Showing 198001 words to 201000 words out of 260401 words
ta ƙasan
ɗ
ankwalin ya kwanta a bayanta.
"Mahaukaciyar ina ce ke, zaki hawo kan hanya haka ina miki horn, amma ki ka yi banza? Wace irin mara hankali ce ke?".
"Kar ka sake ce mini mara hankali, kai ne mara hankalin ai, Yanzu da na mutu..
... Kasa ƙarasa Maganar ta yi, ganin mutumin da yake tsae a kanta, sankacecen ingarman namiji, fuskarsa a
ɗ
aure babu walwala, ko da idanunsu suka sarƙe a na juna, take ta ga ya sake ware idanuna a kanta.
"A..Ab....Abra..My Angel you are still alive, dam
a na gaya musu ba ki mutu ba, dama nan ki ka taho ki ka
ɓ
uya?"
Zazzare ido ta shiga yi tana kallonsa, ita dai bata ta
ɓ
a ganin sa ba, ko mai kama da shi a ƙauyen nan babu, ga kayan jikinsa masu kyau balle ta ce ko mahaukaci ne.
"Abrana ki yi magana ma
na, Angel ashe baki mutu ba" ya ƙarasa Maganar tare da miƙa hannunsa zai
ɗ
agota!!!
Ki biya mu haƙƙinmu kan ki karanta, na ku
ɗ
i ne ₦300 kacal.
08081012143
[11/7, 6:36 PM] Abk: Ganin da tayi ya miƙo hannayensa gaba
ɗ
aya zai
ɗ
agota tsaye, ya sanya
ta daddage ta ƙwala ihu "Wayyo Allah na shiga uku mahaukaci" tsayawa yayi sororo yana kallonta, ta tashi cikin hanzari ta suri farantin gya
ɗ
ar ba ta tsaya ta bia ta kan gya
ɗ
ar da ta watse ba, ta fyalla da gudu kamar ba zabgegiyar budurwa ba, binta Adnan ya
yi yana kiran "Abra, dan Allah ki tsaya ki ji" sai dai kan kace Kobo, ta
ɓ
ace
ɓ
at a cikin gonaki.
Dawowa yayi, wurin da gya
ɗ
ar ta ta watse a ƙasa, ta bar mayafinta a wurin, ya durƙusa ya
ɗ
auka yana jujjuya mayafin, take hawaye ya cika idonsa "Angel, Alla
h ya sa ba gizo kike mini ba, ko dai haukacewa na yi ne ban sani ba? Innalillahi wa Innalillahi raji'un" ya da
ɗ
e a wurin a tsaye, sanan ya shiga motarsa ya ja ya cigaba da tafiya, ji yake tamkar an zare masa lakar jikinsa, ya rasa duk wani kuzarin sa.
Ya
samu ƙasan wata bishiyar tsamiya, yayi parking ya kifa kansa a kan sitiyarin motar, ya shiga duniyar ta sa ta tunani, da hasaso lokutan da suka shu
ɗ
e wanda ya kasance tare da Abra.
Haka ya
ɓ
ata lokaci a wurin, yana ƙara rirriƙe mayafin yarinyar nan mai gy
a
ɗ
a, yana son tabattar a zahiri Abra ya gani, ko mai kama da ita ce kawai, ko kuma dai duk gizo ne?
Ganin ba shi da mai ba shi wannan amsar ne, ya sanya ya fito daga motar ya tambayi wasu samari, gidan maigari, suka kwatanta masa yayi musu godiya ya koma
motarsa.
Tunani ya dinga yi ya aka yi bai tsaya ko sunanta ya sani ba, to ta yaya ma zai san sunanta yarinyar da ko tsayawa ba ta yi ba ta kwasa da gudu.
"No my Angel can't run like this, sje might be her ghost, or am just hallucinating" ya yi maganar
a fili yana taune le
ɓ
ensa na ƙasa.
Gaba
ɗ
aya Hajiya Na'ima ta rasa me yake mata da
ɗ
i, duk ta birkice ta fita hayyacinta jin batun kishiyar nan, gashi Abbi ya sa ana ta gyaran gida, zai ƙara Aure, kuma duk wannan haukan da take, ko kallo ba ta ishe shi b
a, balle ya bi ta kanta, sabgar Aurensa ce kawai a gabansa sai jikarsa Aishatul Humaira.
Na'ima na zaune a
ɗ
akinta, tana rungume da Little Abra, sai dai gaba
ɗ
aya hankalinta ba ya jikinta, she can't imagine sharing her husband with a prostitute.
Sallam
ar Abbi a
ɗ
akin ce ta dawo da ita hayyacinta, ba ta amsa masa ba, kuma ba ta kalli in da yake ba.
Ya ƙaraso yana yiwa little murmushi, ya yin da ita kuma take
ɗ
an murmusawa har dimples
ɗ
inta suna lotsawa, haryanzu ba ta da wayo sosai, dan baka ba ta wani
gane wasa, amma duk in da ta ga Abbi, tana yawan bin sa da idanunta, ko ma ta
ɗ
an dinga yi masa murmushi.
Abin har mamaki yake bawa Na'ima, dan Aishatul Humaira ba ta yi wayon gane wasa ba, amma tana gane Major.
Ya miƙa hannu zai
ɗ
au Little, amma Naima t
a ƙanƙameta a jikinta tana watsa masa wani mugun kallo.
"Ya haka? Ki bani yarinyata in gani".
"Ba zan bayar ba, ka fita sabgata da ni da yarinyar nan, ka je ka yi rayuwarka mu yi ta mu".
"Hmm ikon Allah, madam kenan, har kin manta jikar karuwa ce Hu
maira?".
"Kar ka ƙara danganta mini 'ya da karuwa".
"Ohh sorry, ai ba ni na fara fa
ɗ
a ba, ke ce ki ke fa
ɗ
a, ko har kin manta Abra 'ya ta ce da karuwa ta haifa mini?"
Wata irin nadama da dana sani ne suka ziyarci Na'ima, ta tafka kuskuren da lokaci
n gyara ya ƙure mata.
"Kinga gara in kawo kakarta, ta kula mini da ita yadda yakamata, kar ƙiyayyar da ki ka nunawa uwatta ya shafeta ita ma".
"Ka ce mini ba zaka yi aure ne dan ka hukunta ni ba, amma wannan ƙananun maganganun da kake na menene?"
Bai amsa mata ba, sai murmushi da ya yi. Ya kuma miƙa hannu zai
ɗ
au Little.
"Khamal ka ƙyaleni ka rabu da ni na gaya maka, idan duniya zata ha
ɗ
u babu wanda ya isa ya rabani da jaririyar nan, kuma Wallahi ko ma wace tsinannaiyar zaka auro, babu ita ba Litt
le, ka ƙyaleni ka rabu da ni".
Major ya ce "Allah ya baki haƙuri, zaki tsorata yarinyar ta ki, dama na zo ne in tambayeki, part
ɗ
in ki kike so, ko wancan da ake gyarawa?"
"Ban sani ba, ida ka ga dama ka jani ka kai ni titi ka yar ka ha
ɗ
a mini da saki
, ka yi Aure ka sa a gidan".
"Hmm Na'ima mai rikicin gangan, ai duk wani abu da za ayi, muna tare forver, duk da
ɓ
ata mini rai da ki ke yi, kina da wata kima da daraja a idanuna, shiyasa na ke tambayar ki abin da ki ke so, amma tin da ba kya so, shikena
n" ya ƙarasa maganar tare da miƙewa ya fice.
Yanzu da Abra tana nan, da wataƙila ita zata gayawa damuwar ta, ko ba komai ta tayata jin babu da
ɗ
i, amma Salman shi ba damuwa zai yi ba ko ta gaya masa, ga yadda suka ƙare da Anty Suwaiba, ta ƙanƙame Aisha t
a fashe da kuka.
Da gudu ta shiga cikin gidan, tana ta uban haki kamar ta yi dambe da kura, Yaya Musa da yake jan ruwa a rijiya ya kalleta ya ce "ke meye haka? Gudun me ki ke yi ne?".
Da hanzari Inna ta fito daga wurin da suke girki, ta kalleta
ta ce "meke faruwa haka? Ina gya
ɗ
ar?".
Jifa ta yi da farantin gya
ɗ
ar ta nemi wuri ta zauna tana ta haki.
Yaya Musa ya ce "Wai ma a haka ki ka fita aiken? Ina mayafinki?".
"Dan Allah ka bari in dawo hayyacina" ta yi maganar tana haki.
Sai da ta
samu nutsuwa sannan ta fara ƙoƙarin tashi tsaye, Inna ta ce "Ina kuma zaki, ba ki mana bayanin mai ya faru ba? Ina aiken da na yi miki?".
"Wai Inna ke ta gya
ɗ
ar ki ma ki ke yi ba ta ratuwata ba ko? Wani mahaukaci ne fa ya buge ni da mota, kuma ya fara
kirana da wani suna yana ƙoƙarin rungumeni".
Dafe ƙirji Inna ta yi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ban gane rungumeki ba, ya rungumekin ne ko kuwa?".
"A'a, kan ya rungumenin ne na
ɗ
au farantuna na gudo gida".
"Ki gaya min gaskiya dan ub
anki, mai ya yi miki?".
"Be fa yi mini komai ba, ban bari ya ta
ɓ
a ni ba".
Yaya Musa ya ce "Wannan yarinyar wataƙila ma ƙarya take, wata maganar ta je ta
ɗ
auko".
Murgu
ɗ
awa Yaya Musa ba ki ta yi, ta nufi
ɗ
akinsu.
"To ina gya
ɗ
ar? Ko baki kar
ɓ
o ba?
".
"Ni fa wannan gya
ɗ
ar ta watse a hanya, kuma ban tsaye tsintowa ba, dan ban san me zai mini ba idan na tsaya".
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, shikenan yau asara ta hauni, gya
ɗ
ar duk ki ka watsar mini, kin kyauta".
"Au Inna, in tsaya tsinto
gya
ɗ
a ya rungumeni ko? Kuma in dawo ki hau cajeni"
"A'a ni bance ba, Allah ya mayar mini da alkhairi, amma dai kin gama da ni".
"Allah sarki Baba, da yana nan da shi zai biyaki ku
ɗ
in gya
ɗ
ar nan, ki daina yi mini mita, amma yanzu ba mai biya mini sai
mita ki ke yi, Allah ya jiƙan ka Baba"
Inna ta ce "Ameen, amma ai dole in yi mita, tun da asara ki ka janyo mini" Inna ta ƙarasa maganar tana
ɗ
agowa, sai dai tuni hawaye ya wankewa 'yar Baba fuska.
"Wai ba zaki daina wannan koke koken haka ba? Kina
tunanin kukan nan yana da amfani a gareki da kuma Baban ne? Ko shikenan idan kin yi laifi ba za ayi miki fa
ɗ
a ba?" Cewar Yaya Musa da jikinsa ya yi san yi.
"Yaya Musa, ba ina kuka ne saboda fa₦an Inna ba, in dai wannan fa
ɗ
an ne ai na saba da shi, ina ku
ka ne saboda rashin Baba, da kuma yadda aka yi Baba ya rasa ransa. Ka san wacece ni, kuma ka san waye Baba a wurina, na so ace ya yi tsawon rai a duniya, dan in nuna masa gata. Ina fatan Allah ya bani damar da zan yi ilimi mai zurfi, yadda wani talaka kama
r Baba, ba zai ƙara rasa ransa ba, saboda shi talaka ne ba. Wallahi ba zan ta
ɓ
a yafewa wa
ɗ
anda suka yi sakaci a kan rayuwarsa ba, na san lokacinsa ne ya yi, amma ya mutu a wulaƙance ba kulawa, Allah ya tsinewa wa......
"A'a A'a, kar ki kuskura in ji iri
n wannan mummunan furicin a bakin ki, ai ko baki fa
ɗ
a ba, Allah ishashe ne, kuma ya ga abin da ya faru, shi baban na ki tunda ki ke da shi, kin ta
ɓ
a jin ya tsinewa wani? To kar in kuma ji, maza je ki yi alwala ki
ɗ
au carbi, ki ta masa addu'a".
Abi
n duniya ya bi ya addabi zuciyar Bulama, ko wurin aiki ba ya iya zauwa, sai dai ya wuni a gida, kusan kullum cikin zarya yake tsakanin Asibitin da aka ce Adnan ya kwanta da kuma gidansa. Maƙwabcin Adnan ne ya nunawa Bulama gidan Adnan, da ya gaji da zaryar
da yake masa, gidan Adnan
ɗ
in ma idan yaje, sai mai gadi ya ce masa baya nan.
Babban abin da ya ƙara
ɗ
agawa Bulama hankali, bai wuce yadda aka ce masa yarinyar nan ta mutu ba, saboda zuciyarsa ta azalzalu da son ya ganta, ya gano ya aka yi ta zama 'yar s
a, sai dai har duniya ta gushe, ba zai fasa
ɗ
orawa kansa da Asibitinsa laifin da sa hannunsu a kisan Abra ba.
"Yanzu kenan na bada gudunmawa wurin kashe 'yar da na haifa, idan ta tabatta 'ya ta ce?" Ya yi wa kansa wannan tambayar.
Wasu hawaye ne da bai s
hirya zubarsu ba, suka gangaro a kan kuncinsa, bai ta
ɓ
a aikata abin da ya zo ya dame shi ba, ya hana shi sukuni ba irin wannan. Shiryawa ya yi ya kuma
ɗ
aukar mota, ya tafi gidan Adnan.
Ya na zuwa ya tarar da maigadi suka gaisa, mai gadin ya ce "Wallahi ra
nka ya da
ɗ
e, yau ma baya nan, yama yi balaguro fa".
Bulama ya ce "Bulaguro zuwa ina kenan?".
"Wani aiki aka tura shi ƙauye, ka san jami'in tsaro ne".
"Amm, ko zaka iya gaya mini cikakken sunansa?".
"Wallahi ban sani ba, kawai dai Adnan na sani,
amma ban san cikakken sunansa ba, da yake ban da
ɗ
e da fara yi masa gadi ba. Tun da dai matar nan ta sa ta rasu, gaba
ɗ
aya ya zama sai a hankali".
Bulama ya yi ajiyar zuciya, ya ce "Wane ƙauye aka tura shi aiki?"
"Yo ni ina zan sani?".
"Dan Allah
idan ba damuwa, ka bani lambar wayarsa".
Mai gadi ya ce "Babu damuwa, bari in baka" ya bawa Bulama lambar Adnan, ya yi masa sallama ya tafi.
Ko da Adnan ya ƙarasa gidan maigari, aka yi masa iso, ya shiga suka gaisa, ya ce musu "Ni baƙo ne daga
cikin garin Kano, ga takarda da aka bani na taho da ita zan yi wasu 'yan kwanaki a nan, kan in wuce".
Mai gari ya nuna farin cikinsa da jin batun Adnan, suka kar
ɓ
e shi hannu bibbiyu aka ba shi masauki, a wani gida, wanda galibi a nan suke saukar baƙin s
u, sai dai hankalin Adnan, sam ba ya kan aikin da aka turo shi, yana kan a ina zai sake ganin yarinyar nan? Ko kuma dai kamar yadda yayi tsammani, tsabar sanya Abra a ransa ne ya sanya ya ke ganin fuskarta na yi masa gizo a fuskar mutane?.
Yayi alwala ya
yi sallolin da suke kansa, bai nemi Abinci ba ya zauna ya cigaba da aikin na sa na tunani.
Wayarsa ce ta fara ringing, ya duba wayar amma ya ga baƙuwar lamba, kawai sai ya share, ya cigaba da tunaninsa.
Jin an cigaba da kiran ba ƙaƙƙautawa ne ya sanya, y
a
ɗ
au wayar zai sanya a silent, amma ya fasa ya
ɗ
aga ya kai kunnensa tare da yin sallama.
"Wa'alaikum salam, barka da yamma".
"Yauwa wake magana?" Adnan ya fa
ɗ
a cike da ƙosawa.
"Doctor G.Y Bulama ne"
Wani uban tsaki Adnan ya ja, "Me zan yi maka
? Me ka kirani ka gaya mini?".
Bulama ya kwantar da muryarsa ya ce "Dan Allah ka yi ka haƙuri ka tsaya mu fahimci juna".
"Babu wata fahimta tsakani na da kai, ka jiraye ni zuwa lokacin da zan kai ka kotu, a kan kisan mata ta".
"Kana da right
ɗ
in d
a zaka yi haka, amma dan Allah ina son ka mini bayani yadda zan fahimta, ya aka yi yarinyar nan ta zama 'ya ta?".
"Au mamaki ma ka ke yi? Bayan har gidanka na kai maka envelope da hotunan ta a ciki da wasiƙa watannin baya? Meyasa tun a lokacin ba ka yi
ƙ
oƙarin neman 'yar ta ka ba, sai yanzu da ka kasheta?".
"Adnan ka daina fa
ɗ
an haka, ban kasheta ba, amma dan Allah ina son mu ha
ɗ
u".
"Mu ha
ɗ
u ka yi mini me? Da fari ka kashe mahaifiyata shekaru Ashirin da uku da suka gabata, cike da zalunci ka sayar
da jinin da za a sa mata, ka yi mata gur
ɓ
atacciyar allura, wadda ta yi ajalinta, katsam Allah ya ha
ɗ
ani da 'yar ka wadda ita kanta ba ta sanka ba, da yake Allah ba Azzalimin sarki ba ne, sai gashi irin halin da ka ke wa mutane na wasa da rayuwarsu, ka yiwa
'yar ka har ta rasa ranta. Haƙƙin rayukan mutane ba zai barka ba, kuma daga kan matata ba zaka ƙara wasa da lafiyar wani ba" Bulama zai yi magana, Adnan ya katse wayar, ya cillar da ita gefe, ya dafe kansa yana wani irin huci tare da ha
ɗ
a gumi.
Bulama
ma ajiye wayar ya yi, ya dafe kansa yana tunanin, wace envelope aka kai masa? Shi ba wanda ya kai masa wata envelope.
Ta da motarsa ya yi, ya ja ta a guje, ya nufi gida, yana parking ya fito, ya nufi wurin maigadi a sukwane.
Ganin da mai gadi yayi Bu
lama ya nufo shi, ya sanya ya taso da sauri ya taho, tare da risinawa a gaban Bulama.
Bulama ya kalleshi ya ce "Kwanakin baya, ko ma in ce watannin baya, an kawo wata envelope an ce a ajiye mini?".
Mai gadi ya yi shiru, can ya ce "Tabbas Yalla
ɓ
ai an
yi haka, an kawo saƙo an ce a ajiye maka watannin baya".
"Ina takaddar?".
"Yalla
ɓ
ai ban duba ba, ban san ko takadda ce a ciki ba, na kaiwa Hajiya ta kar
ɓ
a ta ce zata ajiye maka".
Jinjina kai ya yi ya tafi da sauri, Hajiya Saudat na
ɗ
akinta, tana k
walliya a gaban mudubi, Bulama ya fa
ɗ
a
ɗ
akin ba bu ko sallama.
"Doctor lafiya kuwa?".
"Watannin baya an kawo saƙo a envelope, an bawa maigadi, shi kuma ya ce mini ya baki ki ajiye mini, ina saƙon?".
"Wane saƙo kuma? Ni ba wani saƙo da ya bani".
"Kar ki mini wasa da hankali, envelope aka kawo mini, da takadda a ciki da hotuna suna ina?".
Gabanta ya yi mummunar fa
ɗ
uwa, amma ta dake ta ce "Ni babu wata envelope da aka kawo mini, ka dai tambaye shi wanda ya bawa".
"Shut up Saudat, Mutumin nan
ba zai miki ƙarya ba, ki bani saƙon nan".
"An ya ba ciwon damuwa ne ya kama ka ba, ya ke neman ya ta
ɓ
a maka ƙwaƙwalwa ba?".
"Ni ki ke gayawa ƙwaƙwalwata ta ta
ɓ
u? Kin kyauta amma na fara tunanin wani abu, akwai abin da nake tunani, idan har ya tabbata
zaki ga abin da ba ki tsammani ba".
Ya juya fuuuu, ya tarar da