Showing 120001 words to 123000 words out of 260401 words
baya ya shiga takawa cikin nutsuwa.
"Zaki tarwatsa min zuciya sweetheart?
Kullum kuka Ohhh yaaaa shiru da bakin ki a nan wajan"
Shiru ta yi masa sai ajjiyar zuciyar da ta ke saukewa wanda ya ke jinta sosai ta cikin wayar a kame ya ce.
"Ki daina kuka sbd Allah da kuma ni Abbinki bani da nutsuwa" a sanyaye ta ce "na daina Ab
bi ya aiki? Ka yi waya da Salman?"
"Kince ke
ɗ
aya ce ko?"
Ya tambaya tare da yin rejecting questions
ɗ
in ta."E,Abbi" jinjina kansa ya yi kafin ya ce.
"Ta shi kije Garden ki sha fresh air zaki ji sauƙin zuciyarki,amma idan kika sake kuka mun
ɓ
ata ba
ruwana da ke" da sauri Abra ta ce "ban sakewa Abbi"
"That's my girl Abra Khamal Khamis smile"
Murmushi ta sakar masa "Thank you Abbi" bai ce komai ba ya kashe wayar baki
ɗ
aya.
Wayar ta bi da kallo sai kuma ta miƙe tare da ajjiye ta a Parlour ta nufi
Garden.
Uncle Faisal ne tsaye a gaban Mami sai Masifa ya ke. "Ni nace ina son Yarinyar nan kuma auren ta zan amma sbd an raina min hankali aka bawa wani ita, na cire kunyata har wajan fake father
ɗ
in nata naje amma ya nuna bai amince ba"
"Saurara F
aisal ni kake son tunawa asiri? Matsayin ƙanin uwa kake wajan Abra sai kuma kace kana son ta? Kasan abinda hakan ke nufi? Yana nufin tona asirin shekaru kusan ashirin ke nan, wanda kuma daidai ya ke dana rasa igiyar aurena, bana son shirman banza kada ka s
ake yi min magana akan Abra,banda masifa me zakai da ita?" Mami ta ƙare zan can cikin
ɓ
acin rai da kuma damuwa.
A fusace shima Uncle Faisal ya ce.
"Igiyar auren ki bata gabana, kuma aure ne anyi mugani sai dai idan bana raye wallahi, Abra mallakina ce
tun tana ƙarama nake fama da son ta a zuciyata to ayi mu gani idan tusa zata hura wuta"
Yana fa
ɗ
in hakan ya fice da ga cikin gidan baki
ɗ
aya, Anuty Suwaiba ta ce.
"Kan uba me Faisal ke nufi? Me zai aikata Na'ima ba kiga ta zama ba, idan baki son ki da
wo gida mu jere matsayin zawarawa sai ki san
abinyi"
Dafe kai Mami ta yi cikin rashin sanin Abinyi ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
A hankali motar Fayyad ta shigo cikin Railway quarters
ɗ
in yana zaune
ɓ
angaren mai zaman banza sai Fayyad
da ke driving yana tsokanar Sp Adnan.
"Da safe munyi waya baka ce min zaka zo ba, sai yanzu naji kira da ga sama wai kana airport"
Idanunsa akan gate
ɗ
in gidan su Abra ya ce.
"To Ubana ne kai da zan fa
ɗ
a maka? Ko shi bai san zan zo kano ba"
Parking F
ayyad ya yi yana fa
ɗ
in.
"Fitar min a mota to mara mutunci" kafa
ɗ
a ya
ɗ
aga irin ko a jikinsa
ɗ
in nan. Fita ya yi a motar Fayyad na fa
ɗ
in "babu ko godiya?" Banza ya yi masa. Walking slowly ya nufi gate
ɗ
in, yana zuwa gatekeeper ya bu
ɗ
e masa
ƙ
ofar cikin girm
amawa, gaba
ɗ
aya sojojin da suke wajan suka gaishe sa dake duk sun san shi.
Wayarta ya fara kira amma bata
ɗ
auka ba, ga shi ba abin ya shiga gidan kai tsaye ba, kuma ba zai iya komawa bai ganta ba, tafiya ce da shi zuwa Egypt. A hankali ya kalli
ɗ
aya da
ga cikin sojojin kafin ya yi magana wani ya ce.
"She's in the garden"
Hanyar Garden
ɗ
in aka nuna masa, a hankali cikin nutsuwa da kamala ya nufi ciki, tun daga nesa ya hango ta ƙasan wata bishiya ta
ɗ
ora kanta akan wani ƙaramin dining dake wajan sai b
ottle water da ke kusa da ita, ta
ɓ
oye kanta a hannayenta. Kamar mai bacci a hakan, har ya Ƙarasa inda take ya ja Kujera ya zauna bata sani ba.
Hannunsa ya sa baki
ɗ
aya ya
ɗ
agota, ganin bacci ta ke a hakan ya sa ya
ɗ
an tsora mata shanyayyun idanunsa, yana
ƙara yaba kyan da Ubangiji ya yi mata. Kumatun ta ya shiga bubbugawa daidai kunnen ta ya ce.
"Open your eyes Wife ga mijinki ya amsa kira"
Turo baki tayi ta ce
"Faris i knw one day zaka dawo gareni please kada ka sake barina" ta fa
ɗ
a tana ƙanƙame jik
in Sp Adnan Aliyu Matawalle tare da
ɓ
oye fuskarta a ƙirjin sa a tunaninta Faris ne, domin bacci ta ke amma mafarkin sa ta ke.
Bakin ta Sp ya kama ya murza yana fa
ɗ
in "Ohh Wannan Faris anya ba zan tayaki biko ba?" jin yadda ake murza bakinta ga Ƙamshin P
ur oud da ke ratsa hancinta ya sanya tayi saurin bu
ɗ
e idanunta da ke cike da bacci.
Ha
ɗ
a idanu sukai ta ganta male-male a jikin mutum, jikinta na rawa ta fara ƙoƙarin sauka amma ya riƙeta sosai.
"Ba inda zaki, tunda a nan kike bacci gwamma kiyi a jikin
mijinki" ya fa
ɗ
a yana ƙara riƙe ta. turo baki tayi ta ce "ka cikani ba ruwana da kai" ganin abinda ya ke ƙoƙarin yi tayi saurin
ɗ
auke fuskarta ta shiga dokan ƙirjinsa tana sakin kuka..
"Ba ruwana Allah ba kace ba zaka zo ba?kayi tafiyarka ni ban son aur
en na fasa"
"Baki son auren ko baki sona" kuka kawai ta ke sakar masa hadda shassheƙa, shiru ya yi mata yana ƙara riƙeta a jikinsa.
Washe gari bayan taiwa Sp rigima sosai a makaranta da ke a Kano ya kwana da ƙyar ya rarrashe ta, ta ce Faris ya tafi s
hima zai ta fi ya barta a haka suka rabo da al'ƙawarin zai dawo Soon. Har yamma tana shcl karatu ya fara
ɗ
aukan zafi, da ƙyar ta ke yaƙi da zuciyarta wajan ganin tai karatu amma tunanin Faris da Unknown Kullum da su take kwana ta ke ta shi, wanne hali Fari
s ke ciki? Fushi ya ke da ita ko mene?. Waye Unknown mene ya sa kalamansa suke da tasiri a Zuciyarta yaushe zai bayyana gareta mene ya sa ya daina yi mata messages yanzu?.
Meenal ce tsaye a gaban makeken Bulama hospital, cikin nutsuwa ta shigo reception
ɗ
in tana bin mutunan wajan da kallo. Wata mata dake riƙe da yarinya mai Sikila ta kalla kafin ta ce.
"Ya kike zaune da ita tana soma? Ko ba soma bane?" Kafin tai magana da ga bayanta akace "ku kaita Emergency room yanzu, ai mata duk abinda ya dace ban sa
n mene ya sa kuke barin patient ba kulawa haka ba"
"Daddy"
Meenal ta fa
ɗ
a daidai kunan Bulama, hannunta ya kama yana nufar office
ɗ
insa da ita ya ce.
"My dear zuwan ba zata?" Fari tai da idanu ta ce.
"Wallahi Daddy kawai naji ina son zuwa hospital n
aka, amma banji da
ɗ
in yadda naga marasa lafiya haka ba"
"Shi yasa na so ki karanci Ɓangaren lafiya amma kika watsa min ƙasa a idanu, gaba
ɗ
aya basu da serious akan aikin su, banda muna da tsananin kulawa ban san zai dinga faruwa ba, wasu da ga cikin Lik
itocin kuma idan ba ku
ɗ
i basa duba mara lafiya"
"But this is not fair Daddy, yaya mutum zai idan bai da ku
ɗ
i gsky ana kulawa wanda ya taimaki wani sai Allah ya taimake sa" kallon Meenal Daddy ya yi kafin ya ce.
"That's why na ware
ɓ
angaren marasa ƙarfi
ana musu komai as voluntary"
Yana zaunar da itace a office
ɗ
in ya fito da sauri yana ha
ɗ
a kan Likitocin da nurse's
ɗ
in ya ce. "Duk wanda suke reception a duba so kyauta don't make any mistake" kamar yasan Meenal zata zaga asibiti ganin komai lafiya was
u sai godiya suke ta ƙara gasgata girman tausayin Mahaifinta.
A hankali lokacin ya fara juyawa, satittika suka fara zama kwanaki har Ubangiji ya kawo satin bikin Abra Khamal Khamis da Sp Adnan Aliyu Matawalle. Shiri ake da ga ko wanne
ɓ
angare, abinka
da masu ku
ɗ
i sai ka rasa wanne
ɓ
angare ne ya fi ji da bikin. Gefen Abra abin ba sauƙi ta rame sosai Kullum cikin kuka ta ke, gaba
ɗ
aya ta tashi hankalinta akan Salman, wanda ya sa Ammi ta
ɗ
auke ta zuwa can gidanta a can ake mata gyara jiki. Sp Adnan ango K
ullum yana tare da amaryarsa a waya yana yin iya bakin ƙoƙarinsa wajan ganin ya faranta mata, gefe guda kuma har lokacin Abbi bai dawo ba, Khairy sai shige da fice suke domin sun ha
ɗ
a plain na dinner a
ɓ
oye ita da Usman da su Fayyad.
The day.
Yau ya ka
ma ranar juma'a wanda ya yi dadai da ranar da za'a fara biki wato Kamu. Tun safe aka fara zuba decorations a harabar gidan Abbi sai ka
ɗ
auka babban hall aka kama sbd tsarin wajan. Har yamma babu amarya babu labarinta, Hankali ta she Mami ta kira Khairy ta
ce.
"Ummulkhairy ina Abra?"
Khairy da ke gidan kwalliya ta ce. "Mami ina gidan kwalliya Abra ma tana gidan da za'ai mata kwalliya"
"Ok call her immediately"
Katse kiran ta yi, khairy ta kira number Abra a kashe hakan ya sa ta kira number mai make u
p
ɗ
in tana
ɗ
auka ta ce.
"Hello don Allah Abra fa?" Mai make up
ɗ
in ta ce "Tun 3 aka gama mata kwalliya na ce ta jira ta ce zata da ganta yanzu wajan 5 ake nema na yamma tayi kusan 2hours da tafiya"
A fili Khairy ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji
'un kanan dai ta gudu kamar yadda ta ce.....
Littafin ku
ɗ
i ne,biya ₦300 via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank... Idan katin waya ne zaka Turo 500 shaidar biya 08081012143
[10/10, 4:17 PM] Abk: Jiki na rawa, Khairy ta kira Mami tana salati tana s
alallami, Mami ta
ɗ
aga wayar ta ce "Ya aka yi? Ta na ina ne, mutane sun fara taruwa fa?".
Khairy murya na rawa ta ce "Mami na kira mai kwalliyar ta ce mini tun uku, aka gama kwalliyar, kuma ta tafi".
Mami ta ce "Ta tafi taje ina?"
"Mami Wallahi ba
n sani ba, ba guri
ɗ
aya muka je kwalliyar da ita ba, ni gurin da naje daban".
Mami ta ajiye waya tana fa
ɗ
in "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yarinyar nan gidan ubanwa ta tafi ne? Ace an gama kwalliya tun uku amma har ha
ɗ
u da rabi ba ta iso gida ba,
ga mutane sun fara taruwa".
Anty suwaiba ta ce"Allah yasa ba guduwa ta yi ba".
Mami ta zare ido ta ce "Ta gudu ta je gidan uban wa? Lallai ma yarinyar nan".
Abu kamar wasa, ba Abra babu dalilinta, tun ana maganar ƙasa_ƙasa, har mutane suka fara ji
n halin da ake ciki.
Abokan aikin Adnan ne, suke ta shiri cikin shigarsu ta police, domin dai za'a yi parrate na ban girma ga Adnan da amarayarsa.
Usman ne ya kalli Adnan da ke ta ha
ɗ
e rai ya ce "Wai ha
ɗ
e ran me kake ne?".
Adnan ya ce "Am jealou
s ne, duk wannan garadan sai kun je kun kalle mini mata".
Aminu ya ce "Kai dalla ware, ai kaima gardin ne, sai kace a kanka aka fara Aure, ko da yake tsiyar mutum ya zama tuzuru kenan, duk sai ya fara behaving abnormal".
"Meye banbancina da kai? Har
gara ma ni yanzu zan shige daga ciki, kai kana waje".
"Nima ina hanya ne" Usman yayi Maganar yana murmushi.
Daga haka suka kammala shirinsu, suka fara haramar tafiya gidansu Abra.
Granny ce ta shiga sashin Na'ima tana fa
ɗ
in "Ke Na'ima, wai wac
e Maganar banza nake ji ne? Wai kamar Ana Abra ta
ɓ
ata, gidan ubanwa ki kai ta?"
"Haba granny, Ina kuwa zan Kai ta, daga zuwa kwalliya ba ta dawo ba".
"Ƙarya ki keyi, ana Magana kina wani ƙifta ido kamar ta Allah, ki fito da yarinyar nan duk in da ki
ka kaita, kan in samo madoki in shemeki a gurin nan".
Ammi ce ta ce "Granny ki yi haƙuri, ya za'ayi ta aikata haka ga 'yar ta, Yanzu dai muyi ta addu'a, kuma a kira shi angon a sanar masa dan a san abun yi".
Granny ta ce "Wai ke Yaushe zaki gane kan
makircin wannan yarinyar ne? Ai duk abun da akace tayi babu mamaki, yau duk abun da za'ayi sai an nemo mini jikata. Amm ke nace ina tabarau na ne? in ƙarewa wannan mara Kunyar kallo, in kalli idanunta sosai, dan ni idan na kalli idon mara gaskiya ina gane
shi".
Ammi ta ce "Glass
ɗ
inki yana in da ki ka yi salla, amma dan Allah ki dena wannan maganganun, bari a san abunyi, ko a tura wasu gurin mai kwalliyar".
Na'ima kuwa iya ƙuluwa ta ƙulu, ji take kamar ta rufe Granny da duka, shegiyar tsohuwa hayyata
ciya, sai tsawon rai kamar dabino, ta ƙi mutuwa kuma kullum cikin rikici take, tsawon shekarun da Na'ima tayi tare da Khamal Granny ba ta ƙaunarta sam.
Gida ya rikice ana neman Abra, ita kuma Granny ta rikice tana neman tabarau, ta
ɗ
ora da masifar cewa
bayan sace Abra da Na'ima tayi, ta kuma sace mata glashinta, saboda baƙin hali.
Anty Suwaiba ta ce "Wai ke Na'ima ba wani mataki da zaki
ɗ
auka a kan wannan sokuwar tsohuwar, shegen surutun tsiya kamar an jefeta a ka?".
"To ni ya zan yi da ita? Wannan
kaidinta ya fi yadda kike tunani, yanzun nan za ta ƙullawa mutum sharri.
Ɗ
akin Salman Granny ta nufa, tana cigaba da zage Na'ima, Ammi ta ce "Granny me zaki yi a nan kuma?".
"Tabarau na nake nema".
"To mai ze kai glass
ɗ
inki nan kuma? Na ga tunda
muka zo baki je nan ba".
"A'a, ance idan raƙuminka ya
ɓ
ata ka neme shi har kura tandu, yo na sani ko wannan algungumar ta yi garkuwa shi ta kai ta
ɓ
oye" ta ƙarasa Maganar, tana nufar
ɗ
akin Salman.
Sai dai tana shiga
ɗ
akin, ta ƙwala uban ihun da ya j
anyo hankalin 'yan biki.
"Gata nan ku zo gata!" Ta yi maganar cikin ihu.
Su Ammi na zuwa, suka tarar da Abra a zaune, fuskarta sharkaf hawaye.
Ashe tun bai fi uku da rabi ta dawo gida ba, ta shiga ta ƙofar baya, tabi ta kitchen ta shige
ɗ
akin Salm
an abunta, kuma ta kashe wayoyinta.
Ammi ta ce "Abra, dama kina nan ki ka
ɗ
agawa mutane hankali? Kuma kalli duk kin fara
ɓ
ata kwalliyar".
Cikin kuka Abra ta ce "Ammi Faris
ɗ
ina, zan yi Aure baya nan, dan Allah Ammi kice musu na fasa Auren nan a dawo
mini da Faris
ɗ
ina".
N'a'ima a fusace ta ce "wannan wane irin sakarci ne haka Abra? Mun tara mutane kina neman ki bamu Kunya? Kawai kin
ɗ
agawa mutane hankali".
"Mami ni bana son Auren nan na fasa, dan girman Allah Ku dawo mini da
ɗ
an uwana" tayi maga
nar tana ƙoƙarin cire
ɗ
aurin kanta, ga numfashinta da ya fara sama.
Ammi ta girgiza wa Na'ima kai, alamar ta dena yiwa Abra fa
ɗ
a.
Granny ta ce "Ji min 'ya da wauta, ke yanzu sai ki fasa Auren, aikuwa da kin yiwa kanki kutunguilar tsiya, hmm jiya ba y
au ba tsohuwa ta tuna kwanan turaka, yarinya karki cuci kanki" Granny ta yi maganar tana watsa guntun goronta a baki, ta bar
ɗ
akin, murmushi Ammi ta yi, Granny ba ruwanta haka take sakin 'yan maganganunta idan ta raya mata".
Ammi ta maida hankalinta kan
Abra, ta din ga yi mata Nasiha tana rarrashinta, ƙarshe sai da aka kira Abbi video call, shima yayi ta rarrashinta, Sannan ta haƙura.
Aka samo wata mai kwalliyar ta gyara mata kwalliyar da ta fara
ɓ
atawa da hawaye.
Na'ima ma ha
ɗ
awa tayi cikin wani rants
atsten leshi fari da golden, tun daga wuyanta zuwa yatsunta gwal ne.
Hakan yayi daidai da ƙarasowar Adnan da da abokansa, haka zalika mota mota na 'yan uwan Adnan
ɗ
in suka hallara a ƙatuwar harabar gidan Major Khamal Khamis, wadda akai matuƙar ƙawatawa.
Mami ce da kanta ta kamo hannun Abra ta fito da ita daga cikin gida, duk da kanta a sunkuye yake, ta rufe jikinta da mayafi, amma hakan be hana Adnan tsinkayen farar fatarta da ta sha gyara ba.
Nan masu police band suka sauke gangunan su, suka fara bu
gawa domin gabatar da parrate na ban girma ga Ango sha gu
ɗ
a Sp Adnan Aliyu Matawalle, da matarsa gimbiya Abra Khamal Khamis, abun na masu
ɗ
amara ne, dan haka parrate
ɗ
in ya ƙayatar matuƙa, tare da crossing sword da aka gabatar duk dan murna ga amarya da an
go.
A ka zo
ɓ
angaren kamu, a kama amarya ta bu
ɗ
e fuskarta, ƙanwar Hajiyar Adnan, ta ce sun biya dubu
ɗ
ari biyar a bu
ɗ
e musu fuskar Amarya.
Nan wasu suka shiga tafi, yayin da Mami ta ce "ita dubu
ɗ
ari biyar yayi ka
ɗ
an". Ammi ce tsawatar dan kar ayi halin
ƙ
aranta.