Showing 147001 words to 150000 words out of 260401 words
furta so ba. Amma me ya sa ya kasa gane pretending kawai Na'ima take? Duk
da kasancewar shi mai saurin fuskantar abu. _ƙaddara_ zuciyarsa ta ba shi amsa.
Hand bag kawai Na'ima ta
ɗ
auka ta saka hijabi
tare da zira takalmi ta fice cikin tsananin tashin hankali. Domin ba ta ji a ranta ta bar gidan Khamal kenan, zuciyarta ba za ta iya
ɗ
aukar hakan ba, tana son Mijinta ba ta son rabuwa da shi.
Aunty Suwaiba ce ke kaikawo a parlour bayan Na'ima ta gama
zayyane musu abun da yake faruwa. Cikin damuwa ta ce. "Wautarki ta yi yawa Na'ima, abun da nake jiye miki kenan tun farko, shi ya sa nake tausar ki akodayaushe akan ki dinga danne ƙiyayyar yarinyar nan da kishinki a kanta, amma ki ka ƙi ji, gashi nan ya s
ake ki." Cikin kuka Na'ima ta ce. "Wallahi Aunty ba ni da masaniyar abun da yake zargi na da shi, ni ban fa
ɗ
a wa yarinyar cewa ba mu muka haife ta ba har yau."
"To waye ya fa
ɗ
a mata? Ni dai a sani na ko Kaduna ba ku ta
ɓ
a zuwa ba, balle a ce wani ya san
ku a can ya fa
ɗ
a mata. Kuma abubuwan da kike yi wa yarinyar ne ya saka ko da ba ke kika fa
ɗ
a mata zai ce ke ce."
"Dan Allah Aunty ki bar ni da maganganun nan, in ji da abun da yake damu na mana, haba."
"Na bar ki Na'ima, amma ko kin ƙi ko kin so s
hegen kishin da
ɗ
ora wa kanki ne ya jawo miki."
A ƙufule Mama ta ce. "Wai wannan maganganun na mene ne? Abin da ya faru ya riga ya faru sai dai mu nemo hanyar da za a gyara shi, tunda kin ce saki
ɗ
aya ne ko?" Ta ƙarashe maganar idanunta a kan Na'ima. G
ya
ɗ
a mata kai ta yi tana sharar hawaye. Duk wannan fafutukar da boloƙon da ta yi saboda Abra ta bar musu gida amma ƙarshe abin a kanta ya ƙare, tana murna shirinta ya tafi daidai ashe zai warware ne tas.
Tana ji Adnan ya shiga toilet ya yi wanka ya f
ito amma ita ta kasa ko da
ɗ
aga
ɗ
an'yatsanta ne, wani irin nauyi take jin kanta ya yi mata, ga duk jikinta dake mata ciwo saboda gajiyar da Adnan ya tara mata. Ita ka
ɗ
ai ta san me take ji a cikin ranta na tsantsar damuwa, addu'a take yi Ubangiji ya sa mafa
rki take ba gaske ba ne ABBI BA SHI NE YA HAIFE TA BA. Zuciyarta ta kasa yarda da hakan duk kuwa da yanda Adnan yake ta nanata mata, tabbas a yau ta yarda Adnan ba ya ƙaunarta kamar yadda yake furtawa, tunda har iya fa
ɗ
a mata abin da zai tarwatsa mata zuci
ya. Idanunta a kansa yana shiryawa cikin kwanciyar hankali da nisha
ɗ
i, alamun rayuwar tana yi masa da
ɗ
i. Wasu hawaye masu
ɗ
umi ne suka shiga kwaranya daga cikin idanunta. Cikin dauriya ta tashi zaune da ƙyar ta ja rigarta ta saka, hannunta dafe da ƙirjinta
saboda nauyin da ta ji ya yi mata, cikin haki ta ce. "Adnan! Don girman Allah dan darajar iyayenka ka taimake ni ka sauwaƙe mini aurenka, ba don ni ba." Sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya da karyar da zuciyar duk wani mai imani. Wani mugun kallo ya wur
ga mata cikin tsawa ya ce. "In kin ga kin bar gidan nan to gawarki a ka fitar." Kallon shi ta yi tana son ta yi magana amma ta kasa.
A tsawace ya ce. "Malama ki tasar mini daga kan gado da najasa a jikinki, ki kuma gyara mini shi kafin warin abin da kika f
itar ya hautsina mini ciki." Duk da yanayin da take ciki amma sai da ta yi wani murmushi da ya fi kuka ciwo sannan ta yunƙura ta sauka daga kan gadon. Kamar yadda ya umurce ta, ta kama zanin gadon da nufin cire shi amma sai ya bar hannun nata saboda rawar
da jikinta yake yi kamar ana ka
ɗ
a mata gangi. Dafe kanta ta yi da sauri saboda juyawar da ta ji yana mata, ƙofa ta nufa don ta fice zuwa
ɗ
akinta, kafin ta kai ga yin hakan ta fa
ɗ
i a ƙasa sumammiya. Adnan dake kallon ta ya ja tsaki cikin takaici ya ce. "Yar
inya sai ka ce mai farfa
ɗ
iya, abu ka
ɗ
an sai ki zube salon ki janyo wa mutane masifa." Kamar wata Dabba haka ya ja ta ya fitar da ita parlour ya juya ya koma
ɗ
akinsa ba tare da ya ƙara bi ta kanta ba.
Sai wajen ƙarfe
ɗ
aya na dare Adnan ya fita dan da ya
ha
ɗ
a coffee, a inda ya bar ta ya tarar da ita kwance tamkar gawa, tsaki ya ja ya ƙarasa ya bu
ɗ
e fridge ya
ɗ
auko ruwa mai sanyi ya shiga sheƙa mata daga tsaye, kusan 3 minutes sannan ya ji ta ja dogon numfashi tare da motsawa. Ta
ɓ
e baki ya yi ya tafi ya bar
ta. A hankali ta bu
ɗ
e idonta da suka yi mata nauyi ta bi bayansa da kallo, ta da
ɗ
e a haka sannan ta miƙe da ƙyar ko gani ba ta yi sosai ta shiga
ɗ
akinta ta fa
ɗ
a kan gado.
Rabi da rabi baccin Abbi ya kasance a yau saboda tunanin halin da Abra take ci
ki. Washegari da sassafe ya shirya direbansa ya kai shi airport ya bi Flight
ɗ
in ƙarfe takwas zuwa Kaduna.
Wata dattijuwar mata ce zaune a gaban gadon marasa lafiya da wani tsoho yake kwance, ta yi tagumi tana kallon yanda numfashisa yake fita da
wani irin sauti gami da
ɗ
agawar da ƙirjinsa yake yi, lokaci zuwa lokaci tana share hawayen dake fita daga cikin idonta. A hankali ta
ɗ
aga kanta tare da amsa sallamar da wani matashi yake yi a kusa da ita. Cikin damuwa ta ce. "Ba su zo ba ko Musa?"
Numfa
shi ya sauke cikin damuwa ya ce. "Ba su zo ba Inna, sai wa
ɗ
annan masu fararen kayan ne kawai."
"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, kalli yanda numfashin Malam yake fita fa musa, wallahi gabana sai fa
ɗ
uwa yake, ina tsoron kar mu rasa shi." Inna ta fa
ɗ
i ha
ka cikin kuka.
"Ki yi haƙuri Inna, insha Allahu Malam zai samu lafiya, cuta ai ba mutuwa ba ce.
"Ba za ka gane ba Musa, ka kira masu fararen kayan don Allah su zo ko za su iya yi masa wani taimakon."
Wata mata dake zaune a kusa da gadonsu tana ji
nyar nata mai gidan ta ce, "Sai haƙuri Baba, haka muke fama da likitocin nan, ba sa son zuwa da wuri, Nurses
ɗ
in nan kuma ba wani abu za su iya ba, sai dai kawai su ta ƙara wa mutum ruwa da
ɗ
an abun da ba za a rasa ba."
"To me ya sa su likitocin ba sa
zuwa da wuri? tun cikin dare Malam yake wannan abun, wa
ɗ
anda suka yi aikin kwana sun yi masa gwaje-gwaje sun ce mu jira sakamakon idan likitan da zai kar
ɓ
i aikin safe ya zo zai ba mu, muna ta jira har ƙarfe tara amma babu wanda ya zo."
"Hmm, asibitin gw
amnati kenan, sai haƙuri, ku yi ta addu'a kawai. Dan shi wannan likitan ma da zai duba shi sau
ɗ
aya yake zuwa a sati"
Girgiza kai Inna ta yi ta ce. "Allah Sarki takaka, shikenan bari mu jira."
Sai Asuba sannan Abra ta iya tashi ta shiga toilet ta yi
wanka tare da
ɗ
auro alwala ta fito ta yi sallolin dake kanta a zaune. Sosai ciwon da kanta yake mata ya tsananta, tamkar zai tarwatse haka take ji. Ga wani irin zafi da ra
ɗ
a
ɗ
i da zuciyarta ke mata. Tana idar da Sallar ta koma kan gado ta ƙudundu ne a ciki
n bargo saboda sanyin da ta ji yana ratsa ta, wani irin zazza
ɓ
i mai zafin gaske ne ya rufe ta wanda ya haifar mata da rawar
ɗ
ari. A haka Adnan ya shigo
ɗ
akin ya tarar da ita tana numfarfashi. Cikin nuna ko in kula da halin da ya gan ta a ciki ya watsa mata
singlets and boxes
ɗ
insa a jikinta tare da ba ta umarnin tashi ta wanke masa a lokacin.
Ɗ
aga kai ta yi da ƙyar ta dube shi amma ta kasa magana, hawaye ne kawai yake zuba daga cikin idonta. Ƙoƙarin jan bargon da ya yaye mata ta yi amma ya riƙe bargon ta
re da buga mata tsawa da fa
ɗ
in. "Tashin ne ba za ki yi ba ko me da kike ƙoƙarin jan bargo? Wato ga mahaukaci yana magana ba za ki tashi ki yi abin da na saka k....." Ƙarar doorbell ta hana shi ƙarasa fa
ɗ
ar zancensa. Ƙwafa ya yi tare da nuna ta da hannu ya
ce. "Na dawo na tarar ba ki tashi ba, wallahi na lahira sai ya fi ki jin da
ɗ
i." Ya ƙarashe maganar tare da yar
ɓ
ar mata da bargon a fuska. Lumshe idonta kawai ta yi tana jin yanda zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri. Adnan da matsalarsa ba su ne damuwarta
ba a yanzu, damuwarta kawai sanin gaskiyar abin da Adnan ya fa
ɗ
a mata na cewa ita TSINTACCIYA ce, Abbinta mafi soyuwa a gare ta ba shi ya haife ta ba, ba ta fatan hakan ya kasance, domin ta san zuciyarta ba za ta iya
ɗ
auka ba bugawa za ta yi. Addu'a take
Allah ya sa Abbinta ya musan mata ya ce ba haka ba ne, domin ta ƙudurce a ranta duk wanda zai fa
ɗ
a mata ba za ta ta
ɓ
a yarda ba, ko da Mami ne da Salman kuwa, Abbi kawai zai tabbatar mata da gaskiya ne ba shi ya haife ta ba ta yarda.
Adnan yana bu
ɗ
e ƙofa
kamar a mafarki ya ga Abbi tsaye cikin wani irin yanayi, sai da gabansa ya fa
ɗ
i amma bai nuna hakan ba, murmushi ya yi tare da yi masa iso zuwa cikin parlour'n cike da girmamawa.
Sai ƙarfe tara da rabi wani likita ya zo ya ƙara dudduba jikin malam,
bayan ya gama ya ce su Inna su same shi a office. Bayanin ciwon dake damun Malam
ɗ
in ya yi musu wato ciwon zuciya wanda already sun san da shi.
Ya ƙara da fa
ɗ
in, "Ciwon nasa ya yi tsanani sosai, don haka ana buƙatar yi masa aiki cikin gaggawa. Amma g
askiya wannan Asibitin ba mu da kayan aikin, sannan likitan da yake aikin bai ƙaraso ba"
A ru
ɗ
e Inna ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un! To likita ku yi masa aikin mana, don Allah ka taimake mu ka ceto mana rayuwarsa, idan muka rasa shi za mu shig
a cikin wani hali, shi ne bangon rayuwarmu."
Cikin son kwantar mata da hankali likitan ya ce. "Kar ki damu Hajiya, zai samu lafiya insha Allahu, sannan kuma a nan asibitin ba mu da kayan aiki masu kyan da za mu yi masa aiki, amma zan tura ku wani babba
n Private Hospital wanda da yardar Allah za a yi aikin successfully."
"Likita ina ne firaben honfital kuma?" Inna ta tambaye cikin damuwa.
"Asibitin ku
ɗ
i kenan, sunansa G.Y BULAMA, suna da ƙwararrun likitoci gami da kayan aiki masu inganci."
"As
ibitin ku
ɗ
i fa ka ce
ɗ
ana, ai ba mu da ku
ɗ
in da za mu biya, na gwamnatin ma da ƙyar muke iyawa."
"To Hajiya, in dai kuna son samun lafiyar shi gaskiya ku je can
ɗ
in."
Inna za ta kuma magana Musa ya hana ta da fa
ɗ
in. "Shikenan likita, mun gode sosai
." Sannan ya dubi Inna ya ce. "Mu je Inna."
Bayan sun fita Inna ta saka kuka ta ce. "Allah ka fitar da mu daga cikin wannan tashin hankalin, yanzu Musa ya za mu yi?"
Cikin damuwa Musa ya ce. "Inna mu je can inda ya ce manan kawai, don gaskiya likit
an nan ya fa
ɗ
a mana a asibitin nan ba yi masa aikin za su yi ba, kin manta yanda aka yi ne wancan karon, kullum cikin saka mana ranar aikin suke amma ba su yi ba har Allah ya ba shi lafiya muka koma gida."
Gya
ɗ
a kai Inna ta yi ta ce. "Haka ne, to amma
Musa ku
ɗ
in nake ji, ba mu san nawa za su ce mana ba."
"Allah ba zai hana mu yanda za mu yi ba, mu je ya yi mana kwatancen asibitin."
Jiki a sanyaye Inna ta ce. "Toh, addu'ata kullum kar Allah ya kar
ɓ
i ran malam ba tare da ya sanar da mu aihinin gaski
yar al'amarin nan ba, domin mu san ta inda za mu fara bincikawa, tunda komai daren da
ɗ
ewa sai gaskiya ta yi halinta."
"Insha Allahu Malam zai samu lafiya har ya warware komai da kansa kamar yadda yake da buri, ki kwantar da hankalinki Inna, mu dai mu y
i ta addu'a Allah ya ba shi lafiya kawai."
"To amin amin .Amma naji ance shi likitan da zamu je gurin nasa yana zuwa nan duba marasa lafiya, ba za mu jira shi ba?"
Musa ya ce "Inna ance yau babu lallai ya shigo, kawai gara mu bishi can
ɗ
in, bari in j
e sun ce zasu bamu wata takarda mu tafi da ita".
Inna ta ce "Shikenan, je ka dawo mu tafi". Musa ya juya ya fice, yayin da mara lafiyan ke ta cigaba da kakari.
Kamar yadda aka yi musu kwatance haka suka isa GY BULAMA HOSPITAL AND MATERNITY.
A ga
ggauce Musa ya shiga cikin Asibitin, ya fito da Wheel chair, suka
ɗ
ora Malam a kai, ya tura shi zuwa cikin Asibitin.
Gaba
ɗ
aya Musa a rikice yake, bai tsaya saurarar kowa ba ya fara bulayin in da zai kai Malam ya kwantar.
Wata Nurse ce tayi masa tsaw
a ta ce "Malam lafiya, ya zaka zo da mara lafiya kawai ka wuce mu?"
Musa ya ce "Yi haƙuri, wallahi duk a gigice nake ne, shiyasa daga Asibitin cikin gari aka turo mu nan, aka ce mu zo muga likita nan".
"To ai ba Chemist bane nan, ba haka kai tsaye ak
a ganin likitan ba, zaku fara bu
ɗ
e file dubu goma".
Musa yayi turus, ya ce "bakomai a bu
ɗ
e masa".
Inna cikin damuwa ta ce "Musa idan ka biya dubu goma, abun da zai yi saura a hannunmu ba shi da yawa".
"Bakomai Inna, Allah zai bada yadda za'a yi".
Ya cire ku
ɗ
i ya miƙa, ya biya aka bu
ɗ
e File
ɗ
in.
Nurse Jamila ce ta taho, hannunta riƙe da wasu files, ta kalli Musa ta ce "Bawan Allah, tura dattijon nan daga gefe mana, ka bar shi yana ta haki haka, tallafo kansa ka maida shi gefe".
Musa yaji da
ɗ
in yadda Nurse Jamila ta kula su da nuna wa mahaifinsu kulawa.
Ya ce "Wallahi hajiya a rikice muke ne, mun kai shi babban Asibitin birni, aka ce mana likitan da yake zuwa duba masu irin rashin lafiyarsa sau
ɗ
aya yake zuwa a sati, kuma yau ba zai zo ba,
shine suka turo mu nan da wannan takardar".
Nurse Jamila ta kar
ɓ
i referral later, sannan ta kalli su Musa, wani irin tausayinsu ya kamata, ta ce "Kaga, ga Emergency room can, ku shiga da shi ku kwantar, bari na je na kai wa likitan".
Musa kamar za
i durƙusa wa Jamila abinka da mutumin ƙauye "Mun gode hajiya, Allah ya saka da alkhairi".
"Ba komai ku je, ina zuwa".
GY BULAMA ne ya gifta ta can gefensu, yana cikin rigarsa fara ƙal ta aiki, sai zuba ƙamshi yake yi, yana takunsa cike da ƙasaita, ky
awunsa ya
ɓ
oye tsufansa ma'aikatan suna masa sannu da zuwa, yana
ɗ
aga musu hannu tare da yi musu sannu da aiki".
Musa bai lura da abin da Malam ya ƙurawa idanu ba, sai ji ya yi Inna tana cewa Alhamdilillah, Malam ya bu
ɗ
e ido.
Suna masa sannu haka s
uka kai shi Emergency suka kwantar.
A Office Jamila ta samu MD, ta yi masa bayanin Komai.
Ya kar
ɓ
i takardar ya duba, ya ajiye takardar ya ce "Kije ki gaya musu, yana buƙatar ayi masa aiki da gaggawa, kuma kin san da likitoci turawa muke aikin nan,
dan haka zasu biya 2.5millon, wani rami ne a zuciyar tasa.
Nurse Jamila jiki a sanyaye ta ce "Doctor, Ba su da wannan ƙarfin, dan da alama daga karkara suka zo".
"Well sai ku sallame su".
"Amma da mun je ka gan shi, ko wani taimakon gaggawa ne sai
ka rubuta a yi masa, ba ma sallame su haka ba, yana cikin mawuyacin hali".
"Mai kike so in yi musu? Kin san muddin ba aikin nan aka yi ba mutuwa zai yi, dan haka ku sallame su, kar ya mace mana a nan a zo ana yadda za ai a fita da gawar".
"Please do
ctor, ko yaya idan suka ga an basu kulawa ko mutuwa ya yi, ba za su ce an wulaƙanta su ba, ko oxygen a sa masa a bashi wani abin da zai samu releif".