Showing 213001 words to 216000 words out of 260401 words
da hawayen idonsa amma ya ƙi tsayawa, ganin yadda yake kuka sai jiki
n ƴar Baba ya yi sanyi. Idanunta cike da hawaye ta ce. "Ka daina kuka, ba a son yi wa wanda ya mutu kuka, haka Inna take ce mini idan ina kukan rashin Baba." Bai ce komai ba sai da ya share hawayen fuskarsa duka, cikin raunin murya ya ce. "Ai za ki maye mi
ni gurbin ta ko?" Turo baki ta yi ta ce. "Huh'um, wallahi ni ba na son ka, kalle ka fa baƙi." Duk da halin da yake ciki na tuna Abra sai da ya murmusa saboda yanda ta yi maganar.
"Shikenan, tunda kin fi so na auro wata ta riƙe mini ƴata, in ma muguwa
ce ta cutar da ita idan bana nan."
Shiru ta yi kamar mai nazari tana kallon shi na wasu sakanni, ta
ɓ
e baki ta yi ta ce. "Ina son ƴar taka, tunda ka ce ƴar'uwata ce ta haife ta, yaushe za ka kawo mini ita ko kai ni na gan ta?"
"Ranar da kika fara so
na." Ya fa
ɗ
a idanunsa a cikin nata.
Janye idanunta ta yi da sauri, cikin raunin murya ta ce. "Amma ka san iyayenmu? Me ya sa suka yarda da mu?"
"Ban sani ba, amma ina nan ina bincike akan hakan, ni da wanda ya riƙi Abra."
"Abra."
Ta maimaita su
nan kamar mai tunanin wani abu a cikinsa. Kallon yadda rana ta fito Adnan ya yi ya ce. "Lokaci yana tafiya, mu je ki raka ni gidan Sadin."
"Gaskiya ba zan iya zuwa ba, ni roro na zan tafi, na san yanzu ana can ana ta yi, an kusa rore gya
ɗ
ar ma duka ni b
an je ba."
"Mu je na taya ki."
Kallon shi ta yi cikin mamaki ta ce. "Ai ba ka iya ba."
"Sai ki koya mini."
"Tom shikenan mu je."
Suna tafe yana tsokanar ta har suka ƙarasa gonar, wani irin farinciki da nisha
ɗ
i yake ji na kasancewa da ƴar B
aba, ji yake tamkar Abransa ce ta dawo. Yara da manya damƙam a gonar, sun zagaye tumin gya
ɗ
ar kowa na roro. Cikin takaici Ƴar Baba ta dubi Adnan ta ce. "Ka ga har an cika ban zo ba, ni da nake riga kowa zuwa, kuma alƙur'an sai ka taya ni." Bai ce komai ba
sai idanunsa da yake ba wa abinci yana kallon yadda ake roron gya
ɗ
ar. Ƴar Baba na ƙarasawa gurin aka fara kiran sunanta, ta kula wanda ta ga dama ta share wa
ɗ
anda take jin haushi. Su kuwa ƴan ƙauyen sai kallon Adnan suke, cikin mamakin ganin shi tare da ƴa
r Baba, suna son su tambaye ta wane ne shi, amma yadda ta yi kicin-kicin da fuska ya sa kowa ya ha
ɗ
iye gulmarsa bai fito da ita ba.
"Ka zo ka taya ni, ka tsaya kana kallo na." Ta yi maganar cikin sangartar ta.
Ƙ
arasowa ya yi ya tsugunna a kusa da it
a ya
ɗ
auki ganye
ɗ
aya ya fara cire gya
ɗ
ar yadda ya ga suna yi cikin yamutsa fuska, a ransa yana tambayar kansa ko mene ne amfanin wannan abun?
Wasa-wasa sai ga SP Adnan
ɗ
an gayu mai ji da kansa ya wuni a gona yana roron gya
ɗ
a, don hana shi tafiya 'ya
r Baba ta yi da rigimar ta, Sallah ce kawai take tayar da shi, rashin sabo ya sa duk ya galabaita, kayansa suka yi futu-futu da ƙura da ƙasa. Ƴar Baba kuwa sai murna take gya
ɗ
arta ta fi ta kowa yawa, saboda taya ta da Adnan ya yi. Sai da mai gonar ya zo ya
rarraba ya ba wa kowa ladan roronsa sannan suka tafi, lokacin Magriba ta kawo kai.
Suna cikin tafiya 'yar Baba ta dube shi ta tuntsure da dariya, saboda yadda ya yi wani kalar tausayi, ga shi ya taka ƙaya a gonar da
ɗ
ingishi yake tafiya,
ɓ
ata fuska
ya yi bai yi ce komai ba.
"Gaskiya kai rago ne, kana namiji amma
ɗ
an wannan aikin ya wahalar da kai, ba ni kwanon abincina da robar ruwan idan ba za ka iya riƙewa ba."
Hararar ta ya yi tare da fa
ɗ
in. "Idan na ba ki da wanne hannun za ki riƙe?"
"A kai nake
ɗ
ora buhun gya
ɗ
ata, sai na riƙe kwanon a hannu, haka nake yi kullum."
Jinjina kai ya yi, a ransa yana jinjina yadda mutan ƙauye suke shan wahalar rayuwa. Har ƙofar gida ya raka ta, har ta wuce za ta shiga gida ta dawo ta ce. "Yawwa na tuna,
jiya na tafi kiran Inna shi ne ka gudu ko?"
Cikin gajiyar dake addabar jikinsa ya ce. "I'm sorry."
"Ba zan haƙura ba gaskiya, sai dai in ka yarda in kira Innar ta gan ka yanzu."
"Ki bari sai gobe, zan zo na gaishe ta my Angel, yanzu duk a gaji
ye nake, kin ji ma an fara kiran Sallah, ko da yake na ga ke duk wunin da muka yi a gona ba ki yi Sallar ba."
Murgu
ɗ
a baki ta yi ta ce. "Ina ruwanka, dama saka mini ido kake yi." Murmushi ya yi tare da kama hannunta ya riƙe, idanunsa a cikin nata yana
jifan ta da wani irin kallo.
"Na shiga uku! Don Allah ka cika ni, kar Inna ta leƙo ta gan ni ko Yaya Musa ya zo wucewa." Ta yi maganar cikin tsantsar tsoro da fargaba, idanunta duka a waje tana kallon zauren gidansu.
"Have a nice night, good bye,
I love you."
Ajiyar zuciya ta sauke jin ya sakar mata hannu ta rarumi bugun gya
ɗ
arta ta yi cikin gida da gudu a ranta tana gulmar Adnan. Inna dake alwala ta saki salati tare da fa
ɗ
in. "Wai ƴar Baba kanki
ɗ
aya kuwa? Da magaribar ma ba za kina tafiya c
ikin nutsuwa ba? Wunin yau bakina shiru amma yanzu daga dawowar ki zaki fara sa ni magana, me yake damun ki ne wai?" Ba ta ce komai ba sai da ta koma ta
ɗ
auko kwanonta ta dawo, bayan ta zauna a kan kujera yar tsugunne ta ce. "Inna daga dawowa ta maimakon k
i tar
ɓ
e ni da ruwan sanyi na randa da abinci amma sai ki fara da fa
ɗ
a? Na je na gaji na wahala amma ko ki mini sannu."
"Ba zan yi ba, tunda ke yin abin da aka ce ki yi kike yi, yarinya kina girma amma kullum jiya i yau, ai ta maimaita magana ba kya
ɗ
auka, sai dai ta shiga ta dama ta fita ta hagu, to in ma wani motsin ne a kanki gobe zan kai ki a miki roƙiyya a fitar."
"Ta
ɓ
, wallahi ba zan biki a zane mini jikina ba haka kawai." Ta yi maganar tare da miƙewa ta shige
ɗ
aki.
A matuƙar gajiye ya
ƙ
arasa gidan Hakimi, bai zauna ba sai da ya rage kayan jikinsa ya yi wanka ya shirya cikin
ɓ
addakama ta shiga irin ta matasan garin da kayan wani
ɗ
an Hakimi da ya aro, bayan ya yi Sallah ya na
ɗ
e ƙafarsa da hanky, ya ci cakes
ɗ
in da ya zo da su da lemo ya
ɗ
auki torchlight da ku
ɗ
i ya fita. Da ƙyar yake iya tafiya saboda yadda ƙafar tasa ta
ɗ
aure, ba ƙaramin cakar shi ƙatuwar ƙayar ta yi ba don da ƙyar ya iya zare ta saboda zugi da ra
ɗ
a
ɗ
in da gurin yake masa a lokacin. Ba don dole ba da kwanciya zai yi a yanzu
ya huta, amma aikin da ya zo yi ƙauyen ba na wasa ba ne, ga IG kullum sai ya tambaye shi akan ina aka kwana? Ha
ɗ
uwa da ƴar Baba duk shi ya
ɗ
auke masa hankali. Da ƙyar ya iya gano layin su Sadi
ɗ
an kunama, yana shiga karnuka suka fara yi masa welcome da ha
ushi..
"Kai, waye a nan?"
Muryar wani
ɗ
an tauri cikin shaye-shaye ta doki kunnensa.
Cikin ƙwarewa a aiki ya sauya muryarsa zuwa ta yan yawa ya ce. "Ni ne, abin zuƙa nake buƙata, an ce mini babu inda zan samu sai nan."
Haske shi aka yi da fitila
mai haske ba tare da ya san waye ba, sai da suka ƙare masa kallo sannan wanda ya yi magana da farko ya ce. "Kawo silalla a baka abun duniya Baba." Bai ce komai ba ya zaro ku
ɗ
i ba tare da ya ƙirga ba ya ba su. Wiwi suka ba shi da wani abu a kwalba wanda ya
tabbatar giya ce, kar
ɓ
a ya yi ya zauna
ɗ
an nesa da su yana kallon gurin cikin nazari, wani ƙaton gida da ya banbanta da ginin gidajen garin ya ƙurawa ido, ko tantanma ba ya yi nan ne gidan Sadi
ɗ
an kunama.
Mami ce zaune a main parlour tana ba wa
little abincinta, bayan ta ƙoshi ta kwantar da ita akan carpet ta shiga kitchen don
ɗ
auraye bowl. Kafin ta fito amarya Salima ta shigo parlour'n cikin wasu matsatstsun kaya riga da wando, sai baza ƙamshi take. Ganin little a kwance ita ka
ɗ
ai ya sa ta
ɗ
auke
ta cikin sauri ta fara yi mata wasa tana shilla ta tare da yi mata waƙa.
"Mamana kin fi ta kowa, ƴar fara kyakkywa, mai kama da mamanta."
"Malama ya za ki
ɗ
aukar mini yarinya kina ciccilla ta sama a daren nan? Mene haka?" Na'ima ta fa
ɗ
a lokacin da t
a dawo parlour'n tare da ƙwace little a fusace.
"Ki yi haƙuri kar ki karya mata haƙarƙari."
"In na karya kina da asara ne? Haba, bana son maita, na ce bana son ana
ɗ
aukar mini yarinya amma don naci da rashin zuciya sai an
ɗ
auka."
"A'a, hayaniyar
me nake jiyowa tun daga baranda? Lafiya?"
Abbi da ya shigo gidan ya tambaya idonsa akan Nai'ma.
Hawaye Salima ta ƙaƙaro cikin kissa ta ce. "Ban san me ya sa ba ta son na
ɗ
auki little ba, ko na yi mata wani lefin ne ban sani ba, ni kuma ina da son
yara, shi ya sa bana zuciya na ƙi
ɗ
aukar tata." Duban Na'ima dake huci ya yi ya ce. "Na'ima ke kika haifi yarinyar nan ne ko ke ka
ɗ
ai aka haifawa ita? Abra is my daughter, ke da Salima kuma duk matana ne, don haka yadda kike da iko da abin da Abra ta haif
a ita ma haka, don haka kar na ƙara jin wata rigima ta tashi don ta
ɗ
auki little."
"Wallahi ba zai yiyu ba, Abran ai ni na riƙe ta ba wata can ba, don haka nike da iko da abin da ta haifa."
"Okay, abin da na fa
ɗ
a ne ba za ki bi kenan? To cigaba k
ar ki fasa, kar ki
ɗ
auka wai na sauya ne daga Khamal
ɗ
in da kika san ni saboda kwana biyu ina
ɗ
aga miki ƙafa, fitina ce kawai bana so." Ya yi maganar cikin fusata.
Miƙewa Salima ta yi ta kama hannun Abbi tare da kwantar da kanta a jikinsa, cikin muryar
rarrashi mai cike da salo da shagwa
ɓ
a ta ce. "Honey please ka bar maganar, in dai little ce ba zan ƙara
ɗ
aukar ta ba." Bai ce komai ba sai gefen fuskarta da ya shafa cikin ƙauna.
Tsaki Nai'ma ta ja ta yi wucewar ta part
ɗ
inta, zuciyarta cike da tuƙuƙin
baƙin ciki da kishi. Tana shiga
ɗ
aki ta goye A'isha Humairah sannan ta
ɗ
auki wayarta ta kira Aunty Wasila, bayan ta
ɗ
aga ta fashe mata da kuka.
"To uwar kuka, yau kuma me ya faru?"
"Na gaji Aunty wasila, na gaji da zaman baƙin ciki da ganin takaici,
wallahi zuciyata ba za ta iya
ɗ
auka ba, idan aka cigaba da haka watarana sai dai ku zo ku tarar da gawata."
"Yanzu dai fa
ɗ
a mini mene ya faru."
Cikin gunjin kuka Mami ta ce. "A gabana fa Khamal yake nuna wa yarinyar nan k'auna, ya rungume ta ko ya ba
ta abinci a gabana ba komai ba ne a gurin shi, washegarin da aka kawo ta da yamma har da fitowa main parlour tana tafiya ƙafa a tale, a dole sai ta nuna mini an
ɓ
urma ta, iskanci dai kala-kala."
"Ke ma sai ki tsuro da naki salon, mijinki ne fa, kin fi
kowa sanin shi, ai kowa ya iya allonsa ya wanke kawai, amma kya zauna kina wani koke-koke, har yanzu ba ki bar shashancin nan ba Na'ima? Sai ka ce a kanki aka fara kishiya? Duk kin fice daga hayyacinki."
Shiru Mami ta yi ba ta ce komai ba, ita ka
ɗ
ai ta
san halin zafin kishin Mijinta da zuciyarta take ciki, idan ta ga Abbi tare da Salima sai ta ji tamkar ta shaƙe su saboda tsananin baƙin ciki, ga yarinyar da shegiyar kissa da iyayi da firirita.
Washegari da safe Nai'ma ta fito don ha
ɗ
a wa kanta
breakfast ta tarar da Abbi da Salima zaune akan dinning suna cin abinci a cikin plate
ɗ
aya, Salima sai nanaƙe shi take tamkar za ta koma cikinsa, shi kuma sai jifan ta yake da wani irin kallo ƙasa-ƙasa. Wani irin abu mai kaifi da zafi ne ya soki zuciyar Ma
mi, mijinta abin son ta wanda suka shafe fiye da 20 Years tare amma yau shi ne yake soyayya da wata macen da ba ta fi Yar cikinsa ba a gabanta, ji ta yi tamkar ta juya ta koma part
ɗ
inta, amma dai ta
ɗ
aure saboda kar a gane halin da take ciki ta nufi kitch
en, cikin yaƙi da hawayen dake ƙoƙarin fita daga cikin idonta. Kamar yadda ta yi tamkar ba ta gan su ba haka su ma suka yi, sai Salima ce ta bi ta da kallon gefen ido tare da sakin wani munafukin murmushi.
Rasa abin da za ta girka ta yi, yunwar da tak
e ji ma nemar ta ta yi ta rasa saboda mugun ganin da ta yi, tana hawaye ta dafa noodles guda
ɗ
aya ta juye ta a plate ta fito bayan ta goge hawayen fuskarta. Kakarin aman da Salima ta fara ne ya sa ta tsayawa cak ganin ta tashi ta shiga toilet
ɗ
in dake parl
our'n da sauri, a ru
ɗ
e Abbi ya bi bayan ta yana fa
ɗ
in "Lafiya Baby? Me ya faru?" Ba ta ba shi amsa ba sai da ta gama aman, kamo ta ya yi suka fito yana yi mata sannu, har lokacin Nai'ma tana parlour'n a tsaye ta kasa tafiya.
"Baby ko na
ɗ
auko key
ɗ
in Mo
ta mu tafi asibiti ne?" Ya yi maganar yana shafa bayanta.
Ƙ
ara lafewa ta yi a jikinsa tana kallon Mami cikin yamutsa fuska ta ce. "A'a Honey ba wani abu ba ne, kawai ƙamshin turaren da Maman Salman ta fesa ne bai mini ba, tunda ta fito cikina ya fara
hautsinawa, da ta dawo kuma sai na ji abin ya tsananta." Duban Mami Abbi ya yi cikin ko in kula ya ce. "Please ki daina saka turaren da kika sa, kin ga ya sa Baby amai, ko kuma idan kin san ki daina fitowa parlour idan tana nan." Ya ƙarashe maganar tare da
kama hannun Salima dake ta toshe hanci suka bar parlour'n. Tsananin baƙin ciki da takaicin da Mami ta ji ba zai misaltu ba, ba ta san lokacin da ta saki plate
ɗ
in hannunta ba indomien ta baje a ƙasa ba, cikin kuka mai cin rai ta yi part
ɗ
inta da gudu.
"Doctor magana fa nake maka ka mini shiru, haba, I'm tired da wannan sabon halin da ka tsiro da shi, gaskiya."
"Na miki dole ki zauna da ni a hakan da nake ko kuma na
ɗ
aure miki ƙafarki ne na hana ki tafiya? Idan ba za ki iya ba you are free to
go."
Cikin tsantsar mamaki da shock Hajiya Saudat ta ce. "Yusuf! Yau ni kake fadawa ba ka
ɗ
aure wa ƙafa ka hana ni tafiya daga gidanka ba?"
"Uwata ce ke da ba zan fa
ɗ
a miki haka ba?" Ya yi maganar yana jifan ta da wani mugun kallo, kasa magana ta
yi saboda tsananin al'ajabi. Dogon tsaki ya ja ya
ɗ
auki coat
ɗ
insa da briefcase ya bar mata
ɗ
akin. A wahalce ta yi zaman ƴan bori a ƙasan
ɗ
akin jin kanta na juya mata, wata irin mummunar fa
ɗ
uwa gaba ce ta ziyarce ta, lokacin da wani tunani ya
ɗ
arsu a rant
a.
Daga yanayin yadda ya shigo asibitin ma'aikatan suka san babu lafiya, dama kwana biyu zuciyoyinsu cike suke da mamakin rashin zuwan shi Asibitin, kasancewar wannan ne karon farko da hakan ta ta
ɓ
a faruwa. Suna gaishe shi amma ba ya amsawa, fuskars
a a cukule ya ƙara office
ɗ
insa. After 30 minutes ya aiko a kira masa Nurses and doctors
ɗ
in dake asibitin. Bayan sun hallara ya dinga kiran su
ɗ
aya bayan yana ba su wani envelope. Fuskokinsu cike da mamaki suke baro office
ɗ
in.
"Na shiga uku! Takarda
r sallama fa na gani." Cewar Nurse Basira cikin tashin hankali.
"Ni ma haka."