".

"Matsa can, matata ta fiki kyau, ke ba 'yar gayu ba ce ai".

"

Dan Allah da gaske 'yar uwata ce? Tana ina? Dan girman Allah a ina take?".

Adnan ya kar

ɓ

e wayarsa ya ce "Sai munje kin nuna mini gidanku tukuna"

Da sauri ta tashi, ta

ɗ

au farantin gya

ɗ

ar ta, ta ce "Tashi muje to ka gani"

Adnan ya miƙe ya bita, sun

a tafe tana share hawaye.

"To kuma kukan me ki ke yi?" Kasa magana ta yi, sai sake fashewa da kuka, alamar akwai wani abu da yake damunta a zuciyarta.

"Bana son kuka, idan ba ki daina kukan nan ba, ba zan kai ki wurinta ba" ta saka hannu ta goge hawa

yen fuskarta ta ce "Na daina, dan Allah ka yi haƙuri"

"Kin san wani Sadi a garin nan?"

Zaro idanuwa ta yi ta ce "Kai wannan

ɗ

an daban, me zai ha

ɗ

ani da shi?, na san shi".

"Ya akai kika san shine, sannan A ina yake?".

"Shika

ɗ

ai ne Sadi, ana ce m

asa

ɗ

an kunama, Gidansa a garin nan, yana da mata da 'ya'ya, amma fa sai ya shekara biyar baya garin nan, bama a sanin ya zo balle a san ya tafi, 'yan sanda sun sha zuwa su kama shi, amma ba a samunsa".

A hankali Adnan ya furta "Sadi

ɗ

an kunama"

Ta k

alli bakinsa ta ce "Me kace?"

"Ba komai, watarana zaki nuna mini gidansa".

"Na shiga uku ni kaza, Wallahi ba zani ba, gaba

ɗ

aya layin gidan nan mafarauta ne, karnuka ne sun fi Ashirin a layin nan, wallahi ba zani ba"

"Ashe ba ki shirya ganin 'yar

uwar ta ki ba".

"A'a dan Allah kar ka yi mini haka, Wallahi ina son ganinta, kuma har babanmu da Babarmu duk zaka nuna mini? Dan Allah ba yaudarata ka ke ba 'yar uwata ce? Ya aka yi ka san 'yar uwata ce? An sha yi mini gori a garin nan wai ba'a san iyay

ena ba, Baba ne ya tsinto ni, shi yake mini komai, rashin lafiya ta kama shi, aka tura shi wani Asibiti a Kaduna, wasu azzalumai suka bar shi ya mutu" tuni hawaye ya gama wanke mata fuska.

Wani irin tausayin yarinyar ya kama shi, ya tuna lokacin da Abra

ke masa magiya a kan ya ha

ɗ

ata da mahaifinta, Allah sarki a wannan karon ba zai iya sanar da Afra wane irin uba ne da su ba. Abin da yake birge shi da ita shi ne, ba ta da rufi, yanzun nan zaka ji abubuwa da dama a bakinta, a yanzu haka ya samu abokiyar g

abatar da aikin da ya zo yi garin.

"Matata ki daina kuka, bana son sake ganin hawayenki dan Allah, ina son in goge laifin da na aikata miki a baya".

"Matarka? Wane laifi ka yi mata? Ba 'yar uwar tawa ka ke aure ba amma ka ke kirana da matarka?"

Sa

i da ta yi Magana sannan Adnan ya dawo hayyacinsa ya ce "Ai Yanzu tun da muna tare a nan kece matar tawa".

"Allah ya kiyaye, ji mayaudari".

Adnan ya ha

ɗ

e rai ya ce "Ni kike cewa mayaudari?"

"A'a yi haƙuri dan Allah, ga gidan namu munzo, bari in sh

iga in gaya wa Inna ita ma ka nuna mata hoton, sai ma ka gaya mata ka san iyayena".

Adnan ya yi murmushi ya ce "To shikenan, maza shiga ki gaya mata".

Da hanzari kamar zata kifa, ta dafe farantin gya

ɗ

arta, ta shiga cikin gidan tun daga soro tana kira

n Inna.

Adnan ya ƙarewa gidan da Afra take ido, gidan ƙasa ne, ginin ƙauye ya jinjina kai ya ce "Afra, Allah ne ya so ni da rahama domin in gyara laifukana, ya ha

ɗ

ani da 'yar uwar Abra".

"Inna! Inna fito fito" A gigice Inna ta fito daga ban

ɗ

aki, ta y

i jifa da butar hannunta, tana nema ta dungura, saboda yadda ta ji 'yar Baba na kwa

ɗ

a mata kira.

"Ke lafiya?".

Ta ƙaraso ta riƙe hannun Inna ta ce "Inna Allah ya kar

ɓ

i Addu'a ta".

"Wace Addu'ar?".

"Inna na ha

ɗ

u da wanda ya san iyayena, har ya n

una mini hotunan 'yar uwata, Wallahi Inna komai namu iri

ɗ

aya".

A fusace Inna ta ce "Matsa ki bani wuri mahaukaciya, kawai kin zo kina

ɗ

aga mini hankali".

"Wallahi Inna da gaske nake, ki zo muje yana ƙofar gida ki ganshi".

Ta dinga jan hannun Inna

zuwa ƙofar gida, sai dai suna zuwa Adnan ya tafi.

Ai kuwa Inna ta mangarewa 'yar Baba ƙeya.

"Dan ubanki kawai kin

ɗ

aga mini hankali, kin zo kina mini hauka, ni anya ma ba da gaske aljanu ne suka shafeki ba, yarinya sam ba kya Hankali, tsugunno zan y

i amma ki ka saka na fito a guje, na

ɗ

auka wani abu ne ya sameki, ja'ira mara hankali".

Jiki a sanyaye Afra ta ƙarasa shiga cikin gida, ita ma ta fara tunanin anya ba da gaske aljanu ne suke mata wasa da hankali ba?.

Yaya Musa ne ya shigo gidan, yana

fa

ɗ

in "Inna ke da wa ki ke ta wannan fa

ɗ

an?".

"Ni da wannan yarinyar mana, ta shigo tana ƙwala mini kira, wai wani in zo wai ga wani mutum ya san 'yar uwatta. Ranar lahadi mai zuwa, dan ubanta gidan na rimi zan kai ta ya yi mata ruƙiyya".

'yar Baba

ta zare ido ta ce "Kai, dukan mutane fa yake yi, ni wallahi bani da aljanu".

"Aikuwa sai na kai ki, idan ma iskanci ne abin naki, ya zane mini ke".

Mami ce zaune tana waya da Hajiya Mama, suna hirar yadda Little ta yi wayo, Mama ta ce "Ai

insha Allah cikin satin nan muke sa ran zuwa, mu zo mu ganta".

"Allah sarki, ubangiji Allah ya kawo ku, Allah yasa kar ta yi muku ƙyuwa, dan ta fara gane mutane yanzu".

"Ai ni idan ta mini ƙyuya, ba ta yiwa maigidan na ta ba" suka yi dariya gaba

ɗ

ay

a.

Mama ta ce "Ya Major, da

ɗ

ana Salman?"

"Salman kwana biyu bai leƙo mu ba, yana can makaranta, Major kuma ya yi Aure".

"Subhanallah Aure kuma Hajiya Na'ima?".

"Aure fa, yau kwana takwas".

Hajiya Mama ta ce "Eyya, wannan abu bai yi da

ɗ

i ba,

amma dan Allah ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki, komai nufi ne na Allah. Allah ya baku zaman lafiya kiyi haƙuri" wata irin karaya ta kama Hajiya Na'ima, dan a kwanaki takwas

ɗ

in ita ka

ɗ

ai ta san da yadda ta yi su, gashi yau Major zai dawo wurinta, am

ma sam ko

ɗ

okin hakan ba ta yi, saboda gaba

ɗ

aya haushinsa ta ke ji.

"Ya na ji kin yi shiru?" Cikin raunin murya Mami ta ce "Ba komai".

"Na'ima, na san na fiki shekaru, kuma nima mace ce, ƙarewa am a Marriage counsellor, na san abin da ki ke ji, irin

wannan babu da

ɗ

i, kinga sanadin 'ya'ya Allah ya riga ya ha

ɗ

a mu, mun zama 'yan uwa, dan Allah idan zan baki shawara, kar ki yadda wani ko wata su ziga ki, a 'yar ha

ɗ

uwar da muke yi, mijinki yana nuna miki soyayya, kiyi amfani da damarki kar ki ce zaki bar

mata shi ki zuba musu ido, kiyi ƙoƙari ki riƙe fadarki a wurinsa, na san da ciwo amma ki yi haƙuri".

Mami ta yi ajiyar zuciya ta ce "To shikenan, na gode sosai".

"Yauwa, sauran maganar idan na zo ma tattauna".

"To shikenan Allah ya kawo ku lafiya

, gaida Abban".

Hajiya Mama ta ce "Zaiji insha Allah".

Mami ta mayar da kallonta kan Little, da ta ƙura mata ido, Mami ta yi murmushi, ta janyo little tana shafa mata hoda a goshinta, daga ita sai Pampers.

Mami ta ce "Sweetheart, bari in miki vide

o in turawa Daddynki Salman, na san yanzu suna lectures da mun yi video call ko?" Ta yi maganar kamar Little tana jin me take fa

ɗ

a.

Ta

ɗ

auko Comb ta shiga tajewa Little uwar sumar da ta cika mata kai.

Ta ƙurawa Little ido, yarinyar tubarkallah, Allah

ya yi mata kyau, ko sallama aka yi, Mami

ɓ

oyeta take yi, ko yawan da ita ba ta yi, saboda baki.

Ganin Mami ta ƙura mata idanu ne ya sanya, ta fara dariya har dimples

ɗ

inta suna lotsawa, sak kammaninta da Abra suka ƙara bayyana.

"Allah sarki Abrana,

Allah ya yi miki rahama, ya raya mini abin da ki ka bari, ke babu ke, Faris ba ya kusa da ni, ga abin da babanku yayi mini, da muna tare da na san zaki tayani jin babu da

ɗ

in halin da nake ciki. Ina ma ban raba alaƙar da ke tsakanin ki da Faris ba, dama na

bari kun yi Aure, kai na yi kuskuren da babu damar gyarawa" ta ƙarasa maganar tana hawaye. Sai da tayi mai isarta, sannan ta tashi, ta

ɗ

au ado cikin wani rantsatsen leshi, ta sha ado sai zuba ƙamshi take yi, ta shirya Little cikin wasu ha

ɗ

a

ɗɗ

un kaya sannan

ta

ɗ

auko wayarta ta kira Salman video call.

Murmushi ne ya bayyana a fuskar Salman, ganin kiran Mami, ya amsa kiran, murmushin fuskarsa ne ya ƙara fa

ɗ

a

ɗ

a da ya yi tozali da fuskar Mami tare da little.

"Wow my little Angel, always looking so cute dea

r" Dariya little ta bu

ɗ

e baki ta na yi, tana miƙa hannunta kan screen

ɗ

in wayar.

Kissing

ɗ

in screen

ɗ

in system

ɗ

insa Salman ya shiga yi, yana

ɗ

agawa Little hannu.

"To mai 'ya, ko ta ni baka yi, sai 'yar ka ko?".

"Am sorry Mami, gaskiya am missing

daughter Mami, ba kiga kamannin angel sun sake bayyana a jikin yarinyar nan ba, Mami ba zan zo in tafi da 'yata ba kuwa?"

"Say hi Daddy, My Angel look up, baki kamar na mamanta" yayi Maganar yana murmushi. Idonsa ne ya kai kan Mami, da idanunta suka cik

a da hawaye.

"Mamina, lafiya na ga idanunki kamar za ki yi kuka?".

"Salman na kiraka a waya, nace ina son ka zo da gaggawa amma ka yi burus ko Faris?".

"Mami ba burus na yi ba, muna daf da fara exams ne, kuma Abbi ne ya ce kar in zo".

"Ai tunda

ya san abin da yayi mini, dole ya fa

ɗ

i haka?".

"Mami me ya yi miki kuma?".

"Aure ya ƙaro, yau kwana takwas kenan, ya auro budurwa".

"Aure kuma Mami? Abbin?".

"Zan maka ƙarya ne Salman?"

Salman ya girgiza kai ya ce "Mami, na san Abbi ba zai

ta

ɓ

a yin abin da zai cutar da ke ba, dan Allah kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki, kwanakin nan damuwa ta miki yawa, dan Allah kar ki bari wani ciwon ya kama mini ke Mami, dan Allah ki cire komai daga ranki" Mami ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, Alla

h ya bada sa'ar exams".

"Ameen Mamina, kiyi haƙuri dan Allah, kar ki ji haushin Abbi"

Murmushi ta yi mai ciwo ta katse kiran.

Ta miƙe tsaye, ta

ɗ

auki Little ta sa

ɓ

ata a kafa

ɗ

arta, ta fito falo.

Tana fita falon ya gauraye da ƙamshi, hakan ya yi daid

ai da fitowar Abbi, tare da Salima.

Bin Mami da ido ta yi, ba ƙarya Mami akwai iya gayu.

Major ya yi mata wani lallausan murmushi ya ce "Wurinki zan taho ai, na zaci baku tashi ba".

"Ni na tashi tun

ɗ

azu" tai maganar tana nufar hanyar kitchen.

Salima ta ce "Honey dan Allah ko sau

ɗ

aya a bani Little in

ɗ

auka mana, tun da na zo gidan nan ban ta

ɓ

a

ɗ

aukarta ba".

Major ya ce "My dear, a taimaka a bamu aron Little mu

ɗ

auka mana".

"Duk abin da ya shafeka ban mata iyaka da shi ba, amma abin da ya

shafeni da iyalina ni ya shafa, dan haka babu ruwanta da iyalina".

"Na'ima meye haka ne? Wannan wace irin magana ce kike yi?"

"Sai kuma kayi ai" ta wuce kitchen abinta.

Ƙ

arfe goma da rabi na safe, Adnan ya tafi hanyar wucewarta ya zaun

a, ya shafe a ƙalla awa

ɗ

aya da rabi, sannan ya hangota, tana tahowa, yau buhu ne ta maƙalo hammatarta, tana tafe tana murmushe gya

ɗ

a tana ci.

Tana tunkaro wurin taji ƙirjinta ya tsananta bugawa, ga kuma ƙamshin turaren sa da ya cika mata hanci, ji tayi

kamar ta juya ta gudu gida, karta kuma ha

ɗ

uwa da mutumin nan da ba ta da tabbacin mutum ne ko aljani.

"Budurwar ƙauye, ƙaraso mana kina tafe kina ciye ciye, ko kunya ba kya ji?"

Tsayawa ta yi cak tana kallonsa.

"Idan kika gudu ba zan kai ki wurin

'yar uwakki ba".

Ta yatsine baki ta ce "Ai na fuskanci raina mini hankali kake, yaudarata kawai ka ke, jiyan in shiga gida in fito da Inna ka gudu, ka sa ta dinga yi mini fa

ɗ

a, har da zata kaini wurin masu ruƙiya aljani ya shiga jikina".

Dariya Adna

n ya yi ya ce "kin manta yadda ki ka dinga wahalar da ni ne nima? Ai ramawa nake yi, yanzu ina zuwa?".

"Gona zani"

"Me zakiyi a gona kuma?"

"Roro zani".

"Kinga, yanzu muje ki fara rakani gidan Sadi".

Waro masa manyan idanunta ta yi "Ta

ɓ

kawa

i aje a gaya wa Inna an gani a layin gidan, duk fa 'yan farauta ne a wurin masu shaye-shaye".

"Na dai ga alamar ba kya son in nuna miki in da iyayenki suke".

"Wai kai sai ka yi ta amfani da wannan damar kana tursasani, yanzu aiken Innan zan fasa muje

naka?"

"Hukunci ya rage naki ai".

Ta

ɗ

an tura baki sannan ta ce "Naji zan raka ka, amma da shara

ɗ

i, nima zaka rakani gona ka tayani roro"

Shiru Adnan ya yi, sannan ya ce "Na amince"

"To muje, kuma daga baya zan tsaya in nuno maka gidan in dawo

, dan karnuka ba zasu cinye ni a banza ba"

Nan ta yiwa Adnan jagora, suka nufi hanyar gidan Sadi

ɗ

an kunama, wato baban yaron riƙaƙƙen

ɗ

an ta'addan da ya addabi ƙasa tsawon shekaru.

Cin gya

ɗ

arta ta cigaba da yi, Adnan ya fizge ledar gya

ɗ

ar ya jefar y

a ce "Ke kamar ba mace ba, ko kunyar ciye ciye ba kya ji?".

"Kaga nifa ba zaka takurawa rayuwata ba gaskiya, kai Wallahi da gani mutum ne mai son kai, wannan 'yar uwa tawa da gani tana haƙuri, ka fiye masifar tsiya Wallahi".

Jikin Adnan ya yi sanyi d

a jin abin da Afra ta fa

ɗ

a, sai ya kasa ce mata komai sai cigaba da bin ta da ya yi.

Sai da suka zo daidai wata ƙatuwar bishiyar tsamiya, ta ja ta tsaya ta kalleshi ta ce "Kaga hanyar can, da wancan karen me baƙin baki yake kwance? To duk wanda ka tamba

ya zai nuna maka gidansa".

"Muje ki nuna mini mana".

"Ai Wallahi ko me zaka yi, taku

ɗ

aya ba zan ƙara ba, duk fa Mutanen banza ne a wurin"

"Alright, hakan ma na gode".

"To dan Allah yaushe zaka je wurin Inna ka gaya mata, muje ka kaini in ganta

, ni ko ba 'yar uwata ba ce, dan Allah ka kai ni in ganta, ka ga kan in mutu dai na ga wani nawa a duniya"

"Ina wanda ya tsinto ki?".

"Ba nace maka ya rasu ba"

Adnan ya yi ajiyar zuciya ya ce "To ke a ina aka tsinto kin?".

Ta

ɗ

an yi shiru sann

an ta ce "Nima ban sani ba ni dai kawai yadda na ji labari, Baba ne ya tsinto ni, ya kai ni gidansa, sai ya je wurin 'yan sanda ya gaya musu ya tsinci jaririya, sai suka ce yaje Allah ne ya bashi. Sai Baba ya ce musu, ba wani bincike da za ayi? Sai suka ce

ba yau aka fara haihuwar shegu a yar ba, dan da gani wannan kyan nawa ta hanyar banza aka sameni, ba lallai a samu iyayena ba, dan sun samini suna Afra saboda kyauna, yaje in zai riƙe sun bashi, to daga nan ya riƙeni ya sani a makarantar boko ai ta cewa b

ani da iyaye, samari da yawa na sona, amma saboda tsinto ni aka yi, sai su fasa aurena, wani

ɗ

an gidan

ɗ

an majalissa ne ya ce zai aureni, babansa ya ce bai yadda ba, da ƙyar babansa ya amince, an kusa kawo ku

ɗ

in Auren kuma, yayi hatsari ya mutu, kallon fa

shegiya ake mini a garin nan" ta ƙarasa maganar fuskarta ta jiƙe da hawaye.

Hanky

ɗ

insa ya ciro a aljihunsa, ya shiga goge mata hawayen fuskarta.

"Angel, ke ba shegiya ba ce, ina da yaƙinin ke 'ya ce ta sunna, ina ga ke ce zaki dace kiga iyayenku, sh

iyasa Allah ya

ɗ

auke mini Angel ya kawoni garin nan na ha

ɗ

u da ke".

"Me kake nufi?".

"Twin sister

ɗ

inki da na aura, Allah ya yi mata rasuwa kwanakin baya, ta rasu ta bar mini 'yar jaririya mace" yayi Maganar hawaye na zubowa daga idonsa.

Zubewa ta y

i a wurin ta

ɗ

ora hannu a kanta ta ce "Na shiga uku!"



300 NE DAN ALLAH KU SIYA KAN KU KARANTA MANA

08081012143

[11/12, 3:38 PM] Abk: Ƙasa Adnan ya yi da kansa cikin ƙoƙarin tsayar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login